HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 9 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}
HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 9 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}
Wannan Rana tayimin tsayi dayawa har nakasa gane fari da Baki, bansan yadda Akaiba kawai Sai ganina nayi Abedroom Dina Akwance A Kan gadona Yaya nagani ya shigo dakin jinayi yace sannu heedaya kin farfado kenan tausayinsane yakamani na rushe dawani irin kuka me taba zuciya, A bakin gadon yazauna, sannan yace kuka kuma heedaya yafada Yana kallona, share hawayena nayi nace masa” yaya meya samenine, faduwa kikayi dazu Afalo Amma Abin yazo da sauki, tunda bakiji ciwoba.
Wayata ya mikomin hannu nasa nakarba, shikuma ya Mike Yana cewa Bari ya dubo meerah, harya fice ban kuma maganaba, wayata na kunnah, sabuwar ce dal, number momy yasamin data Abba, Sai Anty saudat, saita Yaya taufiq, saita sadiya Amma Babu numbern iya.
Momy nagwada Kira naji ta Fara ringing Alamar da kudi Aciki, da sallama tadauka, inajin muryarta na Fara kuka lafiya heedaya ta Fada daga can bangaran.
Momy Anty meerah fa cikine da ita gaban momyne yayanke ya fadi Amma dayake A gaban iyane saita maze ta Kama Fada to Dan meerah tanada ciki saime ita haihuwa Bata Allah bace ni banasan sakarci, iyace ta warce wayar takara Akunne heedaya lafiya kike kuka, kuka nasawa iya dama Anty meerah ce takeda ciki.
Yau Ashe Akwai bala’in A gidanan wato iyayanki sun San sun shirya makirci shiyasa suka kalallameni da dadin Baki wai nabari ki kwana 2 nazo naganki jinayi ta katse wayar nikuwa na cigaba da kukana.
Iyace tashigo bangaranmu tayi sallama taji shiru kaita sawo ciki mezatagani meerace dare dare Kan cinyar shuriem Yana Bata yogourt da spoon tana Sha tana yatsina Aida sauri ta Isa wurinsu ta tan kwabe robar tazubewa meerah Ajiki da sauri suka Mike kallansu tayi ta nuna shuriem da yatsa Tace” kaci Amanata shuriem kaci Amanar babarka yanzu shine kazo kadibgawa wannan tsohuwar guzumar ciki to Bari kaji duk Abinda zakayi Atafin hannuna kake saboda Agabana Aka haifeka, bawani layencemin dazakayi.
Kuma na baka wata biyu idan bakaiwa heedaya cikiba saina rabata da gidanan, hakuri yashiga bawa iya Dan yasan halin kayarsa, meerah kuwa tsayawa tayi tana kallon ikwan Allah, iyace ta gyara tsayuwa sannan tace shuriem karka dauki maganata dawasa, idan wa adin Dana dibar maka yacika heedaya kuma ba ciki zanzo intafi da ita, Kan merah ta juya tazabga Mata wata uwar harara sannan tayi falon heedaya.
Iya nashiga taga ba kowa Afalo cikin dakin tashiga da sallama nikuwa Ina ganin iya nakara sautin kukana Rarrashina tashigayi tana cewa” barni da Dan banza heedaya zega yadda Ake danyan Kai Dan duk saina tashi hankalin duk wani mahaluki Agidannan Dani suke zancan Tana kaiwa Nan tatashi ta fice…
Bangaran momy kuwa Anty saudat takirawo tasa Mata kuka tana cewa” na banu na lalace Anty saudat D’ana shuriem, daga can bangaran Anty saudat Tace” kardai Abinda muke gudune yafaru kalu innalillahi wa Inna ilaihirraji un, Dena kuka momyn Yara Allah baze Basu sa’a ba zanzo gidan zuwa gobe sallama sukayi momy ta Ajiye wayan tana kuka.
Bangaran shuriem kuwa gidanma yabari gaba daya Dan Yama rasa Abinyi, meerah kuwa daki ta kule takira mamanta Awaya tana dagawa Tace mama Albishirinki inada ciki sati 5 Ai maman meerah da sauri Tace Alhamdulillahi burinmu yakusa cika saura kadan.
Yanzu Abinda za’ayi Bari nakira rahanatu Kai tsaye , kashe wayantayi ta dokawa ummy Kira ummy nadauka maman meerah taiwata uwar guda Ayyuri Yuri yuriiiiiiiiiii, na taba ki da Alheri saura kiris yanzu haka merah nada ciki meye kudurinmu nagaba,
Shewa tayi harda rawarta Tace” kisan shureim shine kudurinmu nagaba
Yanzu Akwai gubar dana tanada saboda wannan lokacin Bata kisa lokaci daya tanabin jikin mitumne takan dauki Awa 24 kafin ta Gama da mutum yanzu kituramin numbern ita meeran Adarannan nakeso Ayi Aykin banasan jira gudun samun matsala.
Ummyce takashe wayarta tanata fara’a can taji shigowar sako tana dubawa taga numbern Kira tayi Nan da Nan tadaga cikin kasa kasa da murya Tace meerah ummice Tace nagane mama tayimin bayani, ummice takatseta da cewa ke kadaice, eh nikadaice cewar meerah, ummi kuwa kamar me rada tacigaba da cewa” zanyo hanyar part dinku Kinga yammace yanzu kowa Yana part dinsa, kifito muhadu, toh meerah ta amsa.
Tasowa meerah tayi tafito tana jiran ummy can ta hangota tataho mika mata gubar tayi Aleda tareda Yi Mata gargadin ta kiyaye karba tayi suka bar gurin da sauri Dan Kar Agansu.
Tsaye nake gefen taga Ina hangensu bana iya jiyo Abinda suke Fada Amma Naga Ambawa Meera wani Abu da sauri nasaki labulen nakira Anty saudat kwantarmin da hankali tayi tace zatai wani Abu.
Dawowa meerah tayi ta sheka girkinta tayi takawo tajera Kan dining sannan ta koma ta sheka wankanta,bayan sallar isha’i yayane ya Fara Zama sainima na fito zuba masa Abincin nayi Nima nazuba nakamaci.
Can saiga meerah ta dauko plate da indomie Aciki tazo tazauna tanaci tana wani murmushin mugunta……
Nice na Fara cin Abin cin sannan Yaya ma yadauki nasa yanaci murshi meerah take tayi Nima namaida mata da murmushi Amma takasa gane ni nawa murmushin dawace manufa nakeyinsa.
Kallan ta nayi nace Anty Meerah dagani yaukina cikin nishadi dariya tayi tareda d’akko lemonta ta kora Dan yanayin nai Mata dadi, sannan tace” badole kiga Ina nishadi ba D’an Shuriem Kwance A cikin cikina kin ga kuwa nafi kowa sa’a A duniya, Yaya ne Yayi Murmushin jin dad’i San nan yace”Nima Ina Alfahari da hakan yau zan samu d’a nawa na kaina, A Duniya.
Wani malolon bak’in ciki ne ya tur nikeni, haka dai muka karasa cin Abincin kowa da Abin da ke Ransa.
Yaya ne ya fara tashi Yace” zeje ya kwanta yay mana sallama” sannan yawuce, wurin ya rage daga ni Sai Meerah kallona tayi Tace” Heedaya kidena hada kanki Dani Domin Nai Miki fintin Kau baza ki iya ka moniba, kuma kisani ke yanzu gawace Nake magana dake A Yan zu.
Saboda lokaci kalilan na Baki daga ke har Yayan naki zan Gama daku wani makirin murmushi, nasaki Ina jin jina wautar Anty Meerah cikin raina lallai Anty Meera wawu yace ta Ajin karshe, wai ni take gayawa wadan Nan, magan ganu.
Murmushi nayi San nan na tashi na kalleta Ina mamakin sokonci irin nata nace” tamu ba irin taku bace, ME LAYA KIYAYI ME ZAMANI…..
Hanyar dakina nayi Ina wata irin dariya, ita kuwa Baki ta saki tana kallona harna shige falona.
🌹FLASH BACK🌹
Bayan Naga su Meerah Ita da ummy Anty saudat na Kira nagaya Mata kwantar min hankali tayi Tace zata kirani, can Anjima ta sake kirana Ina dauka tacemin kije ki dubo min me Meerah take girkawa Amma cikin wayo da dabara sannan ba kince Kinga Anbata wani Abu ba eh nace da ita, to ki nitsu sosai zan Baki wani Ay ki toh Anty Ina jiki.
Daga can b’an gar’an Anty Saudat taci gaba da magana” Heedaya ki kulla gishiri A farar Leda saiki samu baka kisa Aciki, sannan kije cikin kitcheen din Meeran kice Zaki tayata Aiki duk inda maganin yake baza tayi nisa dashiba.
Saiki faki idonta ki canza maganin da gishirin San nan ki Kira kafin kifito kitabbatar kinga ta Dan Dana Abincin saboda mu tabbatar Bata zuba Maganinba kafin ki shiga.
Kiyi sauri kije kiyi Abinda nace Ammafa ki kiyaye Heedaya”, Amsawa nayi San nan ta datse Kiran, kitchen Dina na nufa na d’auki gishiri nayi yadda Tace sannan na makale kuguna na fita.
A kitchen Na sameta ta hada zufa sosai tana ta faman girki da Sallama nashiga nace Mata Anty sannu da Ayki Amsawa tayi tana ta kokarin kammala Abincin matsawa nayi gurin sink nace Mata” bari natayaki da wanke wanke batace min uffan ba domin batani takeba, Wucewa nayi nakama wanke wankena Amma Ina kallanta ta gefen Ido can sainaga ta bude ta Dan Dana miyar stew din A zuciyata nace Alhamdulillah sainaga ta fito da bakar ledar da Ummi ta bata kuma ko me ta tuna saita Ajiye Akan drowern kitcheen din ta shige cikin store da A Zama na dauke nasa Mata gishiri.
Lokacin data fito harna Gama nace Mata” natanfi” Nagode tacemin batareda tabi ta kainaba ta Baya nazagaya nasa ledar Ashara sannan naje na labe tawajen tagar kitcheen din can na hangota ta zuba Abincin cikin kuloli Sai Naga ta d’auko ledar Dana Ajiye ta barbada Kan Abincin, wani wuri nasamu nadan jima sannan na koma babban falo, ta rarwa nayi harta jera Abincin ta nayi murmushi sannan nakoma daki nakira Anty Saudat.
Bayan ta daga nai Mata Baya nin Abinda ya faru hamdala tayi sannan tace” nakuma sa Mata Ido Kan meerah.
WASHE GARI………..
Meerah shiru shiru taga tsaka nin nida Yaya ba Wanda yay ko ciwan ciki Nan ta tada bala’i Abu kadan Sai masifa Kota kusa da’ita na wuce Sai Tace na takata tasa Yaya yay tayimin bala’i hakan bai ishetaba Tace ita yanzu ba Abinda zata dingayi haka Aykin gidan yadawo kaina.
Inaji inagani banida bakin magana saboda cikin jikinta, bayan Aykin gida har sharar daki take sani da wankin toilet, haka Yaya kesani gaba nayi Dan dole ba yanda zanyi.
Haka naketa Shan Azaba Acikinsu kullum Sai shegen Aiki ga hantara ga ba godiya.
Wata Ranar lahadi Ina kwance Ina barcin wahala naji an kwaramin ruwa Ajikina figit natashi Naga Meerah Akaina panties dinta ta watsomin Kan fuskata sannan ta jefeni da wani mugun kallo wai nadauka naje na wanke. Kallan bakida hankali nai Mata sannan narike kuguna nace” bazan wanke ba kiyi Abinda Zaki kiyi, dan yau masifa nakeji Sai dai duk Abinda ze faru ya faru, hannu tasa ta yarfan Mari muka Kama ko kawa da ita dama Abab ban falone muke mune har bakin kofar shigowa, muna zuwa na Murda kofar ta bude na daddage na wujjigata na wurgata Kan step din da Ake yajawa in za’a shigo, Sai kuwa ta Fada tafara min ginawa Kan kace kwabo jini ya Fara malala dan ta Fada da karfi.
SHURIEM ne ya dai daita parking din mota ya fito yayo burinmu da sauri duk don duk Abinda ya faru Akan idansa ya faru……⁴⁵,⁴⁶