HEEDAYA CHAPTER 42 BY By Khaleesat Haiydar
HEEDAYA CHAPTER 42 BY By Khaleesat Haiydar
Khaleel yace “Ohk…” Tace “Why do u ask” ya buda ido sosai yace “Nothing, I only want to know…. yau din xa ki
wuce schl?” Tace “Aa sai gobe, na xo yi ma Kaka sallama” yace “Ke da wa?” Tace “Ni da ya Shureen” yyi shiru, sai
kuma a hankali yace “Me yasa kike son bin sa, why not Junaid?” Tace “Ya Junaid ya tafi aiki ai shi” Yace “Shi
Shuraim din baya aiki?” Tace “Da safe yake dawowa, he is a military Dr” Khaleel yace “Uhn I see….” Tace “Xaka
xo ne anjima?” Yace “Probably” tace “Probably? Baxa ka xo ba bayan gobe xan wuce schl” kamar xata yi kuka ta
kare maganar, yace “Xan xo” a hankali tace “Toh sai ka xo” yace “In sha Allah” yyi kasa da murya yace “Tell me
Heedayah, who is ur first love?” Dariya tayi tace “Yar yarinya da ni? I don’t love” Yace “Uhm ko?” Tace “Ehh mana,
baka gan ni yar karama ba” yace “How old are you?” Tace “Soon xan yi clocking 17…” Shiru yyi, can yace “Can u
marry someone 2 times ur age?” Dariya tayi tace “Aa nima ban sani ba” Yace “Uhm to shkkn, sai na xo anjima, ana
kirana yanxu a waya” duk sai bata ji dadi xai katse wayar ba, a hankali tace “Ohk bye” yace “Take care of ur self
pls” tace “And you too” ya gyada mata kai kamar tana ganinsa yana murmushi, daga haka ya katse wayar. K’in fita
Heedayah tayi daga dakin su Zainab don ta sa a ranta baxata bi Shuraim ba, she is finding it hard to withstand the
sight of him, daga karshe kawai ta tafi dakin mum din Zainab ta gaisheta ta koma dakinsu Zainab ta sa makulli tayi
Kwanciyarta hankali kwance. Da yamma tana dakin Hajiya Hauwa tare da Zainab da dawowarta makaranta kenan
kaka ta leko dakin tana kallon Heedayah, tayi kasa da murya tace “Wllh naji dadin yanda kika tafi kika boye abinki
ya gama jiransa kamar debabbe ya wuce, kawai mutum ba tsoron Allah naga kamar sai wani makale maki yake, ni
dai ba ruwana, ga abinci can na ajiye maki a daki” Hajiya Hauwa tayi dariya tace “Ta ma ci abinci a nan” Kaka tace
“Atoh, idan ya kama anjima ni da kaina sai in mayar da ita gida, waye kuma Shureen Allah na tuba, d’an banxan
yaro me mugun hali” daga haka tayi ficewarta, sai kusan Magrib Heedayah ta shigo dakin kaka, Xaune ta tadda kaka
da junaid kaka na masa hira, Ta wara ido ganinsa ta tafi ta xauna kasa tana kallonsa tace “Yaya… ” Kaka tace “Ai
yanxu xan tafi in kira ki dama, wai Rakiya tace ya xo ya tafi da ke gida, kinsan shima ya lalace yanxu baya gaida mutane” Junaid dai murmushi kawai yyi yana shafa kansa, kaka tace “Kuma naga duk ya rame kamar yana tare da
damuwa na tambayesa meye ya ki gaya min, to ya sani ko ina da abinda xan masa in taimaka masa??” Junaid dai bai
ce komai ba, Heedayah ta mike ta dau jakarta, Junaid ya mike shi ma yace “Toh sae da safe kaka” sabulu kwara uku
da soyayyen nama a leda daban ta ba Heedayah tace “Babu komai a dakin, duk an bar ni a gantale nace su bar ni in
fara sana’a ko ta Maggi ce da manja sun ki gashi ni basu dauke min lalurorina ba” Dariya Heedayah tayi, Junaid ya
fiddo dubu ukun aljihunsa ya mika ma kaka yace “Ba kudi wajena kaka, gobe xan shigo in sha Allah” Kaka ta amsa
tana wani murmushi tace “Allah yyi maka albarka, gobe ka dawo mu yi magana da kai, tunda ita Rakiya bata gane
kana da damuwa ba ni na gane, idan ma baka xo goben ba sai in iya biyo ka har gida” da sauri yace “Aa xan xo
kaka” tace “Toh ina saurarenka, bari in je Hauwa ta sama mana canji in ba Deedayah ko dari biyu ne ta siyi abu a
hanya” Junaid yace “Aa xan bata a madadin ki” Kaka tace “Toh Allah yyi maka albarka” daga haka suka fita dakin
tare da Heedayah da tayi mata sai da safe ta bi bayansa, a hankali Junaid ke driving, can yayi kasa da murya without
looking at Heedayah yace “Tell me…. a ina kika san Khaleel din nan Heedayah?” Heedayah ta d’an yi shiru, sae
kuma tace “Ban san sa ba, shine dai kawai yace min ya san ni, but his voice sounds familiar, na ta6a jin muryarsa”
Junaid yace “A ina kika ta6a jin muryar tasa?” Ta d’an yi shiru sai kuma tace “When I was unsighted” Junaid ya
kalleta da mamaki yace “Where precisely?” Ta buda masa hannu alamar bata sani ba, yace “No, ki tuna inda kika
ta6a jin muryar tasa now” Heedayah tayi shiru, sai kuma tace “But I seriously can’t remember, I have tried hard”
Yace “You just have to, when u where unsighted ai ba fita kike ba, you are home always to a ina kika san muryar
tasa” Bayan wani lkci ta girgixa kai tace “I can’t remember” Bai kuma ce mata komai ba har suka isa gida, ta ga
motar Khaleel a waje, a tare suka shiga parlon da Junaid, Junaid ya ba Khaleel hannu suka gaisa ya gaida Mami
dake parlon ita ma snn ya wuce sama, Heedayah ta gaida Mami ta gaishesa ita ma ta wuce sama. Mikewa Khaleel
yyi sbda kiran wayarsa da Zayyad ke ta yi tun shigowarsa parlorn not less then 15mins ago yana kallon Mami yace
“Let me answer a phone call” Mami tace “Alright dear” kofa ya nufa ya fita ya tafi can kan daya daga kujerun dake
ajiye a compound din with round table ya xauna, snn ya daga kiran yyi shiru, Zayyad yace “Khaleel why are u
behaving anyhow this days, I really don’t want u to get into problem, I get u are newly in love now, but ka dinga
controlling kanka pls, Nobody is stopping you from loving” Khaleel dake ta sauraronsa yace “Wnn shine dalilin
kiran da kake ta yi min haka Zayyad?” Zayyad yace “No!! me yasa Oga Arne ke kiranka baka daga kiransa? First u
spoilt the show of kidnapping Alhaji Ahmad, secondly….” Khaleel ya dakatar da shi calmly yace “Wnn ya fi karfin
ku yi kidnapping dinsa when I am alive and breathing” Zayyad yace “See you, ka dai san some big leaders gat our
back Khaleel, you like it or not dole ne sai an yi kidnapping wnn mutumin kafin xabe ya gabato” Khaleel yace
“Then we shall see” Zayyad yace “Duk wnn ma ba shi ne ba, coz they are still planning on it, the main issue in here
is that why… ka ki fitowa operation shekaranjiya bayan san sanar da kai, meeting din ma kuma da aka kira baka xo
ba” Khaleel yace “Na ce masu I need rest, and seriously I need that rest, ko basu yadda da abinda nace masu
bane….” Zayyad yace “What nonsense, rest din sati nawa, wllh Brainiac ka bi a hankali suna watching every
movement dinka without you knowing, ni kaina I just noticed ba wai gaya min aka yi ba, ka ma san bbu wanda xai
gaya min, and you know what… da matsalar iya kai xai tsaya ma da sauki, they are seeing it as bakinmu daya da kai,
to ni yaushe rabon mu hadu yanxu, 24/7 kana kwance gida daga waya da yarinya sai xuwa wajen yarinya, ni
damuwata a nan wani riba kake ga xaka ci dating that teenager da ko hannunta naga baka rikewa, meye mamorarta?
ka xo ga manyan babes a gari in jonaku amma ka ki ka makale ma yarinyar da there is nothing to write home about,
sannan mind you, wllh gidan wnn innocent barristern da kake xuwa xa su iya tracing su je can kuma kasan abinda
xai iya faruwa” lkci daya jikin Khaleel da yyi shiru yana sauraron Zayyad yyi sanyi, Zayyad yace “And nima kana ja
min matsala ne da damuwa gunsu, suna ganin komai da kake yi har da hadin bakina nasan komai, Oga Manga Vow
to have ur legs shoot yanda xaka xauna waje daya tare da su” Khaleel dai bai ce masa komai ba, Zayyad yyi kasa da
murya yace “Wllh Khaleel tun da ka koma gefe ka wani yi isolating kanka abubuwa suka daina tafiya smoothly,
operations are always not successful this days, sae ynxu su kansu suke sanin you mean a lot, don Allah ka tsayar da
hankalin ka gu daya, no one is stopping you from dating that little girl da ka haifa a haihuwar kaji amma ka daina
wasa da sana’arka, snn kar ka xama butulu Oga Arne bai yi deserving haka daga gare ka ba, Kuma ka fa san irin
yanda yake sonka yake ji da kai” Ganin Heedayah na tahowa da tray me dauke da drink da ruwa Khaleel ya katse
wayar ya sa a flight mode cikin few seconds, ta karaso ta ajiye tray din a table tana kallonsa a hankali tace “Are you
okay?” Ya kirkiri murmushi ya shafa beard dinsa yace “Sure” Xaunawa tayi tace “Mami tace in kawo maka ruwa”
yyi kasa da murya yace “Thank you” shiru ne ya biyo baya, ta bude drink din ta debar masa a glass cup, a hankali ta
ji yace “Wani class kike yanxu Heedayah?” Tace “Ss1 3rd term xamu fara yanxu, sai in shiga ss2 a nan xan rubuta
waec” Shiru yyi yana kallonta, can yace “You know what Heedayah?” Ta girgixa masa kai, a hankali yace “I have
left a lot of me because of you…. Saboda ke naji I might just have to give up on many things….” Ta katse sa tace
“Like?” Yyi shiru, can yace “My personality, who I am.. and so on, I don’t know how that is going to be…. But
promise me Heedayah, no matter any circumstance, no matter the up and downs, no matter the situation kar ki guje
ni don Allah” Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa bbu, ya ci gaba cikin sanyin murya yace “I don’t know why I am having this feeling kamar xaki gujeni soon, very soon xa ki gujeni Heedayah” Lkci daya jikin Heedayah yyi sanyi
tace “Me yasa kake tunanin haka, me ka min da xan guje ka? Meyasa kake ga xan guje ka?” Ya lumshe ido ya bude
a sanyaye yace “sbda wani dalili da ya kamata ki gujeni din, you just have to leave me for that reason, but plss don’t
Heedayah, idan kika gujeni I don’t know what will become of me, don’t forget I have nobody, I know nobody, and I
don’t know the love of family” ta girgixa masa kai in an assuring state tace “Ni baxan guje ka ba sai dai in kai xaka
gujeni” yace “Make me that promise Heedayah” shiru tayi tana kallonsa gaba daya jikinta yyi sanyi ne, ta sauke
idonta kasa, bayan few seconds tace “I promise” Murya can kasa yace “Nagode Heedayah” ta sakar masa murmushi
bata ce komai ba, yace “Yaushe ake xuwa maku visiting a schl?” Tace “Anytime if we are free ana barin mu” yace
“Alright, may be next week xan wuce Holland, I need rest, much rest” tayi shiru sai kuma tace “Yaushe xaka dawo?”
Yace “Tunda kina makaranta sai idan kun yi hutu, that is after ur waec” a sanyaye tace “You will be away for almost
a year?” Ya gyada mata kai, ta sauke idonta kasa tace “But I am going to miss you” yace “I will too, but I have to go
so you will concentrate on ur studies, ranan da aka gama waec xa ki gan ni idan Allah ya yrda” Bata iya ta ce masa
komai ba, kamar yanda yyi shiru shi ma a ransa kuwa yana tunanin idan yyi nisa da Nigeria for that period of time
oganninsa xa su basa breathing space, he will have rest of mind, yasan ko da Heedayah na makaranta xai ce sai ya
xo ya gaida Mami don har ransa yake jin matar, he can’t resist coming to her, kuma kamar yanda Zayyad yace yasan
ba wani abu me wahala bane gun su Manga suyi tracing dinsa din su gano gidan, kiran da Zayyad ke tayi masa duk
da wayar a total silent yake ya sa yyi ma Heedayah sallama, ita dai bata iya tace masa komai ba, ya sa hannu a
aljihunsa ya ciro kudi me yawa without thinking twice ya kamo hannunta ya saka kudin, ta wani xaro ido yace “This
is my own sweat not Haram Heedayah, it’s all I have got (Halal)” gaba daya yyi confusing dinta kafin kuma tace
komai yace “Till after a year in sha Allah Heedayah, do not try to forget me even for a second during the year
Heedayah, I will think of you till the last day of 365 days to come in sha Allah, kice ma Mami na tafi, I appreciate
her love and kindness toward me, kuma ta dinga saka ni a addu’arta don bani da me yi min” Daga haka ya sake
hannunta ya nufi gate, ta bi sa da ido ko kiftawa bbu, hawaye ne ya gangaro idonta…. Mumy ce tare da Salima da
Sadiya a gun Mutumin da Salima tace xata kai su, a wani d’an karamin kauye a garin Kaduna Mutumin yake, tafiyar
kusan awa uku ne kuma ya kai su gun Mutumin, mata biyar suka tarar a gabansu, duk manyan mata, suna xaune
suna jiran turn din shigarsu, Mumy tace “Na samu labarin yau Heedayah ta koma makaranta gaba daya, kun ga
kuma idan ta tafi nasan sai candy xata dawo gida, yau da safe ina jin Barrister da d’an uwansa suna tattaunawa a
waya amma bai san I was eavesdropping ba, wai tunda uwarsu ta nuna bata son auren toh baxa a sake tada maganar
ba, ni yanxu duk ba wnn ba, ku fada min ya xa ayi da wnn tsohuwar dake neman kawo mana cikas?” Salima tace
“Ita wnn tana da wani alkibla ne dama, tsohuwar da ko dubu biyar kika ajiye gabanta xata canxa xance, duk ba wnn
ba matsalar ina ga fa daga Shuraim xai fito, don banga alamar yana son yarinyar nan ba, baya yinta ko kadan, abinda
kawai ya kamata ayi shine a daura masa mugun sonta ynda xai birkice ma Ubannin nasa da ita kanta Kakar yace shi
dai sai Heedayah, kinsan duk da suna ‘yar tsama ta fi sonsa cikin jikokinta idan kuwa taga ya birkice kinsan dole ta
amince bbu bata lkci, snn tunda Barrister yace a bar xancen kinsan baya magana biyu, wllh ya bar batun auren kenan
har abada, don haka idan Shuraim yaji mahaukacin son yarinyar na neman yi masa illa to wllh lkcn da xai je gun
uban yarinyar da kansa a Abuja yace shi ita yake so ma baxai sani ba, kuma uban yarinyar baxai ta6a cewa Aa ba
sbda hallacin da Barrister yyi masa, xai kuma so hada wnn auren ko don ya nuna appreciation… Toh daga baya ana
auren sai a warware sihirin Shuraim ya dawo dai dai ya fara cin uban yarinyar cikin ruwan sanyi” Mumy ta dinga
mata wani shegen kallo tace “Idan kuma bai daina son nata ba fa?” Sadiya tace “Matsalar ki kenan dama, tunda aka
iya sa ya so ta don abubuwa su tafi dai dai ai bbu abinda xai sa a kasa warware son, asiri ne fa Maryam…” Salima
tace “Rabu da ita mana, ae rashin daukan shawarar ne ke cutarta, ga dai abu cikin sauki ayi a wuce wajen, in dai ba
tsinanne ne uban yarinyar ba ai baxai hana Shuraim yar sa ba bayan halaccin da uban Shuraim din yyi masa, ni
kinga Yaya duk abinda muka ce maki kawai kice to, don ke baki da wani shawara da tunanin kirki sae rudewa kamar
tsohuwa” Mumy dai tayi shiru, can tace “Toh ai fa yanxu yarinyar ta koma makaranta nace maku” Sadiya tace
“Baxata gama bane, mu dai ba dai kawai shiri kawai xa mu fara ba, kamar gobe ne xaki ga har ta gama fa” Mumy
tace “Balle ma naji Barrister na cewa ta kusa xana waec” Salima tace “Yauwa to kinga” A haka suka yi ta tattaunawa
har layi ya xo kansu suka shiga gun Mutumin a ‘yar bukkarsa. Kaka ce xaune parlon Baffa dake ta kallonta da
mamaki, ta ci gaba da abinda take cewa hankalinta kwance “Shine nace in xo in sanar maku kada ku ce na raina ku”
Baffa yace “Haba Kaka yaushe suka koma har xa ki bi su” kaka tace “Toh wai ce maka nayi xuwa xan yi in ja6e
masu, magana fa mai muhimmanci ne xai kai ni, karewa ma da wnn yaro Junaid xa mu, shi xai rakani kuma mu
dawo tare, a motarsa ma xamu tafi” Baffa dai ya rasa abun cewa, Kaka tace “Ni bance lallai ku bani ko sisi ba junaid
xai kai ni ya dawo da ni kuma wllh wllh kwana biyu kacal xan yi” Baffa yace “Toh shkkn, Allah ya kiyaye hanya” ta
mike tace “Ameen” daga haka ta nufi kofa yace “Xan tura ma Junaid din kudi da xai baki” Ko tankasa bata yi ba ta
kara gaba. Shiru Mami tayi tana kallon Heedayah da take ta kokarin ganin hawayen dake kawowa idonta bai sakko
ba, a hankali Mami tace “Ina yace maki xai tafi?” Heedayah tayi kasa da murya tace “Holland” Mami tace “Toh
Allah ubangiji ya tsare sa ya basa abinda ya je nema can din, amma da ya tsaya ai mu yi sallama” cikin sanyin murya Heedayah tace “Yace ki dinga yi masa addu’a bashi da me yi masa” Mami bata ce komai ba sai dai gabanta
faduwa yake ta rasa dalili, Heedayah ta mika ma Mami kudin da ya bata dake cikin Hijab tace “He gave me this, and
I couldn’t say no” Mami ta dinga kallon kudin tace “You shouldn’t have collect it” tace “Kiyi hakuri Mami, he didn’t
allow me to say anything” Mami tayi shiru… Dubu talatin ne kudin da Khaleel ya bata sai dai kalmar da ya fada
mata a yayin bata kudin ya tsaya mata sosai “It’s all the Halal he have got, it’s his own sweat not Haram… How is
that??” Washegari before leaving for Lagos don a can xai yi boarding flight da xai bar kasar Khaleel ya dauko daya
daga many sims dinsa da yake amfani da shi only if the need arises, ya dau number Mahaifin Heedayah da suka yi
exchanging daga wayarsa ya shiga rubuta masa text kamar haka….. After sending the text ya kashe wayar ya cire sim
card din ya balle ya jefar nan kasan lafiyayyen dakinsa ya dau jakarsa ya fita dakin.
1 year few days later