HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 1 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 1 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tafe muke Ahanya yayinda muketa faman sauri inaiwa sadiya mita       “shikenan mu baza’a barmu musake ba sisto nifa Am 18yrs fa yanzu ina level 1 A university Amma kullum Ana rulling dina Kamar wata yar’ 6yrs mutum yabi yatakurawa rayuwarmu”  sadiyace tace ” kedai kiyi shiru kinsandai yau yayanmu na gida Abba yasashi wani Aiki, karmu karasa yajiki musha najaki “dif nayi saboda nasan ba karamin Aikinsa bane, Muna shawo kwanar layinmu na hangoshi Atsaye Akofar get dinmu Yana Danna waya Araina nace shi yayanmu baya gajiya, Muna karasowa duka muka rissina muka hada baki Yaya sannu da hutawa, dagowa yayi fuskarnan ba fara’a da kallo nabishi Masha Allah, Allah yayi halitta wani santalelen saurayi nagani Fari tas dashi, fatar Nan tasa dagani Bata Saba da wahalaba, idonshi dara- dara farare tas, gasajennan nasa yakwanta A fuskarsa, sanye yake cikin white T-shirt da black jeans.

Dr. Shriem Ismail Mai Dala kenan saurayi Dan kwalisa shekarunsa bazasu haura 28yrs ba yakai dakika goma sannan yace kuwuce mikewa nayi har ina  gware  da sadiya Bude get din mukayi muka shiga Wanda yay dai dai da fitowar ummi daga part dinta hango mu tayi tace kuzo Nan munafukan banza karasawa mukayi inda take tareda tsugunnawa.

Ke tashi kiwuce tanuna sadiya kekuma jirani inazuwa aykafin tarufe baki sadiya tayi hanyar part dinmu Dan ummi batada sauki Akwai mugunta part dinta tashige canjimawa Naga yafito dawasu Kaya Niki Niki kallona tayi tace ki dauki kayannan Heedaya nayiwa me wanki waya yana wajen get Yana jira, ki Kai masa yanzu, yaza’aima na iya daukan kayannan bayan itama da kyar tafito dasu, rankwashi tazubamin tunanin me kike dabazki daukaba, ummi kinsan Abba yahanamu fita waje indai ba school zamuba nace mata, toh tarike haba yau Naga ikon Allah to da yan’ gd yake badake Agolaba, Agolar banza Agolar wofi Zaki dauka ko Sena shekeki da mari, jakata na Ajiye Agefe daukan kayannayi dakyar nadora Aka Dan bazan iya dauka Ahannuba.

Ay Ina fita wajen get yayanmu ya hangoni keee… Yadakamin wata uwar tsawa bansan sanda nayarda kayan wankinba karasowa yay inda nake taredayimin kallan sama da kasa inazaki da wannan uban kayan yatambayeni idonane yakawo kwalla kekin Raina mutane koh? Ko kofar get kinsan Abba yahanaku fita koh?  Ke bakyajin mgn ko?   Abba yasa doka kisa kafa kitakeko? To Dede nake da zamaninki, cikin in Ina nasoma magana Yaya ummice tace inkawowa me wanki wajen get koma ciki  zanbashi, Amsar daya bani kenan.

Dasauri nashiga gd har Ina tuntube zuwa nayi nadauki jakata inda nabarta nayi part dinmu da sallama nashiga bakowa A falon dakin momy nashiga nace mata nadawo sannan nawuce namu dakin sadiyar natarar hartayi sallah tanacin Abinci plate din nadauke tareda fadin sistona bakida kirki me makwan kijirani nashigo,  kanki Akeji Inna biya ta taki saina kwana da yunwa  Niki bani Abincina mikata nayi Ina fadin zan ramane sisto Dani kike zancan jakata na Ajiye narage kayan jikina nafada toilet danyin wanka……………..✍🏻

Misalin karfe 8:00pm.   Alh. Ismail Mai Dala ne Acikin katafaren falonsa sunacin Abinci da iyalan gidan gaba daya, wannan  Yana daga cikin Al’adarsa cin Abinci tareda iyalansa, momy nace Sai ummy    suke zaune Akusa dashi saini Heedaya saikuma sadiya, saisu Kamal yaran ummi yayanmune yashigo tareda sallama, momy ce ta amsamai da fara’arta tareda cewa “yarona karaso ciki shigowa isowa yayi gurinmu,  harara yawatsamin dasauri natashi daga kusada momy na manta wurin zamansane zama yayi tareda gaisheda Abba, Amsawa yayi tareda fadin ya aykin naku Alhmdlh ya amsa gaida ummy yayi ta amsa bayabo ba fallasa, momy yakalla da murmushi A fuskarsa momyna barkanki da gida Amsawa yayi tareda jawo plate tazubamai Abinci sadiyace dasu Kamal naji suna gaisheshi kaina na dago karaf muka hada ido wata uwar harara ya gallamin nikuwa na sunkuyar da Kaina bawanda ya lura bangaishe Shiba saboda sun hada baki wurin gaisuwar.

Spoon yadauka yafaracin Abincin, ciyake momy tana Kara masa  tareda shafa kansa kallo daya zakai musu kagano zallar kaunarda uwar keyiwa danta, Ajiye spoon din yayi tareda kallonta Ashagwabe yace mata “momyna nakoshi, kallonshi tayi tace haba son meyasa bakasan cin Abincine, dariyace takufcemin ganin babba godai godai na shagwaba, momyce tawurga Min wani kallo tareda cewa “ke bakida kunya ko? To dariyarme kikeyima? dauki Abincinki kiwuce daki kikarasaci Acan, Abbane yay mgn ” haba zainab meyasa kike takurawa Heedaya kan dannan naki me zafin ran tsiya, niraini ne banaso kadai San halin Heedaya da rashin kunya mamy ta fada ranta abace,  Yaya kwa ba’a magana Dan yakai bango , 

Tashi nayi zan nufi daki, ummy ce tasa kafa tashureni batareda kowa yagantaba, tafita nayi luuuu zan Fadi yayanmu Ashe Yana Ankare da ita da zafinnama yataroni, ummyce ta Mike dasauri ranta Abace Dan ba hk tasoba zanyi maganinku nagani dan ganinku cikin farinki, kullum zuciyata tana kuntata, dole nadau mataki, tafe take tana mgnr Kamar mahauka ciya tayi side dinta, 

Cikin Azama na Mike daga jikinsa, anatyimin sannu dakyar nafara takawa sadiya ta rikeni muka tafi dakinmu kan katifa na kwanta, inajin radadi akafata danta shureni da kyau, 

Kogin tunani nafada me nayiwa ummi ta tsaneni meyasa Bata Sona Bata kaunata, bana manta wata rana Ina yarinya naje side dinta, natarar da TV tana Aiki bakowa A falon wuri nanema nazauna kan kujera nai dare dare inashan kallo Abuna ban Ankaraba naji Ankwadamin mari Ashe ummi tafito ta ganni dare dare kan kujerarta shine hartazo gabana bansaniba zumbur nayi tareda kwala ihu Ina kuka harda majina.

Haushine ya kuleta tayi wurgi Dani kaina yadaki kujera wata razananniyar Kara take jini ya wankemin fuskata nasume Agurin bansan me yk gudanaba Sai farkawa nayi naganni Agadon Asibiti.

 Asalin labarin………….✍🏻

        Asalin labarin……

Alh. Ismail Mai dala shararrene Kuma yayi suna sosai A harkar canjin kudi.  

Asalinsu Yan kanone karamar hukumar kumbotso mahaifinsa malam sani da mahaifiyarsa Haj. Larai wadda suke kiranta da iya Nene Allah be Basu Yara dayawaba, yaransu 2 Ismail Sai yayarsa saudat, suntaso cikin kulawa duk da Mal. SANI bawani karfi gareshiba Amma Yana kula dasu yadda yakamata, saudat ya Fara aurarwa sakamakon ita macace Bata dogon zama a gida Anty saudat ta haifi Yara 3 Mami itace babba me sunan iya, Sai Kuma  khalifa Wanda yaci sunan malam wato mahaifinsu saudat, Sai Autanta mubashshir shikuma suna kiransa taupiq Wanda yaci sunan mijin Anty saudat, taufiq shine sa’an shriem sun shaku sosai tun suna yara,

Alh. Ismail ya Fara kasuwanci a kasuwar wapa dake fage da Farko ya Fara da yaron shago Sannan daga bisani shima Allah yadauka Kashi yazama hamshakin dankasuwa,

Ya auri mahaifiyarsu SHURIEM Haj. Safiya ,mace me kirki dasanin yakamata sun zauna cikin kauna da soyayya da Farko SHURIEM suka Fara Haifa daganan Sai haihuwar tsaya sun Jima Basu, haihuba kwatsam watarana Yana zaune office dinsa saiyaji anbude kofa bako sallama ta shigo Bazar Bazar da mamaki yabita da kallo yarinyace dabazata wuce shekara shabiyarba da farantin goro akanta kallo daya zakai mata kasan tarbiyya Bata ishetaba washe jajayen hakoranta tayi  tace dama Alh. Tundazu nake zaune awaje Inajira kazo in maka tallan gorona masu kyau gasu Dan kwala Dan kwala tafada ta jagwal gwala goron shi tausayi ma tabashi wannan yarinyar kamata yay Ace yanzu tana makaranta bawai tallan goroba, kudi yadauko masu yawa yabata, yace takai gida asata amakaranta, karba tayi tana ta zuba godiya ta juya buguzu buguzu tabar office din, gida takoma takaiwa mahaifiyarta kudin dayake uwar me idon cinnerace cewa tayi Aradun Allah kinsamu miji rahanatu zama be kamaniba gidan boka taje yay Aikinsa saiga Alh. Ismail na naimanta ido rufe hk suka sahi gabada asiri Saida ya aureta,lokacin SHURIEM nada shekaru 10.

Ummi Kamar yadda SHURIEM yake ce mata, macace Yar’ bakinci, ga kyashi, ga batason kowa yacigaba, itadai kanta tasani, burinta tacika gidan da ya’ya ta mallake dukiyarsa, saidai Allah baibata haihuwaba, SHURIEM nashan Azaba agurinta, saidai mahaifiyarsa macace me kawaici ga hakuri da juriya, Bata kula Abinda ummi takeyi, kwatsam haj. Safiya takuma samun ciki murna gurin Alhaji ba’a mgn ummi kuwa jitake Kamar takashe kanta don bakinci Haj. Safiya ta santalo yar’ta mace Alh. Ismail yarada Maya suna Halimatussadiyya hankalina ummi yatashi matuka wani lokacin harbata iya dannewa saita ja Anyi masifa A gidan hankalinta yake kwanciya rayuwa natafiya har ummi ta shekara 3 baciki hankalinta yatashi, takira aminyarta Haj. Amina tashaida Mata halin dayake ciki, shewa tayi tareda fadin “Ai kallanki kawai nakeyi kizo nakaiki gun malam Sha yanzu magani yanzu, hk tarakata wurin bokanta, ummice tace ” sotake Akashe momy kawai batasan ganinta tunda ita haryanzu haihuwa ta gagara, magani yace yabata tazuba mata A Abinci, Aikuwa ummi nacin Abincin tace garinkinan Alh. Ismail yayi bakin ciki sosi da rashin matarsa,

Haka rayuwa tacigaba SHURIEM  da kanwarsa sadiya nashan bakar Azaba agurinta, Danma iya Nene nazuwa  ta kwana 2, Agaban mutane Bata takura musu ko gaban Abba Amma inbayan idone Sai Abinda hali yayi,

Azuwanda Nene keyi ne tafahimci SHURIEM da sadiya nacikin takura sosai da sosai shine ta shawarci Aminyartakan tabawa danta Auran yar’ta Amma bazawace Tatabayin aure ta haifi yarinya guda daya Heedaya Sai mijinta yarasu, sunan Haj. Fatima.

Haj. Fatima

Macace me hakuri da juriya, da Fari ummi cewa tayi Heedaya bazata zauna agidanba, Abarta taji da balain datake ciki ma ya isheta Banda yaran gida harda wata Agola za’a dauko, Saida Nene tayi Jan ido tace Bata isaba tuknna ta hkr Dan ba yadda ta iya, don iya Nene ma Inka tabota Akwai bala’i da masifa,   su shuriem sun samu   sassauci sosai danyanzu sunkoma wurin maman heedaya, wadda suke kiranta da momy don saboda kirkinta har ganinta suke tamkar mahaifiyarsu,hk rayuwa tacigaba, shriem ya kammala karatunsa na degree sannan yawuce master’s yanzu shuriem yazama babban likita yanada Katafaren A sibiti Mai suna safiyya hospital wanda yasaka sunan mahaifiyarsa,inda Heedaya da sadiya suna level 1 a university.  

Ummy ta haifi Yara 2 Kamal da na’im Amma duk da Haka kudrinta na Nan saima cigaba dayayi.  

        Cigaban labari……

Ummy ta Isa dakinta tana mita tana kuka kamar wadda Aka aikowa da sakon mutuwa, wayarta tadauka takira Aminyarta Haj. Amina ringing 2 tadaga, ummi  tarushe da wani irin kuka, Haj. Amina hankalinta a tatshe tace Kinga rahanatu kashe wayar ganinan zuwa maganar Bata waya bace  tafada tareda katse kiran,

Ummyce tacigaba razgar kukanta, cikin Abinda bewuce Rabin awaba saiga haj. Amina tafado dakin ummi hankalinta Atashe,

Meye yake faruwane rahanatu tukima nakasayi saboda tsabar yadda najiki Sai driver NASA yakawoni,

Ummyce ta tsagaita kukanta  tareda fadin “kawata mutanan gidannan so suke su kasheni daraina nashiga 3 kiyi shiru kawata kuka banaki bane dama ni tun tuni nasamo Miki mafita da sauri ummi ta Mike tsaye tareda fadin nasan bakya aikin banza duk aykin dakikasa hannu Sai Anyi nasara maza sanardani yazan mallaki dukiyar Alh. Ismail dukanta.

Itama mikewa tayi tafara zagaye Adakin Aikine me hatsari zamuyi, Amma Yana bukatar sirri, Dafarko zamusa dansa shuriem yayi aure Amma muzamu samo Mai wadda zai aura, tabdi Amma gaskiya bakisanma me kikeba kinsan yarannan kuwa Aybazai aminceba.

Haj. Amina nisawa tayi, shi yaki Dan barane rahanatu, nasamo yarinyar dazata aureshi har mahaifiyarta ta Amince dataji ruwan kudi. Kuma Yar’ masu kudice zataje tanemi Aiki A Asibitinsa dazarar tasoma saita janyo Mana ra’ayinsa idan ya aureta munaso tayi ciki da wuri dazarar tasamu ciki saimu aika shuriem din shima yabi uwarsa.

Bayan Anyi sadakar Arbain saimu Aika Alh. Ismail shima Kinga riba 2 ga kudin yaron Gama uban, Ay take farin ciki ya lullube ummi harda taka rawarta, Haka sukayi ta kulle kullensu.

 Washe gari da safe muna break fast momyce takalli Yaya nikuwa ya maganar yaron dakaiwa Ayki yaji sauki kuwa, kallanta yayi sannan yace eh yanasamun sauki sosai to Alhmdlh Haka Akeso mikewa yayi tareda fadin “momy zanwuce office sunkuyawa yayi yamiko Mata kansa tayi masa Addu’a tare fadin Allah yakaremin Kai son, murmushi  yayi, ya Amsa da Ameen momyna Nina wuce yarannan su sameni Amota in ajiyesu yafada tareda fita daga falon Nina, Fara tashi nacewa sadiya ta Mike muwuce sallama mukaiwa momy nadauko bag Dita muka wuce.

A mota muka sameshi duka muka shige baya, waye drivernku mukaji yafada,sadiya na mintsuna inaimata nuni tafita make kafada tayi, nikuwa nayi shahqda nakoma, Ai Ina zama ko kofar ban rufe naji yace wato kece fitsararriya ita taki zuwa saike,

Turo baki nayi tareda fadin to Ina ruwanka dani, mekikace yafada Azafafe haryana tasowa daga seat dinsa kamar ze rufeni da duka, bakina narike bansan maganar tafitoba,

Kwafa yayi yace zanyi maganiki soon Heedaya, motar yafiga muka bar gidan, mudanyi nisa

 najiyo wayata cinkin bag tana ringing da sauri nadauko hayaty nagani take cikina ya Murda Dan Yaya yahanamu kula samari, saboda acewarsa Wai duk ba auranmu zasuyiba, kife wayar nayi, har Kiran yatsinke Aka sake Kira jinayi Anyi taka burki, dubawa nayi Naga harmunzo sadiyace ta fara fita Nima na yunkura zanbi bayanta, kwatsam naji yace bani wayarki banida zabi Haka na Mika masa, nawuce cikin school, 

Jefa wayar yayi A Aljihu yaywa motar key baizame ko inaba Sai kofar Asibitinsa, kashe motar yayi yafito yashiga, staff ne keta gaisheshi ya Amsawa, ko office baijeba yafara duba patients dinsa najiya daya Bari bayan yakammala yawuce office, waya yadauko yakira taufiq din Anty saudat suna tsaka da waya Akayi knocking, A shigo yafada, wata staff ce tashigo sanye da farin uniform Ajikinta Dan tsayawa tayi ya kammala wayar sannan tace Dr. Kanada bakuwa,

Kice tashigo ya fada Yana duba wasu files na marasa lafiya, fita tayi tasanar Mata, da sallama tashigo office din kamshintane yafara cika office din dago Kai yayi wow yafada aransa gaskiya kyakykywace ta nunawa sa’a dauke Kai yayi tareda ce mata Bisimillah zauna, zamatayi shiru yabiyo baya can tace masa suna MEERAH SADAU DAN MALIKII……….⁷,⁸

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE