HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Dana ga Anty Meerah ce da wani irin salo nai Mata wani makirin Murmushi, ita kuwa A harzuk’e tace” Meya kawoki gurin mijina bayan ya sakeki, murmushi nasakeyi sannan nace” Mata beyi Miki bayani ya mayar Dani ba Anty Meerah kiyi hak’uri gaskiya ba’akyauta Miki ba.

Cikin zafin kishi ta bangajeni na tafi taga_taga zan fad’i Allah yasa na dafa kujerar dake d’akin, wani kukan kura Yaya yayi zeyi kanta da sauri na tareshi hannu NASA na Kama shafa k’irjinsa kamar Ana rarrashin k’aramin yaro Ajiyar zuciya yakama saukewa hak’uri nashiga bashi cikin kissa da salo nace” Yaya na kayi hak’uri mu Mata muna da kishi dole kuma in muka ga wani Abu Daya D’an b’ata ranmu Dole saiya motsa Bakaji Ance kishi kumallon Mata ba.

Kuma Anty Meerah Ai tagama yimin komai d’a tabani sukutum fa Aduniyar Nan Inbq Masoyinka  ba wazai maka irin wannan, kallon wulak’anci yay Mata San nan yace” kinci darajar Heedaya badan haka ba da saikin Raina kanki wlh.

Wani Azababben kuka ta fashe dashi ta juya tabar mu Agurin, Yaya kuwa dai_daita nutsuwarsa yayi San nan yace” Heedaya ki fahimci wani Abu Taufiq k’arya yakemin wlh karki kuma Dan ganta cikin Nan da Meerah wallahi Allah cikin nawa ne nidake kinsan bazan rantse Miki Akan k’arya ba.

Murmushi nayi kawai najuya nabarshi A tsaye kamar Andasa shi, bayan ta fiyar Heedaya hannu Shuriem ya dun k’ule ya naushi iska sannan yace” wai me yake faruwa Dani ne yarinya k’arama ta Fara juyani Kai da sake Ni yanzu Ai Girmana fad’uwa zaiyi wayyo Allahna kansa yarik’e ya koma ya kwanta Kan gadon Momy.

Lokaci Nata tafiya cikina ya Shiga wata 8 saura wata 1  na haihu cikin yayi wani irin girma Abubuwa sun faffaru ciki harda saranar Yaya Taufiq da Sadiya, San nan Malam Mijin iya wato mahaifinsu Abba da Anty Saudat yarasu, Munji rashinsa sosai domin Mutumne Me matuk’ar hak’uri ga Addini da sanin yaka mata, San nan A zuwa wan Nan lokacinYaya yay matuk’ar shak’uwa Dani sosai Ni kaina na fahimci haka, Anty Meerah kuwa Bata samun lokacin Yaya kwata_kwata kullum Yana tare Dani Amma tun ranar da Yaya yagano Ina da ciki ban kuma Bari wata mu Amala tashiga tsaka ninmuba kullum siyasa nake Masa yanzu ne Nagano maganar Momy gaskiya ce ta ruwan Sanyi gashi yake dahuwa shi kansa Yana kewata dayawa Acikin idansa nake gane hakan.

Yau yakasance Sunday Yaya nagida baije ko inaba nida Momy muna zaune Afalo iya na d’aki na barci Sadiya ta tafi  School, Kiran Yaya Akai Awaya yazo yacewa Momy Ana kiransa zaije yanzu yadawo nikuwa ko kallona beyiba domin haushina yakeji Dan yanzu yace” yagaji kawai nakoma d’akina, nikuma nace Masa saina haihu tukunna,saboda inada Abinda na shirya kansu Meetah, bayan yafita ne Sai mukaji sallamar Anty Saudat ita da Yaya Yaufik Sai gasu da Kaya nik’i_nik’i.

Da k’yar na mik’e natafi taro ta tana cewa karna tashi Amma Saida naje kamoni tayi ta dawo Dani ta kamani na Zauna, Kallanta nayi nace”Anty gaskiya zan biki gidanki Yaya Taufiq yaringa siyomin Sweet ina sha, don Anan Momy da Yaya hanani suke, Murmushi taimin San nan tace” muma munzo muzauna daku  na tsawon watanni domin Daddyn Taufiq yaje Aiki wata k’asa kuma Aikin ze d’aukeshi tsawon Shekara guda.

Da Murna na rungumeta wani naushi naji Acikin cikina da sauri naja da Baya, cikin da muwa Anty Saudat ta Fara magana” kiringayin Abu Ahankali Heedaya Saboda bake kad’ai bace, Kai kawai na iya d’aga Mata saboda Ni Nasan me nakeji.

Yaya Taufiq ya duk’o Yana min sannu, sallamar Yaya mukaji yadawo, Ai Yana ganinmu Ahaka be Duba ma halin da nake cikiba Nan ya hau sirfamin bala’i nida Yaya Taufiq wai meye haka Yaya Taufiq yace” bata Jin dad’ine Shuriem ne yace” ba wan Nan natambaye kaba.

Me kakeyi haka magani kake Bata kome Kai ranar munga masifar Yaya, kaina yadawo kuma wai haka nake yawo Gaban maza ba hijabi saboda Rashin mutuncima harda wata karay Raya nake na fake da ciwo Sai  masifa yakeyi  kamar wanda Aka Aiko shi, ko lura dasu Momy beyiba.

Su kuwa su Momy Murna fal cikinsu Dan sunsan Shuriem A yanzu ya Gama kamuwa da son Heedaya, tashi nace mutafi kuma yau zan kwashe Miki kayanki daga Nan part d’in bazaki kuma Zama ba kuka na saka nace” Ni ba inda zani.

Se Asan Nan Anty Saudat Tai magana Tace” Shuriem Babu inda zataje yazakayi da ita da ciki, cikinma na ya’ya 2 kasauke fushin Nan tun wuri ya Isa haka.

Sai Asan Nan ya lura dasu Sosa Kai ya shigayi yace” to Ai Anty yarinyarce Bata jin magana wlh, kuma had’e Rai Anty Saudat tayi Tace” to ai Kai ji kakeyi kasamin yarinya Agaba kabarta ma taji da Abinda ya dameta, kusa da Momy ya koma ya lafe tamkar jinjirin Daya wuni be ga Mamanshi yanzu kuma ya ganta, Ahankali ta Fara shafa kansa har Saida ta tabbatar ya sauka daga fushin dayake.

Washe gari mun tashi da wani babban tashin hankali Abbane yakasa tashi San nan bai iya motsa ko Ina na jikinsa inda Allah ya Tai makeshi Yana gani yanaji kuma Yana magana.

Anty Saudat ce tatara mu gaba d’ayanmu d’akin Momy Dan samun Mafita……Dukkan mu cikin tashin hankali muke gaba d’ayanmu  Anty Saudat ce ta Fara magana kowa Acikinku yasan me yake faruwa Agidan nan ban da Kai Shuriem da muka b’oye maka to Ayanzu zakasan komai Nan Anty Saudat taimai bayanin komai Amma Bata Gaya masa sun San cikin Heedaya nasa be shida Heedaya ba kawai dai Tace masa An Masa Asiri Akan Arufe Baki Aiwa Heedaya dashe kuma gashi sunyi nasara, to yanzu ga Abinda yasamu Ababa Mene mafita.

Da sauri Shuriem ya mik’e yace” Momy kiyimin Izini inje in sakar musu yar’ su don daga Rana irin ta yau bazata kuma kwana Agidan nanba.

Kuma indai sunana Shuriem saitayi Dana sanin sani na, Taufiq ne Shima ya mik’e tareda cewa calm down bro Kai kaga matsalar ka kenan shiyasa tun farko bamu Gaya ma Abinda ke faruwaba.

Momy ce Tace” dukkan ku kuzauna Zama sukayi San nan Momy taci gaba da magana”  Mafita biyu garemu na farko dole Abba Agaban Ummy zai kasance Mara ji da magana San nan Abu na biyu dole Taufiq ya saki.Meerah sakin ma 3 nakeso yay Mata bayan Nan bazamu Kai Abba Asibitiba zamusa Aringa Yi Masa saukar Alk’ur’ani Mai girma domin dukkanmu munsan ciwansa bana Asibiti bane.

Kowa ya gamsu da shawarar ta dukkansu eh sukace, Akwai kuma Wanda yake da wata shawarar cewar Momy,  Anty Saudat ta Fara magana kamar haka” eh inada Shawarar Akwai wani Abokin babanmu Sunansa malam ALU Ajihar katsina yake Meze Hana gobe muje Musa meshi nida Taufiq da Shuriem ke kuma Momy kizauna kijere Heedaya da Abba.

Kowa ya gamsu da maganar Anty Saudat data Momy haka kowa yatashi jiki ba k’wari muka fita Shuriem b’angaransa ya nufa zuciyarsa na Mai suya gaskiya y’an uwansa ba k’aramin Sansa sukeba da yanajin haushin Taufiq Ashe shi Mai k’aunarsa ne, gaskiya Momy uwace ko uwar data haifeshi Abinda zatai Masa kenan, ta saudarkar Masa da Yar’ta tilo Dan kawai Tace to rayuwasa shida mahaifinsa.

Gaskiya Dole Ajin jina mata uwace ta gari, kuma gashi duk Abinda yaywa Heedaya ko Afuska Bata tab’a nuna masaba gaskiya Dole ne yarik’eta hannu bibiyu ya Bata kulawa sosai da sosai.

 Yana Shiga d’akin Meerah yaywa tsinke,  zaune ya hangota gefen gado tana faman Danna waya takaicinta ya kasa dannewa cikin ransa zuwa yay ya Fara ball da ita San nan yazare belt ya Shiga jibgarta, kasan cewar da tazara tsakanin part d’insu Dana Momy shiyasa bawanda yajiyo ihunta Saida Yay Mata lilis sannan yabarta jina jina tareda Dan k’ara Mata saki har 3 San nan yace” ta tsaya Yana zuwa Taufiq yakira yace” yasamo Masa me Akori kura kuma inyatashi samowa yasamo Mara mutunci, jimawa kad’an Sai gasu da Memota kayanta Akashiga labtawa cikin Motar ko cokali nata ba’a rage ba, Kan kayanta Bayan Akori kura Shuriem ya je fata Taufiq na magana Amma Shuriem YAK’I sauraransa gurin Me motar Shurien yaje yace Masa” zata nuna maka hanyar gidansu inkaje zasu baka kud’in motarka in kuwa Basu baka ba kasan yadda zakayi dasu.

Meerah Kam kuka take tayi Amota har suka Isa bayan sun isane tashiga tana kuka maman na ganinta hankalinta yatashi tambayarta tashiga Yi me yasameta Ai tana bud’e Baki zatai magana me mota yayo Aike, dukkansu su kayi waje.

Suna zuwa suka tarar da yajuye musu Kayansu Ak’asa Nan fa Maman Meerah tashiga zazzagawa me mota bala’i shi kuwa da yake yasaba da irinsu cewa yay malama bani kud’in kayan Dana D’auko na ware ni jirana Akeyi, kallan baka da Hankali Tai masa, San nan takalli Meerah Tace” wai meke faruwane, kuka tasaka Tace” wallahi mama bansaniba kawai Ina d’aki naji ya shigo ya rufe ni da suka San nan yace ya sakeni.

Saki 3 shine ya Kira Memota yace” ya kwashemu nida kayana in.munzo Abiya kud’in Motar Anan, me Motane ya gaji yace” Malamai nagajifa nifa sanfewa zanyi.kuna b’atamin.lokaci dadai Haj. Laila taga ba mutuncine dashi ba tambayarsa Tai nawa ne kud’in San nan ta koma gida tad’auko tabashi.

Almajirai suka Samu suka shigar musu da kayan Bayan sun Gama Shiga dasune Haj. Laila takira baban Meerah tasanar dashi Abinda ke faruwa Shima yaji takaici sosai yace” gaskiya bazai bar Shiriem ba se ya makashi A kotu ko Abinda ya mallaka zai k’are Sai yay Nasara Akansu Shida mahaifinsa.

Su Anty Saudat kuwa k’arfe  8 na safe suka d’auki hanyar katsina, tafiya sukayi me nisan gaske sannan suka Isa, sauka sukayi daga babban titi, suka d’auki hanyar dazata sadasu da gidan Malam ALU Koda suka Isa gidan, Anty Saudat ce ta Shiga gidan sukuma su Shuriem suka tsaya A k’ofar gidan da sallama ta Shiga gidan wata dattijuwa tayi Arba da ita tana Hura wutar ice, tsakar gidan ya bud’e da hayaki.

Tasowa tayi don taga me sallamar hab’a Dattijuwar tarik’e Tace” saudatu kune yau Again maraba maraba gaskiya yau muna da manyan bak’i gashi kinyi sa’a malam d’in Yana Nan ke kad”ai kike tafe Anty Saudat Tace” A Ah Inna nida jikokin kune.

To to kuma kika barsu Awaje yanzu dai shigo daga ciki wani d’aki ta bud’e mata  Tace’ shigo shigo Maraba lale da kanawan Dabo.

Bayan sun gaisa Dattijuwar Tace” Bari Nasa Badd’o takira jikokin namu fita tayi tashiga wani d’aki suka fito tareda wata  Budurwa zatakai kimwanin Shekara 19 Bayan sun fito takalli budurwar tace” Badd’o Akwai bak’i Awaje  kije kice su shigo wadda Aka Kira da Badd’o waje tayi Dan kiransu.

Ita kuma takoma gun Anty Saudat Kan kace meye wan Nan ta cika mata gaba da kayayyakin ciye ciye.

Su Shuriem ne suka Yi sallama Tare da Badd’o har d’akin da Anty Saudat take tarakasu Bayan tagai sheta takoma d’akin da Aka kirawota.

Bayan su Shuriem sun gaisa da Dattijuwar ficewa tayi jimawa kad’an Sai gata sun dawo da wani farin tsoho, da sallama suka shigo d’akin Shima yayi mamakin ganin Anty Saudat Bayan ya Zauna sun gaisa.

Anty Saudat Tai Masa bayanin su Shuriem, kallon Shuriem Malam yayi yace” kad’o idanka kenan Hala babanka be Gaya maka Alk’awarin Aurenka da Badd’o ba tun kuna Yara mahaifinka da d’an wurina Yako sukayi Alk’awarin tsakaninsu zasu had’a ku Aure kaida yar’ uwarka.

To yanzu kuwa lokaci yayi da zamu cikawa marigayi Yako burinsa, Anty Saudat ce tayi gyaran Murya Tace” Malam wannan maganar haka take kuma insha Allahu zamu cika Alk’awari.

Yanzu Abinda ke tafe Damu shine Nan tabawa Malam labarin Rashin lafiyar Abba Shi kansa Malam ya firgita sosai da Jin wan Nan lamari nanda Nan fuskarsa tasauya zuwa jajawur yace” mu za’ayiwa haka to ta Allah Bata mutumba indai Ayar Al’kur’ani na Aiki to kusawa ranku isma’ila ya rabu da ciwansa ya Gama Dan haka zan Baku Rubutu na karya sammu Aringa bashi yazama ruwan Shansa.

Nan dai yahad’a musu rubutu Ak’aton galon don yace musu tsakanin katsina da Kano Akwai tazara gwara yabasu da d’an dama yadda bazai k’are da wuriba.

Sallama sukayi da Malam da matarsa. Bayan sun fito k’ofar gida Aka Aiko Badd’o da tsaraba ta kawo musu Shi kuwa Taufiq mezeyi inba Dariya cikin Rashin Dani Badd’o taje ta mik’awa Shuriem kayan wata harara ya maka Mata tareda cewa Nika d’ai kika gani Agurin Nan Taufiq ne yay Saurin cewa Matarmu bani Nan Ni na Kar b’ar Masa Taufiq taje ta mik’awa  kayan cikin kunya.

Nan tajuya gida da gudu Anty Saudat itama danne tata Dariyar take Amma Sai data Dara.

Mota suka shige suka d’au hanyar Kano da Anyi tafiya kad’an Sai Taufiq ya kalli Shuriem Yace” Mijin Badd’o saiya kwashe da Dariya………

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE