HEEDAYA CHAPTER 41 BY By Khaleesat Haiydar
HEEDAYA CHAPTER 41 BY By Khaleesat Haiydar
Mumy ta ja wani tsaki tace “Ni an gaya maku ta mukamin ubanta nake, Ina ruwana da wani government house
yarinya ta bi ta cuceni ta tarwatsa min rayuwa shekaru biyar kenan” Salima tace “Ke dai wllh Yaya kina da matsala,
ga hanya dai mafi sauki da xaki musguna mata bbu me ce maki don me, wllh Aliyu na auren yarinyar nan shkkn sai
yanda kika juyata kika takata, beside xa ma ki iya shiga ki fita idan ma yana da niyyar sonta watarana ki cire masa
son nata a ransa gaba daya yaji ya tsaneta, you won’t even give any space for him to begin having feelings for her,
axabtar da ita kawai xai dinga yi wllh, Kai ko shimfida idan baki son su hada baxa su hada ba, dama fa sbda yanda
kike tsangwamata ne ya sa ban kai ki gun wnn mutumi me min aiki ba, wllh yanxu haka d’an minister of finance
nake hari, gashi har ya fara kulani a Instagram muna chatting yanxu har ya bukaci yaushe xa mu hadu, dubu 80 na
kai ma mutumin yyi min wnn aikin duk da dai har yanxu ina son Junaid kuma shi nake burin aure, yanxu idan kin
amince da shawarar nan da na baki kawai sai in kai ki gun Mutumin, kiyi ma Barrister karya kice xaki gidan
Gwaggwo Rumaisa, wllh Yaya sai yanda kika yi da Heedayah da shi kansa Shuraim din, kuma sai dai ya ajiyeta a
matsayin hoto bbu abinda xai faru tsakaninsu, snn ayi maki aikin da xata dinga tsoron ki tana maki biyayya kiyi ta
juyata kamar masa, daga karshe ma idan kika so ki saka Aliyun ya saketa shkkn kinga ta xama bazawara, idan kuma
aure kike son ya kara sai ya kara, daga gefe ke kuma kin samu connection da masu kudi, tunda duk da matan
gwamnoni da manyan mutane iyayenta suke hulda” Mumy dai tayi shiru abun duniya ya dagule mata, Sadiya tace
“Atoh dai, dadina da ke Salima akwai kwakwalwa” Mumy ta sauke ajiyar xuciya tace “Ku kuna ganin hakan da xa
ayi shine mafita?” Sadiya tace “Mafitan gaske kuwa, ke kina da wata mafitar ne banda wnn din” Mumy tayi tagumi
tace “Toh ai tsoro nake kada wnn karan abun ya sake juye min, nifa wllh wllh ko mutuwata bana jin sa kamar yanda
nake jin wnn yarinya, a dalilinta fa na shiga gararin rayuwa mijina ya juya min baya duk da biyayya da yake min”
Salima tace “Bbu abinda xai juye kanki, wnn mutumi da nake gaya maki Gwaska ne wllh, gashi nan ya min na fara
ganin aiki da cikawa kawai ke dai nemi karyar da xa ki gilla ma lauyan mijinki ki shirya mu je mu san tudun
dafawa” a hankali Mumy tace “Toh bari ya dawo, amma fa….” Salima ta ja tsaki tace “Amma me, ke dai kin cika
fitina wllh yaya, ga rashin bin shawara” Mumy tace “Toh goben sai mu je kawai” Sadiya tace “Ni connection din da
xamu samu ma shi ya fi min dadi wllh, ko ba komai ai a fara damawa da mu a kasar” Da daddare Abba na parlonsa
yana operating system Mumy ta shigo, xaunawa tayi gefensa tace “Sannu da aiki my Barrister” ba tare da ya kalleta
ba yace “Sannu” tayi kasa da murya tace “Baka sha Watermelon din ba My Barrister” yace “When I am done…”
shiru ne ya biyo baya, bayan wani lkci tace “Barrister dama akwai wata magana da nake son mu yi da kai” Abba
yace “Ohk ina ji” tace “Ko in bari ka gama abinda kake” yace “No fire on, ina jin ki” Tana murmushi cikin tattausan
murya tace “Barrister naga yanda kake ji da Heedayar nan, ga kuma yanxu Allah ya bayyana iyayenta cikin sauki
bbu tashin hankali, nasan kuma shkkn yanxu idan ba wani ikon Allah ba tafiya xa su yi da ita idan xa su koma Abuja,
toh sai nake ga don xumunci yyi karfi da iyayen nata me xai hana ka nema ma Shuraim aurenta gun Mahaifanta,nasan baxa su ce a’a ba, and I must confess my barrister duk da naki rike Heedayah, ita din yarinya ce me hankali
nutsuwa da ladabi nagani, bata da hayaniya snn she will make a perfect daughter in law, ni gaskiya tsoron yan matan
yanxu nake barin ma na nan kaduna, kada yaje ya kawo mana warce xata fi karfinsa ya fi karfinmu, kasan yanxu
abinda ke faruwa kenan a duniya, shine tun da rana nayi wnn naxarin naga bashi da wani aibu, kuma xai kara karfafa
xumuncinmu da iyayen Heedayah, hakan kadai xa suyi maka su kwatanta abinda ka masu na rike masu ‘ya bisa
amana, duk da matsalolin da ka fuskanta daga gareni wanda hakan ba komai bane facce sharrin shaidan, kuma wllh
wllh nayi nadama, don d’a na kowa ne bawa sai mai shi” Abba dai sai danne dannensa yake yana murmushi bai ce
mata komai ba, A sanyaye tace “Kayi shiru My Barrister” yace “Ehh ina jin ki” tace “Toh ai na gama” ya kalleta yace
“Good, a xamaninmu an mana auren dole?” Tayi shiru tana kallonsa yace “Answer me” tace “Aa” yace “Toh baxa
muyi ma yaranmu ba, Shuraim bai ce yana sonta ba, ita ma bata ce tana son Shuraim ba don haka ki ajiye wnn
shawaran naki a gefe, it’s shaky, with or without aure xa ayi xumunci da su sosai, don iyayenta yan Babban gida ne…
Ba kananun mutane bane” Mumy ta bata rai amma ta rasa abun cewa, Barrister yace “That’s just it” Mumy ta
marairaice tace “Barrister auren kadai ne xai sa ayi xumunci wllh” Da mamaki Abba yace “Why are you bothered sai
anyi xumunci da su? Saboda Mahaifinta na neman wani mukami a gwamnati and you have ur selfish interest da kike
son achieving??” Ta mike tana masa wani kallo tace “Alhmdllh kasan dai ni ba kwadayayyiya bace, Ina ruwana da
mukamin ubanta, su suna kano ni ina nan Kaduna, me ya kawo wnn magana, an basa mukamin ne ma balle kace
min haka, shkkn daga kawo shawara sai a fassara ni, mummunan fassara kuma, daga nayi ma d’a na sha’awar
aurenta sbda hankali da nutsuwarta sai ace ina kwadayi, me garesu da xa su bani wanda Allah bai bani ba” Abba dai
bai ce mata komai ba yana ci gaba da abinda yake, ta juya a fusace ta fice daga parlon. Washegari Shuraim na
dawowa gidan daga wajen aiki ya tafi parlon Abbansa da ya kirasa tun safe, gaida Abbansa da ya fito bedroom ya
xauna saman kujera Shuraim yyi bayan ya xauna kasa kusa da shi, Abba yace “Ya aikin?” Ya shafa kansa yace
“Alhmdllh…” Abba yace “Ya issue din Transfer da kace xa ayi maka” Shuraim yace “Still working on it, may be next
year….” Abba yace “Good” shiru ne ya biyo baya, Abba yace “Are you listening?” Shuraim ya kallesa yace “Ina ji”
Abba yace “What are ur plans on settling down with a wife” Shuraim yyi shiru yana kallonsa, can ya sauke kansa
kasa, Abba yace “Xan fita office don haka you need to talk fast” Shuraim yyi kasa da murya yace “In sha Allah
soon” Abba yace “Kana da warce kake so ne” nan ma yyi shiru kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Mun yi
magana da Baffa, yace xa ku yi magana” Abba yace “Toh shkkn, you can go” Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa
Abba ya bi sa da kallo har ya fita, Da sauri Mumy ta bar bakin kofar ta koma bangarenta, Shuraim dai ya bi ta da ido
bai ce komai ba ya wuce dakinsa, yana shiga ya cire shirt din jikinsa sai ga kiranta, ya daga tace “Ka sameni parlona
yanxu” Ya fita dakin nasa ya koma bangarenta, Tsaye ya ganta parlonta, tana ganinsa tace “Wanka xaka yi ne” yace
“Nayi wanka, kwanciya xan yi” tayi kasa da murya tace “Me Abbanka yace maka?” Yace “Aa kawai yace xan ajiye
sa anjima kadan” Mumy ta daure fuska tace “Karya kake wllh, ni xaka munafurta??” Ya buda manyan idanuwansa
yace “That’s it mum, abinda yace min kenan, nace masa Allah ya kai mu” Mumy tayi shiru tana kallonsa, can tace
“Baxa dai ka gaya min ba” yace “I am serious mum” ta nuna masa kofa tace “Toh fita” ba musu ya juya ya fita ya
kullo mata kofarta, ta cije yatsa, murya can kasa tace “Dole ma kawai abun nan ya tabbata, in sha Allahu sae auren
nan ya tabbata kwanan nan ba da dadewa ba” tana fadin haka ta shige dakinta xata kira Salima. Kaka nata goge
gogen windown dakinta sae da taga yyi fess ta juyo tana kallon Baffa dake xaune parlon tare da Abba tace “Idan na
barsa ban karasa ba sae shaidan ya mantar da ni, kunga haka kuma bbu kyau, tunda bbu me taimakona sae Allah, ‘ya
yanku dama sae dai su shigo su xagi iyayena su fita” tana kai wa nan ta xauna tace “Wata kullalliyar kuma ku ka
kulla xa a sanar min yanxu?” Baffa yyi dariya yace “Aa bbu, shawara muka xo nema…” Tace “To ina jin ku” Baffa
yace “Ya kika ga idan aka ce xa a nema ma Shuraim auren Heedayah gun iyayenta?” Kaka tayi shiru tana kallonsu
kamar ranan ta fara ganinsu, can tayi mitsi mitsi da ido tana kallon Ac dake dakin kamar me naxari tace “Waye
kuma Shureen?” Duk suka yi shiru suna kallonta, tace “Aa ba batun wasa ba, don Allah ku sanar min waye Shureen
din?” Nan ma bbu wanda yace komai, a fusace tace “To ni nasan wani Shureen ne? ba sai ayi min bayani ba duk kun
wani min shiru, idan baxa a sanar min waye shi ba ku fita ku bani waje in ci gaba da tsaftace dakina ni dai” Baffa
yace “Aliyu” kaka ta hade rai tace “Ban gane Shureen ba sai wani Aliyu, ko dai wiwi ku ka sha kafin ku shigo min,
nifa kar a dinga damuna, ku min bayani filla filla yanda xan fahimta, idan kuwa kunbiya kunbiya za ku min ku fita”
Baffa ya nuna Abba yace “Shuraim din Ahmad….” Kaka ta bude baki a hankali tace “Shureen din Ahmad kuma???
Ashe da gaske shi din ne ku ke nufi xuciyata taki amincewa….. To wiwi ku ka dirka halan ku ka ga hada Deedayah
da Shureen ya dace” Abba dai TV kawai yake kallo, kaka ta mike tsam tace “Toh wllh bbu ruwana da wnn
konanniyar shawarar taku duk kauri, a rasa wanda xa a ace xa a ba Deedayah sae Shureen, yaron da har yau uban da
ya haifesa bai san xuciyarsa ba balle mu karere, to wai ma ina Deedayah xata kai gantsamemen Mutumin nan, anya
kuna tsoron Allah kuwa Amadu, snn ko kakanninku ba a masu auren dole ba balle Deedayah…. To ba ruwana,
Shureen kuma da tuntuni nayi masa mata yar gidan Rakiya ai maganar na nan bata mutu ba lkci kawai ake jira, ashe
kuma dai kwadayayyu ne ban sani ba, daga ganin ubanta gwamna ne sai ku fara kokarin makala mata d’an ku da
bashi da tarbiya bashi da kirki” A tare Abba da Baffa suka kalleta, Baffa yace “Subhanallah” Kaka ta zare masa ido tace “Ehh din, ba kwadayin bane ke dawainiya da ku xaka ce min Subhanallahi…. Mutumin da ko xo bai ta6a hadasa
da Deedayah ba balle tafi xaku wani ce a aura masa ita, duk fa ina lura da komai ni ba Mahaukaciya bace, takama da
ya dinga nuna mata cewar gidan ubansa take duk ina lura, to meye kuma daga ganin uban yarinya babban mutum ne
sai a nemi makala mata sangamemen mutum, to ya xata yi da shi fisabilillahi jama’ah??” Mikewa Abba yyi yace
“Sae da safe” tace “Allah ya tashe mu lfya” daga haka yyi ficewarsa daga parlon, Baffa yace “Haba kaka….” Kaka ta
tsuke fuska tace “Kai… Kai ma sae da safe na sallame ka” mikewa yyi ya nufi kofa tace “Ko kun mance ni yar
gaskiya ce, Kai ni ko da ma suna son junansu baxan yarda wnn katon ya aureta ba, ya xata yi da shi mutum
gantsameme haka gashi soja yaje ya hallaka yar mutane mu shiga uku, balle ma bashi da hali kwata kwata wllh,
yaushe rabon ya xo yyi min gaisuwar mutunci har na manta, to ni nasan inda Amadu yaje ya samo sa ya xama d’an
sa duk da shi ma Amadun haka yake ai” Ranan Monday Ammin Heedayah da Abbanta suka koma Abuja leaving
Heedayah with Mami don Mami tace masu sun yi resuming boko, Ammi felt as if kara rabata xa ayi da Heedayah
but ko kadan bata nuna haka ba ta danne xuciyarta sosai, amma har ranta ta so su tafi da Heedayah a sata a wani
makarantar a can Abuja, she had no other alternative then to leave her behind suka wuce da Abbanta. Heedayah na
hada abubuwan da xata koma makaranta da shi don gobe xa su koma da yamma, Farida ma na dakin amma tana
kwance tana danna wayarta, Heedayah ta karasa kulle jakarta tana kallon Farida tace “In dafa Indomie din da ke?”
Farida dake kallon screen din wayarta tace “Noo” Heedayah bata ce komai ba ta juya ta fita dakin, karfe sha daya
saura ne na safe, su biyu kawai ne gidan don Mami ta fita office amma tace ba dadewa xata yi ba daga can ma xata
yi masu shopping, Heedayah ta gama dafa Indomien tana xuba masu a different plate ita da Farida duk da tace
baxata ci ba amma har ita ta dafa, taji kamshin turare ya cika hancinta, juyowa tayi da sauri suka yi ido hudu bata
san lkcn da ta saki tukunyar hannunta ba a rikice, sauran Indomien ciki ya xube kan gas, ya karasa cikin kitchen din
da sauri ya janyeta daga wajen yace “Are you okay” Jikinta ya dau rawa tace “Noo” gaba daya ta rude, kallonta
kawai yake, can ya daure fuska yace “Dodon ki ne ni?” Da sauri ta girgixa masa kai, yace “Toh meye kika xubar da
Indomie daga ganina” kamar xata yi kuka tace “Tsorata nayi” ya dau plate din Indomie da ta fara xubawa ya mika
mata, amsa tayi bata yrda ta kallesa ba, yace “Ina farida?” Tace “Tana sama” Farida ce ta shigo kitchen din waya
kare kunnenta a dai dai lkcn, dakatawa tayi da farko bayan sun hada ido da Shuraim, Can ta mika ma Heedayah
wayar tace “Mami wants to talk to you” Karba Heedayah tayi ta kai kunne a hankali tace “Ina ji Mami” Mami tace
“Ku shirya yanxu, Shuraim is on his way, xai ajiye ku gidan Baffa ku yi ma kaka sallama sai ya maido ku gida”
Heedayah tace “Toh” Mami ta katse wayar, Heedayah ta mika ma Farida ta amsa ta fice daga kitchen din, Heedayah
bata yrda ta hada ido da Shuraim ba ta ajiye Indomien xata fita yace “Dauka ki wuce ki ci” dauka tayi ta nufi kofa ta
fita ya bi bayanta, daki ta kai ta ajiye don taji ya ma fita ranta gaba daya, Ganin Farida a kwance tace “Ke baxa ki
ba” Farida tace “Ehh” Shiru tayi tana kallonta, can tace “Toh ai Mami cewa tayi ni da ke” Farida tace “Na kirata
yanxu nace baxan iya xuwa ba so kiyi tafiyar ki, I am having cramps” Heedayah ta bata fuska tace “Toh ni kadai xan
je?” Farida tace “Ga dai wanda ya xo tafiya da ke kice ke kadai, I tot u will like following him ai” Heedayah bata
tanka ta ba ta sa Hijab dinta ta fita, Ganin Shuraim baya parlor ta karasa waje, cikin mota ta samesa xaune waya kare
kunnensa, ganinta ya katse wayar yana kallonta yace “Ina faridan?” Heedayah bata kallesa ba tace “She said she is
not going” yace “Har kin ci abincin?” Tace “Uhm” bude front seat tayi ta shiga ta kulle, tada motar yyi suka bar layin
sai da suka dau hanya yace “Let me ask you” Heedayah ta d’an yi shiru sai taji kamar ba da ita yake ba, can ta juya
suka hada ido ta dauke idonta da sauri, yace “Tsoron me kike min?” Ta ki cewa komai, yace “What if kika ganmu
gida daya, daki daya, ya xa ki yi ranan?” Lkci daya ta d’an xaro ido, sai kuma tace “Ae hakan ma baxai ta6a faruwa
ba” Wani murmushi yyi bai ce komai ba, ta kallesa tana imagining dama ashe ya iya murmushi, can yace “Haka kike
gani?” 6ata fuska tayi tace “Eh mana ta ya xamu ganmu daki daya?” Yace “Xan nuna maki ta taya ranan” Sosai taji
gabanta ya fadi, hakan yasa bata kuma ce masa komai ba, shi ma bai ce komai ba har suka isa gidan Baffa, ta bude
motar ta sauka ta wuce ciki ya jinginar da kansa da kujeran motar ya bi ta da kallo. kaka tace “Ya naga ranki a bace
kamar wani ya cuce ki, sannan waye ya kawo ki?” Kin cewa komai Heedayah tayi tana xaune kan kujera aka bude
kofar dakin Shuraim ya shigo, kaka tace “Waye wnn kuma, me ya hada tafiyarki da shi ni Patuu” Heedayah taki
cewa komai, Kaka tace “Aniyar Amadu da Umaru dai ya bi su, meye kuma na hadaki da Shureen ya kawo ki wajena,
akwai wani abinda ya hadaku da shine ban sani ba” Shuraim yace “Xa ki sani kwanan nan” Kaka tace “Ni dai ba
ruwana, ni ban ma ta6a ganin inda aka bar Soja cikin gari yyi ta gantali ba a aikasa daji yaje yayi yaki da ‘yan
ta’adda ba” Shuraim yyi murmushi ya shafa kansa yace “Ke ma ai ‘yar ta’adda ce dole in tsaya kusa don in dinga
maganin ki” Shiru kaka tayi tana kallonsa, can ta xauna saman kujera tana matsar kwalla, yana kallon Heedayah
yace “Meet me at the car” daga haka ya juya yyi ficewarsa ta bi sa da harara da murguda baki, kaka dai na xaune
tana ta matsar kwalla ance mata yar ta’adda, Cikin dubara Heedayah ta dau wayarta ta fice daga dakin, duk ranan
basu yi magana da Khaleel ba, da yake da wayar Farida take kiransa kuma ganin duk yau Farida bata sake mata ba
yasa bata ma tambayeta wayar nata ba…. Can dakinsu Zainab ta shiga ta rufe snn tayi dialing number sa, sai da ya
kusa katsewa ya daga, murya can kasa tace “Ya Khaleel” Jin muryarta yace “Yau kin mance ni, ina ta tunanin ki….
let me call you back” daga haka ya katse wayar ya sake kiranta, tana dagawa yace “Tell me first, me Ummi ta fi so?” Heedayah ta wara ido tace “Wai Mamin mu?” Yyi kasa da murya yace “Nima Mamina ce ai ko?” Dariya Heedayah
tayi tace “Sure, Mami tana son Apples sosai, with grapes, and tana son hanta gasasshe….”