IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 11 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 11 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Da wannan takaicin ta kwana, amman washe gari cikin farin ciki ta farka sabida wayar Kamal ce ta tasheta daga bacci, kuma ya fada mata maganganu masu dadi, bayan sun gaisa farin ciki ya mamaye zuciyarta domin tun tafiyarsa bai kirata a wayaba, ganin tsararrun nambobin kasar waje yasata murmushin jin dadi cikin nishadi tana daga kwance ta manna wayar a kunnenta ta dan kwantar da murya tana dariya, “Hello Kamal yaya kana lafiya?” Daga daya ɓangaren yace.
“Yaya mutanen Nigeria da fatan kowa yana lafiya?”. Tace “Kwarai kowa yananan lafiya”.

Da kyau haka ake so, yaya kike?” Tace
“Nima hakan nake sai tunaninka daya cika min
zuciya”. Cikin jin dadi yace mata Nima kamar
yanda nake kenan, nima begenki yana neman ya
narkamin da zuciya”. Ta sheke da dariya
zuciyarta cike da nishadi”
Anya Kamal da gaske kake kana jina a
ranka kamar yanda nake jinka?”
Ina ji mana shi ya saka nake Allah-
Allah na dawo Nigeria domin naga kyakkyawar
fuskarnan taki mai cike da annuri ko kinsan bana
gajiya da kallon fuskarki domin ganin idonki yana
sanya zuciyata cikin nishadi”. Tadan basar kamar
bata ji ba sannan tace “Yaushe zaka dawo ne? Www.bankinhausanovels.com.ng
Yace Gaskiya zan dan kwana biyu sabida ni
kaina bansan takamaimen lokacin da zan dawo
ba, amman bana jin zan dade sosai, da zarar an
gama abinda ya kai ni zan juyo gida domin yanzu
I have life duk inda nake zuciyata tana tare dake,
me zan kawo miki tsaraba?”


Banson komai bukatata kawai Allah ya
dawo min da kai lafiya”. Ya ji dadin addu’arta
cikin murmushin farin ciki yace “Ina godiya amma
dai nafi son nasan abinda kika fi so” Tace Ba
damuwa kana iya kawo min abinda kake ganin ya
dace da ni” Yace.
Ai ni idan za ki barni komai na Ingland
gani nake ya dace dake”
Haba dai-haba dai ba komai ba”.
Safina cikin dariya daga karshe waya yace What
a beautiful music” Tace “A inda kake”.
Aa ina nufin dariyarki kamar busar
sarewa take a kunnuwa na, zazzakar muryarki
kuwa takan koremin duk wani bacin rai, shiyasa
idan kina Magana bana son ki daina”. Kalamansa
Sun jefata cikin nishadi har bata son su daina yin
waya amman daga karshe dole suka yi sallama,
Safina tana matukar murna haduwarta da Kamal
sabida gayen ya hadu da yawa, gashi ya iya
SOyayya sosai, kalaman shi suna
burgeta, ko tunawa tayi dashi sai ta tsinci
Zuciyarta a cikin nishadi da farin ciki.
Duk irin wulakanci da kora da halin da
Safina ta ke yiwa Sulaiman da farko bai gane inda
ta dosaba sai da tafiya ta yi nisa shi ya dauka
karatu ne ya dauki zafi shi ya saka bata samun
cikaken lokaci kamar yanda tafada, shi yasa yake
daga mata kafa, ya rage yawan ZUwa gidansu sai
lokaci-lokaci yakanje zance, amman ya wancin Www.bankinhausanovels.com.ng
lokuta sai dai su gaisa a way shima daga baya
sai ya daina damunta da wayar saboda duk
lokacin daya kirata sai tace masa tana wani uzuri
littafai, ire-iren
wadannan abubuwan ne yasa baya damuwa da matsa
mata domin tasamu
ko kuma tana nazarin wasu
yakan tsahirta waya,
nutsuwa, baya son ya kade mata hankalinta akan
karatun ta gwara ta nutSu ta maida hankalinta sai
dai ya lura da wasu sauye-sauye a tattare da ita,
sam ta daina nuna masa damuwa koda ya kirata,
kuma daya je gidansu da kar yaje duka bai
dameta ba gashi kuma ta hanashi zuwa daukota
daga makaranta, tun abubuwa basu dame shi ba
yanzu har sun dawo suna damun shi, domin bai
san dalilin sauyinta ba.
Yanzu har takai wayarsa sai taga dama
take dagawa, idan bata ga dama ba sai tayita
ringing har ta katse ba za’a dauka ba. Wannan
abun ya soma tada masa hankali, ya fara tunanin
ko dai wani laifi ya yi mata bisa kuskure, shi yasa take son hukunta shi ta wannan hanyar,
idan ba hakaba me ya yi zafi da har zata dinga yi
mai wulakanci, ya yi iya tunaninsa har ya gaji
domin ya gano babu abinda ya yi mata take fushi
da shi, dan haka ya ci gaba da yi mata naci ko
zata sauko ta ci gaba da kula shi, yau ma ya cije
ya kuma kiranta a waya ta yi ringing kamar ba za
a dauka ba sai da ta kusa tsinkewa sannan aka
daga.
Hello” Ta fada a hankali kuma ba a
cikin dadin rai ba, jikin Sulaiman har rawa yake yi
Jin muryata yace “Safina ya gida ya kuma jin dadi
da fatan kowa lafiya?” Ta amsa a dakile “Eh lafiya
kalau” cikin sanyin jiki yace.
Ya naji kamar baki gane mai Magana
ba? Cike da rashin kulawa tace “Na gane ba Www.bankinhausanovels.com.ng
Sulaiman bane?” Ya ji wani iri domin yanayin
yanda take maganar a dakile kamar da wani can
bare take magana ba wanda ta sani ba, sam bai ji
dadi ba don haka ya yi shiru yama rasa abinda zai
ce, jin shiru ya yi yawa sai tadan yi Magana
kasa-kasa tace Sulaiman are you there? Ka barni
rike da waya ina fa da aikin yi a gabana”. Ya yi
Magana “Ok kiyi hakuri daman na yi kwana biyu
bamu gaisaba shi ne na bugo miki na tambayi
lafiyarki”.
“Kar ka damu ni lafiyata kalau”.
To ina son idan babu damuwa zan
Bullo gobe domin mu tattauna akan wata matsala
da take shirin kuno kai a tsakanin mu”
Gaskiya gobe bana nan sai dai wani
jikon”. Ya yi shiru sabida rashin sanin abin yi,
domin kanshi ya kulle matuka, jin ya yi shiru sai
kawai ta kashe wayar bayan tace sai anjima ko?
Ya kalli wayar data barshi rike da ita, jikinshi ya yi
sanyi sosai wai yau shi Safina takewa haka abin
har yakai ta kashe mai waya, ita da ada har bata
son in suna waya ya yi sallama, a lokacin zata yi
ta jan hirar zata ce bata gaji da jin muryarsa, to
menene yake faruwa haka tsakaninsa da Safina? Ya
SO ya yakice komai daga zuciyarsa don kar abin
ya janyo masa damuwa amma ya kasa, haka
kuma yaso ya yi mata uzuri don kar yaga laifinta
amman hakan bai samu ba domin zargi da dama
ya shiga zuciyarta har yana zargin akwai abinda
ke shirin faruwa shiyasa Safina take mishi abinda
taga dama.
Washe gari duk da karfin halin da yake
yi amma abin yananan a ranshi damuwar taki
wucewa, har an kawo mishi abinci yasa a gaba
yana shirin ci amma daya tuno Safina da abinda
yake faruwa tsakaninsu nan da nan yaji abincin
ya fita daga ranshi, ya ture kwanon gefe saboda
tsabar damuwa ji ya yi komai ya gundureshi a
yanzu babu abinda yakeso kamar yasan
takamaimai abinda ya hadashi da Safina take yi
mai wulakanci haka? In banda wulakanci tayaya
za’ace wayama ta nemi ta gagara a tsakanin su
bayan ta riga ta sabar masa kullum sai sun ji
muryar juna,kuma sukan dauki tsawon lokaci suna
hira, har batason wani abu ya katsesu, nan take
wani tunani ya darsu a zuciyarshi karfa karatun
Safina ya nemi ya zama barrier a tsakaninsu, shi
yana murna ya samar mata admission domin koyi Www.bankinhausanovels.com.ng
da ilimin da a al’umma za su amfana dashi, ita
kuma tana neman yin amfani da damar ta wata
hanyar daban, nan take ya yanke shawarar zuwa
gidansu Safina domin jin dalilin da yasa take yi
mishi haka.
Ana idar da sallah magaruba ya tafi
unguwar su Safina, yana isa kofar gidan ya samu
wani almajiri ya tura ya kirata, kai tsaye ya shiga
cikin gidan cikin sa’a ita ya soma tararwa a bakin
famfo tana wanke hannu bayan ya yi sallama
yace, Wai ana kiran Safina a waje” Ga alama
yaron’ bai san ita bace tace masa “Jeka’ ka
tambaya wane ne?. Ya fita ya dawo yace mata
Wai Sulaiman ne”. Cikin wani matsiyacin tsaki
tace masa Kace bata nan ta tafi unguwa”. Da
yake ta gane almajirin bai santa ba, badan
unguwar bane, yaron ya komaya fadawa
Sulaiman sam baiji dadin rashin samunta ba, ya
jima a kofar gidan duk jiki a mace, yana shirin
barin
wajen ya jiyo kamar muryata a soro tana
Magana da wasu yara, duk da ya gane muryata
ce domin ko a mafarki bazata bace masa ba,
amman duk da haka sai yake wasi-wasi sam
zuciyarshi taki aminta Safina ce, ya kauda zargin
daga ranshi domin ya tabbatar babu wanda zai
masa karya a gidansu Safina, saidai ko muryar
Fatima ko Naja’atu ya ji, amma ba maganar
Safina ba ita kuwa tunda ta shaidawa almajiri
cewar ace batanan sai ta labe a soro ta aiki yaron
makotansu ya duba ko Sulaiman ya tafi, sannan
cikin sauri taje ta kashe wayarta dan kada ya
dameta da kira.
Sulaiman kuwa ‘daya gaji da tsayuwa
sai ya tafi masallacin dake layin dan yabi jam’in
sallah isha, daganan ya sake dawowa kofar
gidansu Safina domin yaji ko ta dawo, amman
daya sake turawa aka ce bata dawo ba, sai ya
zauna jiran dawowarta yana ta dube-duben
hanya yaga ta inda zata bullo, amma har karfe
goman dare shiru baiga dawowarta ba, haka ya
karaci gyangyadi akan dakalin gidan su Safina da
yaga bata da niyyar dawowa dole ya hau mashin
dinsa ya tafi gidansu zuciyar sa cike da tunane-
tunane, ita kuwa Safina ina ta tafi takai har karfe
goman dare bata dawo. ba? Kodai acan zata
kwana? Anan ya yanke shawarar gobe zai sake
dawowa watakila ya sameta da wannan shawarar
ya kwanta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Washe gari baiyi kasa a gwiwa ba,
magaruba tana yi ya sake komawa gidan su
Safina, nan ma daya aika yaro ya dawo yace
masa ance bata nan, ya sake maida yaron ya
tambaya ina ta tafi? Jin kadan yaron ya dawo
yace waita tafi gidan yar uwarta Rahama,
Sulaiman ya gyada kai ya yin daya zaro ragowar
canjin dake aljihunsa ya salami yaron, nan take
ya zaro waya ya kira nambar Safina amma abin
haushi Sai yaji a kashe take, can dai ya yanke
shawarar ya bita tunda ya san gidan Rahama. Ya
buga babur ya nufi gidan Rahama daga soro ya
tsaya ya yi sallama Rahama da kanta ta amsa ta
leko data ga shi ne tayi masa jagora har cikin
gidan tana ta fadin haba Sulaiman ya ka tsaya a
soro kamar wani bako shigo mana, bayan ta kaishi falo suka gaisa ya tambayeta lafiyar mai gidan
tace masa yana nan lafiya, yanzu ya fita siyo ice
cream, taje ta kawo masa abinci da lemo, ko
soma ci bai yi ba ya soma tambayarta “kardai
mutuniyar bata Zo ba” Tace.
Gaskiya bata z0 ba, domin ta kwana
biyu rabonta da gidanan”. Sulaiman cikin mamaki
Yace “Na yi mamaki da kika ce bata zo ba, domin
daga gidanku nake kuma aka tabbatarmin gidanki
ta zo”. Rahama tace.
Kaga kuma bata zo ba, amman kadan
saurara ko tana hanya tunda daga gida aka
fadama,daba don kar inyima gardama ba sai nace
maka Safina bata zuwa gidana da daddare,
hasalima ya yan gidan mu basa zuwa ko ina da
daddare, Sulaiman ya yi shiru domin bashi da ta
cewa sabida Rahama ba zata yi masa karya ba,
jin ya yi shiru yasa tace.
Bara na kirata naji tana ina?” Nan ta
kira wayarta taji a kashe, ganin duk ya damu ta
shiga kwantar masa da hankali.
Kayi hakuri insha Allahu zan je da
kaina naji dalilin daya sa take rufe waya”.
Sulaiman dai ya yi sallama da ita duka jikinsa a
sanyaye, ranshi ya yi tsananin baci domin bai san
dalilin daya sa Safina ta koyi karya da yaudara
wanda ada ba halinta bane, yanzu dai ya tabbatar
ba daga gidansu aka ce ta tafi gidan su Rahama
ba, ita ce kurum ta shirya wannan karyar, a haka
ya isa gida zuciyar shi babu dadi.
Bayan kwana biyu sai ya kirata a waya,
cikin sa’a kuwa ta dauka suka gaisa ba yabo babu
fallasa, sai can yaji hayaniya a kusa da ita yace
Safina hayaniyar me nake ji haka?” Tace masa
Hayaniyar kannenane kasan yanzu duka suna
gida muna hira” Yace “Ya kamata kidan kebe
nesa dasu domin mu samu damar tattaunawa a
nutse” Tace
Haba sulaiman meneyake damunka
bayan kasan duk mutanen da nake tare dasu
yan gidanmu ne babu bako kasansu, suma sun
sanka, shi ne kuma dan zan amsa wayarka saina
fita daga cikinsu na kebe kaina?”
Haba Safina amman dai ai komai yana
bukatar sirri”. Tace. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dakata Mallam gaskiya ba zan iya tashi
daga cikin jama’a ba domin ba wani abu zan iya
fada ba, idan ba zaka fada min Magana a cikin
‘yan uwana ba sai dai ka hakura ka bugo wani
lokacin'” Sulaiman ya yi shiru kamar ruwa ya ci
shi domin abun na ta ya shallake tunaninshi, tayi
tsaki kawai ta katse wayar,anan ya kara
tabbatarwa lallai akwai matsala tsakaninsu da
Safina domin ada bata iya amsa wayarsa a gaban
jama’a duk lokacin da ya kirata a waya sai ta
kebe suke tattaunawa nan take Sulaiman ya
yanke shawarar bari ta huce sai ya sake kiranta
ba sai an dauki lokaci mai tsawo,  haka kuwa aka
yi bai nemeta ba sai da aka dauki tsawon sati hudu

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE