HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 8 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 8 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

SHURIEM ne yacigaba da magana kamar haka “Na farko banasan fitina ko wacce tazauna da yar’ uwarta lafiya, sannan kwana 2 nakeso kowaccen tadingayi in kungama sati dai dayan dayan da zakuyi sannan a tsarina bazan ringa bin mace dakintaba ita zatazo ta sameni, sannan Abu nakarshe ban yarda dayawan zuwa unguwaba, idan dawadda Abinda nafada Acikinku be mataba zata iyayin magana.

Meerah ce takalli shureim tace dear itafa Akaida tayi kwana kinta nice yanzu innayi sati Sai muci gaba da kwana bi biyun dakace, Ai inajin haka nace billahi lazi Baki isaba idan Kinga nabar Miki kwana na Niba sunana heedayaba.

Yaya shureim ne yadaga Mana hannu, kowacce Acikinmu ta nitsu, sannan ya kalleni yace heedaya meerah ta fiki gaskiya Dan haka kiyi hakuri inta Gama kwana kinta saiku cigaba da kwana bi biyun, Ai banasan sanda nai zaraf nace wlh Yaya Bata isaba duk ba kusan tare mukazo gidanba yadda kace tayi sati Nima wlh sainayi sati guda din, yayane ya kalleni ransa Abace saboda yadda nake yarfashi gaban meerah Yana fada Ina bashi Amsa, heedaya yakira suna na, kallansa nai batareda na amsaba Nima raina Abace sannan yaci gaba da cewa” muzuba ni dake Dan halak kafasa tunda kin koyi rashin kunya, kuka nasaka nace wlh Banga Wanda ya Isa yatakemin hakkinaba Nima Ay dawayona saboda ita babbar banzace zata zauna tana cemin wai bazanyi kwanakinaba kuma A haifema ta haifeni, shureim ne ya zabura zeyi kaina jin ana ciwa Rabin rantasa mutunci.

Meerah ce tai saurin rikeshi Tace masa haba dear wannan har wani Abinda ze Bata maka Raine kabarta Aikai keda kwanan base tayi muganiba, rufemin Baki nace Mata cikin tsawa, ke harkin Isa kishiga tsakanina dashi, daki daya Aka rainemu ya bani Abinci Abaki, ya goyani Abayansa, sannan innakasa Yin barci haka yake kwana Yana rarrashina har sainayi tukunna Shima sai yayi to ke Aciki gayamin guda daya Wanda yay Miki, Ai bankai ga karasawa ta fashe da kukan munafurci nikuwa naruga falona nasa key dannasan Yaya ya hadiya dan bakaramin aikinsa bane yay min shegen duka Agabanta.

Murmushi nayi muzuba nida ke Meera Babu gudu Babu Jada Baya kuma ita kissa bada ita Ake hai huwar mutum ba Aduniya yake koyarta bakina ganina yarinyaba, ruwa Naga dama bazaki shaba.

Hakan muka ringa rayuwa nidasu da dadi Babu dadi, Amma ko muna Fada da Yaya bana nunawa Agaban meerah kullum kyautata masa nake wannan kuma salon Anty saudat ce ta koyaminshi.

Yau na karbi girki harnayi kwana 2 na innaje dakin Yaya Baya wani hiradani saboda wai inaiwa matarsa rashin kunya.

Yau takasance Sunday yaya Yana gida bashida Aiki da sauri nayi Aikina nagama dare nayi wankansa Adakina nayi Alwalata ta barci nashige dakin batareda yaganniba don naji karar ruwa A toilet kuma nasan shine da sauri na shige na rufe kofar da key shi kuwa daya fito yaji shiru meerah batazoba Sai kawai yayi kwanciyarsa.

Nima fitowa nayi na kwanta Kan kujerar bedroom din inata faman Addu’a kada Allah yasa yatashi yaganni candai bacci barawo ya saceni.

Meerah kuwa Ansha gayu Anfeshe jiki da turare Antaho wurin dear tans isowa bakin kofa Aka Kara gayarawa hannu tasa ta Murda taji A kulle.

Bakin ciki ne ya turniketa lallai na miji muna fikine wato tana ciki sun kulle kofa da haushi takoma dakinta tana tsinewa heedaya Aranta.

Tana Isa dakinta waya tadauka takira mamanta ta rushe mata da kuka, duk Abinda ya faru saida ta zayyane mata, hakuri tabata sannan ta Dora da cewa, meye ma na fushi meerah saura kiris fa, kiyi hakuri mucimma burinmu haka dai taita kitsa mata tuggu iri iri sukayi sallama ta kashe wayar.

Shikuwa shuriem bayan yatashi da daddare be kunna fitilaba ya haska wayarsa ya Alwala ya shiga yin na filolinsa, bayan ankira sallah yamike yay haryanyar fita zashi masallaci kofar ya Murda yaji A rufe mama kine yaka mashi shidai yasan bai rufe kofaba Amma ya Akayi Aka rufe kofar sauri yake bashida lokacin wannan tunanin  Murda key din yayi don dama Ajiki yake barinsa  ya bude kofar yafita.

Ni kuwa ban farka ba Sai karfe 7:00am da Addu’ar tashi daga barci na farka Aida sauri na Mike nayi hanyar fita saboda haske Dana gani Yana shigowa ta windown dakin sauri nakara Ina zuwa babban falo Naga meerah Kan dining ita da ba tatashi dawuri Amma yau ta tashi da sauri tazo tasha ga bana ni kuwa natanadani kalolin rashin mutuncin dazan Mata idanta kulani……

Meerah ce takama girgiza Agabana, nikuwa Ina tuna no irin rashin mutuncin dazan Mata, kallo na tayi Awulakance Tace”meya kaiki dakin shuriem bayan kinsan yau kwana nane, murmushi nayi nace” to ke meyake kaiki? Abinda yake kaiki Nima shiyake kaini.

Afusace tacemin ke!  Ya isheki haka nizaki rainawa hankali to shuriem nawa ne ni kadai Baki Isa ki shiga tsakaninmuba karyarki Tasha karya.

Zagayeta nayi zan shige saboda Naga Abinnata Sai uzuri hannu tasa ta figoni ta wankan mari, sannan Tace kinsan meyasa na mareki saboda kinje kin kwana da mijinta, karar bude kofa naji natabbatar yayane Aikuwa na kwalla wata uwar Kara, gashi merah ta ca kumeni tafiya nayi luuu nasaki jikina ita kuma dayake Sha shace saita sakeni da gudu Yaya Azamo yarikeni, nikuwa kwakkwaran motsi ma kinyi nayi idona Arufe.

Darawar muruya ya shiga tambayarta meerah me kikayiwa heedaya, meyasa bakida hakuri yarinyar guda nawa take ke Dena firgita ta Dan Allah narokeki, heedaya da kike gani Bata da fitina duk wannan Abun da kike gani inasane ki kike jawoshi Dan haka wallahi kinji narantse idan wani Abu yasameta bazan taba kyalekiba.

Inajin Yaya yarungumeni tsam tsam Ajikinsa tari na farayi Dan karyace zamu Asibiti, Ahankali na bude idona nadinga kallansu daya bayan daya, nuna meerah nashigayi da hannuna nace Yaya mugunta takemin wlh ni wurin Abbana zan koma bazan iya Zama da ita ba.

Ai Yana jin na ambaci Abba hankalinsa yatashi, yasan zan kwanto masa ruwa, kingani heedaya badai duk Akan kwana bane Aketa wannan bala’in to nadawo Miki da kwananki. 

Meerah dai da Ido take binmu Dan Abun yafi karfinta, shureim ne yajiyo gateta yace” meerah kiyi hakuri kibata kwana kinta, banasan wani yakumayin magana sannan yajuya yawuce dakinsa, Ai dana tabbar ya shige kusa da ita naje nace tawa ba irin Taki bace meerah Aje Akara koyowa katuwar banza tazo zata kwacewa yar’jaririya miji.

Wata wawura takaimin nikuwa na ruga Aguje domin Nasan in ta kamani Sai mun dambatu nikuwa banida lokacinta, dataga nasa key Akofar falona bubbuga kofar taringayi kamar zata balla Saida Yaya yafito yayi kamar ze daketa sannan ta hakura Dan meerah badai Nacin masifaba.

Haka na kwana dakin Yaya komai na kyau ta tawa inai masa bana tabayin wani Abu dazai Bata masa Rai haka rayuwa tacigaba da tafiya da dadi badadi, yau munkai wata 2 da Aure Amma ba Abinda yataba shiga tsakanina da Yaya.

Yaudai natashin da kudurin amso wayata, saboda zaman kadaici nada muna, Adaki nasameshi nace Mai Dan Allah inason yabani wayata wlh ni bazan kuma yin wani Abu da ze b’ata maka Rai shiru yayi kamar bejiba can kuma yace” bude drowern can Akwai waya kidaukomin” tashi nayi nadauko nace” masa gata, sabuwar wayace da sabon sim Aciki kuma nai Mata chargy Amfani kawai Zaki farayi daita.

Godiya nashiga Yi masa tareda yiwa iyayansa Adda’a shuriem yaji dadi sosai Amma be nunamin ba, Ina tsugunne gabanshi mukaji kamar kakarin Amai da sauri muka tashi nidashi mukayo babban falo meerah muka gani kwance tanata yunkurin Amai Amma Aman YAKI zuwa,  yayane yaje yadagata yazaunar daita jikinta zafi Rau, tashi yayi yashiga daki saigashi da waya Ahannusa, sister umaima yakira yace” tazo yanzu madam ba lafiya meyake da munta tatambayeshi Atakaice yay mata bayani cewa tayi masa gatanan zuwa sannan takashe wayar.

Cikin mintuna kalilan Sai gata tashigo, gaisheta nayi ta amsa mun cikin fara’a domin munsaba da ita sannan suka gaisa da yayaunmu matsawa tayi kusada meraah tashiga Yi Mata tambayoyi tana amsawa, roba ta bata tace tatashi ta daure tayo fitsari ta kakawo mata, da kyar ta daure tatashi ta kawo fitsarin cikin mintuna kalilan ta auna fitsarin saiga result ya fito positive kallon shureim tayi Tace cogratulation matarka nadauke da juna 2 harna tsawan sati 5…….⁴¹,⁴²

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE