HEEDAYA CHAPTER 37 BY By Khaleesat Haiydar
HEEDAYA CHAPTER 37 BY By Khaleesat Haiydar
Bude kofar parlon Heedayah tayi suka yi ido hudu da shi yana xaune parlon yana danna wayarsa, ta kara daure fuska
ta tafi ta xauna saman kujera murya can ciki tace “Ina kwana” Jin bai amsa ba ta daga kai ta d’an kallesa, ajiye wayar
hannunsa yyi still not looking at her yace “Congratulations for reuniting with ur parent” Tace “Thank you” bayan few seconds jin bai ce komai ba tace “A kawo maka breakfast in ji Ammi?” Ya mike yace “Not hungry” daga haka
ya nufi kofa ta bi sa da wani kallo har ya fita, ta kyabe baki ta mike ta fice parlon ita ma, tana jin yana sallama da
Amminta ta makale ta ki karasawa, Ammi tace “Breakfast din fa?” Yace “No na yi breakfast nagode” Ammi tace
“Ohk hospital din xaka tafi yanxu?” Yace “Aa, Kaduna xan wuce” Ammi tace “Yau din?” Yace “In sha Allah” Ammi
tace “Toh Allah ya tsare, sai mun xo” Yace “In sha Allah” Bayan Azahar Heedayah da Farida suka tafi asibiti tare da
Amminta, she is just happy tun fitowarsu ko ba komai xata ga condition din Khaleel, Junaid ne kadai xaune ward
din, Khaleel kuma na kwance yana bacci, Ammi suka gaisa da Junaid tana tambayarsa me jiki, yace “Alhmdllh da
sauki” Ammi tace “Toh Allah ya basa lafiya, Allah ya tashi kafadunsa” Junaid yace “Ameen ya rabbi” Heedayah ta
ajiye abincin dake basket din hannunta da suka taho da shi tana kallon Junaid a hankali tace “Ina yini ya Junaid” ya
sakar mata murmushin da iyakarsa lips yace “Lafiya” Gaishesa Farida tayi ya amsa ta nemi kujera ta xauna, bayan
few minutes Ammi tace “Toh idan ya tashi ka gaida mana shi, xa mu koma, Allah ya basa lafiya” da sauri Heedayah
ta kalli Ammi amma dai bata ce komai ba, Farida ta mike ganin Ammi ta yi kofa tana amsa sallaman da Junaid ke yi
mata, Heedayah kamar xata yi kuka ta mike a hankali, xata fita Junaid dake lura da ita ya kalli kofa ganinsu Farida
sun fita ya riko hannunta ba yabo ba fallasa yana kallonta yace “Bayan tafiya gidansa da kika yi kika kwana, do u
still have any undone business with him???” Heedayah ta buda ido tace “But he is sick and I have to pity him…”
saketa yyi yace “Toh xauna kiyi jinyarsa” Ko kallonsa bata sake yi ba ta bi bayan Amminta da sauri ta fita. Suna
komawa gida Ammi ta shiga gidan Dinar tare a Heedayah da farida, Mami na parlor xaune Dinar tayi tagumi tana
kallonta tace “But you need not to be this worried Mami, ke komai sai ya baki tausayi, ba sanin wannan mutumin
kika yi ba me yasa xaki damu kanki haka a kansa, beside yana samun lafiya ai ko, ni fa har yanxu I am not happy at
the way ya kai Heedayah gidansa har ta kwana, no responsible person will do that, and dubi fa har waya ya bata a
boye, what’s the meaning of that, gidan iyayenta na asali kuma da ake ganin kamar shine silar xuwanta everything
just happened coincidentally ba wai ya san sune iyayen nata bane, I see no reason da kowa xai wani dinga ganin
kamar shine silar reunion dinta da parent dinta, it’s not so plss, da ta ci gaba da xama a nan kafin hutunsu ya kare
dole Mum Islam xata shigo ta ganta daga nan komai xai bayyana….” Mami dai sai kallonta take, Dinar ta ci gaba
tace “But the way u people are treating d guy kamar ba shi da laifin dauke yar mutane ya kai ta gidansa ta kwana
daga shi sai ita is alarming, who does that, nobody is even talking about this fa, duk mijin da ya fito xai aureta in har
fa ya ji wnn labarin da karamin matsala xai ja ba, yarinya budurwa ta tafi gidan saurayi ta kwana ta yini duk a daga
ma mutane hankali, but nobody is talking about it, ni fa shi sa Shuraim din nan ya burgeni wllh, ya san abinda yake”
Mami tace “Enough Dinar, I trust Heedayah, kila dai kun yi mata wani abun ne da bata ji dadi ba ta bar maku
gidanku amma ba abinda xai kai ta gidan namiji da son ranta, wanda Allah ya riga da ya kaddara dole sai ta bar
gidan ma xata hadu da mahaifanta, ta silar wnn bawan Allahn kuma….” Sallamar da aka yi bakin kofa ya sa Mami
tayi shiru, Farida ta bude kofar ta shigo parlon Heedayah na biye da ita sannan Ammi, a sanyaye Heedayah ta karasa
gun Mami ta duka kusa da ita tace “Ina yini Mami” Mami ta sakar mata murmushi tace “Lafiya lau, kun dawo
asibitin?” Heedayah tace “Mun dawo” Maman Fadil ta mike tana ma Ammi sannu da xuwa, Ammi ta amsa da
murmushi ta xauna snn suka gaisa da Mami, Mami tace “Nima yanxu nake shirin xan tafi asibitin, da yau din ma xa
mu wuce Abuja da Barrister amma nace bari in kara kwana daya in ga jikin bawan Allahn” Ammi tace “Allah sarki,
da muka je ma bacci yake ynxu, and he is the one holding us back too don xa mu tafi Kadunan mu ba, ya ce mu jira
ya ji sauki tukun mu je” Mami tace “Toh Allah ya bashi lafiya” Ammi ta amsa da “Ameen” drinks Dinar ta kawo ma
Ammi da bata ta6a shigowa gidanta ba sai ranan, Ammi tace “Ae da kin barsa Maman Fadil, Ina Fadil din?” Dinar
tace “Yana bacci a sama” Ammi tace “Allah sarki” Kitchen Dinar ta tafi ta ci gaba da girkin da take Farida ta mike ta
bi bayanta, Heedayah dai na xaune kusa da Mami, Mami tace “Ki je ku yi girkin” Ba musu ta mike ta bi su kitchen
din, Ammi ta mike ta dawo kusa da Mami ta xauna ta fara magana cikin sanyin tace “Hajiya muna alfahari da ke da
Barrister, kun yi abinda ba ko wani d’an Adam Allah ke ba ikon yi ba, kun rike Heedayah xuciya daya ba tare da
sanin daga inda ta fito ba, Allah ya saka maku da alkhairi, ya biya ku da aljanna, domin mu kam bamu da abinda xa
mu biya ku” Mami tayi murmushin karfin hali tace “Allah ya taimaki nawa haka nima….” Ammi tace “Ameen” Suna
parlon har kusan la’asar kafin Ammi ta mike tace “Xata koma gida tayi sllh” Mami tace “Nima sllhn xan yi nasan
Dinar sun gama girkin sai mu je asibitin” Ammi tace “Toh Allah ya dawo da ku lafiya” Mami tace “Ameen, amma
don Allah kar a sake kawo wani abincin, wanda aka kawo ma Allah ya amfana, Ga Dinar tayi girki ma yanxu”
Murmushi kawai Ammi tayi, ta kara mata sallama ta fita parlon. Mami na idar da sllh Dinar ta fito da abincin da ta
gama a basket, Mami tace “Kin yi ma Usman din magana?” Dinar tace “Ehh bari in dauko Hijab” Heedayah ta sakko
daga upstairs bayan ta idar da sllh Mami tace “Ga abinci can a kitchen ki kira Farida ku deba kuyi lunch” Heedayah
ta xauna a hankali tace “Mun ci abinci” Mami tace “Ohk” Shiru Heedayah tayi, can tace “Asibitin xa ki tafi Mami?”
Mami tace “Ehh” A hankali Heedayah tace “In bi ki Mami?” Mami tace “Ba daga can ku ke ba yanxu?” Heedayah
bata ce komai ba, Dinar dai ta saka hijab dinta ta dau basket din abincin ta fita waje bayan ta dau makullin motarta,
har Mami ta nufi kofa ta juyo tana kallon Heedayah da ta bi su da kallo tace “To taso mu je” Heedayah ta mike ta
dau mayafinta ta bi bayan Mami cike da farin cikin da bata nuna a fili ba. Har suka isa asibitin bbu wanda yace
komai cikin motar, Dinar tayi parking a space din da aka tanadar don haka a asibitin snn ta bude motar ta sauka,
Mami ma ta sauka, Heedayah ta dau basket din abincin ita ma ta sauka, Zayyad ne kadai dakin da Khaleel dake
xaune yana shan grapes a roban grape din, Tun da Mami ta shigo yake kallonta, Kafin kuma ta karaso gun gadon
ward din ya sauke idonsa, Zayyad ya gaisheta ta amsa da murmushi tace “Ya mai jiki?” Yace “Alhmdllh” Gaisheta
Khaleel yyi not looking at her, ta amsa tace “How are you feeling now?” Yace “Alhamdulillah” Xaunawa Mami tayi
tace “Toh Allah ya kara lafiya” Dinar tayi masa ya jiki ita ma ta xauna, Kallonsa kawai Heedayah dai take, ya d’an
kalleta suka hada ido, ta buda ido tace “How are you feeling?” Ya gyada mata kai yace “Fine Alhamdulillah, in sha
Allah” tace “Allah ya sauwake” yace “Ameen” Heedayah ta xauna kusa da Mami, Shi dai Khaleel ya ci gaba da shan
grapes dinsa slowly, bayan wani lkci ya daga kai suka hada ido da Mami dake ta kallonsa, Mami tayi saurin cewa
“Nace ga abinci nan abokin ka ya dibar maka koh?” Zayyad ya mike kafin Khaleel yace komai sanin bai son cin
abincin ya tafi gun basket din abincin don debar masa, dai dai nan aka bude kofar ward din, Khaleel ya dakata da kai
grape din hannunsa bakinsa yana kallon wa enda suka shigo, Manga ne da Bala, ko wannensu sanye da manyan kaya
irin na mutanen kirki, ga bakin glasses da suka kwama, Khaleel ya mayar da grape din hannunsa ya ajiye, Mami dai
sai kallonsu take, Manga na kallonta da katon muryarsa yace “Sannu Hajiya” Mami tace “Yauwa” Bala yace “Ya me
jiki?” Mami tace “Mun gode Allah” Manga yace “Madalla” karasawa yyi gadon yana kallon Khaleel, Shi dai Zayyad
bai yrda ya juyo ba yana xuba ma Khaleel abinci, Manga dake kallon Khaleel yace “ya jikin?” Khaleel yace “Na
warke” Manga yace “To madallah” Zayyad ya juyo ya mika ma Khaleel abincin hannunsa, Bala yace “Sannu da
jinya” Zayyad yace “Yauwa” Mami ta mike tace “To xa mu koma, may be kafin in tafi gobe da safe xan leko in sha
Allah” Khaleel ya kalleta yace “Toh nagode kwarai” Jikin Heedayah yyi sanyi, she wants to talk to Khaleel amma
har yanxu bata samu ta yi masa magana ba, Mami bata yi ma su Manga sallama ba ta fita ward din, Dinar ta mike
tayi ma Khaleel Allah ya kara lfya, tayi ma Zayyad sai anjima snn ta fita, Manga ya bi su da kallon gefen ido, A
hankali Heedayah ta mike tana kallon Khaleel dake ta kallonta, ta sauke idonta kasa sai kuma ta karasa gun sa tace
“Xa mu tafi, Allah ya sauwake” yyi shiru bai ce komai ba, tace “Do you need anything?” Ya d’an kalleta snn yace
“Nothing Heedayah” tace “Toh Allah ya sauwake” Yace “Are you travelling together with them tomorrow?”
Heedayah tace “I don’t know too” yace “Ohk, ki tafi suna jiran ki” Ta gyada masa kai ta nufi kofa su Manga suka bi
ta da kallo, ko kadan bata san su waye ba sai a snn Khaleel ya ga amfanin rashin barin ta gansu da yyi daren ranan,
tana kulle kofar Bala ya kalli Khaleel da jajayen idonsa bayan ya cire glasses din idonsa yace “Kafin in isar maka da
abinda ya kawo mu, wacece warcan matar da ta fito, a ina ka santa? Kuma yaushe ka saki jiki da bare har haka ku ke
mu’amala bamu da masaniya?” Khaleel yace “Bana tunanin you have any business to do with that Boss” Manga yyi
wani nishi yana kallon Bala yace “Follow her, get few information” Bala ya fice da sauri, Manga yace “Anyway, ba
wani abu ya kawo mu nan ba illa mu sanar maka our next operation na dauke Alhaji Ahmad is in 3 days time, wnn
lkcn idan ka kuskura ka kawo mana cikas, Arne yyi alkawarin aikaka lahira, amma kar ka yi tunanin a take xaka
mutu, idan ka mutu a take ka ci riba ma kenan, wllh wllh idan ka sake kawo mana wani cikas a wnn operation din
sai dai ayi wani Brainiac din ba kai ba, idan kana da sama da mu a duniyar nan ka fito ka nuna” Khaleel yyi wani
murmushi ya ci ga da shan grapes dinsa, Bala ya karasa dai dai kusa da Khaleel cikin husky voice yace “Be careful
with us, don’t mess with us…..” Daga haka ya fice daga ward, Khaleel ya juya yana kallon Zayyad ya diro daga
saman gadon fuskarsa a murtuke ya nufesa yace “Why did you let them know where we are?” Zayyad ya buda
hannu yace “I only told Maska, yace Oga Arne na nemana nace ina tare da kai you are sick, is anything wrong with
that….” Khaleel sai kallonsa yake yana huci, can ya nufi kan gado ya dau wayarsa ya fice daga ward. Da Magrib Heedayah na dakin kanninta tare da Nannynsu da ke shiryasu tayi masu wanka, tun dawowarsu tare da
Mami daxu daga asibiti Mami tace ta shiga gidan nasu gun Amminta, Ammi ce ta bude kofar dakin tana kallon
Heedayah tace “Gwaggon ki ta iso Heedayah, come out and meet with her” Heedayah ta mike ta d’an buda ido tace
“Yakumbo?” Ammi tayi mata murmushi tana nodding mata kai, Fitowa Heedayah tayi dakin da sauri don Yakumbo
na daya daga mutanen da take son gani ido da ido, kafin ta karasa main parlor suka yi kicibis da Yakumbo, Yakumbo
ta koma baya ta kare mata kallo daga sama har kasa sai kuma ta rushe da wani matsanancin kuka tace “Allah ya ga
xuciyar mu, bama nufin kowa da sharri a duniya, bama nufin d’an kowa da sharri, yanxu Heedayah ce wnn nake
gani Aisha? Heedayah ce wnn ta xama gandareriyar yan mata haka aure yau ko gobe?” Kuka take yi sosai ta koma
parlor ta xauna tana cewa “Xuciyar mu daya laya, bama nufin kowa da sharri duniya da lahira…. Yau ba ga ranan hakuri ba amma da mata duk kin bi kin daga ma mutane hankali kin dami mutane, kowa na jin haushina ana ganin
kamar hada baki muka yi da ‘yan kinnafas din, toh ni dai duk a gaggauta neman gafarana don an xalunce ni da
mummunan xato wanda har duniya ta tashi baxai gogu a raina ba, aka shiga tsakanina da d’an uwana da na rike tun
