IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 12 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 12 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

daga cikin jama’a ba domin ba wani abu zan iya
fada ba, idan ba zaka fada min Magana a cikin
‘yan uwana ba sai dai ka hakura ka bugo wani
lokacin'” Sulaiman ya yi shiru kamar ruwa ya ci
shi domin abun na ta ya shallake tunaninshi, tayi
tsaki kawai ta katse wayar,anan ya kara
tabbatarwa lallai akwai matsala tsakaninsu da
Safina domin ada bata iya amsa wayarsa a gaban
jama’a duk lokacin da ya kirata a waya sai ta
kebe suke tattaunawa nan take Sulaiman ya
yanke shawarar bari ta huce sai ya sake kiranta
ba sai an dauki lokaci mai tsawo,  haka kuwa aka
yi bai nemeta ba sai da aka dauki tsawon sati hudu

hudu nan ya yi shirin ziyartarta ya daidaici ranar Asabar da yamma saboda yasan babu makaranta dole ya sameta a gida, yana isa kofar gidan ya faka mashin dinsa ya tura wata yarinya tayi mishi sallama da Safina tana shiga gidan sai ga Naja’atu ta fito ta karaso cikin fara’a suka gaisa sannan tace kadan jira kadan tana zuwa, domin yanzu naga ta fito daga wanka ko shiryawa batai ba. Yace shikenan babu damuwa, duk sanda ta kammala ta fito ina jiranta, Safina shiru bata fito ba sai data ɓata lokaci dan kawai ya gane matsayinsa.
Amman sam shi bai ji haushi ba da yake Naja’atu ta tsaya a wajensa suna ta hira, sai da Safina ta kammala yankwanenta sannan ta fito ita kuma Naja’atu ta shiga gida bayan sun gaisa yace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Safina kwana biyu ganinki ya yi wuya”.Ta kauda kai.
‘Ai ba abin mamaki bane sabida uzururruka sun yi wa jama’a yawa”. Yace “Kwarai haka ne amman duk da haka idan za ki yi min adalci ‘yar gaisawa a waya ai ba zata gagara ba a tsakanin mu, saboda naga abubuwa da dama suna faruwa gaskiya bana jin dadin su”. Safina ta yi banza dashi kamar bada ita yake Magana ba,ta share ta sako wata hirar shi kuma dadi yake ji ganin ta sakar masa fuska yaci gaba da janta da hira, ganin hirar zata yi tsayi tace masa.


“Nifa na fito mu gaisa ne sabida ina da uzuri, kasan ranakun weekend ba a rabuwa da bukukuwa, yauma bikin wata kawarmu za mu je har na riga na shirya”. Nan da nan gaban Sulaiman ya fadi domin ya lura abin nata bana kare ne, kullum tana da abin yi kuma kullum sabon abu zata bullo da shi, yana shirin zai yi mata bayyanin makasudin zuwan shi sai ga kawarta Nafisa an sauketa a wata dalleliyar mota kai tsaye wajen su ta nufo ta gaida Sulaiman kadaran-kadahan tana kallon yadin da yake jikinsa a hakikanin gaskiya Sulaiman ya tsani Nafisa kuma baya son kawancen su da Safina don dai babu yanda zai yi ne, kamar daman jira take ta zo Safina ta kalle shi tace masa.


“Sai dai fa kayi hakuri ka dawo wani lokacin, kasan na fada maka gidan biki za mu”. Duk da bai ji dadi ba amman ya kanne “Shi kenan babu komai sai kun dawo cikin shakiyanci suka hada baki “A sauka lafiya”. Yana barin wajen suka tafa suka sheke da dariya “Wahalalle kawai”, Inji Safina, Nafisa tace “Ashe har yanzu bai kyaleki ba?”.”Rabu da dan wahala sai kora da hali nake yi masa amma har yanzu yaki gane wa sai dada nacewa yake yi, indai nice ya gamu da wulakanci kenan har sai ya gaji ya kori kanshi da kanshi”. Nafisa tace.
“Gaskiya ya cika naci da yawa gwara kiyi ki sallame shi a huta, domin sam ba irin ajinmu bane, dubi suturar dake jikinsa duka idan aka hada ba zata iya sayen koda takalminki bane”. Safina ta tabe baki. “Ai kuwa na so tafka babban kuskure
lokacin da nake tunanin zan iya auren shi”. “Ai dakin aure shi da kin rugurguza rayuwarki, sabida da yanzu kuna nan kamar almajirai balle yanzu da bashi da aikin yi. Haka kawai ke ki bige da soyayya da talaka, yanda kika hadu dinan bana fidda rai za ki auri dan gwamna ko dan minister, gaki da kyau ga wayewa kuma ga babban jari kina karatu”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Uhm kedai bari Nafisa shi ya sa nake son na auri Kamal domin zan yi auren kece raini, zan faso gari kowa ya sanni”.
Tun daga ranar bata sake bi takan Sulaiman ba bare tasan a wanne hali yake, da bai kirata a waya ba bata damu ba sabida daman neman silar rabuwa da shi take, shi kuma Sulaiman yana can cikin tsananin bacin rai, haka ya kasance cikin rashin jin dadin abinda Safina ta yi masa ya yarabu da ita na dan lokaci domin ya bata dama ko zata yi nazari ta gane rashin kyautawarta, ta gano bai cancanci wulakanci daga garetaba.
Ana cikin haka Kamal ya dawo daga England, kwananshi daya da dawowa ya kawowa Safina ziyara, ta rika murna sam ta kasa zaune ta kasa tsaye shima ya rika dokin ganinta sabida ya dade bai ganta ba, dan haka dukan su cikin doki suke. Nan da nan ta zagaye shi da abubuwan cida sha suka shiga hira cikin kulawa tace.
“Gaskıya na yi kewarka da yawa, ji nake kamar na zama tsuntsuwa na bika” Yace “Haba ke din wa? Koda yake taki zuciyar kawai kika sani”. Tace “To ya Ingilar? Da fatan ka dawo lafiya?”
“Yes na baro Ingila lafiya kuma na iso gida cikin koshin lafiya”.
“Madallah haka nake fata” Ya sake dubanta yana murmushi “Kinsan wani abu?”.Aa sai ka fada”.
“Kwata-kwata banji dadin wannan tafiyar ba domin ban samu nutsuwa ba, saboda tsabar tunaninki kullum bana cikin sukuni, na gaza ci da sha bare kuma bacci saboda tsabar bege fa yanzu dana dawo Nigaria na dora idanu akan kyakkyawar fuskarki mai cike da anuri”. Ba karamin dadi maganar tayi mata ba, cikin jin kunya ta rufe fuskarta da gyalenta tace.”Kai kenan da zaka iya siffanta halin da ka shiga ni duk kurkuwa sai dai nace na tsinci kaina cikin wani irin yanayi ko kuma nace na shiga wani tabki wanda bani da karfin da zan iya fiddo kaina, a yanzu burina kawai bai wuce nasan wasu daga cikin halaye da dabi’unka, kuma nasan wasu ra’ayoyinka kamar abubuwan da suke burgeka da wadanda suke ɓata maka rai, da abubuwan da kake so da wadanda baka so”. Cikin murmushi yace.
“Abu mai sauki kenan domin ni ko a mafarki ko a farke, ko cikin duhu ko haske idan aka tambaye ni mai nafi so zance Safinatu, domin a yanzu kece wacce wutar sonta take ruruwa a zuciyata har nake neman manta komai”. Safina cike da annashuwa ta dan murmusa sabida hirar yau tafi ta koyaushe dadi bataki su kwana suna hirar ba, har bata fatan abinda zai katse musu hira, cikin shagwaba tace masa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“A ture maganar wasa da gaske ina son
nasan abinda yafi bata maka rai” Yace. “Ganin Safina a cikin damuwa da rashin sukuni shi ne yake bata min rai, a kullum ina son ganin ki cikin nishadi da walwala”. Ganin ya maida abin wasa tace “Shi kenan mu koma batun abinci wane irin abinci kafi so?”. Ya daga kai yana daga gira.
“Ina matukar son girke-girken gargajiya amma a yanzu sai wanda Safina ta zabarmin”. Sun dade sai wajen karfe tara suka yi sallama saboda su Lalla kanen shi suna ta yi masa waya, ta rakashi bakin mota tana cike da alfahari irin son da Kamal yake yi mata saboda yanda ya tsallake kowa yace ita yake so alhalin akwai wadanda suka fita kyau, suka fita ilimi suka fita nasaba da komai ‘ya ‘yan manya attajirai. Amman duka ya tsallake su ya zo wurinta, wannan abu yana kara mata alfahari, yana dada fasa mata kai da kanta ta bude masa mota ya shiga ya zauna, ya dubeta yana murmushi, irin murmushin da zata dade tana tunawa da shi yace mata.
“Wai yanzu tafiya zan yi na barki?” Cikin murmushi itama tace masa “Kana da zabi ne?” Ya langwabe kai yace “Aa sai dai hakuri har zuwa lokacin da burin zuciyata zai cika” Ya dauko wasu manya ledoji guda biyu ya mika mata, Safina uwar ladabin karya har da rusunawa ta karba tana godiya suka yi sallama yaja mota ya tafi tana daga masa hannu cike da shauki, ashe duk abinda ake yi akan idanun Sulaiman da bata san da zuwan shi ba, bai dade da zuwa ba yana yunkurin aikawa a kirata, kai idonshi ya hangota sun fito daga sitroom ita da wani hadadden matashi,sun jero kafada da kafada tana ta dariya tana fara’a da ganinta anga wadda take cikin farin ciki take tare da wanda take tsananin so, suka tsaya a jikin dalleliyar motar Kamal kamar ba za su rabu ba, matukar mamaki ne ya kama Sulaiman domin sai yau yaga zahirin abinda yasa Safina take wulakanta shi, wato Safina tana son nuna masa ainahin kalarsu ta ‘ya ‘ya mata.
Ta zo zata shiga gida ya tare mata hanya, ta waigo a razane sosai nan da nan wata irin matsanaiciyar kunya ta lullubeta domin tabbas ya gansu tare da Kamal, sai ta wayance cike da burin kunya suka yi cirko-cirko suna kallon juna, shi ya fara Magana “Yanzu abinda za ki yi min kenan? Ashe a tsakanin mu akwai cin amana? Ashe sabida kin samu wani shi ya saka kike wulakanta ni da rashin kulani? Ni a tunani na hakan da kika yi min baki yi min adalci ba tunda akwai alkawarin aure a Www.bankinhausanovels.com.ng tsakanin mu, ko kinyi sabon saurayi bai kamata ki canza matsayina daga zuciyarki ba, ashe saboda shi kike yi min kame-kame kina kwane-kwane kika daina saurarata? Yanzu Safina kina ganin kin kyauta”.Ya karasa fada cikin wata irin muryar shi tana rawa, wata irin kunyar kanta da kanta ta kamata, amma cikin borin kunya ta daga mai hannu.
“Dakata Sulaiman ba zai yiwu ka zo har kofar gidanmu kana ci mun fuska ba, kawai daga ganina da mutum sai kace saurayina ne bazaka tsaya ka bincika kaji alakata da shi ba sai kace wani mijina?ko aurena ka yi ina cewa kaima neman aurena kake yi? Kasan kuma duk wajen da take samari su rika rubibinta, ita ai allurar cikin ruwa ce mai rabo yakan dauka”.Ya gyada kansa.
“Duk naji abinda kika ce, amman ni har yanzu ban yarda cewar ba saurayinki bane, idan kuma kika ce ba saurayin ki bane sauye-sauyen da nake gani a wajen ki kuma fa mene dalilin haka”.Wannan kuma matsalarka sai dai kai ne ka sauyawa kanka”.”Haka kika ce?”.
“Kwarai haka nace”. Daga nan bata sake cewa komai ba sai wani kallo data bishi dashi mai cike da tabbatar da abinda ta fada, ta shige gida ta barshi a tsaye, saboda bacin rai ko kayan da Kamal ya bata, bata bude ba haka kawai tana murna zuwan Kamal wani can ya zo yana bata mata rai, sai data kammala komai tayi shirin kwanciya ta bude kayan da Kamal ya kawo mata, kayan kwalliyane irin tsadaddun mayukan nan da turarruka, ledar tarkacen kayan barci ne, sai kuma wani karamin akwati mai dauke da gidan awarwaraye ta fiddosu na gwalne masu bala’in kyau, murna ta cika Safina harta kasa boyewa what a surprise! wai ita ta mallaki awarwaron na makudan kudade? Lallai tayi dabara data amince da auren Sulaiman fa,da yanzu ta cuci kanta, to ina Sulaiman zai iya yi mata wanan kyautar, da yanzu ya kashe mata kasuwa kowa ya fito neman aurenta sai ace ta fida miji, dan haka yanzu ya zamar mata dole tayiwa kanta gata wajen ganin sun rabu da Sulaiman, dole ta yarda kwallon mangwaro domin ta huta da kuda domin tana da ‘yanci yin haka.
Washe gari dataje makaranta suka hadu da kawarta Nafisa ta labarta mata abinda ya faru, tanagama ji taja wani matsiyacin tsaki “Ke dai wallahi kin zama sakarai, inbanda ke sakarai ce ya za a yi ki yarda ya turkeki yana tuhumarki kamar wani mijinki ko aurenki yake yi? Ni idan ni ce yama isa ya yi min irin wannan? Waike me kike tsoro ne ba za ki iya cin mutuncinsa ba? Kawai ki jajirce kiyi masa fata-fata yanda ba zai sake zuwa gidanku ba, kuma kifito fili ki gaya mai ke ba za ki iya aurenshi ba, dan ke ba ajinsa bace a yanzu kinfi karfinshi, inbanda shi Www.bankinhausanovels.com.ng wawa ne ai shi yasan ke ba irin matansu bace, ko bai duba kalar fatar jikinki bane,aike kalar hutuce”. Safina kuwa ta hau duba jikinta tana gasgata maganganun Nafisa, sai kuma ta danyi tunani sabida da tasan ba haka take ba, Sulaiman din ne ya soma fito da ita harta zama abar so a wajen wasu samarin. Ya sha shiga siradai a dalilin soyayyarta, shi ya saka nake lallaba shi mu rabu cikin ruwan sanyi, bana son muyi rabuwar tsiya-tsiya da wani ne bashi bada tuni na rufe idanu na ketashi yanda a gaba ba zai sake kulani ba, amman Sulaiman yana da kima a idanuna sosai idan na masa rashin mutunci zagin jama’a kawai ma ya ishe ni.
Nafisa tace “Tsaya jin kunya ki cuci kanki, idan baki koreshi ba, haka zai ci gaba da nace miki yana zuwa gidanku yana raina miki hankali, banda rainin wayo ina ruwan shi da samarin ki? Ke da kike da kamar Kamal me za ki yi da wani Sulaiman”. Da wannan hudubar ta Nafisa ta zuga ta tsaf harta kuduri aniyar yiwa Sulaiman korar kare domin a yanzu kadan take jira su rabu har Allah-Allah take Sulaiman ya yi wani dan yunkuri domin tasamu kafar da zata yi

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE