HEEDAYA CHAPTER 39 BY By Khaleesat Haiydar
HEEDAYA CHAPTER 39 BY By Khaleesat Haiydar
A boye Mumy ta dinga goge hawayen da ya cika idonta daga inda suke tsaye bayan kujera da kawayenta, Mum din
Sudais kuwa sae xare ido take, Bayan duk anyi gaisuwan mutunci a parlon Baffa da Abba ma duk suna parlon,
Mami ta iso gidan tare da Hajiya Zuwaira matar Baffansu Junaid, ruwa da lemo da snacks iri iri na alfarma da
peppered chicken wanda Step mum din Sudais tayi aka ajiye ma bakin, Abban Heedayah yayi kasa da murya yana
kallon kaka da ta nemi waje ta xauna tayi tagumi tana facing dinsa kamar marainiya, a nutse yace “Inna mun xo ne
don maki godiya….” Ta dakatar da shi da sauri tace “Aa ba ruwana ka gode ma Allah, Mu dai ba mu rike Deedayah
don a bamu komai ba ko ayi mana wani abun, amma fa an sha barnan kudi ba na wasa ba kaji in gaya maka,
gwangwanin milon nan da Madara har sai da na dinga tarasu buhu buhu ina yi ma ‘yan gwangwan sadaka, a karshe
dai sai da tattalin arxikin Amadu ya jijjiga don ma ina taimaka masa ban bar sa yyi ta wahalan shi kadae ba, kuma ko
kallon banxa bamu ta6a yi ma yarinyar nan ba, ynxu haka rabona da xuwa Makka tunda Amadu ya tsintota, Atoh
hidima tayi masa yawa mana ga kudin gyaran ido ga kudin kayan shayi ga kuma hidimar iyalansa, ga dai ta nan ka
tambayeta ko an rageta da komai shekaru biyar din da tayi da mu…” Ta fada tana nuna masa Heedayah dake xaune
kusa da ita, Heedayah dai bata ce komai ba, kaka ta ci gaba tace “Ni fa wllh na dauka ma iyayenta sun rasu ne ta
shigo duniya, kuma ni ban sace ma Amadu gwiwa ba da ya kawota matarsa ce ma ta so bamu matsala, kai ta ma
bamu sai dai a bar kaza cikin gashinta, to yanxu duk ba wannan ba, babban damuwata a nan shine…. Shekaru kusan
biyar kenan tunda wancan mutumi….” Ta fadi haka tana nuna gwamna ta ci gaba, “Tun da ya hau mulki kafin ma ya
xarce nake fama da Shureen ya kai ni wajensa in basa shawarwari in kuma ce ya ji tsoron Allah kada giyar mulki yyi
ta debarsa yana abinda ya ga dama amma wnn yaron ya ki kai ni, titin unguwarsu aminiyata ta Salla fa duk ya
gantale ya ki shimfida masu sabo, idan kaje layin xaka xata a ruga kake, mu kaga dai namu ai ko kwarzane bai yi ba
tunda duk manyan masu kudi ne a layin suka hada kudi suka yi abun su bakinsu alekum, can kuwa bbu me yi duk
talakawa ne, ni fa dalilin titin yasa bana son xuwa wajen ta Sallah, to kaga kuwa ya raba xumunci, snn kuma inji ko
ya hau mulki ne don ya dinga musgunawa talakawa uwa shi ya halicce su, ina fa da labarin kwace masu filaye da
yake yi yace na gwamnati ne, to banda lalacewa a gidan ubanwa filaye ya xama na gwamnati? Filayen da ke nan tun
kan a haifi uban da ya haifesa, na fa san uban nasa, yana nan wani tsamurmuri kamar buzu tare muka yi wasan kasa
da shi, snn shi mutumin kirki ne bansan garin ya d’an sa ya gantale ba da cuta….” Shi dai me girma Gwamna banda
murmushi bbu abinda yake yana kallon kaka da ta hakikance, Abban Heedayah dai kansa na kasa yana sauraron
kaka, Abba da Baffa ma duk sun kasa dago kai kowa da abinda ya damesa a xuciya, Shuraim kam banda harararta
babu abinda yake, Mami dai dake xaune tare da Hajiya Zuwaira da Hajiya Hauwa tayi tagumi tana kallon kaka,
Ammin Heedayah da matar gwamna sai murmushi suke su kam, Mumy da mukarrabanta na ta tsaye bayan kujera
kamar munafukai, Mumy dai bata ma san me ake cewa a parlon ba sai share xufa take tana gwala ido… Kaka tace
“Toh ba ruwana na fita hakkin ka na fada maka gaskiya Allah baxai tambayeni ba ranan gobe kiyama” gwamna yyi
murmushi yace “Gaskiya ne” Kaka tace “Atoh” kallon Mumy kaka tayi ta nuna ma Alhaji Ahmad tace “Kaga uwar
gidan Amadu can, ita ta haifi Shureen din da nake fada maku, mu dai kawai a bar kaza cikin gashinta…..” Alhaji
Ahmad ya kalli Mumy yace “Mun sameku lafiya Hajiya?” Mumy na kirkiran murmushi cike da karfin hali tace
“Alhmdllh wllh, sannun ku da xuwa….” Yace “Mun gode, Allah ya saka maku da alkhairi ya duba gabanku da
bayanku…..” Kaka tace “Na dai ce a bar kaza cikin gashinta amma wllh tllh mu muka san abinda muka gani, amma
kawai dai a bar kaza cikin gashinta, to matar da…. Bari kawai dai a bar kaza cikin gashinta” Mumy dai sai xufa take,
Shi dai Abban Heedayah kansa na kasa, Ammin Heedayah ta d’an kalli Mumy sai kuma ta dauke kanta, kaka tace
“Tunda mu dai muna sonta kuma ba mu cuceta ba ai shkkn tone tone ba kyau, amma dai Heedayah ta sha wahala
wllh” shiru duk aka yi a parlon, kaka tace “Bari dai kawai shirun ya fi, amma tunda nake ban ta6a ganin mugunta a
fili da bakin hali irin wanda na gani ba, to wnn bai wani dameni ba don wllh kanta tayi ma, ni baxan tona mata asiri
in fadi irin tsana da kyara da tsangwamar da ta dinga yi ma Heedayah ba ta nuna ita baxata riketa ba, ta xo har gida
ta dinga xugani kar in amsheta ince ma Amadu xan masa baki idan bai mayar da ita inda ya tsintota ba, to wllh
baxan tona mata asiri ba, Allah kuma ya rufa min asiri yanda na rufa mata amma kaga warcan….” Ta fada tana nuna
Mami, tace “Surutu ba shi da amfani, amma wllh tllh ta dalilin Deedaya ta amince ta auri Amadu don ta riketa ganin
bata da gata, kasan abokiyar aikinsa ce dukaninsu lauyoyi ne, mijinta ya mutu ya bar masu uban dukiya ina jin da
kyar idan bata fi Amadun ma kudi ba, amma ta yrda ta auresa duk sbda Deedaya tunda an ki riketa a gidan, baxan
dai fadi warce ta ki riketa ba, in gaya maka Rakiya ta sadaukar ta auresa ta rike Deedayah fiye da ynda bafillatanar
uwarta xata riketa, ko ku kunga wani alamar cutarwa tare da Deedayah da ku ka ganta??” Abban Heedayah yagirgixa kai yace “Ko daya” Kaka tace “Atoh, don haka idan ma duk shekara ka dinga kai Rakiya makka wllh baka
biyata ba, duk da ni dai bance a kai ni ba tunda sbda Allah na yi ba sbda a kai ni Makka ba, Amadu kuma ynda xaka
biyasa kawai ka bar masa Deedayah na har abada ya ci gaba da rikon abarsa, da ace yana da d’a namiji me hankali
ne ma sai ka basa auren Deedayar, to babu, Allah bai basa ba, sae dai da ace ita Rakiya na da d’a namijin amma
banda Junaid sae a hadasu kawai don ita ma ta bauta mata, amma dae baxae ma yiwu ba, Heedayah ba gantalalliya
bace….” Heedayah dake ta kallon kaka ta dau lemo daya ta mike tayi wucewarta dakin kakan tana turo baki.
Xaunawa tayi gefen gado ta bude drink din hannunta tana sha, sae kuma ta mike da sauri tana duba dakin ko xata ga
wayar kaka, ta gansa ta nannadesa da handkerchief ta ajiye a kusa da pillow, dauka tayi ta duba ko akwai kati, ganin
akwai tayi dialing number snn ta kai kunne, ba a dau lkci ba ya fara ring aka daga, sallama tayi, aka amsa calmly
daga daya bangaren, tace “Ka shigo Kadunan ne?” Yace “Yea tun da rana, I’ve been waiting for ur call tun daxu” tace
“Bamu dade da isowa ba, ya jikin?” Yace “Na ji sauki sosai, Alhmdllh” tace “To kana shan maganin?” Yace “Ai kin
ce in sha, so I just have to take it” Tace “Toh Allah ya kara lafiya” Yace “Ameen, where are you now?” tace “Muna
gidan Yayan Abbana yanxu….” Yace “Ohk, how about Mami” Tace “Ita ma ta xo nan din” yace “A nan xa ku
kwana?” Heedayah tace “Aa xa xan bi Mami mu koma can gida” shiru ya d’an yi, sai kuma yace “Can I come later?”
Ita ma tayi shiru kafin tace “Just pretend as if u came to greet Mami” Yyi murmushi a hankali yace “Ohk, but….” Sai
kuma yyi shiru, tace “But what?” Yyi kasa da murya yace “Shkkn dai, I will come in sha Allah da daddare….” Bude
kofar dakin ta ji anyi ta katse wayar da sauri ta xame daga kunnenta ta ajiye kan gadon ta jawo pillow ta rufe ba tare
da ta kalli wanda ya shigo ba, satan kallon mirror din kaka tayi taga Shuraim bakin kofar, ya shigo ya rufe kofar
dakin ya karaso ciki, ita dai ta ki juyowa, can kuma ta mike da xumar xata fita still wanting not to look at him,
calmly yace “Don’t move….” Tsayawa tayi ta hade rai kamar xata yi kuka tace “To me nayi” yana kallonta daga sama
har kasa ya karasa har gabanta yace “Kina da grit din da xa ki tafi gidan saurayi kamarki ki kwana ki yini, and you
are happy and comfortable bcos nobody is saying anything to you about that right? Everyone is just concentrated on
ur reunion with ur parent, and ur stupid mind is letting you think you are right ko??” ita dai bata ce komai ba, Ya
d’an daga murya yace “Now tell me, uban me kika je yi gidansa at the first place, and uban waye shi din, why did u
follow him to his home, What were u busy doing for 24 hours in his home?” Ta fashe da kuka tace “Ni fa Ya
Shureen ban sani ba, kuma ba gashi na dawo ba dai…..” Ya dinga kallonta bbu ko kiftawa, ta marairaice tana
kallonsa ita ma ganin ko kadan bbu wasa tattare da shi, yyi kasa da murya fuskarsa daure yace “Now tell me, meye
tsakanin ki da shi, and a gidan uban wa kika san sa? Snn a ina kika kwana a gidan nasa” Turo baki tayi kafin tace
komai ya Fixgota dab da shi ta 6ara baki xata yi ihu bata ankara ba sai jin bakinsa tayi a nata, and he gave her the
first kiss of her life, a french kiss it was, everything happened in just a minute, lkci daya ya saketa ya fice daga
dakin…. Ta kusa minti biyu tsaye bata ko motsi bayan fitarsa, a hankali ta kai hannu bakinta da ta ji yyi mata sanyi,
sai kuma ta sulale kasa a hankali ta xauna gabanta na wani irin bugawa, ganin abun take kamar a mafarki, ta sake kai
hannunta bakinta, lkci daya ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba ta mike da sauri ta fada kan gadon kaka ta rufe
fuskarta da pillow tana kuka sosai…. Kiran sllhn Magrib ya sa kaka ta shigo dakinta baki har kunne, har sannan
Heedayah na kwance saman gado tayi kukanta ta koshi tayi shiru, kaka ta washe baki tace “Sannu Deedayah, har kin
tashi? Kina son wani abu ne?” Heedayah ta turo baki ta girgixa mata kai ta mike xaune tace “Suna parlon?” Kaka
tace “Wani parlon, sai kace dai gantalallu, sun sallameni sun wuce amma ubanki yace xai dawo gobe da safe, bari in
sa a kawo maki abinci idan abincin bai maki ba ma sai a samo maki abinda ranki ke so” Heedayah tace “Mami fa??”
Kaka tace “Ai ta riga su tafiya, kinsan matar akwai kamun kai, in gaya maki gwamna ma yace bana da ita xa aje
makka idan Allah ya yarda, ni dai nace masa A’a amma ya ki saurarata to bbu yanda na iya tare xa mu je da ita yace,
anjima kuma xa a kawo min motata a adana min a garejin Amadu abinda na tambayi ubanki kenan farat daya ya
bani” Kaka ta nuna mata dankwalelen Zinari na zobe tana washe baki tace “Matar gwamna kuma ta bani wnn, wai
tana so na, yanxu gobe xan je in gaisheta da safe, sannan Babanki yace idan xa su koma Abuja in hada kayana tasss,
to ni bana son in tsaya muna musu da shi ina matsayin babba shi yasa nayi shiru rai bbu dadi, Maryam kuma na can
dakin uwar Sudais ta kasa wucewa gida ni da naga yanayinta ma na xata bori xata hau, wato ta girgixa ba kadan ba,
Allah ubangiji ya rabata da hawan jini farat daya dai, ga shi bbu wanda ya bi ta kanta sai Rakiya da ni ake ta kulawa
don ma ban tona mata asiri na fadi irin tsanar da ta maki ba, gwamna kuma yace xai ba Rakiya wani mukami na
lauyanci ina jin a gwamnati, ni dai kawai nayi shiru ne amma ga dai Amadu me yasa xai ce sai Rakiya idan ba kyasa
ta yyi ba, balle ma da aurenta a kai take gantali, don Amadu ai bai saketa ba, yanxu gobe xan lallaba Shureen in basa
duk abinda yake so ya kai ni gwamnet house….” Sai da gaban Heedayah ya fadi da kaka ta ambato Shuraim, Kaka
kamar xata yi kuka ta nemi waje ta xauna a hankali tace “Allah sarki Sudess baya nan wnn abun alkhairin ke faruwa,
bai kamata a mance da shi ba don shine silar xamanki a gidan nan” Heedayah dai tayi shiru, can tace “Kaka ni fa
gidan Mami xan wuce” Kaka tace “To ai ta tafi idan ba dai Shureen ya ajiye ki ba, yana can parlon Baffansa bari in
je in samesa” Heedayah da hankalinta ya tashi da sauri tace “Aa kaka kar ki ce masa….” Kaka tace “Aa ba ruwana ya
xa ayi a bari ki kwana a nan ba da son ranki ba, ba sai Allah ya kama mu ba idan ranki ya bace, bari inje nasan idan
Baffan nasa yyi masa magana xai kai ki har parlon Rakiyar idan xai iya” Bata jira cewar Heedayah ba ta fice, Kai tsaye ta shiga bangaren Baffa, shi da shuraim kadai ne xaune parlon, kaka ta kalli Baffa da yyi shiru ganinta, snn ta
kalli Shuraim da kansa ke kasa, tace “Me ya faru kuma?” Baffa ya sauke ajiyar xuciya bai dai ce komai ba, Kaka ta
nemi waje ta xauna tace “Nace me ke faruwa, shi gashi ya xauna gabanka kamar me neman gafara, laifi yyi ma uban
nasa ne?” Baffa yace “Aa, ko daya, muna tattauna wani batun ne daban” Kaka tace “Toh ni ba wannan ba, Heedayah
ce tace xata tafi gidan Rakiya kuma kaga bbu me kai ta, gantalallen dreban ka dare nayi yake kama gabansa, don
haka nace Shureen ya je ya ajiyeta kada mu shiga hakkinta, kaga dai tana da hankali bata ce xata bi iyayenta ba sai
uwar rikonta, kaga kuwa ai ba butulu bace ita” Baffa yace “Toh xai ajiyeta idan xai wuce” Kaka ta mike tayi
ficewarta daga parlon ranta fess, ga sabuwar mota, ga zinari, ga tafiya makka, gobe kuma xata gwamnet house,
Baffa na kallon Shuraim da ya ki dago kansa yace….