yana karami duk sbda an sace Heedayah a gidana kamar ni na sace ta….” Heedayah dai sai kallonta take, can ta tafi
ta rungumeta da murmushi fuskarta, Yakumbo dai sai kuka take, Ammi kuma ta xauna saman kujera tana karasa
saka ma Ashnaah kayanta, knocking aka yi, Ammi ta kalli Heedayah dake ta kallon Yakumbo kamar ta samu TV,
nan kuma Kaka kawai take gani wajen a xaune, mikewa Heedayah tayi ta nufi kofar ta bude, ido hudu suka yi da
Khaleel bakin kofar, ta koma baya tana kallonsa da mamaki, can tace “Anyi discharging din ka ne?” Ya gyada mata
kai yace “Ur Dad… is he in?” Tace “Ehh yana sama” Juyawa tayi tana kallon Ammi tace “Ammi it’s ya Khaleel”
Ammi tace “Ohk, let him in” shigowa parlon yyi, Ammi na kallonsa tace “Sannu da xuwa” ya gaisheta ta amsa tace
“Daxu Abbansu Islam ke ce min anyi discharging din ka…. Ya karfin jikin?” Khaleel yace “Alhmdllh naji sauki, na
xo yi masa godiya ne” Ammi tace “Ohh bbu komai ai, he is coming downstairs now, have a sit….” Xaunawa Khaleel
yyi yana gaida Yakumbo dake ta kallonsa tayi mitsi mitsi da ido, can ta share hawayen idonta tana kallon Ammi tace
“Shi kuma wnn din waye?” Ammi tace “Shine Honorable ke gaya maki ai” Yakumbo ta tabe baki tace “Toh ni dai ce
masa nayi wa ya sani ko shi yayi kinnafin din nata da ya gaji ya ga ba sarki sai Allah ga yasin ana ta jifarsa da shi ya
maido ta” Ammi ta d’an hade rai tace “Haba Yakumbo, wani magana ne wnn, Heedayah dake hannun mahaifiyar
makociyar mu a kaduna, shi dai ta dalilin sa aka kawota nan gidan, ba wai wani abu ba” Yakumbo tace “Atoh ni
babu ruwana wllh, ke baki ga kirarsa bane kamar ta mutan da, ai irin su ne ke kinnafin din yanxu, a ajiye batun wani
kyansa, wllh duk haka suke ba muna gani a TV ana nuna mana su ba kullum” Ammi bata kuma cewa komai ba sai
dai ranta ya baci sosai, Shi dai Khaleel kansa na kasa, Heedayah sai kallon Yakumbo take kamar xata yi kuka,
Yakumbo ta kyabe baki ta bude yar jakarta ta fiddo tissue da aka nannade ta warware ta ciro goronta ta fara ci tace
“Na nannade kayana kada kura ya fada kai in cutu….” Ammi dai ko kallonta bata yi ba ta kalli Heedayah tace “Ku je
da shi gidan Dinar ya gaida Mamin ki a can kafin Abbanku ya sakko” A sanyaye Heedayah ta mike tana kallonsa, ya
mike yyi ma Ammi godiya, amma shi ma gaba daya jikinsa yyi sanyi, ya bi bayan Heedayah da har ta kai kofa,
Yakumbo tace “Toh Allah ya maka albarka, ai da ba don kai din ba da har yanxu ana ta xargina ana kullatata a
xuciya, 6atan wnn yarinya bbu irin bakin jinin da bai ja min ba a duniya, duk inda na kutsa nuna ni ake da d’an yatsa
har ya kai ya kawo na dena fita, ko kasuwa na shiga anyi ta leko ni kenan a shaguna” Heedayah ta kulle kofar bayan
Khaleel ya fito, tana kallonsa cikin sanyin murya da damuwa tace “Kayi hakuri plss, Ammi na ta gaya min haka take,
she’s strange because she is old” Yyi mata murmushi bai ce komai ba, tace “Baka yi kama da kidnapper ba, kuma
baxa ka ta6a kama da su ba” Kallonta yake without blinking, xata wuce a hankali yace “Why did you think so” Ta
juyo da sauri tace “Dama me yasa xaka yi kama da kidnapper? My Yakumbo is just saying that out of frustration,
Allah ya raba ka da kama da su, they are the deadliest set of beings on earth….” Sauke idonsa yyi bai ce komai ba, ta
fara tafiya ya bi bayanta har suka isa gate, ta kallesa tace “Seems you are not still happy about what Yakumbo
said…” Da sauri yace “Noo, it’s nothing, nasan haka tsofaffi suke” A tare suka shiga gate din Dinar, ya tsaya bakin
kofar parlon ta shiga sanar ma Mami xuwansa, a hankali ya xauna saman kujeran da ya gani a wajen, lkci daya
hawaye ya kawo idonsa abinda tun da ya san kansa bai ta6a yi ba, sai dai ya ga ana kuka amma shi bai ta6a ko digon
hawaye ba don ya taso xuciyarsa a kekyashe ne, Bai ta6a jin ya tsani rayuwarsa irin na wnn lkcn ba, he just hate
everything about him immediately, a da ya kan ji hakan amma baya wani tasiri a xuciyarsa don in few minutes yake
dawowa normal, yau kuma sai yaji hawaye na xuba idonsa sosai, fitowa Heedayah tayi tace “Ya Khaleel an ce ka
shigo” Jin bai dago kansa ba ta isa gabansa tace “Ya Khaleel” durkushewa tayi gabansa ganin hawayen idonsa, lkci
daya ta rikice ta kamo hannunsa tace “Are you okay? Me ne ya faru, ko kirjin naka ne ya fara, tell me plsss” ya
girgixa mata kai trying hard to control the tears ya kamo hannunta amma ya kasa cewa komai ya xamo kasa, kuka
take sosai tace “Plss ka gaya min what’s wrong ya Khaleel, me ya same ka” cike da karfin hali cikin rawar murya
yace “I… I want…. you to be a father… mother… and sibling… to me” Shiru tayi hawaye na sauka idonta tana
kallonsa, ganin ya sauke kansa kasa hawaye na ci gaba da sakko masa ta rungumesa ita ma hawayen na xuba idonta
tace “Did you lost them??” Gyada mata kai ya dinga yi amma ya ki cewa komai, tace “Talk to me plss, did u lost
them” cikin sarkewar murya yace “I never had them” ta fashe masa da kuka sosai tace “I promise I will be, I promise
you that…” Bude kofar parlon aka yi, Heedayah ta sake sa da sauri har lkcn tana kuka ta mike, Mami ce tsaye
bakin kofar ta fito da mamaki tace “What happened???” Heedayah dai ta kasa cewa komai sai goge hawayen da ya
ki tsaya mata take, Mami ta daga kan Khaleel da ya sunkuyar da kansa ya ki dagowa, ganin idonsa tace
“Subhanallah what happened, are you Okay” ya girgixa mata kai cike da karfin hali ya mike cikin sanyin murya yace
“I… I came to thank you Ma, I appreciate ur care toward me….” Hawayen dake sauka idonsa yasa Mami ta ji lkci
daya nata idon ya cicciko tace “But you don’t need to dear, you don’t need to….. Come in” kama hannunsa tayi xuwa
parlon Dinar, Heedayah ta bi bayansu tana goge hawayen dake xubo mata, Xaunawa Khaleel yyi saman kujera lkci
daya yaji ya samu nutsuwa, xuciyarsa ya daina masa xafin da yake masa with just Mami’s word, daki Heedayah ta
wuce ta ki tsayawa a parlon don gaba daya xuciyarta tayi rauni abinda yace mata, Mami ta sa mai aikin Dinar ta kawo abinci da ruwa ta ajiye masa, shiru yyi kawai yana kallon abincin, tun da ya san kansa sai dai ya shiga eatry ya
ci abinci bai san dadin abincin da aka girka a gida ba, muryar Mami ya ji tace “Ka ci abincin” Ya kalleta snn ya
xamo kasa a hankali ya xauna ya bude plate din abincin, shinkafa ne da miya with many meat sai coslow a wani d’an
bowl a rufe, ya dau spoon ya fara cin abincin a hankali, Mami dai sai kallonsa take don exactly yanda Junaid ke
xaman cin abinci ya xauna, Dinar na sakkowa xata dauko ma Fadil fresh yo a kitchen ta tabe baki tayi wucewarta
kitchen din, kawai ita dai ta ji ranta bata yarda da Khaleel ba, ga shi da innocent face, very innocent, but ita dai bata
yrda da shi ba. Abba ya dau makullin motarsa xai fita parlonsa Mumy dake ta kallonsa a tsaye tace “Yau naga ikon
Allah, Ina kuma xaka daga dawowa barrister ko hutawa baka yi ba, ga abinci can nace maka na gama ka dau
makullin mota xaka fita” Yace “Nace idan na dawo xan ci Maryam, xan je can gidan Dr ne Yanxu” Mumy ta kyabe
baki tace “Toh aiki kaje yi Abujan ko har yanxu kan batun 6atan Heedayar ne, ni fa wllh da na ji shiru bbu wani
labari kuma babu wanda ya sake cewa komai na xata an ganta ne” Abba ya juyo yana kallonta yace “Eh an ganta, a
gidan mahaifanta a nan garin Abujan” Mumy ta saki wayar hannunta ba tare da ta shirya yin hakan ba tace “Ban
gane gidan iyayenta ba?” Yace “Yes biological parent dinta, idan kina jin Honorable Ahmad Yusuf Ishaq, shine
Mahaifinta” Mumy ta masa wani kallo tace “Ban gane ba, wacce Heedayar wai kake fadi barrister, Heedayah da ba
lallai a sake ganinta ba kake nufi ko warce?” Abba yace “Toh ki tambayi d’an ki xai fi yi maki bayani in details a kan
abubuwan da suka faru, tare aka yi komai da shi a Abuja, as for now sai na dawo….” Bai jira cewarta ba ya fita, ta
cire dankwalin kanta jin wani xufa dake keto mata tun daga saman kanta har kasa duk da Ac dake kunne parlon, da
dankwalin ta dinga fiffita ma kanta iska can ta dau wayarta da screen din ya tarwatse ta shiga kiran Shuraim, yana
fara ring ya daga tace “Duk inda kake kuma duk me kake yi ka barsa ka dawo gida yanxun nan ina jiran ka” Jin
yanayinta yace “Lafiya Mumy??” Kuka ta sakar masa tace “Ni dai nace ka dawo yanxun nan Aliyu” Daga haka ta
katse wayar ta sake jefarwa kasa tana xagaye parlon, gaba daya xuciyarta ta ki yrda ko na second daya da xancen
Abba sai kace wani film, wai wani Alhaji Ahmad Yusuf Ishaq shi ne uban Heedayah, ta ina?? Bayan ko kama da shi
ma bata yi ba, yarinyar da aka ce an tsinto a daji, to amma kuma ai barrister baya mata karya wasu hawayen da bata
san dalilinsu bane suka shiga sakko mata tace “Aikin banxa, uban wa xa ayi ma wnn karyar, Alhaji Ahmad Yusuf
Ishaq ne ubanta shine da ta 6ata ba a ji a duniya ba….” Tsaki ya ja ta nemi waje ya xauna tana kara tabbatar ma kanta
raina mata hankali kawai Abba yake, ya ma san wanda ya ambato mata a matsayin uban Heedayah kuwa, abinda
ance mata Heedayah ta shiga duniya kenan ba dawowa, mikewa tayi ta sake daukar wayarta tana neman layin
Sadiya.