HEEDAYA CHAPTER 53 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 53 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washegari da safe misalin karfe tara Heedayah da Farida da Maid din Mami na serving din bak’in dake parlor 

breakfast na soyayyen Irish, kwai, shayi da farfesu with bread, yawanci duk cousins da aunt din Khaleel ne da kids 

dinsu a parlon, kana ganinsu dai kasan babu ta inda suka hada hanya da talauci, Mami ce ke ba su Farida breakfast 

din su kai parlor ita tana tsaye kitchen din, bude kofar parlon aka yi Kaka ta shigo sakale da katon jakarta ta yafa 

katon mayafi, ga sarkan zinarinta sai sheki yake a wuya da dankunnensa, tsaye tayi bakin kofar ta dinga bin mutanen 

parlon da wani kallo, can tace “Ya haka kamar ana yunwa, tun fa daga iyafot motocin sojoji dake bayanmu ke jiniya 

ana sanar da jama’a xuwanmu ana ta bamu hanya har muka shigo anguwar nan, ku baku ji bane?? Yanxu ta ina xa 

mu bi mu wuce ta nan duk dankali da kwai, matar gwamnan kano da mu ne fa ke tafe tun daga kano, a jirginsa na 

kansa kuma aka dauro mu aka kawo mu nan garin, muna dira iyafot motocin sojoji suka hau jiniya ana sanar ma 

kowa ana ta bamu hanya a titi, to kuma mun shigo gida bbu hanyar wucewa don Allah” Mami ce ta fito daga kitchen 

jin muryar kaka, da fara’a tace “Sannu da xuwa kaka” Ta bayan kujera kaka ta bi ta tana taku dai-dai ta wuce sama, 

Duk occupant din parlon suka bi ta da kallo, Yakumbo ta shigo parlon ita ma tana kare ma parlon kallo ta rike ha6a 

tace “Al’adar bahaushe dai ba kyau, komai dai ace sai anci abinci, gidan mutuwa abinci, gidan biki abinci, gidan 

suna abinci, daga bayyanar yaro ma an xo jaje an hau cin abinci, to mu dai rabon mu da abinci wllh tun jiya da 

daddare, yau da safe ma da kaji muka karya muka sha yagwat muka kamo hanya abun mu” Mami dai tsaye tayi tana 

kallonta ta kasa cewa komai duk jikinta yyi sanyi, Ammin Heedayah da frnd dinta na tsaye balcony ko wannensu ya 

kasa shigowa, Yakumbo ta bi hanyar da kaka ta bi sai kuma ta juyo da sauri tana kallon mutanen parlon tace “Ina 

kwanan ku?” Few daga cikinsu ne kadai suka amsa, tace “Ya muka ji da wnn abun al’ajabin?” Bbu wanda yace mata 

komai, tace “Toh Allah ubangiji ya raba mu da duniya lafiya, ya kare ‘ya yanmu da jikokinmu da tatta6a kunne da 

hihihin, su kuma wa enda suka cuci wnn yaro Allah yyi kasa kasa da su ya tsine masu albarka, ya bi masa hakkinsa, 

tunda iyayena suka haifeni ban ta6a jin irin wnn labarin ba sai jiya, ni dai dama ina ganinsa nace yyi kama da yan 

kinnafas to ile ga maganata nan ashe D’an kinnafa dai Rahinah ce ta haifesa, kuma duk wanda ya ta6a xaginta a kan 

d’an nan nata sai Allah ya saka mata ya bi mata hakkinta don ba ita ta aikesa ba, ba ita ta saka sa ba” daga haka 

Yakumbo ta wuce sama, sai a snn Ammi suka shigo parlon, Mami tayi murmushi tana welcoming dinsu, Ammi ta 

xauna nan parlon suka gaisa da mutanen dake ciki snn suka wuce sama su ma. Heedayah da Farida ne suka kai masu 

breakfast sama suka yi masu sannu da xuwa, Yakumbo ta sa Farida ta hada mata shayi tana kallonta tace “Toh ina shi 

d’an uwan naki yake?” Farida tace “Yana nan” Kaka tace “To yanxu ya isilin dukiyoyin jama’ah da ya kwamushe fa” 

Farida dai bata ce komai ba lkci daya jikinta yyi sanyi, Heedayah ta hade rai, Kaka ta fara matsar kwalla tace “Haka 

kawai a rabaka da d’an ka tun yana dan yaye a tafi a daurasa a muguwar harka, anya mutanen nan xa su wanye lafiya 

da duniya kuwa? Toh yanxu ya xa mu yi mu rabasa da wnn mugun hali da yake yi, sun fa riga sun cucesa halin ya 

shigesa, sai dai kawai ya yaudare mu yyi tuban muzuru, wataran yana iya koma tunda ya ji dadin rike makudan kudi, 

mu ma kanmu ba wai tsira muka yi ba, ga gwalagwalai na rataye a wuya da kunne, to ni dai ba ruwana ya xo mu 

gaisa inyi ta kaina in wuce gidan Amadu” Tagumi Ammi tayi bata iya tace komai ba, Heedayah ta mike ta fice daga 

dakin hawaye har ya kawo idonta, Mikewa Farida tayi ta bi bayanta ita ma, Ammi tayi kasa da murya tace “Haba 

kaka?” Kaka ta juyo da sauri tace “Haba me?? ban tsine ma shegun da suka sa shi a harkan bane xaki ce min haba? 

Meye nawa daga fadan gaskiya? Wllh idan bamu yi taka tsantsan ba sai ya iya yashe mu cikin dare” Yakumbo tace 

“Toh uwar me xai yi da gwalagwalanki na karya shi da ya saba kwamushe manyan motocin jama’ah masu tsada da 

gidajensu? Meye kuma gantalallun gwalagwalanki” Mikewa Ammi tayi ta fita daga dakin ita ma ranta bai mata dadi 

ba, Kaka ta ta6e baki tace “Ni dai ba ruwana, to gidan uwata ce nan din da baxan wuce gidan Amadu ba dama? Daga 

cewa xanje in gaida Amadu sai cibi ya xama kari? Ita kuma waccan figaggiyar kamar kazar Hausa ni ta banke ma 

kofa wai ta fita, to wllh Amadu ta banke ma kofa ba ni ba, ina ruwanta da d’an mutane da xata ji haushi don na fadi 

gaskiya a kansa, ko meye hadinta da shi, kuma ai dole dama sai mun hada masa da rokon Allah idan kuwa ba haka 

ba muna nan mun saki baki xai ci gaba da danyen aikinsa a boye, Allah dai ya saka masa amma kam an cucesa wllh, 

Amadu dai yace yau yan sanda xa su je su kwashe sauran shegun yan uwan nasa” Yakumbo tace “Toh ai banda 

uwarsa mutuniyar kirki ce dama babu abinda xa mu xo yi gidan nan mu ja ma kanmu salalan tsiya, barin ma ya ji 

daga gidan gwamnati muke, ni duk a tsorace nake ma wllh….” Kaka tayi tagumi tace “Ga mu ga Allah dai” Asiya 

kawar Ammi sanin halinsu bata ce masu uffan ba sai operating waya take, Bude kofar dakin aka yi Mami ta shigo 

Khaleel na biye da ita, daga kaka har Yakumbo suka yi tsit sai yan idanuwa, Mami ta xauna, shi kuma ya duka nan 

gabansu ya gaishesu da ladabi, babu warce ta yrda ta hada ido da shi, kaka sai cewa take “Sannu d’an nan, yau dai na 

takura uban Heedayah ya ara mana jirginsa mu taho dai kada Rakiya ta kullace mu” Yakumbo tace “Wllh kuwa, 

Allah ya bi maka hakkin ka, Allah ya saka maka, an xalunce ka kam, an bata maka rayuwar ka” Kuka Yakumbo ta 

saki, Kaka ma ta fara matsar kwalla tace “Ni da xa a kai ni wajen ‘ya yan shegun sai in ji dalilin da suka daukesa 

bayan kashe ubansa da suka yi, nasan xa su fada min, tun muna yara ake mugunta a duniya har yau ba a saduda ba, 

wnn tsiya da me yyi kama???” Mikewa Mami tayi ta fita, Kaka na share idonta tace “Tashi ka tafi kai ma, Allah ya 

saka maka kawai” Mikewa Khaleel yyi ya fita daga dakin, Yakumbo na kallon kaka tace “Toh yanxu meye hukuncin 

uban dukiyoyin da ya tara ta muguwar hanya?” Kaka ta gyara xama tace “Hukuncinsu a raba ma marayu kawai, ga 

dai mu nan da yawa a duniya ba iyaye tun muna yara” A ranan yawanci relatives din Khaleel dake Abuja duk suka 

koma, gidan ya rage daidaikunsu da xa su koma gobe. Da yamma Ammi da frnd dinta na xaune dakin Mami, Hajiya 

Zuwaira da Aunt din Khaleel ma duk suna dakin, Yakumbo da kaka na can dakin da suka fara sauka bbu wanda ya 

tafi inda suke balle yaji kayan takaici, Aunt din Khaleel tayi breaking din silence din dakin tana kallon Mami tace 

“Toh Allah ubangiji yasa mu ji alkhairi, Allah ya baku nasara” Ammi tace “Ameen” Hajiya Zuwaira tace “Ae tunda 

aka samu aka cafkesu gaba daya anyi mai wuyar ai, amma shi abokin Khaleel din ya isilinsa ynxu?” Mami tace 

“Barrister yace ya bar garin, yanxu haka yana Bauchi” Hajiya Zuwaira tace “Toh amma a record din ai shi Aliyu ya 

ambaci sunansa, kinsan kuma dole a kotu xa a bukaci ganin abokin nasa da ya ambata” Mami tayi murmushi tace 

“Barrister ya so yanke wajen nace kar yyi, idan suka bukaci Zayyad a court din xa mu kirasa ya xo, kuma xa mu yi 

iya kokari na ganin mun wankesa shi ma idan Allah ya yrda, sure xai yi iya yiwuwa yyi xaman gidan yari na 

kankanin lkci but not life imprisonment, shi ma Aliyun hakan xai iya faruwa da shi” Hajiya Zuwaira tace “In sha 

Allah kotu xata yi masu adalci da taimakon ku, hakan ma baxai faru ba” Mami dai bata ce komai ba, A hankali 

Ammi tace “Allah xai baku nasara in sha Allah” karfe biyar kaka ta bude kofar dakin Mami tace “Toh Rakiya mu dai 

xa mu wuce gidan Amadu mu kwana” Mami tace “Baxa ku kwana nan ba kaka?” Kaka tace “Mu kwana nan kuma? Oh oh gwara mu je gidan Amadu nan jama’ah sun maki yawa, ga dai motoci can waje duk inda xa mu a Kaduna xa 

su kai mu ai” Ammi tace “Baxa ku bari mu tafi can din gobe ba daga can sai mu wuce?” Kaka tace “D’a na ne fa 

Amadun? In xo har Kaduna in kasa xuwa gidansa in kwana, lalacewata bata kai haka ba Aisha, mu dai ba mun xo 

mun jajanta abinda ya faru ba, kuma gashi sai wani hade rai mutumin yake kamar baya son ganinmu a gidan mun 

rasa me muka masa, ba gwara mu san inda dare yyi mana ba kada mu je abu ya lalace mana tsakar dare a shiga uku” 

bbu wanda yace mata komai dakin ta juya ta fita, Mikewa Mami tayi ta fita tayi masu sallama ita da Yakumbo, 

Mami na kallon Heedayah dake parlor tace “Collect the bag for them” Heedayah dai bata ce komai ba, Farida tuni ta 

dauke kai dama, can dai Heedayah ta mike babu walwala ta amshi ledan hannun yakumbo, xata amshi jakar kaka 

kaka ta makale a hammata tace “Aa bar min kayana, kina hararana xaki wani amsar min jakata ki saka min mugun 

abu, meye hadina dake banda kawai muna mutunci da ubanki ya takura sai na dawo gidansa da xama kwata kwata, 

tun fa maganar da aka yi daxu a daki shine take ji kamar ta caccake mu da wuka” Yakumbo ta nufi kofa Kaka ta bi 

bayanta, Mami dai ta bi su da kallo har suka fita sannan ta koma sama, Sumayya na kallon Farida tace “Who are 

they?” Farida tace “Yan uwanmu ne” Sumayya bata kuma cewa komai ba sae ta6e baki da tayi. Khaleel na xaune 

compound din gidan tare da Junaid suna hira sama sama, su kaka suka fito tsakar gidan, da sauri kaka ta dauke kai ta 

nufi gate, Mikewa Junaid yyi bayan ya ajiye glass cup din drink dake hannunsa yana kallon Khaleel yace “Mu je 

kayi masu sallama” Mikewa Khaleel yyi ya bi sa, Sojojin dake bakin gate tsaye suka ba su Yakumbo hanya suka fita 

gate din, waje ma sojojin tsaye ne sai lafiyayyun motoci biyu da motar sojoji a baya, ganin Khaleel Yakumbo tace 

“Ae da baka ba kanka wahala ba d’an nan” Kaka na kokarin shigewa cikin mota Junaid yace “Xa ku tafi gidan Abba 

ne Kaka?” Kaka ta shige motar tace “Ehh Junaidu gwara mu je can din dai kawai ya fi mana” Yakumbo ma ta shige 

motar, Khaleel yyi kasa da kai yace “Allah ya tsare” kaka ta daga masa hannu bibbiyu tace “Ameen” Yakumbo tace 

“Sai ka dage da Sallan dare kana rokon Allah kaji?” A hankali Khaleel yace “In sha Allah” Kaka ta fixgo ledan 

Yakumbo dake hannun Heedayah da ta wani hade rai murya can kasa tace “Mayya kawai” juyawa Heedayah tayi ta 

shigewarta cikin gida, Junaid na murmushi yace “Amma xa ku dawo nan ko?” Kaka tace “Aa mun gama da nan, ita 

dai Aisha idan ta gama galantoyinta sai ta same mu gidan Amadu, ai gobe Amadun kano yace mu dawo, kaga baxa 

mu tsallake umarninsa ba ai” Junaid yace “Toh shkkn, sai mun xo” Kaka tayi kasa da murya tace “Kai da wa??” 

Junaid yace “Xa mu xo tare da Khaleel in sha Allah” Yakumbo tace “Ehh to ai da kyau hakan, amma fara yawo ba 

nasa bane yanxu, killacesa xa a dinga yi har tsoron Allah ya shigesa, abinda ma Amadi yace xai xo nan tare da 

gwamnan Kaduna su gaishesa su jajanta masa, ai ba sai yaje kano ba, mu ma xa mu dawo idan Allah ya yrda” Kaka 

tace “Ai shine naga….” Khaleel dai kallonsu kawai yake, Kaka tace “Gaskiya jini ba wasa bane, sai da suka tsaya a 

tare naga mugun kamar da suke da Junaidu, har lotsawan kumatun Allah sarki” Murmushi Junaid yyi, Khaleel yace 

“Allah ya kiyaye hanya” A tare Yakumbo da kaka suka ce “Ameen” daga haka ya juya ya koma ciki, Kaka tayi kasa 

da murya tana kallon Junaid tace “Kace ma Rakiya tayi ta tashi cikin dare tana sllh tana kuka tana nema masa gafara 

wajen Allah, na manta ban gaya mata ba wllh, snn tayi ta masa nasiha cikin dubara akan daukan abinda ba hakkinka 

ba, snn tayi ta nuna masa illar yin haka, ta dinga nuna masa kudi a nan duniya ake samunsa kuma a bar sa a mutu” 

Junaid bai iya yace mata komai ba, Yakumbo tace “Driver mu je magariba nayi, Allah dai ya kai mu lfya” Driver ya 

ja motar, na sojoji na biye da su a baya suka bar layin. Bayan isha Khaleel na xaune parlor idonsa a kan wani movie 

da ake yi a tv, xamansa a parlor umarnin Mami kawai ya bi amma bai son xaman cikin parlon, Mami kuma bata son 

yana xama shi daya a daki ne, he is always silent snn bashi da walwala, Junaid kuma ya fita, Farida da Sumayya ne 

parlon suna labarin movie din da ake yi kasa kasa, Farida ta kallesa tace “Yaya ko ba haka bane?” Kallonta yyi snn 

ya kalli Tv din, can yace “Ban san me ku ke cewa ba” Sumayya tayi murmushi tana fari da ido tace “Labarin film 

din mu ke yi” yace “Ohk but I don’t know about the film” bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da kallonsa, Sumayya 

tace “To a kawo maka abincin yanxu?” Kallonta Khaleel yyi yace “Aa” Heedayah dake xaune dining ta kallesu ta 

dauke ido ta tabe baki ta ci gaba da cin abincin gabanta, bayan few minutes Khaleel ya mike ya tafi dinning din ya ja 

kujera ya xauna, Heedayah bata kallesa ba tana ci gaba da cin abincinta, Tuni Sumayya ta daina kallon da take yi, ta 

shiga xaga parlon da idanuwanta kamar me neman abu, Khaleel na kallon Heedayah yace “Baki bani abinci ba” Ba 

tare da ta kallesa ba tace “Ba naji ance xa a kawo maka ba” Bai ce komai ba, ta dago kai tana kallonsa, tashi tayi ta 

tafi kitchen ba a dau lkci ba ta fito rike da plate din abinci, a bakin kofar kitchen din suka hadu da Sumayya ta ba 

Heedayah hanya snn ta shiga kitchen din, Heedayah ta ajiye masa abincin a gabansa a hankali yace “Thank you” 

Fitowa kitchen Sumayya tayi rike da nata abincin ta nufi dinning ta xauna, Farida ta saki baki tana kallonta, A 

hankali Khaleel ke cin abincin gabansa, Heedayah dake xaune dinning din sai ta ma kasa ci gaba da cin nata, Lkci 

daya Khaleel ya tashi ya dau plate din abincinsa ya bar dinning din. Sha daya saura na dare Mami ta shigo dakin 

Junaid, Khaleel na kwance yana kallo Junaid kuma yyi bacci, ya mike xaune ganin Mami, Mami ta ja kujera ta 

xauna tana kallonsa tace “Baka yi bacci ba” Yace “Eh ban yi ba” tace “Ka ci abincin kuwa?” Khaleel yace “Na ci” 

Mami tace “Ohk, kana ji na” yana kallonta yace “Ina ji” Tace “Da mun so sai after this case sai ku tafi da aunt dinka 

can gombe wajen family din Abban ka, kayi sati daya a can, amma bayan xaman court na gobe sai ku wuce da 

Aunty Nafisa da Sumayya” Khaleel ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Toh Allah ya kai mu” a hankali Mami tace Ameen” shiru ne ya biyo baya, Mami tace “Aunty Nafisa autarsu mahaifinka ce, Sumayya kuma daughter dinta ce, 

but naga kamar baka saki jiki da ita ba” Khaleel yace “Ita wa?” Mami tace “Ita Sumayyar” Khaleel yace “Mami to 

me xan mata” Mami tace “The mother suggested….” Da sauri yace “Suggested what?” Mami tace “A hada ku aure da 

ita sbda situation da ka tsinci kanka” Khaleel ya girgixa kai yace “Ni ina da warce nake so Mami” 

Mami na kallonsa tace “Wacece ita?” Khaleel ya sauke idonsa yyi shiru” tace “Speak ur mind” Ya kalleta yace 

“Heedayah” kasa ce masa komai Mami tayi ta kura masa ido, bayan wani lkci ta mike tace “Sai da safe” a hankali 

yace “Allah ya tashe mu lfya” Daga haka ta nufi kofa ta fita. Washegari karfe uku saura Ammi ta iso gidan Mami, 

bayan sun gaisa Mami ke tambayarta su Ashnaah, Ammi tace “Suna gida” Farida ce ta kawo ma Ammi drink da 

ruwa ta bar parlon, Ammi tace “Daxu Barrister ke gaya mana anyi adjourning case din xuwa sabon wata da xa 

shiga” Mami tace “Ehh in sha Allah, nan da sati uku idan Allah ya kai mu” Ammi tace “Toh Allah ya bada nasara, ya 

kai mu lkcn lafiya” Mami tace “Ameen” Heedayah ta shigo parlon ta duka kasa a sanyaye ta gaida Amminta, Ammi 

ta amsa sannan ta mike ta bar parlon, Mami tace “Xa ku tafi tare da ita ta gaida Abbanta tun da bbu abinda take a 

nan kawai Hajiya” Ammi tace “Ku baxa ku kawo mana ziyara ba?” Mami tayi murmushi tace “Bayan case din nan 

idan Allah ya yarda” Ammi tace “Toh Allah ya bada nasara, Ina Khaleel din?” Mami tace “Sun wuce Gombe tun 

daxu da aunt dinsa amma kwana biyu yace xai yi ya dawo” Ammi tace “Toh Allah ya dawo da shi lfya” Mami ta 

amsa da “Ameen, su Kaka suna lafiya?” Ammi tace “Lafiya lau, nan da yan mintuna xa mu koma kano in sha Allah, 

shi sa na xo Sallamar ki” Mami tace “Toh bari in ma Heedayah magana ta hada kayanta” Ammi tace “Farida fa ita 

baxata ba?” Mami tace “Ai tana xuwa makaranta Hajiya” Ammi tace “Ayya, toh shkkn” Sama Mami ta wuce ta bude 

dakinsu Heedayah ta shiga, Mami na kallonta tace “Idan xa ki sake ranki ki sake ki shirya kayan ki xa ku tafi kano 

da Ammin ki yanxu” Lkci daya hawaye ya kawo idonta da damuwa tace “Mami ban son xuwa kanon fa, don Allah 

kice mata ina xuwa islamiyya” Mami ta hade rai tace “Toh me kike yi a nan din da baxa ki shirya ku wuce ba, yau 

sati nawa da yin candy dinki, you are sitting doing, islamiyyar xuwa kike balle kice ace kina xuwa? what’s wrong 

with you going to greet ur father?? Malama kar ki bata masu lkci ki hada kayanki ke take jira” Daga haka Mami ta 

fita dakin, Hawaye ya gangaro idon Heedayah, Farida dai sai kallonta take bata ce komai ba don tasan me yasa 

Heedayah bata son tafiya, a sanyaye Heedayah ta mike ta hau hada ironed cloth dinta a daya daga travelling bag 

dinta, A hankali Farida tace “What’s making u Sad Heedayah?” Kallonta Heedayah tayi tana goge hawayen da ya ki 

tsaya mata amma bata ce komai ba, sai da Mami ta sake shigowa dakin tace “Minti kusan ashirin har yanxu baki 

gama hada kaya ba Heedayah, me ke damun kanki?” Heedayah ta dau mayafinta ta yafa tana janye da trolley dinta, 

Mami ta juya ta fita, mikewa Farida tayi ta rungumeta tace “Allah ya tsare hanya, when will u be coming back?” A 

hankali Heedayah tace “Ai ya Khaleel yace kwana biyu xai yi ko?” Farida tace “Uhm…” Heedayah tace “Nima 

kwana biyu xan yi in dawo” Murmushi Farida tayi tace “Toh Allah ya dawo mana da ku lfya” Cikin sanyin murya 

Heedayah tace “Ameen” tana jan trolley din ta nufi kofa ta bude ta fita, tsaye ta tarda Mami a corridor tana jiran 

fitowarta, sauke idonta kasa tayi, Mami tace “Heedayah” Ta kalli Mami tace “Na’am” Mami tace “Me yasa baki son 

tafiya gidan ku wajen iyayenki?” Heedayah ta girgixa mata kai kawai, Mami tace “Toh ki sake ranki before going 

downstairs, Ammin ki baxata ji dadi ba idan kina haka, idan kika kwana biyu a can ba sai ki dawo ba” Kamar xata yi 

kuka tace “Mami dama two days din xan yi ai” Mami tace “Aa ba irin wnn kwana biyun ba, ranan da aka ce ki dawo 

xaki dawo” Hawaye ya kawo idonta tace “Mami plss idan mun tafi after few days ki kira ki tambaya yaushe xan 

dawo sbda islamiyya” Kallonta kawai Mami take kafin tace “Can ma gidanku ne kuma xa ki iya xuwa islamiyya” 

Heedayah ta goge hawayen idonta tace “Mami bbu wanda muka saba da a can fa, ni kadai ce xan dinga xama” Mami 

tace “Ga Ammin ki da Stepmum dinki with ur little cute sisters, su xa su xama companions din ki a can ai, and 

Shuraim is now working in kano, definitely xai dinga xuwa can gidan kinga ai kin samu wanda ku ka saba sai ku 

dinga hira idan ya je” Turo baki Heedayah tayi bata ce komai ba, Mami tace “Go downstairs now, gani nan 

sakkowa” Sauka Heedayah ta shiga yi a stairs din, Mami ta wuce dakinta, tun da ta fito parlor Ammi ke kallonta bata 

dai ce komai ba, Ba a dau lkci ba Mami ta sakko parlon, turararruka ta ba Ammin Heedayah, Ammi tayi mata godiya 

sosai, Mami tace “In sha Allah after everything xa mu taho kanon” Ammi tace “Toh Allah ya kawo ku lfya” Har gate Farida da Mami suka raka Heedayah da Mum dinta, tun da suka shiga mota hawaye ke sauka idon Heedayah ta daga 

masu hannu suka bar layin tare da escort din Amminta, Har suka isa gidan Abba Ammi bata ce ma Heedayah komai 

ba ta sauka motar ta shiga cikin gidan, Heedayah ta sauka ta bi bayanta, Kaka da Yakumbo na xaune parlor tare da 

Mumy, Mumy ta shiga yi ma Ammi sannu da xuwa bayan sun shigo parlon, Yakumbo tace “Toh har xa mu tu6e 

kayan, bamu san ko fasawa kika yi baki sanar mana ba, abun ka da masu abu da abun su” Ammi dai bata tanka ta ba, 

Xaunawa kasa Heedayah tayi ta gaida Mumy dake ta kallonta, Mumy tana murmushi tace “Lafiya qlau Heedayah, 

baki da lafiya ne na ganki haka?” Heedayah ta girgixa kai tace “Aa lafiya na qlau” Daga haka ta gaida su kaka ma, 

Kaka tace “Me aka maki a gidan Rakiyar kike cika kike batsewa?” Ammi ta dau handbag dinta tana kallon Mumy 

tace “Hajiya xa mu wuce airport yanxu” Mumy tace “Lahh na xata xa ku bari sai gobe ai Maman Heedayah” Ammi 

tace “Aa yau xa mu koma in sha Allah” Mikewa kaka tayi ta dau jakarta dake gefenta tace “Toh idan Amadu ya 

dawo ace masa da alkhairi” daga haka ta nufi kofa, Yakumbo ma ta mike tace “Toh Maryam a gaida yaran idan sun 

dawo islamiyya….” Mumy ta mike tana murmushi tace “To sai yaushe kuma Mama?” Yakumbo tace “Atoh kilan sai 

na rako patu idan xata dawo wani satin ko?” Da sauri Kaka da har ta isa kofa xata fita ta juyo tana kallonta, Ammi 

dai bata jira ta sauraresu ba ta fita daga parlon Heedayah ta bi bayanta, Mumy ta bi bayan Ammi da sauri tana cewa 

“Toh Hajiya baki ci dambun ba ai gashi ma har na sa maki a cooler wllh” Ammi tace “Aa Alhmdllh nagode” Mumy 

ta 6ata rai tace “Aa don girman Allah ki tafi da shi ku da jirgi xa ku bi nan da yan mintuna xa ku sauka, kuma dambu 

ai abun marmari ne” Bata jira cewar Ammi ba ta shige ciki da sauri sai ga shi ta fito da wani karamin warmer me 

kyau cike da dambu, ta saka shi a wani fancy leda, Yakumbo tace “Tun da yaron nan na can kanon sai a bashi 

coolern ya maido maki idan xai xo” Tuni Mumy dai ta fice ko mayafi bbu ta rakube bakin gate tana mika ma 

Heedayah dambun, Heedayah ta risina ta amsa, Ammi tayi ma Mumy godiya, Mumy tace “Kai haba, babu komai 

wllh Hajiya, Allah ubangiji ya sauke ku lafiya” Ammi tace “Ameen, yaushe xa ku shigo kano?” Mumy tace “Ai ko 

muna da biki satin nan, in sha Allah ina sauka xan kira ki tunda na amshi number ki” Ammi tace “Toh Allah ya kai 

mu, ya kawo ki lfya” daga haka Ammi ta shiga mota Heedayah ma ta shiga, Mumy sai murmushi take kamar warce 

aka yi ma wani gagarumin albishir, Kaka da Yakumbo suka fito kaka na cewa “Banda dai shi Uban Heedayan yace 

sai na xauna wajensa dama me d’a na ya rage ni da shi xan ki xaman gidansa, kuma ko da xa a siyar da Gwamnet 

house din gaba daya da kyar a iya biyan Amadu abinda yyi ma Deedayah da kudin…” tuni Yakumbo ta shige daya 

mota, Mumy dai sai kallonsu take ta gefen ido, kaka ta tsuke fuska ta shige motar da Yakumbo ta shiga ita ma, 

Mumy na daga masu hannu baki har kunne tana Allah ya kiyaye har suka bar layin, tana murmushi ta dinga tunanin 

wani bikin karyar xata kakalo da xai kai ta kano a satin nan…. Tsaye Heedayah tayi tana bin dakin da Stepmum dinta 

ta nuna mata as nata da kallo, babu abinda babu a babban dakin that is well furnished da tsadaddun furnitures, 

karasawa tayi gefen gado ta xaune lkci daya hawaye ya kawo idonta, ko kadan bbu abinda ya burgeta a gidan nan 

dai tun shigowarsu, ta rasa damuwar da ya tsaya mata a rai, ji tayi kamar ta fashe da kuka sosai ko xata ji dadi a 

ranta, Wata maid ce ta biyo ta da trolley dinta dakin, Heedayah ta mike ta amshi trolleyn ta ajiye sa a gefe, Maid din 

na kallonta tace “Hajiya xa a kawo maki abinci ne, ko kuma da wani abun da kike na daban a kawo maki?” 

Heedayah tayi shiru, sai kuma a hankali tace “Tea” Juyawa maid din tayi ta fita, Heedayah ta kwanta gefen gadon 

hawaye me xafi ya gangaro idonta. Bayan Magrib Heedayah ta gaji da xaman daki bayan tayi wanka ta sauya xuwa 

doguwar riga me shara-shara ta fito, a wani parlor ta tadda Amminta xaune ita kadai tana answering din call, 

Heedayah ta xauna kasa ba tare da ta sake kallonta ba, har Ammi ta gama wayar ta ajiye, Heedayah ta daga kai a 

hankali tana kallonta tace “Ammi ina su Ashnaah?” Wani kallo Ammi tayi mata tace “Sai yanxu kika san da su?” 

Shiru Heedayah tayi bata ce komai ba, Ammi tace “Idan ma xaki kama kanki kiyi tun wuri, ni baxa ki kawo min 

iskanci a gidan nan ba, da kika san baki son xuwa wani gulman ya sa kika biyo mu dama, tun farko ai sai kice 

baxa ki xo ba, uwar wa xaki biyo kina hade haden rai, ko me xaki min a nan din idan kin xo” Girgixa kai Heedayah 

tayi cikin sanyin murya tace “Aa Ammi bance bana son biyo ku ba….” Kwankwasa kofa aka yi Ammi ta bada izinin 

shigowa, Maid ce ta shigo rike da tray me dauke da plate din dambu ta dumama, plated with pepperd chicken, ga 

Tamarind drink da bottle waters biyu da glass cup biyu a gefe, karasowa ciki tayi inta ajiye gefe ta dauko wani 

lallausan carpet ta shimfida ta dau tray din ta daura a kai snn da ladabi tace “Hajiya ga abincin” Ammi ta kalleta tace 

“Nagode Amina, kin debi dambun?” Aminar tace “Aa ba shi da yawa Hajiya” Ammi tace “Aa ku deba ku je ku ci 

tare da ‘yan uwanki” Amina ta mike ta fita sai gata ta dawo da plate ta debi kadan ta fita daga parlon, Ammi ta sauka 

kasan carpet din ta dau spoon daya tana kallon Heedayah dake bin abincin da kallo tace “Idan xa ki ci ki fita kitchen 

ki dauko spoon” Girgixa kai Heedayah tayi tace “Aa, kawai chicken din nake so” Ammi ta jawo wayarta ta kira 

Amina tace ta debo ma Heedayah pepperd chicken din, ba a dau lkci ba ta kawo mata. Heedayah na cin kazar a 

hankali Ammi kuma na cin dambunta, Heedayah tace “Ammi wani makaranta xan fara yanxu?” Ammi tace “Ki 

tambayi Abbanki nima ban sani ba” Heedayah bata ce komai ba tana ci gaba da cin naman gabanta, Bayan sun gama 

Heedayah ta kwashi tray din tana kallon Ammi tace “Ina ne kitchen din?” Ammi tace “Don’t worry ki tafi kiyi Isha 

xan kira su Amina su kwashe” Heedayah bata ce komai ba Ammi ta kira Amina ta shigo ta kwashi tray din tana 

kallon Ammi tace “Kun yi bako a parlor Ammi” Ammi tace “Waye?” Amina tace “Sojan nan ne” Ammi tace “Ohk Shuraim, I’m coming” Lkci daya Heedayah ta daure fuska, Ammi tace “Kije ku gaisa, I want to lay ur sisters to bed 

nasan suna can suna wahalar da Nannynsu” shiru Heedayah tayi tana kallonta, Ammi ta mike tace “Sai ki ajiye masa 

drink da abinci” Daga haka ta fita parlon ta tafi bangaren da girls dinta suke, lkci daya hawaye ya kawo idon 

Heedayah, ta fi minti shidda a xaune kafin ta mike tsaye a hankali ta koma dakinta ta shiga bandaki ta dauro alwala 

ta fito ta dau hijab dinta har kasa ta saka tayi sllh, bayan ta idar ta fita xuwa can main parlor, bbu kowa parlon sai 

kamshi dake tashi ga sanyin Ac da ya cika parlon, tun kafin ta karaso cikin parlon take kallonsa, yana xaune saman 

kujera ya jinginar da kansa jikin kujeran idonsa a rufe, har ta karaso cikin parlon bai sani ba, ta nemi kujera ta xauna 

fuskarta bbu walwala… Bayan kusan minti uku ta mike ta tafi xuwa kitchen, masu aiki uku ta samu a kitchen din ko 

wannensu da apron, da ladabi Amina tace “Kina da bukatan wani abun ne Hajiya?” Heedayah ta girgixa kai tace “Aa, 

Abinci xa a xuba ma bako in kai masa” Amina ta dau tray ta ajiye snn ta xuba shinkafa a plate, ta sa miya da enough 

cow meat a bowl, ta debi pepper chicken a wani bowl duk ta daura kan tray din, da Tamarind drink da bottle water 

sae lemon kwali, Amina tace “Ina xa a kai abincin?” Karban tray din Heedayah tayi ta fita, a hankali take tafiya har 

ta iso babban parlon, har sannan idonsa a rufe yake ta karasa kusa da shi ta durkusa ta ajiye tray din tana kallonsa, 

lkci daya ya bude ido, ta d’an koma baya ba tare da ta yarda sun hada ido ba, ya xauna da kyau yana kallonta, 

kallonsa tayi ita ma tace “Ina yini” yace “Lafiya” tace “Ammi tace a kawo maka abinci” ya kalli abincin yace “I’m 

full, thank you” Bata ce komai ba, yace “Yaushe kika xo?” Tace “Daxu” Yace “Tare da su Ammi?” Ta gyada masa 

kai, yace “Ya ku ka baro su Mami?” Tace “Lafiya lau” Komawa tayi kan kujera ta xauna, Yace “Can you help with a 

cup of tea” Tace “Ohk” daga haka ta mike ta yi hanyar kitchen ya bi ta da ido, bayan few minutes sai ga ta ta dawo 

da cup din tea, durkusawa tayi ta ajiye masa a kasa kusa da shi snn ta koma saman kujera ta xauna, Ammi ce ta 

shigo parlon da sallama, ta xauna tana kallonsa tace “Ya aikin Shuraim” Ya gaisheta da ladabi yace “Alhmdllh” tace 

“How are you feeling now?” Yace “Alhmdllh naji sauki” Ammi tace “Toh Allah ya kara lafiya” Yace “Ameen” Tace 

“Ka shiga ka gaida su kaka kuwa?” Yace “Aa yanxu xan shiga” Ammi tace “To ka shiga ka gaishesu idan ka ci 

abincin, 3 days ago ma tace baka shiga ka gaishesu ba” Murmushi kawai yyi, Ammi ta mike tana kallon Heedayah 

da ta tsura ma TV ido tace “Tambayi Amina ko ta bada an kai masu Lipton Hajiyata” Daga haka Ammi ta bar parlon, 

Shuraim ya kalli Heedayah, tashi tayi xata wuce kitchen, yace “Did you rinse the cup before making the tea??” ta 

d’an kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma tace “No I didn’t” daga haka tayi wucewarta kitchen dawowa parlon 

Heedayah tayi bayan Amina ta sanar mata ta kai masu, tana tsaye tace “A ina su Kaka suke?” Ba tare da ya kalleta 

ba yace “Xuwa xa ki yi?” Tace “Ehh” ya mike ya fara tafiya, bin bayansa tayi suka haura sama, wani kofa ya bude 

suka shiga wani parlor Kaka na xaune ta daura kafa daya kan daya ta gama cin pepper chicken da aka kawo masu, 

Yakumbo kuma na kishingide gefe tana sakace hokara, Shuraim ya xauna yana kallonsu ya gaishesu, da damuwa 

Yakumbo tace “Ya ka kara ji da jikin?” Yace “Naji sauki” Kaka na kallonsa tace “Kaji wai Umaru bai san ka dawo 

kano da aiki ba, me yasa baka gaya masa ba muna xaman xamanmu ka janyo mana matsala a xumunci, wan ubanka 

ai ubanka ne” Shuraim dai bai ce mata komai ba, Heedayah ta xauna kasan lallausan carpet dake shimfide parlon 

tace “Sannun ku” Yakumbo tace “Kun gaisa da baban naki ko bai shigo ba” Heedayah tace “Bai shigo ba” Tana fadin 

haka ta mike tace “Dama na xo ne in gaisheku” daga haka ta nufi kofa, Kaka ta bi ta da kallo tace “Naga ikon Allah 

ni Patuu, kamar dai warce Rakiya tayi ma wani mugun abu, ba fa ta son xaman gidan uban nata kwata kwata” 

Yakumbo tace “Ashe dai kin gano, tun barowar mu Kaduna take cika take batsewa, ai na fi ta iskanci ita da komawa 

Kadunan nan wllh sai dai idan sallaman ubanta na can taje yi da uwar rikon nata” Kaka tace “Sallaman aure?” 

Yakumbo tace “Da fa? Ai wnn yarinyar naga kamar idonta a bude yake, ko shekaranjiya sai da nayi ma uban magana 

a aurar da ita kawai babu ruwana, kuma kinsan komai na fada ya xauna” Kaka tace “Toh ke kenan da ba haifansa ma 

kika yi ba, ni kuwa wnda na haifan ma nayi nayi da shi yyi ma d’ansa magana ya fiddo mata ayi masa aure yaki, 

gwara Sudais har an kai gaisuwa” Yakumbo tace “Atoh sai ki bar su kawai ai kin fita hakkinsu” Kaka tace “Toh 

Alhmdllh sai dai na tuna na ta6a nema masa aure da dadewa, can xan lallaba kawai in koma, amma ita Deedayar ina 

mijin da kike cewa xa ayi mata aure??” Sake baki Yakumbo tayi tana kallonta tace “Atoh lalacewa ta sameki kuma, 

ba ke kika kawo mana Junaidu d’an gidan Rahinah ba dama?” Kaka tace “Auhoo, ca nake watsa mun kasa xa kuyi a 

ido ku kunyata ni a idon yaron” Yakumbo tace “Aa ni ai na ya6a da halin Junaidu yaro me nutsuwa da hankali ga 

ladabi wllh, amma tsorona kawai yayan nan nasa da ya bayyana kwanan nan, banda haka ai xuri’ar nan tasu tayi wllh, 

barin uwar nan tasa” Shuraim dai kallonsu kawai yake, Kaka tace “Aa ba ruwanmu da wani yayansa har yanxu ni 

ban gama yrda d’an Rakiya bane wllh, kila dai wata dubara da hikima ce yin hakan sbda wani aiki da take, kilan 

akwai wani kess da take kai kuma dole sai ta billo ta haka” Yakumbo tace “Atohh, Allah dai ya sa haka, amma ai ba 

lafiya in dai gaskiya ne, shi ma Junaidun ai da shekaranjiya xa su kawo gaisuwar to wan ubansa ya kira wai a d’an 

basu kankanin lkci ko xuwa nan da sati biyu ne” Kaka tace “Toh Allah ya kai mu” mikewa Shuraim yyi yace “Sai da 

safen ku” Kaka tace “Toh Allah ya kai mu” Kofa ya nufa ya bude, da sauri Heedayah dake makale jikin kofar ta bar 

wajen ya bi ta da kallo yace “Wait” dai dai stairs ta tsaya ta ki yrda su hada ido tana turo baki ya nufeta, Kaka na 

kallon Yakumbo murya can kasa tace “Dama na ta6a nema masa auren Farida, yanxu gobe xan sa a kira min kawun 

faridan kawai inji inda aka kwana” Yakumbo tace “Toh ko dai da warce yake so ne, naga ransa bai masa dadi ba maganganun nan da kike yi” Kaka tace “Toh ba shi ya jiyo ba ni ina ruwana” Yakumbo tace “Aa yaron na da hankali 

ga rashin son magana balle hayaniya, gobe idan Allah ya kawosa xan ja sa parlona in tambayesa ko yana da warce 

yake so ne ya sanar min” Kaka tace “Tab 6ata lkci kawai, ba sai idan yana kula yan matan ba xai samu warce yake 

so” Yakumbo tace “Wllh yana tare da damuwa ni dai na lura” Kaka tace “Shi dai Amadu kullum tausayin irin d’an da 

Allah ya basa nake yi masa wlh, muna nan dake xaki ga wataran jikana Sudess xai xo, yaro wayayye d’an boko me 

faram faram da jama’a ba dunkum ba” Yakumbo tace “Toh ai halitta ce Patuu, wani haka Allah ya haliccesa wllh, 

baki ga irin dagewar da Amadi yyi da shi ba kafin ya dinga xuwa mana nan tun ma bai dawo kanon gaba daya ba, 

yanxu haka har kwana Amadi yace ya dinga yi a nan amma baya yrda ya kwana yana xuwa xai yi wucewarsa, wllh 

da ina da ‘ya mace da na basa aurenta ni dai” Kaka tace “Ki raba kanki bakin hali ke garesa wllh, Shureen abun tsoro 

ne bar ganin kamar mutum” Yakumbo ta tabe baki tace “Ke kika ga haka ni ban gani ba” tana fadin haka ta mike ta 

shige daki, Heedayah na tsaye har Shuraim ya isa inda take ya tsaya yana kallonta.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE