HARSASHEN SO CHAPTER 6
HARSASHEN SO
CHAPTER6
A hanya shalele tunanin Mubarak kawai yakeyi a karkashin zuciyarsa, amma bakin cikin daya da ya masa abinda baiji dadi ba ya dauresa a motar yaja sa kasa kuma tafiya mai nisan gaske dan rashin sanin darajar dan adam, Tunani shalele yakeyi sosai a daren shekaranjiya da kuma safiyar jiya sai kuma yau, yana So ya gano Mubarak ne ya gani lokacin da ake hadari?
Ko kuwa shima wancan wani ne daban? Girgiza kansa yayi cikin yanayin gardama, yaga wani a cikin duhu yaga kuma wani a cikin haske a safiyar jiya daya daure sa ajikin motar kuma so biyu yanajin wani kibiya yana sokar masa zuciya amma kuma yau baiji irin abun ba, Yana wannan nazarin ne yaji an taka burki da sauri ya dawo daga duniyartunani, sauka haka wani soja ya fada, a hankali shalele ya dago kansa ya kalli mutumin sannan yace ba nan zan sauka ba akwai sauran taflya,
Tou ai ba motar haya bace da zaka rika raina mana hankali sojan ya fadi maganar tare da kaiwa shalele wani irin mari yana mai cigaba da cewa dan iska yaro dan uwarka dama jiya inajin haushinka ka sokarmin ido da akaifar ka! Murmushi shalele yayi sannan yakai hannunsa saman kunci sa ya shafa daidai inda sojan nan ya mareshi, lumshe ido shalele yayi cikin sigar bacin rai sannan yace tunda nake a duniya babu dakikin daya taba dukana sai kai! Kaine na farko kaima ka rikeni A daren shekaranjiya, yau kuma ka mareni jinjina kansa yayi, sannan yasa dan yatsan sa daidai saitin da kwakwalwarsa take zaune a cikin kokon kansa ya taba alamar nazari! ‘ Zuwa wani lokaci shalele ya bude idonsa tare da kallon sojan, cikin bacin rai yakai masa wani irin halbi harsai da murfln motar ya bude ya fadi kasa, da sauri shalele ya flta ya hau saman motarya mike tsaye tare da dirowa kasa saman guyawunsa ya sauka saman ruwan cikin sojan nan, Kuma masa kai shalele yayi tayi harsai da tunanin sa ya tsaya, ajikinsa ya fara laluben wuka amma babu da so yayi ya gundule masa hannu, bai samu wuka ba dan haka ya dauko wani katon dutsi ya yayi ta kwamtsa masa a hannu harsai daya tabbatar hannun ya karye sannan ya tofa masa miyau tare da cewa karamin dan iska gobe ma ka kara shiga harkata,
Shalele yana fadi haka ya mike da niyar tafiya, cikin zafin nama sojan nan ya riko kafar shalele da dayan hannunsa, halbi shalele ya sake kai masa da dayar kafarsa, wannan dalili yasa soja fiddo bindiga ya fara sakin ‘HARSASAI’ babuji babu gani, gudu shalele ya farayi dan tsira da rayuwarsa, Saida shalele ya bace sannan ya tashi a wahalce ya koma motar kuma ya daukar ma ransa alkawari duk inda ya sake ganin shalele wallahi saiya kashe sa, haka yaja motar da hannu daga yake tuki,
Shalele kuwa saida ya fara hango gidansu sannan ya daina gudu dan yasan idan yaje yana gudu saiya hadu da azabarda taf’l wanda ya baro a baya! Cike da fargaba ya tun kari gidansu yana mai tunanin yanda zai kare da mai gida, Kai tsaye ya shlga Clkln gldan zuciyarsa tana man halbawa, sauri ya Kara a cikin tafiyarsa dan zuwa dakinsa, amma sai yaji maganar mai gida yana cewa da kyau da kyau,
Tsayawa shalele yayi sannan ya juyo yana kallon mahaifinsa, kusa da shalele mai gida ya tsaya sannan ya daga hannunsa yakai wa shalele mari harsai da ya fadi kasa, wani kebil dake hannunsa yaci gaba da dukan shalele dashi tambaya biyu yake faman maimaita masa amma shalele ya kasa ansa ko daya, ‘ Tambaya ta daya itace? Gidan wai nace ka kona ne? Ta biyu kuma wane dan iska ne wanda ya daureka a jikin motar yaja ka a kasa kamar kare baka babbaka motar ba? Waye shi ……… Mai gida ya tambaya cike da bala”i tare da ci gaba da taka ruwan cikin shalele harsai da shalele yayi amai saboda wahala, mai gida yace a lokacin da wannan bakin labarin ya riski dodon kunnuwa na saida na zira dukan yatsuna a cikin kunne na dan zaro dodon kunnuwa na saboda jin bakin labari banga amfaninji a gareni ba tunda bazaka sa kunnena yaji daddadan zance ba, Duka mai gida yake masa na fitar hankali duk yaransa suna tsaye suna kallo amma babu mai damar ansar shalele, bazakayi min magana ba dan ubanka saina kashe ka? shalele ya kasa cewa komai dan haka mai gida ya juya cikin hargowa yace Balaga maza kawo min bindiga saina kashe dan iska yaron nan haihuwarsa bata da wani amfani,
Ni babban jarumi ne, bazai taba yuwuwa ba na haifl wanda babu jarumta a cikin jininsa ba kuma na zauna dashi,jarumta a cikin jinina take duk dan dana haifa da cikina idan ya zama ba jarumi ba kashe banza nakeyi na ba karnuka na su cinye gawar banza dan sunfi shi amfani,
Da gudu Balaga ya shiga wurin mama ya fada mata halin da ake ciki dan idan mai gida yace sai yayi tou wallahi sai yayi babu fashi, shi yasa yake shan wahalar rayuwa, bayan Balaga ya gama fadawa mama sannan ya koma dakin mai gida ya dauko bindiga amma saida ya cire duk wasu harsasai dake cikin bindigar sannan ya kawoma mai gida, Mama tana daga saman bene tana kallon danta cikin bakin ciki tattare da nadamar duk abinda ta aikata a baya, hakika ta cutawa Basir saboda so data nunawa Mansur ta danne gaskiya dan saka farin ciki a cikin zuciyar Mansur, tajuyawa danta baya wanda bata san halin da yake ciki ba a yanzun, goge hawayen idonta tayi dan tuno wani abu daya faru shekaru da dama dasu ka gabata, Tunaninta ya dawo ne a daidai lokacin da aka bawa Mansur bindiga ya saita shalele tare da danna kunamar bindigar, da sauri shalele ya rufe idonsa dan ansa kiran mahaliccin sa, amma babu abin harbi, Ba tare da tunanin komai ba mai gida yaci gaba da dukan shalele dakan bindiga harsaida ya suma sannan ya barshi, haka mai gida ya juya yabar shalele a cikin wahala ba tare da tausayawa ba!
Bayan shekaru shidda abubuwa da dama sun faru sosai kullum abu kara tabarbarewa yakeyi, shalele kuwa yana ansa munanan hukunci a wurin mai gida matsawar bai masa yanda yake so ba!
Shalele girma yazo sosai amma daga yanayin magana zaka gane mace ce zahiri da zahiri yanayin magana cikin sanyi kamar zaiyi kuka haka yakeyin maganar sa, amma babban abunda ya damu shalele shine yawan tunanin Mubarak mafarkinsa san ganin sa da kuma san yaji maganar sa,
Da idan bazai manta ba tun wannan haduwar da sukayi a palon gidansa basu sake haduwa ba sai a mafarki, bai sakejin maganar sa ba tun wanda yayi masa ta karshe cewa, _Idan ka sake zan cire maka kaya a cikin mutane, ka yadda?_ _Wuce ka tafi Wannan itace magana ta karshe tsakaninsa da Mubarak, wannan magana ta tsaya masa a rai, sai kuma kalmar daya kirasa da ita ta, _Jarumi ko mahaukaci ka tabajin jarumu da muryar “yan daudu?_
Murmushi shalele yayi tare da kwanciya saman gado a hankali, a bayyane yace ‘INA SAN KA’ duk da shalele baisan miye kalmarso ba dan tunda ya tashi a gidansu bai tabajin an ambaci so be sai dai maganar ‘KIYAYYA’ , ‘KIYAYYA’ dai maganar ita kenan guda daya!
Murmushi shalele yayi mai burgewa har gefen bakinsa saida ya lotsa dan yana da cikar kyau mai burgewa da daukar hankali baka gajiya da kallonsa, saida yadan lumshe ido sannan yace nemanka ya zamarwa shalele dole ina san na kara ganinka ko so dayane, Tsayawa tunaninsa yayi dan haka ya tashi zaune, dogon nazari yayi sannan ya mike ya fita daga dakin, dakin mama yaje da sallama ya shiga sannan ya samu wuri a gefen gado ya kwanta, Juyawa mama tayi ta kalli shalele sannan tace barka da fitowa karamin mai gida, murmushi shalele yayi sannan yace barka dai, shiru sukayi na wani lokaci sannan shalele yayi gyaran murya yace mama, na”am mama tace, cikin burkucewar haruffa shalele yace, da Allah tambayarki zanyi, Juyowa tayi ta kalli shalele sosai sannan tace inajinka, tashi yayi zaune sannan yace wai mi yakesa kaji kana yawan tunani, murmushi mama tayi dan bata gane inda maganartasa ta nufa ba, sannan tace tunanin me kakeyi ne?
Wani ne, mama tace fada kukayi ne? Eh amma dai kuma dai miyasa nake yawan tunaninsa wani lokaci har mafarkinsa nakeyi, mama bata kawo komai a ranta ba dan haka tace so kake kayi masa duka ne,
Shalele yace ban tabajin sha”awar zan dake sa ba ko cutuwa ba kuma ban tabajin irin abinda nakeji ba a yanzu sai haduwa ta dashi, inayin mafarkinsa a duk lokacin dana rufe idona, ina tunaninsa sosai so adadin buguwar zuciyata, ban tabayin wani abu ba wanda bana tunaninsa a rayuwata ba, kuma ina san ganinsa haka ina san sakejin maganarsa koda so dayane a rayuwata, Ajiyar zuciya shalele yayi sannan yace nidai kawai ya burgeni, ido mama ta zaro sosai tare da cewa baka da hankali ka taba ganin namiji ya burge namiji? K0 kana so a dauke dan iska ne? Oho inma dai dan iskan ne naji babu komai amma nikam dai ya burgeni ne sos ……. shigowar mai gida yasa shalele hadiye maganar da yake san ida furtawa faduwar gaba yakeji sosai tambayar kansa yake shin mai gida yaji k0 kuwa baiji sa ba?
Hmm