IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 14 BY ZAINAB LAWAN BIRGET
IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 14 BY ZAINAB LAWAN BIRGET
Mun tsaya
sai dayaga ya ware yana kyalkyala dariya sannan suka yi sallama ya tafi atlest dai ya rage kaso mai yawa daga cikin damuwar da Sulaiman yake ciki, dama amfanin abotar kenan, kasancewa tare da aboki a kowanne hali na kunci ko na damuwa.
Sai da aka samu kusan sati biyu sannan Sulaiman ya tuntubi Iliyas da maganar zuwa gidan su Safina, sabida tunda suka yi maganar kullum da ita yake kwana yake tashi, kawai ya bada lokaci ne dan kada Iliyas yaga kamar ya fiye
wutar ciki, sai daya jira ya yi wanka ya shirya sannan ya mikawa Sulaiman makulin mota ma’ana shi ne zai tuka motar, Sulaiman din kuwa tuki yake cike da karsashi, domin ji yake kamar matsalar su da Safina ta zo karshe tunda tana jin nauyin Iliyas.
Sai hira yake yi cikin walwala a cikin hirar ne yake fada masa, mai gidan shi na kasuwa ya zo ya bashi hakuri wai yana neman maslaha na koma kasuwa. Kai kuma me kace masa? Kawai nace masa ya bani lokaci zan yi shawara, to mene ne abin shawara a ciki? Kawai ka hakura ka koma inji Iliyas, Sulaiman yace.
“Ka gane nifa gaskiya kasuwar ce duka ta fita daga kaina, ba zan iya komawa karshin wani ba nafi son naci gashin kaina, musamman yanzu danaga harkokin suna tafiya yanda ya kamata, kaga aikin danake ina samun rufin asiri daidai gwargwado”. Iliyas yace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Banki takaba amman ina son ka zauna tare da mutuminnan domin ya yi maka karshen halacci, halinsa daban ne da na sauran masu kudi”.
“To zanyi nazari kafin na yanke shawara da yake yanzu ba wannan ne a gabana ba, nafi son a warware matsalar Safina tukuna
domin na ci gaba da neman kudi da hujja, sabida yanzu matsalar Safina ita ce a gabana”. A fusace Iliyas yace.
“Ana maganar yadda zaka gina kanka kana maganar Safina, kana tsamanin yarinyar nan mai Isgilanci zata yadda ta aureka idan tasan baka neman kudi, ko baka san kasuwancin naka take kwadayi ba sabida kana kai mata tsadadun suture, sabi da haka ina baka tabbacin duk ranar data ji ka bar kasuwa ranar zata tarwatsa maganar aurenku, sabida na lura gaba daya idanun yarinyar ya gama budewa ba zata ita auren karamin ma’aikaci ko karamin dan kasuwa ba sai babban kusan gwamnati”. Sulaiman yace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Banda zarmiya da son abin duniya irin na Safina nima ina yi mata daidai gwargwado”. Iliyas yace. “Ai hidimar da kake mata ya wuce ace
daidai gwargwado domin tunda ka hadu da ita ka daina ajiye komai”. “Aa Iliyas kada ka yiwa Safina sharri,
Allah ne bai bani ikon ajiye komai ba”. “Ba wani sharri gaskiya na fada yarinyar nan ta maida kai tamkar, wani saniyar tatsa sai sarrafaka take yi yanda taga dama, ka zama sai kace bawanta komai kasamu akantayake karewa, baka da aiki sai hidimarta, gashi ba
godewa take yi ba, shi ya saka kullum nake gargadinka ka bi a hankali domin na lura yarinyar ba tausayi gareta ba, ina gudun kada ta tsiyata ka kuma daga baya ta dawo taki aurenka. Hakan ya saka nake jin haushin irin hidimar da kake yi mata, domin ni tun yanzu na soma karaya da aurenku tunda naga tana neman tayi maka butulci”. A sanyaye yace.
“Dan Allah ka daina fadar min da gaba, ni dai don Allah ka tayani da Addu’a Allah ya saka Safina rabona ce, kai kanka kasan ina son Safina so mai tsanani wanda ni kaina bazan iya fasalta irin son da nake mata ba”. Iliyas yace.
‘Baka da kaico tunda ka nuna mata zallar so ka riga ka siyawa kánka wahala domin ko kayi nasarar aurenta sai ta maida kai kamar bawa domin har yau bakasan wacece mace ba? Ai ita mace mudin kace zaka nuna mata gundarin soyayya sai ta jaka a kasa, ta rika garaka kenan kamar wani kwallo”. A daidai nan suka isa kofar gidansu Safina suka yi parking suka fito a tare Sulaiman ya yi ta waige-waige har ya yi nasarar hango wata yarinya a kofar gidan makwabta ya matsa da sauri ya kirata ya aiketa ta kira masa Safina kai tsaye yarinyar tace.”Ai bata nan domin tun dazu naga sun. fita da wani mai mota mai kyau”. Gaban Sulaiman. ya fadiu amma ya roketa taje ta duba ko Safina ta dawo, kwarai bai ji dadi da aka ce Safina tare da wani mai mota suka fita duk da yasan duka yayyenta suna da mota amma yafi zargin tare da sabon saurayin nan suka fita, jim kadan yarinyar ta fito ta shaida masa Safina fa bata dawo ba, ya daure ya karasa wajen daya bar Iliyas.Bata nan” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ba damuwa mu dan jirata, tunda nasan duk abinta ba zata kai sallah isha a waje ba, domin gidansu akwai tarbiyya da kyakkyawan tsaro”. Suka koma mota suna hirarsu tare da ‘yan shawarwari irin na abokai da suka aminta da juna, basu lura da dawowar Safina ba sai ganin wata tsadajjiyar mota suka yi a kofar gidan an bude boot yara sunata shiga da kwalaye gidansu Safina, Sulaiman ya kurawa motar idanu yace “Anya kuwa Iliyas ba Safina aka kawo a waccan motar ba?”. Nan da nan suka fita daga motar suka nufi wajen motar hala kuwa Safina ce da Nafisa aka dawo da su wani attajiri wanda ya baiwa miliyoyin gaske baya, sai da suka jira aka gama shiga da kayan Safina ta gama rangwadarta mutumin ya tafi, zuciyarta tana cike da nishadi da walwala abin ya bawa Sulaiman
matukar mamaki domin mai motar nan bashi ne saurayin daya ganta da shi ba, duk da zuciyar shi ta gama karyewa haka ya daure ya karasa dab dasu Safina ya yi sallama jin muryarsa yasa ta juya da sauri domin bata zace shi a wannan lokacin ba, tayi maza ta daure fuska alamar bata maraba da zuwan shi, Iliyas ne ya soma sauke nashi girman kan ya soma gaisar da su, suka amsa babu yabo babu fallasa, amman babu wacce ta saki fuska balle tayi murmushi, Sulaiman yace.
‘Hajiya Nafisa ya gari ya jin dadi?” Ta masa wani kallon rainin wayo sannan ta amsa a takaice, ta matsa can nesa da su alamar bata da lokacin su, Iliyas ya juya ga Safina “Mallama mun zo takanas ne gare ki domin mu tattauna wata muhimmiyar Magana dake”. Ta yatsina fuska. “Gaskiya sai dai kuyi hakuri ku dawo
wani lokacin kunga daga unguwa na dawo, akwai gajiya a tare da ni, ina son na huta kuma ai baku sanar da ni zuwan ku ba”. Iliyas ya yi shiru can ya dago yace.
“Shikenan munji mun yi munyi laifi kiyi mana afuwa amman ki daure ki saurare mu koda minti goma ne”. Ta kada kai. “Ina sauraren ku fatan ba zaku wuce Www.bankinhausanovels.com.ng
minti goman ba?”. Sulaiman yadan rusuna “Godiya muke gimbiyar mata”. Ta share shi ko kallon shi bata yi bare ya saka ran zata amsa, Iliyas ya ci gaba “Mallama Safina da farko dai mun zo neman sulhu ne, so muke a hadu a samu maslaha tsakaninki da abokina, sannan kuma muji inda maganar aurenku ta kwana”. Da farko ta danyi jim domin Iliyas duk ya daureta da jijjiyar jikinta,mutumin da ko kallon arziki baya mata shi yau Sulaiman ya dauko domin ya kureta, jin tayi shiru Iliyas yace “Mallama ke muke sauraro”.
“Ai ni bansan amsar da zan baku ba, domin banga dalilin da ina cikin karatu za a zo min da wani zancen aure ba”. Sulaiman yace “Amman Safina idan baki manta ba tun lokacin da zaki fara karatu akwai alkawarin aure a tsakanin mu, ga Iliyas nan shaida ne sabida a gaban shi kika dauki wannan alkawarin, da kika soma karatu nace zan aiko iyayena kika ce na bari sai kinyi nisa tukuna, to gashi a yanzu har kin kusa gamawa shi yasa muka ga lokaci ya yi daya kamata mu tuna miki, a karo na uku muna rokonki ki ba mu dama mu turo manya ayi maganar aure”. A hasale tace. “Tsaya Sulaiman a gaskiya ni ban shirya yin aure a yanzu ba, dan haka ba zai yiwu ka rika takura min da maganar aure ba, wai ya kake so na yi? So kake yi na raba hankalina gida biyu?”.
“Amman ina ga Safina auren mu ba zai hanaki karasa karatu ba”.Nifa na riga na gama Magana ba zan yi aure a yanzu ba, idan zaka jira sai lokacin dana shirya shikenan, idan kuma ba zaka iya jira ba kawai ka nemi wata tunda bani kadai bace mace ba, dan haka babu wani mai takura min da maganar aure tunda har yanzu ban tsayar da lokacin aure ba, kawai ina zaman ‘yanci ba zan yarda na tauye rayuwata ba, domin aure takura ne da zaman rashin ‘yanci. Da zarar mace tayi aure shi kenan ta koma karkashin kulawar mutum daya sai yadda ya yi da ita, ni kuwa ina da ra’ayin ci gaba da rayuwa cikin ‘yanci, sannan ina son na samu zuzzurfan ilimin boko, idan na yi aure yanzu gaskiya na tàuye rayuwata shi ya saka ba zan tsaya yi muku karya ba”. Iliyas ya bata dama sosai sai data gama fadar duk abinda tayi niyyar fada sannan cikin bacin rai yace.
“Duk mun ji bayanin ki idan kuma harmun fahimce ki kina nufin tunda kina son kiyi rayuwar ‘yanci ba za ki yi aure ba?”. Tayi saurin daga kai “To tunda kinsan ba aure za ki yi ba me yasa kika yiwa Sulaiman alkawarin aure? Me kike nufi karya ko yaudara?”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kwarai nasan abaya na yi alkawarin zan aure shi amman a lokacin hankali bai gama bin jikina ba, ban san kaina ba, bansan mene ya dace da rayuwata ba, dan haka zan iya yin ko wane furuci daga baya kuma zan iya sauya ra’ayi tunda nima mutumce kamar kowa, kasan shi dan adam yana iya sauyawa a ko wane lokaci”. Iliyas
yace. “Anya kuwa Safina kinsa abinda kike shirin yiwa abokina? Butulci ne da rashin adalci harda karya da yaudara”.
“Baa bin mamaki bane domin kun kira
ni da wadan nan sunayen tunda naki amsa bukatar ku”.
“Yanzu Safina daman akwai lokacin da za ki juyawa Sulaiman baya ba tare da tunanin komai ba…” Tayi saurin katse Iliyas.
“Kaga Mallam nifa kome zaka fada sai dai ka fada amma bazan tauye rayuwata ba don na farantawa wani can ba”. Iliyas yaga bacin rai ba zai kawo maslaha ba dan haka ya danne ya sassauta zuciyarshi “Haba Safina mai yasa ba zaki tuna baya ba? Mai yasa ba zaki tuna soyayyar da abokina yake miki ba? Mai yasa ba za ki tuna kyautatawa da alherin abokina a gare ki ba? Me yasa ba zaki duba dumbin kaunar shi a gare ki ba? Me yasa ba za ki duba nisa da dadewar da kika yi da shi ba? Me yasa ba za ki duba sabo da shakuwa ba? Me yasa ba za ki yi masa alfarma soyayyar ba”. Gaba daya wadanan jerarrun tambayoyin da Iliyas ya jerowa Safina bata samu ikon amsa ko daya ba sabida sanyin da jikinta ya yi, ganin ba ta da niyar Magana ya ci gaba.
“Wai shin Safina mai yasa kike biye wa son zuciyarki kika zabi ki zamo daya daga cikin azzaluman mata? Marasa adalci, masu butulci, marasa rikon amana da son abin duniya?”. Jin idan ta kyale shi tambayoyin nashi ba za su kare ba yasa ta daga masa hannu “Dakata Mallam cin fuskar ya isa haka? Saboda kawai nace ba zan auri abokinka ba zaka sani gaba kana cimin fuska tare da munanan kalamai har kana dangantani da mata masu
Www.bankinhausanovels.com.ng son abin duniya, to idan dan abinda abokinka ya kashe kuke so a biya ku ko yanzu kuke so akwai wadanda za su biya ku, dan nafi karfin gori kuma har yanzu baku yi arzikin da za ku goranta min ba, wai ma da kuka kwaso kafa kuka zo wajena da maganar aure idan nace yafito dame zai aure ni? Me yake da shi da zai iya aurena? Naga ko aikin yi bashi dashi, idan na amince zan aure shi dame zai yi min kayan aure?”. A fusace Iliyas yace.
“Karya kike yarinya ai ko giwa ta lalace namanta yafi karfin karamin Kwando, sabo da haka kudin da zamu auri mace kamarki ba zai gagara ba, ko a yanzu Sulaiman yana da abinda zai auri mata hudu irinki”. Itama ta fusata.
“Wallahi,na wuce ajin matan da kake kwatance domin niba zan yi auren karma-karma ba, aure zan yi na birgewa na kece raini, kuma na tserewa sa’a wanda naira zata yi kwakwaran motsi wannan ne dalilin daya saka ba zan yi aure da wuri ba domin sai na cika wani babban burina dan haka duk mai son aurena zai iya jira, ni dai har yanzu bance ba zan auri Sulaiman ba kenan yana da sauran dama, idan zai iya jira kofa a bude take yana iya ci gaba da…” Iliyas zai yi Magana Sulaiman ya katse shi cike da Www.bankinhausanovels.com.ng rashin damuwa amma shi kadai yasan irin zogin da zuciyar shi take yi.
“Duk naji bayanin ki kuma na fahimci inda suka dosa ni musulmi ne na kwarai don haka na yarda da kaddara mai kyau da mara kyau, nasan Allah ne ya nufa ke ba matata bace shi ya
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG