HEEDAYA CHAPTER 46 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 46 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Heedayah dai taki yarda ta dago kanta, Mami tace “Wai baxa ki bani amsa ba?” Ta dago a hankali tace “Mami nace 

ba komai, kaina ne ke min ciwo” Mami ta hade rai tace “Ciwon kan yasa kika yi kuka har idonki ya kumbura?” 

Heedayah ta marairaice tace “Yayi min sauki ynxu Mami, ask Farida” Farida dai na xaune can karshen gado tana 

danna wayarta bata ce masu komai ba, Mami tace “Toh yayi kyau, keep on lying, and why did you change your 

mind about going to kano with them?” Heedayah tayi kasa da murya tace “Mami sati daya xan yi in dawo in sha 

Allah, kawai dai ina son in je” Mami dai bata kuma ce mata komai ba ta fita dakin, Heedayah ta goge guntun 

hawayen idonta, Farida ta mike ta dawo kusa da ita tace “Heedayah me yasa baki son gaya ma Mami, why are you 

hiding this serious issue from her” Heedayah ta kalleta bata ce komai ba, Farida tace “It’s better ki gaya mata, kinga 

she likes the guy, gwara ta sani tun wuri wllh, damuwata daya yanxu ya san gidanmu, I don’t think we are safe 

anymore” kamar xata yi kuka ta kare maganar, Heedayah na ci gaba da share idonta tace “Tun da ya san na sani 

ynxu baxai sake xuwa nan ba, and just watch and see” Farida tayi mata wani kallo tace “Wa yace maki?? Mutumin 

dake son ki, snn sbda son da yake maki har ya tona ma kansa asiri ya gaya maki shi wanene, ae wlh baxai ta6a daina 

bibbiyar ki ba, tafiyar ki kano shine kadae mafita gare ki” Heedayah tace “Wait Farida, is he even crazy to come 

back bayan ya riga yasan na san komai a kan sa ynxu??” Farida tace “Ke baki san so ba ko?? Wllh ko xaki tona 

masa asiri in dai yana son ki da gaske baxai daina bibiyar ki ba” Heedayah ta hade rai tace “Then he will be playing 

with fire, I will have to expose him to everyone” Farida tace “Exactly Heedayah, yanxu ki tashi mu je ki sanar ma 

Mami first…” Heedayah tayi shiru lkci daya hawaye ya kawo idonta, Farida ta mike ta kamo hannunta, xame 

hannunta tayi cikin sanyi tace “Baxan iya ba Farida, kawai let just leave him, I don’t want anything to happen to him 

ta dalilina, ni nasan baxai ma sake dawowa ba” Farida tayi shiru tana kallonta. Mami ce tsaye dakin da Yakumbo ke 

ciki tana xuge handbag dinta tace “Toh ni yanxu wa xai kai ni can gidan lauyan??” Mami tace “Driver xai ajiye ku 

yanxu” Yakumbo tace “Ya san gidan ne?” Mami tace “Aa tare da Heedayah xa ku je” Yakumbo tace “Toh ni dai 

Allah ya rufa mana asiri kada tafiyar nan ya sha ruwa yau, ita Aisha na can tana xaga Kaduna da sojoji bata da 

niyyar dawowa, komai dai sai an bata ma mutum rai, amma ba laifin kowa bane laifin Amadi ne” Mami dai bata ce 

komai ba ta fita su Ashfah da suka makale mata na biye da ita, bbu abinda suka mance na Heedayah yaran kawai dai 

ta fi su haske, dakinsu farida Mami ta shiga, Mami na kallon Heedayah tace “Idan kin ga dama kin gama kukan 

iskancin naki sai ki shirya ki raka Yakumbo gidan Abban ki….” Da sauri Heedayah ta juyo tana kallonta tace “Gidan 

Abba kuma, Ba yanxu xa mu tafi ba Mami?” Mami tace “Wannan kuma ban sani ba” Heedayah tayi shiru, Mami ta 

juya ta fita dakin, Bata fuska Heedayah tayi ta rungume hannu, Farida dai na tsaye jikin window tana kallonta, 

bayan minti kusan goma Yakumbo ta leko dakin tace “Toh ni dai idan baxa ki je ba ai sai yar uwarki ta xo ta rakani, 

bbu ruwana da wahala…” Heedayah ta kalli Farida tace “Farida ki rakata ni kaina ciwo yake min wllh” Yakumbo ta 

rike ha6a tace “Ga dukkan alama Rahinah ta sangarta ki, kuma wnn wlh ba halin xaman gidan miji bane, kaji min 

fitsararriyar yarinya kawai” Heedayah bata ce mata komai ba, Yakumbo na kallon Farida tace “Kinga shirya ki 

rakani kin ji yar nan” Farida tace “Toh” Yakumbo ta fice daga dakin ta koma gun Mami, Mami tace “Baxa ki ci 

abincin ba kafin ki tafi?” Yakumbo tace “Kyaleni da abincin nan ke dai, amma a gaskiya wnn Heedayar taki bata da 

hali ko kadan, ga rashin kunya fal cikinta, wai yarinyar ta dubi tsabagen idona tace ita baxata ba sai dai Farida ta kai 

ni, irin tarbiyar da kika mata kenan??” Mami tace “Kiyi hakuri bata jin dadi ne, amma dole ma xata bi ki” Yakumbo 

tace “Aa ba ruwana, ta sha xamanta ni Faridar ma ta fi min sau dubu” Mami ta fita dakin ta koma dakinsu Farida, 

fuska daure tana kallon Heedayah tace “Tashi ki shirya ki fito ku wuce” Heedayah ta mike bata ce komai ba ta tafi 

press dinsu ta bude ta fiddo hijab dinta har kasa, Farida ta bi bayan Mami bayan ta fita, parlor ta sameta tace “Mami 

can I go with them?” Mami tace “Kince kina da lectures by 2, but if you want to go, you can” Farida tace “Toh 

Mami” daga haka ta fita, Nikab Heedayah ta saka ta fito parlor tare da Farida, Yakumbo tace “Allah ya kiyaye, uban 

wa xa ki bi a haka?” Mami dake parlon ita ma a xaune tace “Da shi take fita Yakumbo” Yakumbo tace “Toh ai ba da 

shi na ganta jiya a gun taron ba, Kai ni fa idan ma xata ce ba nice yar ubanta ba bbu abinda ya sha min kai” da 

turanci Mami tace ma Heedayah ta tafi ta cire Nikab din, ba musu Heedayah ta koma ta cire snn ta dawo, gaba daya 

bata da walwala, motar sojoji guda ne a layin tun xuwan su Amminta gidan Mami jiya, Heedayah dai na xaune 

bayan mota tare da Yakumbo, Farida kuma ta shiga gaba suka bar layin. Suna isa gidan Abba mai gadi ya bude masu gate, driver ya shigar da motar yyi parking, Heedayah ta sauka snn Farida, Yakumbo ma ta sauka tayi hanyar cikin 

gidan suna biye da ita… Mumy ta fito daga kitchen kenan suka shigo parlon, ganinsu ta baje fara’a a fuskarta tace 

“Sannun ku da xuwa” kallo daya Yakumbo tayi mata ta nufi kujera tana cewa “Ina patun take?” Mumy na ta 

murmushi ta karaso cikin parlon tace “Ta je gida, Amma yanxu xata dawo” Yakumbo tace “Ya mai jikin?” Mumy 

tace “Da sauki Alhmdllh, yana cikin daki, Heedayah rakata dakinsa” sosai Heedayah tayi mamakin abinda Mumy 

tace, ta dai gaisheta tare da Farida, Mumy ta amsa tana washe baki tace “Ki kai ta dakin Shuraim” mikewa Heedayah 

tayi ta nufi dakin Shuraim Yakumbo na biye da ita a baya, ta bude kofar dakin ta tsaya nan bakin kofa ta ki shiga, 

Yakumbo ta shige dakin tana kallon Shuraim dake kwance yyi rub da ciki yana bacci, he looks so sick and tired, 

Yakumbo tace “Toh kai kuma ya da kwanciyar ‘yan wuta, cuta ai ba mutuwa bace” Shuraim ya bude ido a hankali, 

ganinta tsaye dakin ya mike xaune da kyar, Yakumbo tace “Sannu, ya jikin?” Ya gyada mata kai yace “Da sauki, ina 

kwana?” Tace “Lafiya lau, me ke damun ka haka?” Murya can kasa yace “Na ji sauki” Ta xaro ido tace “A haka?? 

Toh Allah ya sauwake, amma wnn kam ai kana jin jiki….” Ya daga kai ya kalli Heedayah da ta ki shigowa har 

sannan, suna hada ido ta sauke kanta tace “Ya jiki” Bai amsa ba ya cire Duvet din jikinsa ya saukar da kafafuwansa 

kasa, Yakumbo tace “Tana maka ya jiki” ya daga kai ya kara kallonta yace “Fine” Yakumbo ta kyabe baki ta nufi 

kofa tana cewa “Ita ma ai bakin halin gareta” da sauri Heedayah ta bi bayanta bayan ta fita ta kullo masa kofarsa 

suka koma parlor, Mumy tuni ta ajiye ruwa da lemo har da abinci a kasa kusa da kujeran da Yakumbo ta fara xama, 

Yakumbo na kallon abincin tace “Aa mu mun ci abinci kafin mu fito, kamar dai ana yunwa” Tana fadin haka ta 

matsar da abincin gefe ta xauna tace “Me ke damun shi Aliyun haka?” Mumy tayi kasa da murya tace “Wllh bamu 

sani ba, ya ki fadi….” Yakumbo tace “Toh ba a je asibiti bane?” Mumy tace “Yayan Abbansa ya xo daxu yyi masa 

allura ma, toh shine yake ta bacci tun daxun, yana dai complain din ciwon kirji” Yakumbo tace “Toh Allah ya 

sauwake, ita patun yanxu xata dawo kuwa?” Mumy tace “Ehh taje yi masa girki ne kafin ya tashi wai, na ma ce ta 

barsa gashi nayi amma ta ki saurarata” Yakumbo tace “Toh ai da kince mana yana bacci da bamu tashe sa ba yyi 

baccinsa isasshe” Mumy dai sai murmushi take bata ce komai ba, Farida dai idonta na kan TV da gaba daya bata san 

abinda ake ba, Mumy ta mike ta wuce kitchen, ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da cup din shayi ta nufi Heedayah 

dake xaune ta mika mata tace “Tunda ya tashi gashi ki kai masa, tun safe bai ci komai ba, Allah ya sa ya sha wnn din 

ma” Heedayah ta d’an buda ido tana kallonta, ganin mika mata dai Mumy ke yi ta amsa ta kalli Farida dake kallonsu, 

Yakumbo tace “Toh ko baxa ki kai masa din bane tunda kunya bai isheki ba, sai Farida ta amsa kawai ta kai ita” 

Heedayah ta d’an hade rai ta mike ta nufi dakin, Farida ta bi ta da ido, a hankali ta bude kofar dakin tana kallon ciki, 

xaune ta gansa yanda suka barsa ya rike kansa da duk hannunsa biyu, jin an bude kofa ya dago sai dai bai kalli kofar 

ba, ta shigo dakin ta ki kulle kofar, kamar warce aka tilasta tafiyar ta isa inda yake xaune tace “Mumy tace in kawo 

maka” Jin yyi shiru ta durkusa ta ajiye masa cup din tea din, ta mike xata fita taji yace “Heedayah” tsayawa tayi 

amma bata juyo ba gabanta na faduwa, bayan few seconds ta juyo a hankali tana kallonsa…. Bayan tafiyarsu 

Heedayah kafin azahar Ammi ta dawo gidan, Mami na kallonta tace “Amma dai bbu tafiyar ta ku yau ko?” Ammi 

tace “Ehh wai Aliyu bashi da lafiya daxu Abbansu Islam ke gaya min, kuma Yakumbo ma taje can gidan ko?” Mami 

tace “Ehh tana can da su Heedayah” Ammi tace “Dole sai gobe kenan xa mu tafi, anjima daddare xan je dubasa idan 

Allah ya nufa” Mami tace “Allah ya kai mu, xan d’an fita in dawo yanxu Maman biyu” Ammi tace “Toh shhkn Allah 

ya tsare hanya” Hijab Mami ta sa har kasa ta dau wasu files Ashnaah ta fara kuka xata bi ta, Mami ta kama hannunta 

suka fita, Abba take son kai ma files office kamar yanda ya bukata, bayan tayi warming motarta ta fita gidan tare da 

Ashnaah dake xaune front seat…. Mami na fitowa daga layin, aka sauke glass din wata farar mota dake parke nesa 

da layin, Oga Manga ya kalli Zayyad dake gefensa cikin motar yace “Ita ce wancan?” Zayyad yace “Aa….” Wani 

naushi Manga ya kai masa yace “Ba matar nan muka tarar asibiti a Abuja ba??” Zayyad yyi shiru a ransa yana 

mamakin me yasa Khaleel yyi ignoring din message din da yyi passing masa ta waya da safe, Wani naushin Manga 

ya kai masa, Zayyad yace “Ita ce” tada motar Salim yyi suka bi hanyar da Mami ta bi a guje kafin Wani barrier ya 

shiga tsakaninsu, Mami na isa office din Abba tayi parking waje ta dau wayarta ta kirasa don ya fito ya amshi 

envelope din hannunta don baxata shiga ciki ba, Ashnaah dake xaune tace “I want to ease my self…” Mami ta kalleta 

tace “Ohk” daga haka ta bude motar ta sauka ta rufe ta xagayo ta inda take ta bude motar ta sakko da ita, A bayan 

motarta su Manga suka tsaya da tasu motar, duk da ta ga motar bata kawo komai ba ta xata client din Abba ne, 

Manga na kallon Fago yace “Kayi attacking yarinyar karama first….” Fago ya dira motar ya nufi Mami da ke daga 

kayan Ashnaah, lkci daya ya fiddo bindigarsa ya daura mata a kai yana kallonta da masked face dinsa, Xaro ido 

Mami tayi tana kallonsa kafin tace komai ya fixge Ashnaah daga hannunta xai koma motarsu ta bisa a rikice yana 

ganin haka ya bude motar ya jefa ma Manga Ashnaah, Manga na kallonta yace “Ki shigo idan kina son yar ki da 

rai….” Ai Mami bata san lkcn da ta shiga motar ba, ta shiga tashin hankalin da ya wuce misali, a rikice take cewa 

“Ku fadi abinda ku ke so daga gareni amma ku rufa min asiri kar ku tafi da ‘yar mutane…” tuni Fago ya rufe motar 

ya shige gaba Salim ya tada motar suka bar wajen a guje, Zayyad dai ya sunkuyar da kansa ya kasa dagowa, 

Ashnaah ta haye jikin Mami a tsorace tana kuka sosai don gaba daya fuskarsu a rufe yake, Mami ta rungumeta har 

ranta taji farin cikin ba Ashnaah kadai xa su tafi da ba har ita….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE