IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 5 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 5 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Daga nan sai aka ce Ango ya zo ya ba matanshi abin sha ko naci. ‘Yammata masu sanye da kaya iri daya su uku, su ne suka zo suka kawo wani dan tire. a rufe, daya da ‘yan kofuna guda uku, dayar kuma da hankici na share baki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta bude dan tire din, nakiya ce guda uku, ya dauki daya ya ba Aliya ta gutsura, aka yi tafi gami da rangada guda.
Mai kofunan ta matso, ya dauka madarar shanu ce wadda ba a jima da tatsowa ba, ya kurba mata, sannan me hankici ta kawo ya dauka ya share mata. Duk su ukun hakan ya yi musu.

“Sai da yamma immediately after four” Ya dauko wani kwalli da aka daure da wani jan ribbon ya bata tayi masa godiya suka yi sallama. Bata san tsawon lokacin da Kamal ya zo
ba, motar shi kawai ta gani fake a kofar gidansu, cikin karfin hali ta karasa wajen da yake ta kwankwasa glass din motar fitowa ya yi a fusace yana yi mata wani kallon kaskanci kallo na wulakanci.
Ta kasa hada ido da shi saboda ta san asirinta ya gama tonuwa, cike da borin kunya da salon a nade tabarmar kunya tace “Kamal tun yaushe ka zo? Me yasa ‘baka yi min waya ba?, ni bansan zaka zo ba…” Ya katse ta.


“Dakata Mallama kar ki nemi ki raina min hankali, rannan kin cemin waccan mutumin abokin yayanki ne, yau kuma me ya kara dawo da shi wajenki? Ko duk abotar ce haka?”. Kanta ne ya kulle ta rasa abinda zata ce da shi abinka da mara gaskiya.
“Wato kina tuna abinda za ki ce min sabida kin maida ni shashasha?” Tambayar tashi ta fusata tace “Me yai ruwanka da abinda ya zo yi, kai dai kayi abinda ya kawoka domin ba igiyar aurenka bace a kaina balle harkace bani da ikon kula kowa sai kai don haka bazan yarda da tuhuma ba”. Ji ya yi wani abu ya tsaya masa a


Www.bankinhausanovels.com.ng
mako shi domin Safina tayi matukar bashi mamaki, bai taba tunanin haka take ba,wani murmushi yake ya yi dake nuna damuwar dake tare da shi karara yace.
“Safina kenan a gaskiya kin bani kunya kar kiyi zaton har yanzu ban san halin da kike ciki ba, kawai dai ina biye miki ne da sa ran ko za ki gane ki dawo kan hanya amma ina sane da duk motsinki a school da kuma mu’amalarki a cikin gari, babu yanda za a yı na auri mace da bata san mutuncin kanta ba bata san darajar dan adam ba”. Maganganun nashi suka kara tunzura ta tace.
“Ashe zargina kake yi kenan? To bara kaji in fada maka idan ma kannen nan naka ne suka fada maka hakan to na yi, sai ka dauki matakin da ya dace”. Ya lura abin nata ya fara yawa dan haka shima ya harzuko “Kar ki kara shegentamin kanne domin su ba irin ki bane, ai su suna da hangen nesa da sanin ya kamata domin lokacin da suka lura da yanda na kamu da sonki basu taba fada min komai akan ki ba, daga baya Allah ya sassauta min sonki a zuciyata kuma da kaina na gudanar da bincike akan ki.
Me neman kuka ne daman aka jefe shi da kashin awaki, dama abin nema ne ya samu wai matar falke ta haifi jaki, burin Safina bai wuce na
Www.bankinhausanovels.com.ng
samun wata kafa da zata rabu da Kamal din ba, gashi kuma yanzu ta samu dan haka tace “Ni wallahi ba zan ci gaba da zama da mutumin da yake zargina ba, dan haka sai kaje kannen naka su aura maka mai hankali ko kuma ka auri daya daga cikin su kowa ya huta”. Cikin mamaki yace.
“Kan ki daya kuwa? Kannen nawa kike cewa na auri daya daga cikin su, koda yake ai ba abin mamaki bane tunda Hausawa sunce jahilci yafı hauka muni”.
Ta Harare shi “To sarkin malamai kai a naka ilimin babu aure tsakaninka da su? Naga ai ba iyayenku daya ba, ko kana tsamanin ban san komai ba? Sai kaje ka ci gaba da boyewa wadanda basu sani ba amma bani ba”.
Maganganunta suka saka jikinsa ya yi sanyi ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin yace “Safina kenan, ke a tunaninki na boye miki hakan da wata manufa har ga Allah ban boye miki da wata manufa ba, na yi haka ne saboda yadda Alhaji ya rike ni kuma ya yi min komai a rayuwa, bugu da kari kuma kanin mahaifina ne shi, ba zai ji dadi na rika nuna masa iyakarsa ba ina cewa ba shi ne ya haife ni ba, to amman tunda haka kika zaba na gode Allah ya hada kowa da rabonsa na akheri, amma ki sani akwai ranar kin dillanci, kuma bana bukatar komai a
Www.bankinhausanovels.com.ng
cikin kayan auren dana kawo gidanku na bar miki albarkacin kaunar da nake miki, kullum ki rika tunawa ke kika guje ni bani ne na guje miki ba, zan rabu dake badan ina so ba, na barki lafiya”. Ya koma cikin mota ya zauna ya mayar da kofar ya rufe ya fizgi motar a guje ya barta tsaye cike da kunyar abinda tayi, tafi kowa sanin halin Kamal, mutum ne mai sanyi da kuma tsananin hakuri a iya zaman su tare da shi ba zata iya cewa ga rana daya daya ɓata mata rai ba, gaskiya bai cancanci wannan sakamakon ba, amma ai laifin shi ne ya fiye kishi da sanya mata ido, idan ba rabuwa ta yi da shi ba bazata taba sakewa ba, ita kuma yanzu ta gane ita matar manya ce ba kananun kwari ba irinsu Kamal ba. Tana nan a tsaye ta tuna da Sulaiman a lokacin da tayi masa makamancin wannan rashin mutuncin tsaki kawai taja dake nuna ko a jikinta ta juya ta shige gida babu wata damuwa a tare da ita.
Ranar Monday bayan sun fito daga lakcar farko suna tare da wata kawarta tana yi mata bayani akan darasin, suna tsaka da yi Lalla tayi sallama kawar Safina ce ta amsa amman ita ko kallon su bata yi ba, bayan sun kamala karatun ne ta fahim.ci suna bukatar kebewa ne sai tayi
Www.bankinhausanovels.com.ng
musu sallama ta tafi Safina ma ta shiga hada kayanta zata bar wajen kamar bata san da su ba.Sai Laila tace “Haba Safina Yusuf wajen ki
muka zo ai ya kamata ki ara mana lokacin ki
koda kanka ni ne”.
Ta kalle su da wani kaskantacen kallo ta watsar ganin Laila na maida mata martanin kallon tace “Bana jin zan iya domin ina da abin yi”.
Ran Safiyya ya ɓaci matuka amma ta danne tace “Muma muna da abinyi amma dan Allah ki daure ki saurare mu”.
Jin haka sai ta koma ta zauna “My ear are for you”.
Hakan ne ya baiwa Safiyya damar fara maganar data kawosu “Ko kadan bamu ji dadin abinda ya faru tsakaninku da ya Kamal ba, tun farko kauna ce ta hadaku bai dace ku juye zuwa kiyayya ba, babu bukatar a tsaya jin ba’asi abinda ya faru, kamata ya yi ku tattara komai ku watsar a bayan bayanku ku fuskanci rayuwarku ta gaba ta hanyar maida soyayyarku kan bigire da take a baya, masoyi har abada sunan shi masoyi baya taɓa zama makiyi, ina da tabbacin har yanzu kuna son junanku, bacin rai ne kawai ya kawo matsalar da ake ciki”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Safina ta jefi Safiyya da wani irin wulakantaccen kallo kafin tace “Wato zuwa kuka yi ku yi min dadin baki ko, duk ba ku kuka hada munafircin ba? Ai nasan komi bai kamata ku zo wajena ba sai kuje ku bashi wacce kuke so ya aura ko kuma daya daga cikinku ta aure shi, ai akwai aure a tsakanin ku”. Laila ta zaburo.
“Ke Safina mind your language, karki kara zaginmu domin mu bamu san abinda ya hada ku ba, laifin mu ne da muka zo inda kike, dama shi yaya tuni ya rufe babinki, mune kawai muke fatan komai ya dawo daidai, amman yanzu mun fahimci baki dace da yayan mu ba tsarin rayuwarki da tarbiyarki ba su dace da na gidanmu ba, akan haka muke yiwa yayanmu fatan samun matar da tafiki managartar halaye”. “Oho dai, ai ni na fara cewa bana yi”.
Ran Laila ya baci dan haka sam taki saurarawa Safina ta shiga maida mata da martini “Banda ma abin big bros har wannan kucakar ta isa ta bashi headache?, Ga ‘yan mata nan a gari masu asali ya ‘yan manya mutane ba kwadayayyu ba wadanda abin duniya ya rufe musu idanu”. Haka Laila ta zageta ta rika zarowa Safina Magana da gore-gore da ma an ce baki idan yasan abinda zai fada bai san abinda za a mayar masa ba, Safiyya tayi ta kokarin janye
Www.bankinhausanovels.com.ng
Laila gudun karta tara musu jama’a amma abin ya gagara, basu ma san lokacin da Safina ta sulale tabar wajen ba.
Tun daga wannan lolacin suka shiga takun saka da Safina, a duk lokacin da suka hadu kallon banza ne yake raba su, ita kuma Safiyya babu ruwanta duk wajen data ga Safina tana mata Magana kamar wani abu bai hada su ba, a wurin Safiyya wannan ba wani abu bane, Safinar ce ma a kasa tunda ita tayiwa kanta asarar miji mai saukin kai da sanin ya kamata gwarzon namiji.

**

A daren wata juma’a Mallam Yunus ya tattara ahalinsa waje guda kamar yanda ya saba yi lokaci zuwa lokaci idan wani abu mai muhimmanci ya taso wanda ya shafi Iyalin kai tsaye, bayan haduwar tasu ne kowa ya kasa kunne domin jin abinda za a tattauna tunda dai sunsan ruwa baya tsami banza.
Mallam Yusuf ya fara maganarsa cikin nutsuwa da salon Magana irin tasu ta manya yace “Sanin kan kune cewar a duk lokacin da na nemi a hadu a zauna makamancin wannan to babu shakka wani muhimmin abune ya taso dake bukatar a sanar daku a jiya ne na karbi
Www.bankinhausanovels.com.ng
bakuncin wani mutum mai suna Mallam Bala wanda ya bayyana kanshi a matsayin mahaifin wani yaro dake neman auren kanwarku Naja’atu, kwanaki kadan sai dana samu wani yaro daya bayyana kanshi a matsayin wanda yake neman auren Fatima, yace min ya jima yana tuntubarta akan ta bashi dama ya fito tace masa ya dakata tukuna ba a yi auren yayarsu ba, yaushe za a yi nasu, a lokacin sai nace ya bani sati daya domin naji matsayinsa a wajen Fatima idan ta amince sai kuma nayi bincike ‘idan naga dacewarsa sai na bashi damar turo manyan nasa dan ayi maganar auren.
Zuwan mahaifin manemin Naja’atu ne ya kara min kaimi taraku dan musan abin yi akan batun,daman tuni na tuntubi Fatima akan mane min nata na kuma fahimci tana son shi, haka itama Naja’atu na tuntubeta da safe na fahimci itama tana son shi”. Mallam Yusuf ya gyara zama tare da fuskantar Safina yace “Safina tunda Allah yasa tuni maganar Kamal da kayan aurensa sun jima a gidan nan mezai hana ki sanar da shi cewar ya turo magabatansa domin a tsayar da lokacin biki in yaso sai a hada a yi lokaci daya dana kannen ki ko ya kika gani?”.
Gabanta ya yi wata mummunar faduwa
sabida maganar ta zo mata a bazata, daman
Www.bankinhausanovels.com.ng
tasan za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, daman tatsuniyar Gizo bata wuce ta koki, tasan babu yadda za a tashi wannan ba taso da maganar aurenta da Kamal ba, ta lura da yadda duk mutanen gida suka matsu suga tayi aure musamman ma innarta, bayan fargabar dake tare da ita kuma harda mamakin maganar aurensu Fatima, shin nawa ma su Naja’atu suke da har za a yi maganar aurensu? Dududu shekarar su nawa? Gara ma Naja’atu da tayi candy bara amma ita Fatima bana ma tayi candy, su da aka sai musu form din school of Nursing za su su ci gaba da karatu ya za su yi da karatun nasu kenan? Koda yake basu suka fi bata haushi ba, samarin nasu ne suka fi bata haushin musamman ma Muhmod saurayin Naja’atu da tuni ta gama lura da take-takensa da yanda yake rawar kafa a duk lokacin dayazo wurin zance wajen kanwarta tana kokarin hada abinda zata ce sai Abban nata yace. “Safina ke fa muke sauraro, bamu taru
anan dan kawai mu kalleki ba”. Tace “Baba dama…dama…” Ta sake yin shiru.
A fusace yaya Isma’il yace “Dama me? Ki bude baki ki yiwa mutane Magana, ba ki zauna kina inda-inda ba”. Mallam Yusuf yace.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Idan kunya kike ji ga innarku nan ko
kuma Umma sai ki sanar musu”. Take wata dabara ta fado mata tace “Aa ba haka bane Baba”.
“To mene ne?” Ya sake tambayarta cikin
yanayin matsuwa da son jin abinda yake bakinta. “Baba na san yanda kuke son ganin na yi aure, nima burina kenan amman gaskiya Kamal bai dace da mijin aurena ba saboda sam ba mutumin kwarai bane…”
Jin inda ta dosa sai Babanta ya dakatar da ita “Safına a duk lokacin da maganar aure ta taso dole ne a samu mutanen ‘yan bani na iya, za su yi ta kokarin batanci a kowane bangare, ke kinsa abinda ake fada masa akan ki? Idan kika biye ta zancen mutane to babu abinda za ki yi a rayuwarki, mu kanmu kina sane toshe kunnuwan mu muka yi akan surutan da ake yi akan mun barki kin gandame a gida ba tare da kin yi aure ba, haka fa kika biyewa zantukan mutane kika bata da yaronnan Sulaiman idan kika ci gaba da biye musu sai dai in ba za ki yi aure ba”. Tace.
“Baba ai shi Sulaiman danginsa ne basa sona, saboda suna da wacce suke son ya aura, amma shi Kamal dan yaudara ne, bashi da aiki sai yaudarar ‘yan mata, ba aure ne a gabanshi ba, ya sha kai kudin aure gidajen ‘yan mata

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE