HEEDAYA CHAPTER 36 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 36 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mami na xaune tare da Heedayah kan kujerun dake jere a dogon corridor din 4 wards dake wani bangare na hospital 

din, sai Abba da Alhaji Ahmad dake tsaye wajen su ma tare da Zayyad da Junaid, kusan awansu daya kenan a 

asibitin, Babban asibiti ne sosai me kuma tsada don a ward din da ake admitting authoritative patient ma aka 

kwantar da Khaleel, ba kowa ake admitting a wnn bangaren na Babban hospital din ba sai wanda ya isa, but being 

that Honorable Ahmad ne ya taho da Khaleel hospital din, nan aka kwantar da shi, Likitoci biyu ne suka fito babban 

ward din da ko kadan bai wani yi kama da dakin asibiti ba, dayan yyi wucewarsa, sai daya da ya tsaya yana kallon 

su Abba snn ya kalli Mami da gaba daya ta kasa samun natsuwa, smiling to give her assurance yace “His mother?” 

Mami ta d’an yi shiru sai kuma ta girgixa kanta tace “No” Zayyad ya karaso gun likitan gently yace “Ni abokinsa 

ne…” Likitan ya kalli Zayyad yace “Ohk, kai abokinsa ne, to iyayensa fa??” Alhaji Ahmad ya karaso gun likitan yace 

“If there is anything ka sanar min, we brought him to the hospital…” Likitan yace “Ohk sir, mu tafi office” Bin 

bayansa Alhaji Ahmad yyi xuwa office dinsa, Zayyad ya bude kofar ward din, politely wani likitan dake ciki yyi 

masa alamar da he should stay behind plss, rufe kofar yyi ya tafi ya xauna, gaba daya tausayin abokin nasa yake 

sosai don yasan wahalan da yake duk sanda ya samu attack, shi yasa tun safe yake ta kokarin ganin bai wahalar da 

kansa ba considering his condition but all in vain. Alhaji Ahmad na kallon Likitan yace “MI? Is that a disease?” 

Likitan yace “Yes, Myocardial infarction… Damage or expiry of any area of the heart muscle…. And this is as a 

result of lack of flow of blood to the area” Alhaji Ahmad yyi shiru, can yace “Was he born with that?” Likitan yace 

“I don’t know, I can’t tell, amma in sha Allah he will be fine, he just had an attack, amma kasan iyayensa? I mean are 

frnds with the parent?” Alhaji Ahmad yace “Not at all…” Likitan yace “Ohk then, but sbda condition dinsa yana da 

kyau ya dinga nesa da duk wani abu da xae daga masa hankali ko makamancin haka, I mean slightest of it, ya daina 

damun kansa a kan komai, kaga nasa kalan Heart attack din is very dangerous, a likitance ana kiran da wnn Heart 

attack din STEMI… Kuma alamu sun nuna ya dde da ciwon, he just need to learn how to live properly with it, in 

some cases ana surgery but I can’t say tukunna, mun dai daura sa under medication ynxu, kuma in sha Allah xae 

samu sauki, in sha Allah” Alhaji Ahmad yace “Toh Allah ya basa lafiya, ya yaye masa” Likitan yace “Ameen 

honorable, that’s just it, Allah ya kara mana lafiya baki daya” Alhaji Ahmad ya amsa da Ameen snn ya mike suka yi 

sallama da likitan ya fita. Alhaji Ahmad yyi ma Abba bayanin da likitan yyi masa, Mami dai na xaune daga inda take 

tana sauraronsu, sosai taji tausayin Khaleel jikinta yyi sanyi, Abba yace “To Allah ubangiji ya basa lafiya, Allah ya 

tashi kafadunsa” Alhaji Ahmad ya amsa da “Ameen” Alhaji Ahmad na kallon Mami yace “Hajiya I think ya kamata 

mu tafi yanxu it’s getting late” Abba yace “Sure, abokinsa with Junaid can stay with him….” Junaid ya kalli Abba bai 

dai ce komai ba, Heedayah na kallon Mami a hankali tace “Mami pls can I go in and see him before we leave?” 

Mami tace “No Dr yace kar a shiga, gobe da safe xaki duba sa” Likitan da ke cikin ward din ne ya fito, Heedayah ta 

bi sa da kallo, Mami ta mike ta nufi Junaid, ganin haka Heedayah ta mike da sauri ta bi bayan likitan, a hankali 

Mami na kallon Junaid tace “I know baka son xaman hospital but kayi hakuri just for today” Ya gyada mata kai 

kawai, Heedayah na shiga office din likitan bayan ya shiga ya juya yana kallonta, a hankali tace “Good evening sir” 

yace “Evening dear how are you?” Ta marairaice tace “Pls I’m begging you can I go in to check on him?” Likitan yyi 

murmushi yace “He is asleep young lady, Gobe idan kin xo da safe xa ki gansa” Kamar xata yi kuka tace “Ae ba 

tashinsa xan yi ba kawai ganinsa xan yi” ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Ohk, but don’t go hear him ki tsaya daga 

middle of the room check on him and leave, promise?” Ta gyada masa kai da sauri tace “I promise” yace “Good, you 

can go in” Tana murmushi tace “Thank you sir” daga haka ta fita da sauri, Mami har ta fara nemanta a asibitin don 

su Abba da Alhaji Ahmad sun fita haraban hospital din, Junaid na xaune corridor din tare da Zayyad Heedayah ta 

dawo, bude kofar ward din xata yi Zayyad yace “Noo, it’s not allowed” ta kallesa tace “I asked for permission” daga 

haka ta shige ciki, Junaid ya bi ta da ido har ta kulle kofar, kwance ta gansa saman gadon dake babban dakin wanda 

kamar ba a Nigeria ba tsabar haduwar ward din, ta tsaya dai dai inda likitan yace ta tsaya tana kallonsa yana bacci 

breathing dinsa very slowly, bata san lkcn da tayi breaking din promise din da tayi ma likitan ba ta karasa kusa da 

gadon da sauri, lkci daya ta ji hawaye ya kawo idonta, ta durkusa kusa da shi a hankali ta kamo hannunsa tace “Are 

you alright?” Bayan few seconds ya bude idanuwansa a hankali sai kuma ya sake kullewa, cikin sanyin murya tace 

“Are you feeling better now?” Ba tare da ya bude idonsa ba, murya can kasa yace “Sure” tace “Magani suka baka?” 

Ya girgixa mata kai, tayi shiru tana kallonsa don har sannan ya ki bude idon, murya can kasa yace “InjectionsHawayen dake makale idonta ya sauko tace “Allah ya baka lafiya” Ya gyada mata kai, ta kafesa da ido tana ta 

kallonsa, a hankali ya bude idonsa jin shirun yyi yawa, suna hada ido ya mayar ya rufe idon nasa, har sannan tana 

rike da hannunsa da yyi xafi tace “Ina yake maka ciwo” ya daga daya hannunsa da kyar ya nuna mata kirjinsa, ya 

mayar da hannun bayansa, sannan ya dafe forehead dinsa, wasu hawayen suka sake xubo mata cikin sanyin murya 

tace “In sha Allah xa su daina ka ji, you will be fine in sha Allah” ya gyada mata kai, ta xame hannunta daga nasa 

tace “We are going home now, get well before tomorrow plsss” Sae a snn ya sake bude jajayen idonsa murya can 

kasa yace “Thanks Heedayah!!” ta gyada masa kai sannan ta mike ta juya ta nufi kofa ta fita ta kulle, Mami na tsaye 

bakin ward din, da sauri ta sunkuyar da kanta, Mami tace “To mu tafi gida tunda ke baki jin magana” Mami ta yi 

wucewarta daga wajen bayan Zayyad yyi mata sae da safe, Heedayah ta daga ma Junaid da ya bi ta da ido hannu ta 

bi bayan Mami da sauri. A Motar Alhaji Ahmad Mami da Heedayah suka dawo gida tare da excort dinsa dake biye 

da su a baya, bbu ynda Alhaji Ahmad bai yi da Abba su taho nan gidan nasa tare ba Abba yyi declining yace xai tafi 

hotel din da yyi lodge, haka Alhaji Ahmad ya hakura ya kyalesa kawai, ganin Alhaji Ahmad xae shiga ciki da 

motarsa bayan masu gadi sun bude gate Mami tace “Xan sauka ba sai ka shiga ciki ba Alhaji” Alhaji Ahmad yace 

“No Barrister, you can spend the night here” Mami tayi murmushi tace “Thanks sir, xan shiga gidan Daughter na, 

will spend the night there in sha Allah” ita ma bbu ynda bai yi da ita ba ta kafe a kan gidan Dinar xata shiga hakan 

yasa ya hakura, ta bude motar ta sauka tana kallon Heedayah dake ta kallonta, Heedayah ta sauke idonta sai kuma ta 

bi ta xaya sakko Mami tace “Noo dear, go in with ur Abba” Alhaji Ahmad yace “Aa…. go with ur daughter barrister” 

Mami tace “Yau dai ta kwana tare da Ummanta, it’s been long” Bata jira Abban Heedayah ya ce komai ba ta rufe 

motar ta daga ma Heedayah hannu tayi hanyar gate dinsu Dinar, Alhaji Ahmad ya shiga da motar cikin gidan, yyi 

parking a parking space, bude motar Heedayah tayi ta sauka, shi ma ya sauka yana kallonta, ta sunkuyar da kanta, 

duk sai ta ji kewar Mami sosai, Alhaji Ahmad ya nuna mata bangaren Mahaifiyarta yace “Mu je” Gaba ta shiga ta 

nufi inda ya nuna mata yana biye da ita a baya, Bbu kowa a babban parlon, Heedayah ta nemi gefen kujera ta xauna 

amma da ganinta kasan a takure take, Abbanta na kallonta yace “Mu je wajen Ammin ki” mikewa tayi ta bi bayansa 

xuwa corridor din dakuna biyar, ya bude kofar bedroom din Ammi ya ga bata ciki, wani kofar ya bude ya ganta 

xaune saman darduma a dakin dake dauke da gadaje guda biyu na yara, komai na dakin na kids ne, Abban Heedayah 

ya juya ya kalli Heedayah da ta rakube gefe daya yace “Come in” shiga dakin tayi tana kallon girls din dake kwance 

kan each bed, wa enda kila su yi shekara uku, Ammi sai kallon Heedayah take, a hankali Heedayah ta duka kusa da 

ita tace “Ammi mun dawo” Ammi ta sakar mata murmushin karfin hali amma ta kasa cewa komai, fita Abba yyi 

daga dakin, a boye Ammi ta goge hawayen dake kokarin gangaro mata tace “Have you eaten?” Heedayah ta gyada 

mata kai, Uwar tayi shiru, can tace “To tashi mu je ki kwanta” Mikewa Heedayah tayi, Ammi ma ta tashi, ta karasa 

twins dinta ta rufe ko wannensu da blanket ta xauna gefen daya gadon ta tofa masu addu’a snn ta mike tana kallon 

Heedayah tace “Mu je” kofa Heedayah ta nufa Ammi na biye da ita, Ammi ta kulle kofar dakin bayan sun fita, ta tafi 

ta bude wani kofar tana kallon Heedayah, karasowa Heedayah tayi Ammi tace “Sai da safe” Heedayah ta shiga dakin 

Ammi ta kulle kofar, ta wuce nata dakin tana goge hawayen da ya ki tsaya mata. Har kusan karfe biyun dare Ammi 

ta kasa bacci banda sllh bbu abinda take tana kara gode ma Ubangijin ta, she just can’t believe her daughter is back 

after 5 years, bata son tuna baya, bata son tuna shekaru biyar din nan da suka wuce da halin da ta shiga, she just 

want that memory to erase off her heart, ta share idonta daga karshe ta mike ta bude kofar dakinta a hankali ta fita, 

dakin Heedayah ta nufa ta bude kofar in a way it won’t make any sound, haske wutan corridor dake a kunne yyi 

reflecting dakin, Heedayah dake kwance idonta biyu ta kasa bacci gaba daya ta ji bbu abinda ke damunta irin rashin 

lafiyar Khaleel tun da ta kwanta bayan tayi wanka take juye juye, mikewa xaune tayi da sauri jin an bude kofa, 

Ammi ta shigo dakin ganinta a xaune ta kunna wutan tace “Baki yi bacci ba?” Heedayah ta shiga mitsika idonta 

kamar me bacci tace “Na farka ne yanxu” Ammi ta isa kusa da gadon ta xauna tana kallonta, Heedayah ta sunkuyar 

da kanta, a hankali tace “Nayi missing din ki Ammi, I’ve missed you so much” Ammi ta jawota jikinta tana 

murmushi tace “I missed you more daughter” shiru duk suka yi, can cikin sanyin murya Ammi tace “Do you 

remember when you let Yakumbo’s house that very day?” Heedayah ta d’an yi shiru sai kuma tace “Yes, wasu 

mutane ne suka tafi da mu a motarsu da su Ladi, ban san inda suka kai mu ba, we walked a long mile, suka kai mu 

wani waje, I can’t see, I only can hear, so I don’t how the place looks like, har muka yi bacci muka tashi a wajen, it 

seems suna kashe mutane coz then ina jin karan gun shot, sai wani ya daukeni a bicycle muka yi ta tafiya ya kai ni 

wani waje ya ajiyeni ni kadai ya tafi ya bar ni…. He just left me and go not considering that I am blind…” Hawaye ya 

cika idon Heedayah tana kallon Amminta dake saurarenta, Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace 

“Taimakon ki yyi ya fitar dake kilan kar a kashe ki a wajen” Heedayah tace “But he just abandoned me by the road

side” Ammi tace “He is an angel for that, da sun kashe ki yanxu my daughter” Heedayah tayu shiru, sai kuma tabe 

baki tace “Ni ban san me ya faru ba, seems I was knocked down by a vehicle, and daga nan sai Abba ya kai ni 

gidansa, and I began staying with them…. he has a son Ya Shureen” Heedayah ta d’an hade rai tace “Ni bana sonsa, 

baya dariya, baya min wasa, his mother is so mean, bata sona, his sisters are mingy also, they don’t like me even for 

a second” Ammi dai sai kallonta take ko kiftawa bbu, Murmushi Heedayah tayi a hankali tace “Abba ne kawai yakeso na, he was always there for me, he paid for my eye surgery, and Mami…. she is also my mother, I love her, I love 

them” Shiru Heedayah tayi tana kallon Mahaifiyarta, Ammi ta shafa kanta a hankali tace “Sure dear, she is ur mother, 

always take her as one, and take me as ur aunt” Heedayah ta kalli uwarta tayi murmushi bata ce komai ba, a hankali 

tace “But you remain my mother” Rungumeta Ammi tayi tana murmushin ita ma, Heedayah tace “Ya Junaid, Ya 

Sudais, they were always there for me….” Wara ido tayi tace “Kaka…..” Ammi ta janyeta jikinta tana kallonta. Har 

aka yi kiran sllhn asuba Ammi na tare da Heedayah hira sai wanda ta manta ne bata yi ma Amminta ba barin hiran 

kaka, wani Ammi tayi dariya, wani tayi murmushi, wani tayi shiru, wani kuma taji hawaye ya kawo mata, she is just 

imagining, ashe dama akwai wa enda xa su rike yaron da basu san daga inda ya fito ba da amana ynda mutanen nan 

suka rike mata ‘yar ta, bata san da me xa su biya Abba ba, bata san da me xa su biya Mami ba, but ta fi jin Abba don 

da bai dau Heedayah ya tafi da ita ba da bata san wani labarin xa a dinga yi ynxu ba, they owe him greatly…. Bude 

kofar dakin da Abban Heedayah yyi wajen karfe biyar na asuba yasa Heedayah tayi shiru daga labarinta, murmushi 

yyi yana daga tsaye bakin kofa yana kallonsu, can kawai ya juya ya fita xuwa masallaci, Sai a snn Ammi ta tafi nata 

dakin don yin alwala, Heedayah ta shiga bathroom din dakin da take. Bayan Heedayah tayi sllh ta shiga bandaki tayi 

wanka, ta fito daure da towel, sai ga Ammi tare da Mum Islam sun shigo dakin, Gaisheta Heedayah tayi, da fara’a 

mum Islam ta amsa tace “Jiya kafin ku dawo nayi bacci wllh, kayan ki na gidan Dinar in amso maki ko? Naga har 

kin yi wanka” Heedayah ta gyada mata kai, Mum Islam tace “To bari in tafi in karbo maki yanxu” daga haka ta fita 

dakin, Ammi na kallon Heedayah tace “What are you taking for breakfast?” Heedayah ta xauna gefen gado tana 

kallon Amminta a hankali tace “Ammi baxa mu tafi can asibitin ba?” Ammi tace “Da asuba xa a je asibitin? ai xa ki 

bari gari ya waye ko?” Heedayah tayi shiru, sai kuma tace “Toh” Ammi ta tafi ta dauko mata body lotion kafin Mum 

Islam ta dawo. Karfe bakwai da rabi Farida da Dinar suka shigo parlon Ammi… Matan step brothers din Abban 

Heedayah da Kanwar Ammi da few family frnds ne xaune parlon, ko wannensu ya xo gidan nuna farin cikin 

bayyanar Heedayah bayan shekaru biyar, Ammi suka gaisa da Dinar da Farida da fara’a don ta ga kamanninsu da 

Mami tace “Tana ciki ku shiga” Mai aikin Ammi ce ta nuna masu dakin da Heedayah take da kanninta, Heedayah na 

xaune dakin tana ta kallon ‘yan kanninta dake ta xuba mata shirme ko wannensu na son bata labari duk da ba wai sun 

santa bane amma jini ba karya bane, nan kam ita kallon girls din masu kama da ita tana karama take amma 

hankalinta ba a gun su yake ba, Ammi tace mata xa su je kai abinci asibiti amma bata ji ance ta xo su tafi ba tun 

daxu… Farida ce ta fara shigowa dakin, Heedayah ta mike da sauri ta rungumeta sosai tace “Farida…” Farida dai bata 

ce komai ba, haka Dinar da ta nemi waje ta xauna, Heedayah ta koma inda take a sanyaye ta xauna, tana kallon 

Dinar tace “Ina kwana Maman Fadil” Dinar tace “Lafiya lau” cikin sanyin murya Heedayah ta sunkuyar da kanta 

tace “Kiyi hakuri Maman Fadil, I don’t know what came over me, I am sorry…” Tana fadin haka Farida ta fara kuka 

Heedayah ta mike ta koma kusa da ita ta rungumeta tace “I’m very sorry Farida, I don’t know what really happened” 

ita dai Dinar har snn bata iya ta ce komai ba, da yake tasan Ashnaah da Ashfaa don Mum Islam kan shigo gidanta da 

su, sai ta jawosu tana masu wasa, a haka mum Islam ma ta shigo dakin ta samesu. Karfe goma saura Heedayah ta 

fita daga dakin, xuwa lkcn gidansu ya cika da ‘yan uwa da abokan arxiki, ita duk wnn ba shine damuwarta ba, tana ta 

tsaye corridor sai ga Amminta, ganin yanda ta tsaya kamar tana cikin damuwa Ammi na kallonta tace “Do you need 

anything?” Heedayah ta sauke kanta kasa a hankali tace “Ammi an kai abincin da kika ce asibiti?” Ammi tace “Toh 

barin abincin xa ayi ta yi har yanxu ba a kai ba, Abbanki na Kaduna da na nan with ur Mami suna can asibitin, 

anjima nima xan je, and Shuraim is around now, ki tafi kitchen ki hada masa breakfast ki kai masa, yana parlon 

Abban ki” Da sauri Heedayah ta kalleta, lkci daya ta 6ata fuska tace “Ni dai Ammi baxan iya ba, kila ma dukana xai 

yi, ni dai gwara in kira Farida ta kai masa wllh” Ammi ta hade rai tace “Ke nace ki kai masa…” Hawaye ta fara yi 

tace “Ni fa har yanxu ban ma je asibitin ba faaaa”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE