IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 6 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

 IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 6 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya

kanmu kina sane toshe kunnuwan mu muka yi akan surutan da ake yi akan mun barki kin gandame a gida ba tare da kin yi aure ba, haka fa kika biyewa zantukan mutane kika bata da yaronnan Sulaiman idan kika ci gaba da biye musu sai dai in ba za ki yi aure ba”. Tace.
“Baba ai shi Sulaiman danginsa ne basa sona, saboda suna da wacce suke son ya aura, amma shi Kamal dan yaudara ne, bashi da aiki sai yaudarar ‘yan mata, ba aure ne a gabanshi ba, ya sha kai kudin aure gidajen ‘yan mata

amma da zarar ya fahimci manufarshi akan su sai ya janye yace ya fasa auren”. Ta fara hawaye kamar gaske, duka mutanen dakin jikinsu ya yi sanyi.
Amma duk da haka sai Baba yace “Safina me yasa ni nawa binciken bai gano min haka ba, sai ma kyakkyawar shaida daya samu a wajen jama’a? kuma ai ko kallon Kamal ka yi zaka kyautata masa kyakkyawan zato”.
“Idan har kana da kudi a wannan zamanin babu mai fadar laifinka,kuma ita fuska ai ba ma’auni bane, ni kaina da aka fada min hakan kin yarda na yi sai daga baya na gano manufarshi”. Tadan nisa kafin ta kara da cewar “Kuma ai wasu basa yin aikin assha a inda aka san su dan gudun kar mutuncinsa ya zube. Iyayen Kamal mutanen arzikine, haka ma ‘yan uwanshi mata shi ne dai ya fita zakka”.
Mallam Yusuf ya yi ajiyar zuciya yace “Shi kenan zan kara bincikawa”.
Safina ta yi caraf tace “Baba ai ba sai ka bawa kanka wahala ba, ai ba zai kara zuwa kofar gidan nan ba, duk da cewar ya kawo kudin aurena, amma ba zai iya zuwa ya karba ba sabida yasan asirinsa ya tonu, daman duk inda ya cima burinsa ko kuma aka gano nufinsa tunda wuri ba za a kara ganinsa ba, idan da yana da


Www.bankinhausanovels.com.ng
gaskiya ai zai nemi a dawo masa da kudin aurensa, amma da yake ya san bai taki gaskiya ba ko hanyar unguwar nan ba zai sake biyowa ba”. Safina ‘yar duniya tana rufe bakinta ta fashe da kukan munafurci dan ‘yan uwanta su yarda da ita.
Yaya Abbas ne yace “Yaushe za a bi takan wannan batun, kawai ta kawo wani cikin manemanta sai ayi da shi”. Cikin shassheka tace “Ni yanzu bani da wani tsayayye a hannu, karfina gaba daya yana tattare dashi kuma ya bula min kasa a ido” Inna data cika tayi fam tace.
“Mallam nifa ina da shakka akan batun yarinyar nan, auren ne kawai bata so shi yasa ta tsiro da wadannan karya, haka siddan kawai fa ta kori Sulaiman ai daman nasan mayuwanci ne ta samu kamarsa”.
Safina ta kara rushewa da kuka tace
“Baba tunda Inna ta gaji da zama dani na
amince ka samo kowane ne ka hadani aure da
shi, ni kuma na yi maka alkawari zan danne zuciyata na zauna da shi koda kuwa bana son shi…” Kuka ya kara kwace mata kamar da gaske.
Tausayinta duka ya kama mutanen falon shi kuwa Saba yace “Ki kwantar da hankalin ki ni
Www.bankinhausanovels.com.ng
babu wand azan hadaki da shi, insha Allahu da kanki za ki zabowa kanki miji ki kawo shi nan”. Umma da tun da aka zauna batace kala ba ta kada baki tace “Amman duk da haka bai kamata abiyewa Safina ba, ko me za tayi auren nan dai shi ne gatanta dama duk wata ya mace ai bai kamata a aurar da kannenta a gabanta ita tana zaune a gida ba”.
Amman duk. da haka sai Mallam Yusuf yace “Ai ba dole sai ta rigasu aure ba, babu inda aka ce tunda ta girme su sai ta riga su aure, shi aure lokaci ne”. Ya juya ga Safina “Kar kuma kiga mun goya miki baya kice za ki kawo shasshanci karatu dai baya hana aure tunda ga kannenki nan a dakunansu za su ci gaba da karatun su da zarar Allah ya daidaita tsakaninki da wani sai ki turoshi ayi Magana ba wai sai kin gama karatu ba, burin duk wasu iyaye shi ne suga sun aurar da ‘ya ‘yansu mata domin su sauke nauyi dake kan su”.
Nan da nan ta share hawayenta, cikin murna tace “Baba na gode insha Allahu ba za a samu ba”. Tayi saurin ta fice daga cikin dakin ganin irin kallon da Inna take binta da shi dake fayyace tsantsar fushinta da take ji, ita ta rasa dalilin da Inna tanAce lallai sai ta yi aure yanzu, dan tasan irin miji da take son kawo
Www.bankinhausanovels.com.ng
musu bane shi yasa take damuwa, da ace tasan shirinta na samun miji na gani na fada da bata nuna damuwarta ba, haka kuwa ta kasa gane irin kaunar da Inna take yiwa Sulaiman da har yanzu bata dana yi mata mita akan rabuwarsu ba.
Da wadannan karyace-karyacen Safina ta kubucewa auren Kamal maganar ta shirice aka watsar da ita baki daya, sai dai duk da haka Mallam Yusuf ya sha korafi daga wurin ‘yan uwansa na karkara saboda karo na biyu kenan maganar auren Safina na wargajewa gashi har ana shirin kara aurar da kannenta har biyu bayan auren Rahama da aka yi shekaru ukun da suka wuce.
Safina ta samu wannan damar ne saboda irin yardar da mutanen gidansu sukai mata, sanin halinta na baya da suka yi ne yasa suke tunanin har yanzu tana nan bata sauya ba, shi yasa basu cika damuwa su zurfafa bincike akan duk abinda ta sanar da su, watanni shida aka saka domin auren su Naja’atu.

**

Bata san ya aka yi ba suna komawa hutun da suka shiga final year sai ta tarar wai an daurawa Kamal aure da Laila hadawa aka yi da
Www.bankinhausanovels.com.ng
bikin Safiyya aka yi lokaci guda, wani abinda bata sani ba shi ne daman can suna son junan su ko kuwa hadin iyayen su ne? ko kuma sun hakan ne sabida gatse data yi musu? Bata taba sanin tana son Kamal da kishinsa ba sai data ji ya auri Laila, kishi da wani irin matsanancin bacin rai suka ziyarci zuciyarta, ranta bai dada baci ba sai data ga yadda Laila tayi wani fresh, ta kara cika tayi bul-bul daga gani auren ya amsheta, haka kullum tana gani Kamal zai kawota makaranta kuma ya zo daukarta akan lokacin baya barinta tayi jira, yana matukar bata kulawa tamkar ya hadiyeta, Safina dan kunyar kanta da kanta bata taba barin Kamal ya ganta ba, sai dai ta labe taita kallonsu, shima ya sauya sosai kamar bashi ba, babu shakka ya samu mace daya da daya daba zai kara tunawa da ita ba balle har ya ji takaicin abinda tayi masa.
Tunda suka koma hutun kullum cikin damuwa take, ji take yi tamkar zuciyarta zata tarwatse, ba wai dan tsananin son da take yi masa take cikin damuwar ba, kishi Laila da irin kulawar data ga yana nuna mutane yake damunta, sai da tayi da gaske sannan ta iya yakice abin daga ranta ta watsar da duk wani tunani tunda Kamal din nan fa ita ce ta kishi bashi ne ya gujeta ba, kuma ma tasan irin mijin da
Www.bankinhausanovels.com.ng
zata samu a gaba? Ta san tana da haduwar da mijin aure sai ta zaba ta dirje, a yanzu kam ta santa kara tsada, shi yasa ba zata yi aure yanzu ba har sai ta kammala karatunta, tasan a lokacin ba kowane namijine zai zo wurinta ba sai wanda ya isa.
Shirye-shiryen bikin su Naja’atu ya kankama gadan-gadan domin lokaci yana matukar karatowa, ana ta siye-siyen kayan amare, Alhamdullahi su Naja’atu sun more da kayayyaki sosai domin su yaya Isma’il ne suka yi komai, ko tsinke basu bari Mallam Yusuf ya siya ba, gasu sunci sa a Safina ce akan gaba komai nasu mai kyau mai tsada take zabar musu dan ma wannan karon duk bikin ya bata haushi bata wani zakewa a harka, dalili kuwa duka angwayen basu yi mata ba, shi mijin Fatima mallamin wata sakandire ne yayin da mijin Naja’atu ya kasance ma aikacin hukumar Nepa, yanda Safina ke son rayuwar daular haka takeson duk kannenta su kasance a ciki, abin haushi wai duk kyau da kwakwalwar Naja’atu ta kare a auren dan Nepa kuma karamin ma’aikaci.
Bikin saura kwana takwas Safina tana a dakinsu tana tattara muhimman zaune ajiyoyinta waje guda dan gudun kar a shiga kacaniyar biki ayi mata sata, Naja’atu amaryace
Www.bankinhausanovels.com.ng
ta shiga dakin tana amsa waya, da alama ma da angon take waya saboda irin nishadin da take ciki da kuma yanda take Magana cikin siririyar murya, sun dade kamar ba za su rabu ba sannan suka yi sallama.
Safina taja tsaki “Yanzu Naja’atu a matsayina na ‘yar uwarki duk shawarar dana baki kin watsar ko? Babu wani tunani kin yi saurin yardarwa Mahmod, duka-duka yaushe kuka hadu? Ko shekara baku yi ba amma har za a ce aure?”.
Naja’atu ta kauda kai gefe alamun zancen bai gamsar da ita batace “Yaya Safina kenan, kawai dai kice bai dace da irin mazajen da kike so ba, da ace mai kudi ne ko yau muka hadu da shi nace zan aure shi cewa za ki yi ya yi”.
Safina tace “Ni ba cewa na yi bai dace ya zama mijinki ba, ina ganin akwai bukatar ku samu lokacin da za ku fahimci junanku kuma kinsan wane ne shi”. Naja’atu tace.
“Kinga ni kuma ra’ayina ba irin naki bane, sam ban yarda da soyayyar ɓata lokaci ba, ai tunda na yi masa shima ya yi min kuma raayinmu yazo daya kuma zai barni na ci gaba da karatu, ɓata lokaci ma kawai za mu tsaya yi, ai soyayyar gaskiya kawai ayita a gidan aure”..
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mamaki ya kama Safina tace “Au yau da bakin ki Naja’atu kike cewar aure yafi karatu>> Naga da kullum maganar ki ita ce baki da lokacin soyayya ke karatu za ki yi har sai kin samu kwalin digiri”.
“Ai ko yanzu ban ce zan bar karatun ba, insha Allahu zan yi karatun”. Safina ta tabe baki tare da girgiza kai tace “Lallai Muhmod din nan ya kwance miki kai, amma da farko dayace yana sonki ai baki bashi hadin kai ba, da ace ya yi zuciya ya rabu dake maga yanda za ki yi”.
“Ai ko ya tafi sai Allah ya kuma hadamu ta wata hanyar tunda ya kaddara shi ne mijina…” Safina ta katseta “To ya ishe ni uwar tsari,aci soyayya lafiya, ni dai ki fada mai ya shirya mana biki na fita kunya kar mu gayyato mutane mu zo muji kunya domin bana son harkar karanta”.
Naja’atu ta girgiza kai tace “Gaskiya abinda Allah ya hore shi za a yi domin daidai ruwa daidai tsaki, ba wata karya za mu yi ba, fatan mu dai Allah ya bamu zaman lafiya”. Tsananin mamakin da Safina ta tsinci kanta ya hanata cewa komai.
Washe gari suka je wani bridal boutique inda ake saida bridal set da accessories kamar koda yaushe Safina tauraruwace duk inda taje
Www.bankinhausanovels.com.ng
sai ta haska saboda kyau da kwarjininta, ita da amaren ne da wata ‘yar kanwar Umma mai suna Rumanatu. Da zuwansu mai kanti ya nuna yana son Safina, ita kuma ta biye masa ta hanyar cika shi da kalamai dadada tamkar sun shekara da sanin juna, shi kuwa sai washe baki yake yana zaton ya samu karbuwa.
Bayan sun gama siyayya ya yi musu ragi sosai sannan ya basu kyautar kayan da za su yi bridal maid ya kuma karawa Safina da wasu kayan na musamman. Suka yi musayar lambar waya kafin ya raka su zuwa mota, suka shiga tasi ya biya musu kudin motar suka tafi suna dagawa juna hannu.
Suna fara tafiya Safina ta kwashe da dariya “Wahalallen banza mara aikin yi, ai sai ya yi ta yi domin lambar ma ta bogi na bashi don bazan iya bashi lambata ba”.
Cikin mamaki Rumanatu tace “Bangane ba yanzu kin san ba kya son shi amma kika sakar masa fuska har ya yi mana irin wannan hidima haka amma wannan ya zama yaudara”.
Naja’atu tace “Ai ke ce baki san halin yaya Safina ba, wannan kadan kenan daga aikinta”. A fusace ta juyo ga Naja’atu “Ke mind your language, kisan da wadda kike Magana, mene ne da ni daba a sani ba?”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Rumanatu tace “Gaskiya kin bani mamaki, ai ko a fuska baki nuna ba kya son shi ba, ashe duk yaudara ce”.
Sai a lokacin Fatima ta saka baki tace “Wai me yasa kuka damu kanku naga ba rokon shi muka yi ba, maganin irin su kenan”. Jin ta samu goyon baya sai ta amshe.
“Nima dai haka na gani, ai ba a tausayin maza a wannan zamanin, ai ni na yi mishi favour da ban barshi ya yi wahala da yawa ba, tausaya mai nayi”.
Naja’atu ta yi dariya “Gaskiya kam ba a barshi ya sha wahala irin wacce Sulaiman da Kamal suka sha ba”.
Safina ta kuma harararta “Naja’atu ki fita daga idona na rufe, ba dake nake Maganar nan ba amma na lura gigin auren nan yana so yasa ki manta cewar a gaba dake nake”. Ta juya ga abokiyar maganar tata wato Rumanatu “Kin gane ko Ruma, he is not my type, inazan kai wannan mutumin da wannan rusheshen cikin sa? Ai sam bai dace da ni ba”. Tuni Rumana ta kosa da zancen sabida ta lura maganar tafi karfinta, dan ko a karshen hirar sai tace “Allah ya kyauta”. Amman a ranta mamaki ne ya cika ta “Ita kuwa Safina me ta dauki rayuwa ne? bata san rawar ‘yan mata ce na gaba ya koma baya.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE