HEEDAYA CHAPTER 51 BY By Khaleesat Haiydar
HEEDAYA CHAPTER 51 BY By Khaleesat Haiydar
Mikewa Amira tayi ta bi bayan Mami da sauri, bedroom dinta ta sameta xaune gefen gado, ta karasa kusa da ita ta
xauna a hankali tace “Though it’s sad but bai kamata ki bar wajen ba Mami, u invited him here, so you are to listen
till the end” Kasa ce mata komai Mami tayi hawaye na xarya a idonta, Da damuwa Amira tace “Haba Mami sai kace
yau kika ta6a jin irin haka? This isn’t suppose to look new to you, kina fa cases wa enda suka fi haka ma ai” Mami ta
dafa kafadunta cikin raunin murya tace “Amira wnn Kidnapper din da kike gani yayanku ne” Da mamaki Amira ke
kallonta, da farko ta ma kasa cewa komai, can dai tace “Ban gane ba Mami, yayanmu ta Yaya? How is that?” Mami ta fashe da kuka sosai ta kasa bata amsa, Amira ta xaro ido tana kara naxarin labarin da Zayyad ke basu downstairs,
ja baya tayi with shock tace “Yayanmu kuma Mami?” Mami ta gyada mata kai amma ta kasa magana, kallonta
kawai Amira take da idanuwanta kamar xa su yi magana, cikin kuka Mami tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un…
da na sani da ban dage da addu’ar Allah ya sake hadani da Aliyu a nan duniya ba, da na sani da ban dinga wnn
addu’ar ba don gashi ban masa adalci ba ban ma kaina adalci ba, had I known addu’a ta garesa a ko da yaushe shine
Allah ya hada mu a darussalam ba nan duniya ba….” Amira ta fashe da kuka tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un,
Mami ya aka yi kika san yayanmu ne?? How is that even possible?” Bude kofar dakin aka yi Dinar ta shigo, tsaye
tayi bakin kofa tana kallonsu da mamaki, can ta karaso tace “Me ya faru Mami??” Jin Mami taki cewa komai Dina ta
xauna kusa da Amira tace “Ummi Hanan me ke faruwa?” Amira ta sakar mata kuka tace “Wai kiji mutumin nan
yayanmu ne in ji Mami” Xaro ido Dinar tayi tace “Yayanmu kuma? Wani mutumin a ciki? Yayanmu kamar yaya?”
Mikewa Mami tayi ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta dawo dakin ta debi tissue paper dake gaban mirror dinta ta
nufi kofa duk suka bi ta da kallo har ta fita, Dinar na kallon Amira cike da confusion tace “How is that? Meye
hadinmu da Kidnapper xa a ce yayanmu ne, yayanmu ta ina?” Amira ta buda hannu alamar bata sani ba hawaye na
sauka idonta, Dinar tace “Oh My God, I don’t understand this” Amira dai ba bakin magana, Dinar ta mike daga
karshe ta kamo hannunta tace “Mu koma parlon” Xaune suka tadda Mami a position dinta a parlon, Abba na kallonta
ganin yanda tayi wani sanyi har sannan tana hawaye sosai yace “Are you okay Rahinah?” Mami ta gyada masa kai
cike da karfin hali tace “Sure” Abba na kallon Zayyad yace “Go on pls…” Zayyad yace “Tun daga primary school
har junior Secondary position din Khaleel was always first, kuma har ya gama jss3 ba a ta6a fita operation da shi ba,
iyaka dai ana training tare da shi a cikin gida every weekend, tun yana shekara sha biyar ya xama perfect wajen
operating din bindiga ko wani iri ne, a sannan Arne Oganmu na yanxu kadai ne yyi supporting xuwan Khaleel
makaranta don oga Saminu na ganin xuwansa makaranta baxai sa ya samu skills din sana’ar ba, snn a ko da yaushe
xai iya bijire mana ko ya tona mana asiri wataran in har yana mingling da innocent souls, Oga Bala aka sa ya kai
maganar Khaleel wajen mutumin da ke bamu asirin dake taimakon mu samun nasara da ci gaba a harkar yyi duba
kan Khaleel, nan ya sanar cewar a barsa yyi karatun, karatunsa na da amfani garemu sosai a gaba snn xa a samu ci
gaba ba na wasa ba idan ana tare da Khaleel, amma xai yi aiki a kan lamarin don ya ga Khaleel na da taurin kai
kuma bashi da tsoro, wnn shine dalilin da yasa Oga Saminu ya samu kwarin gwiwan ci gaba da biya ma Khaleel
kudin makaranta, a hakan kuma yana kara basa training don kullum sai ya yanke masa amount da xai dawo da shi
gida daga makaranta ta ko wani mean, makaranta ce me tsada yake xuwa a time din, tun da suka fara haka da Oga
Saminu ba ayi ranan da Khaleel xai dawo ba tare da exact amount din da Oga Saminu ya yankar masa ba, he was
doing it perfectly don ba a ta6a kamasa ba, first operation din da aka fara fita da Khaleel yana Ss1, gidan daya daga
classmate dinsa wanda mahaifinsa shahararren me kudi ne aka sa Khaleel yyi leading xuwa gidan, kissan farko da
kuma aka fara yi gaban Khaleel kenan, don nan take Oga Saminu ya kashe yaron ganin ya gane Khaleel duk da
masks dake sanye fuskarsa…. Khaleel ya dauke idonsa da suka sauya launi daga kallon Zayyad, kamar yanda duk
occupant din parlon ke kallon Zayyad din, Mami dai sauraronsa kawai take tana goge hawayen da ya ki yanke mata
da tissue, Abba ya kalleta don sai yaga wnn kukan da take ya wuce na tausayi, Shuraim ma ya kasa gane kan kukan
Mami, this is isn’t something that rarely happen a duniya, hakan na faruwa sosai a duniya, Zayyad ya sauke ajiyar
xuciya yace “I think Khaleel xai ci gaba daga inda na tsaya, don nasan shi kansa bai mance operation din farko da ya
fita ba” Abba na kallon Khaleel da yyi nisa tunanin da yake shi bai taba tunanin haka labarinsa yake daga farko ba,
bai ta6a imagining cewar rabasa aka yi da iyayensa, xuciyarsa ya ji yana masa xafi sosai, ya lumshe ido ya bude, a
hankali Abba yace “Go on Khaleel” Junaid ya tafi gun Mami daga inda yake tsaye ya d’an duka bayanta ya dafa
kujeran da take xaune murya can kasa da damuwa yace “Are you okay Mami?” Mami ta gyada masa kai a hankali
still wiping away her tears tace “Sure” mikewa yyi ya koma inda yake tsaye yana duban Khaleel, Har a lkcn nan
Farida da Heedayah na bakin stairs a tsaye, jikin Heedayah yyi sanyi ba kadan ba sai kallon Khaleel take, a hankali
ta xauna nan bakin stairs din xuciyarta gaba daya babu dadi, bayan few seconds jin Khaleel yyi shiru Abba yace
“Muna sauraronka Khaleel” Ya sauke kansa kasa hawayen dake makale idonsa ya sauko, daga Dinar har Amira
kallonsa suke ko wannensu gabanta na faduwa, Cikin sanyin murya Khaleel yace “Ban ta6a sha’awar sana’ar da
ubannin gida na ke yi ba, na taso cikin mutanen da babu tsoron Allah, babu imani babu tausayi a tare da su, it took
me sometimes kafin in gane babu hadina da Oga Arne coz he always act just as a father to me, a nan naji ina son
sanin su waye iyayena bayan na gano Ogana ba ubana bane, na damu ina son sanin mahaifana, amma no one is
wishing to say even a little to me about them, kullum da tunanin babata nake kwana nake tashi bayan na mallaki
hankalina, na kan dade ina naxarin me yasa ta yarda tayi abandoning dina ga mutanen da basu da tsoron Allah….” Ya
rufe fuskarsa da tafin hannunsa hawaye masu xafi na xubo masa, Mami couldn’t control herself anymore ta sakar
masu kuka a parlon sai dai bata ce komai ba, Abba dai sai kallonta yake, Heedayah ta hade kanta da gwiwa ganin ta
kasa hadiye nata kukan ta fashe da kuka sosai tana jin tausayin Khaleel har ranta, Khaleel ya fi minti daya bai ce
komai ba, Abba yace “Ka ci gaba Khaleel” Cikin raunin murya Khaleel yace “But I am still wishing to meet with her
some days, that’s my biggest wish in life now, ni nasan dalilin tunaninta, da irin rayuwar da na tsinci kai na bbu me fada min gaskiya ko me hanani mugun abinda nake yi yasa ciwon xuciya ya kama ni, su kuma wa enda suka kashe
mahaifina…” Girgixa kai kawai yyi ya d’an yi murmushin karfin hali, bayan few seconds cikin sanyin murya yace “I
don’t want to say all what I passed through being a full time thug, duk da kasancewata mai laifi sosai wajen
Ubangijina ban yada addinina ba, I valued it above everything till today, bana barin lkcn sllh ya wuceni, bana kuma
wasa da tashin dare da axumi, snn ni din me tausayi ne ga victims dinmu kowa ya sani, ban ta6a kissa ba, duk sanda
aka yi kuma sai hankalina ya tashi amma hakan baxai sa in ki fita operation da su ba washegari coz sai da ni suke
ganin dai dai a komansu, a lkcn ma fashi ake ba kidnapping ba, a kullum addu’ata shine Allah ya kawo karshen
rayuwata da mutanen nan, sau da yawa na kan yi attempting guduwa but bana iya kwana biyu xan dawo garesu ba,
dalilin da har ynxu na rasa ganewa, sai in ji without being part of them kamar baxan iya xaman duniyar ba, I was
sponsored by them to the university where I studied Architecture, a nan ne kuma na samu nayi karatun addini don i
was free from them, sai dai duk weekend akwai operation da ni, after my degree, daya daga oganmu ya dage sai na
koma nayi criminology don course din xai kara taimakon mu wajen harkar mu which I did, everything was moving
smoothly for us until 5 years ago na dawo daga Uk na tafi inda ake ajiye kidnapped victims a daji, usually idan ina
nan dama responsibility din feeding din victims dinmu ni ake ba ma, a ranan na shiga inda victims din suke ina basu
bread a nan na ga Heedayah, bayan na fita nake tambayar colleagues dina daga inda aka yi kidnapping dinta seeing
that she is blind, sai suke ce min she wasn’t kidnapped, Oga Salahu ne xai siyar ma wasu yan siyasa part din yara, an
siyar da na daya saura su biyu a ranan ma xa a kashe wata cikinsu, ba sabon abu bane wnn gun oganninmu na kashe
yara, sau da yawa such cases kan tsaya min a rai ya dameni, had it been I had the opportunity da xan kwashe duka su
biyu a lkcn amma sai na dauke Heedayah kadai sbda ailment dinta na fitar da ita bakin gari na ajiyeta nayi wucewata
sbda hakan kadai xan iya yi mata, ya d’an yi shiru snn ya ci gaba kansa a kasa, bayan shekara biyu na sake haduwa
da Heedayah…. Abba ya sauke wani ajiyar xuciya bayan few seconds yace “Yanxu a ina ku ke da xama gaba daya in
particular?” Khaleel ya kalli Zayyad snn yace “Kowa na da gidansa, sai idan akwai wani operation ne ake haduwa a
wani gida” Abba yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Abba ya kalli Zayyad yace “Yanxu shi wannan mutumi ya
daukesa daga gun mahaifiyarsa bayan ya kashe mahaifinsa yana nan?” Zayyad ya girgixa kai yace “Duk sun rasu,
Oga Saminu ya mutu 7 years ago, Oga Salahu an harbesa a wani operation that same year….” Abba yace “Yanxu ku
nawa ku ka rage a harkar?” Zayyad yace “Muna da yawa, ogannimu a yanxu uku ne xuwa hudu” Abba ya girgixa kai
yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Shuraim dai kansa na kasa yana naxarin labarin Khaleel, Mami kuma ta dafa
kanta da yyi mata nauyi, cikin sanyin murya Khaleel yace “Meeting with Heedayah sai na samu courage din dinga
bijire masu, naji bana shakkansu, nake ji kuma xan iya barinsu, ko ma me xai faru ya faru, da suka ga hakan shine
suka yi blackmailing dina suka yi kidnapping Mami, and they ordered me to act as though nine na sa ayi kidnapping
dinta don sun san hakan kadai ne xai rabani da ita da duk wani ahalinta, idan banyi yanda suka ce ba nasan xa su yi
harming dinta shi yasa nayi haka” Shuraim na kallonsa yace “Ya Address din gidan da ku ke xaune gaba daya?”
Khaleel ya d’an yi shiru sai kuma ya gaya masa, Abba ya kalli Zayyad yace “Kai kuma me ya shigar da kai harkan?”
Zayyad yace “Ina almajiranci suka daukeni suka sa ni a harkan” Girgixa kai kawai Abba yyi, shiru ne ya biyo baya a
parlon, can Mami ta mike tayi excusing kanta ta koma sama ba a dau lkci ba sai gata ta dawo, cikin dashewar murya
tace “I have a story to tell….” kowa na parlon kallonta yake, Abba yace “Muna sauraronki Barrister” Mami tayi shiru
wasu sabbin hawayen suka xubo idonta ta goge da tissue snn cikin sanyin murya tace “Shekaru talatin da uku da
suka wuce…… Muna xaune tare da Mai gidana na farko Alhaji Usman misalin karfe tara na dare ya dawo daga wani
business dinsa da yayi a kudu yana cin abinci, shekaranmu biyar da aure a lkcn, d’an mu daya, hira muke yana cin
abinci muka ji kamar karan harbi a tsakar gida, mikewa yyi bai kai ga isa bakin kofa ba aka turo kofa wasu mutane
su biyar suka shigo ko wannensu fuskarsa a rufe, na tsorata sosai na jawo d’ana na rungume jikina ina salati, Mai
gidana bai ce masu uffan ba ya tafi daki da sauri ya dauko masu jakar kudin da ya dawo da shi daga tafiyarsa ya dire
masu yace su yi hakuri gashi nan su dauka su tafi, daya daga cikinsu ya buge kansa da bindiga, su uku suka shige
daki, biyu kuma na daga bakin kofa sai da suka juya dakin gaba daya suka kwashe duk zinarina da wasu kudaden da
suka gani snn suka fito, daga ni har me gidana dake duke kusa da mu bbu wanda yace masu komai, daya daga
cikinsu ya xo ya samesa yace motarsa fa? Me gidana yace shi baya hawa mota bai rufe baki ba Mutumin nan ya
harbesa a kai…. Kowa na parlon kallon Mami yake da mamaki, sai a snn Junaid ya shiga naxarin labarin Khaleel
sosai ya dinga kallonsa, wnn labarin da Mami ke badawa ynxu ya san da shi shekaru masu yawa, kanninsa ne kawai
basu sani ba, Khaleel sai kallon Mami yake ko kiftawa bbu, hawaye na sauka idon Mami a sanyaye tace “A nan take
d’an sa dake jikina ganin abinda suka ma mahaifinsa ya mike ya tafi daki da gudu ya dauko bindigan wasan sa har
biyu ya fito a guje yana nuna masu… Ganin haka daya daga cikinsu xai harbesa aka hanasa, wnn ranan shine rana na
karshe na ganin mijina da d’a na, har lahira suka kashe min miji suka kuma tafi da d’a na Aliyu…” Mikewa Abba yyi
yana kallon Mami with shock, Shuraim ma couldn’t stop looking at her with shock, Kuka sosai Mami take ta sakko
kasa tace “Ni na san so… da tausayin da nake yi ma wnn bawan Allah a cikin kankanin lkci da haduwarmu ba a
banxa bane… there is something I couldn’t understand, he behaves like my blood, Ina kuma jin sa har raina….”
Zayyad banda xare ido bbu abinda yake, Mami ta ajiye hotuna biyu tana kallon Zayyad da ya mike da sauri ya dau hoton yana kallo snn ya kalli Khaleel yace “Wallahi shine wnn, shi aka kawo cikinmu shekaru masu yawa da suka
wuce” Mikewa Shuraim yyi, Abba yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Hawaye ya kawo idon Junaid da ya kasa
daina kallon Khaleel dake ta kallon Mami kamar wanda aka dasa a wajen…..