IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 3 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 3 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

tana da ya ya shida, ya yin da ita kuma Umma
mahaifiyar su Rahama take da ya ‘ya biyar
JImulla goma sha daya Www.bankinhausanovels.com.ng
Gidajen na lyali da aka ginashi bisa
doron hadin kai da kaunar juna, yaya Isma’il ne
Babba likitan zuciya ne (cardiolost) a babban
asibitin kasa dake Abuja yana da matarsa Kubra
da yarsa Amira a can Abujar suke amma yakan
zo ganin gida duk bayan sati biyu, yaya Abbas shi
ne na biyu, shima a bangaren kiwon lafiya yake,
likitan kashi ne (othorpedicst) a Asibitin kashi na
Dala, akwai yaya Umar dakuma yaya Usman
wadanda suke karatu a jami’ar Ahmadu Bello a
halin yanzu, Safina ce kebin yaya Usman sai
kuma Rahama wacce tsakaninsu bai wuce wata

uku ba, yanzu haka ajinsu shida ita da Rahama a
makarantar sakandire ta kimiyya ta ‘yan mata
dake Garko (Girls SCience college Garko) Akwai
kannensu Naja atu da ke ss 1 sai Fatima da Rabi’a
da suke a karamar sakandire sai kuma Nusaiba
wacce itama ta kamala firamare kuma take shirin
shiga sakandire, sai kuma dan auta Aliyu da ke aji
hudu na firamare a duk cikin gidan babu wadanda
suke da shakuwa kwatankwacin wacce Safina da
Rahama suke da ita. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga haduwar su da Sulaiman zuwa
yanzu kwanakin da basu wuce na wata guda ba,
ba zata iya lisafa yawan hidimomin da ya yi mata
ba, domin a duk lokacin da ya zo ba karamin
bajinta yake yi mata ba, cikin dan kankanin lokaci
ya fito da ita sahun farko na hadaddun ‘yan mata
ta hanyar wadatata da kayan kyale-kyale. da
suture yana iyakar kokarinsa akanta, baya barin
ta nemi komai ta rasa, haka yasa ta canza
raayinta akan shi ta karbi tayin soyayyarsa
musamman ma data lura da yanda ya zurfafa a
Sonta, ya ta’allaka duk soyayyarsa akanta, bashi
da wani buri sai nata, koda yaushe burinshi bai
Wuce ya faranta mata rai ba, duk wanda yasan
Sulaiman ya san labarin Safina.
Sau uku kenan yana kawo mata
amininsa Iliyas domin su gaisa da yake iliyas mai
wayayyen kai ne har sun fara sabawa da Safina.
shi ilyas ya yi karatun digiri sabanin Sulaiman,
kaunarsu daga Allah take,akwai shakUwa mai
karfi a tsakaninsu wanda babu wanda yasan
iyakar tsakaninsu, ra’ayinsu daya, shawararsu
daya, basa boyewa juna sirrinsu, komai nasu
tare suke yi.


A hanyarsu ta komawa gidane a motar
Iliyas, Sulaiman yana tuki ya dubi Iliyas yace
“Abokina ya aka yi ne tunda muke zuwa wajen
Safina baka taba cewa komai ba akanta ba?”
Cikin mamaki Iliyas yace “Me kake so nace?”
Aa wai ina nufin baka taba yin sharhi
ko ka yabeta ba, a takaice ma bahaka muka
saba ba, mun saba idan wani bakon abu ya shigo
cikin rayuwar mu mukań zauna mu yi shawara
akai”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Iliyas ya yi murmushi “Kwarai kuwa
haka ne, amma zabin naka ya yi daidai babu laifi
bata da makusa, tana da matukar kyau wanda
har kyawunata ya so tsorata ni”. Sulaiman yace.
Daman kyau yana yin yawa har ya
bada tsoro?”
“Kwarai kuwa, ina tsoron irin wadannan
Yan matan masu tsantsar kyau domin basu fiye
halacci da rikon alkawari a soyayya ba tunda
suna takama da kyawunsu zai iya zamar musu
jari”.
Sulaiman ya yi shiru yana sauraron
abokin nasa, inda shi kuma ya kara da cewa “Ba
wai ina nufin lallai Safina tana cikin irin wadancan
yan matan ba, amma ina son kayi taka tsantsan
ka dinga bin komai a hankali domin ba a gane
ainihin kalar mutum daga fuskarsa, wata mace
tamkar kura take wacce take lullube da fatar
akuya, zaka ganta normal a zahiri -amma baka
san ainihin halayyarta ba. Da yawan kyawawan
‘yan mata irin wadannan sun fi burin auren
hamshakin mai kudi da zai hada musu daular
rayuwa.
Sulaiman ya yi murmushi “Na jin duk
shawarwarinka amma ban a jin Safina zata
kasance a cikin sahun wadancan matan daka
ambata,. domin kuwa ta samu kyakkyawar
tarbiyya, dan haka ina kyautata mata zato.
Abokina karka damu kai dai ka ci gaba da tayani
da addu’a da fatan alheri fatana dai Allah yasa
rabona ce”.
Iliyas ya yi ajiyar zuciya da fadin “To
abokina Allah ya zabar mana abinda yati alheri,
Allah ya sa ita bata daga cikin wadancan din
Sulaiman ya ji dadi Yace “Amin
abokina”.
Lokacin da Safina ta tashi komawa
makaranta ba karamin siyayya Sulaiman ya yi
mata ba, siyayya ce irin ta bajinta ta ya yan
gata, domin saida ya sayi komai wanda yasan
zata bukata a makaranta, kama daga kayan
masarufi, kayan ciye-ciye, kayan kwalliya kai harda littafai da sauran kayan da dalibi zai bukata sun
samu shakuwa mai karfi ta ban mamaki a
tsakaninta da Sulaiman cikin kwanakin hutunta
musamman da yake halintane saurin sabo,
babban abinda ya dada jan hankalinta gareshi shi
ne tsantsar kyawunshi da kuma hangen daular da
take yi masa musamman ma yanda taga yana
kashe mata kudi babu ji babu gani, duk da cewar
bashi da abin hawa amma hakan bai sa ta barshi
a matsayinsa ba, kololuwar matsayi ta kaishi
tana yi masa kallon wani babban dan kasuwa, Www.bankinhausanovels.com.ng
cikin kayan daya hada mata hard la wata
hadaddiyar wayar hannu kirar Android ‘yar ya yi.
Cikin dan kankanjn lokaci Sulaiman ya
caba da mutanen gidansu Safina, Inna ji take yi
tamkar ta hadiye shi, tun tasowar Sulaiman
haka yake da farin jin a wurin mutane, kana
ganinshi zaka ji kana son shi musamman ma daya kasance mai fara’a ga kuma kyauta, cikin
gidansu Safina babu wanda bai san Sulaiman ba
sabida yanda a kullum yaran gidan basa rabo da
zancen sa, Rahama kuwa tafi kowa farin ciki da
wannan hadi na ubangiji, tana hangen matukar
dacewar da Sulaiman da Safina suka yi da juna
musamman idan aka yi la’akari da yanda súke
kaunar junansu da ma ita soyayya ita ce sirrin
samun kyakkyawar zamantakewar aure.
Safina mace ce mai dogon buri da
tsananin son rayuwa mai dadi a  kullum
mafarkinta bai wuce na samun kanta a cikin
aljannar duniya ba, ta tsani duk wani zance idan
bana jin dadi ba, tana matukar kaunar jin zancen
kudi, ta dauki kudi a matsayin maganin duk wata
lalura a’fadin duniyar nan, idan kana da kudi
babu abinda ba zaka yi ba a tunanin Safina kudi
Sun isa komai.
Hausawa ‘sun yi gaskiya da suka ce
zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai,
da halayen Safina sam ba haka suke ba, ta sauya
Halinta ne bayan data fara kawance da Wata mai
Suna Nafisa Ibrahim, tun farko Nafisarce ta nemi
Safina akan su fara kawance, a makaranta suka
hadu da ita, koda ta nemeta sam Safina bata
baiwa abin muhimmanci ba, ita Nafisarce take
biyo mata idan zata tafi aji ko kuma za su prep Ko
masallaci ko za su dinning ko laundry kasancewar
Itama Nafisar ‘yar son a sanice, tana son ace lta
wata ce ko kuma ace tana da kawance da ya
yan wasu, ganin Safina kyakkyawar gaske sai
take zaton yar wani shahararren mai kudi ce, ga
kuma sayayya na a zo a gani da take zuwa da shi
a farkon ko wane zango banda wanda ake hadoo
mata a. ko wane Visiting dama lokacin da ban a
visiting ba idan an zo ganinta. Hakan ne ya saka
take zuzuta Safina. tana cewa ita babbar mace ce
ba kalar kowa bace sai manya mutane masu
kumbar sUsa.
Nafisa ‘yar masu kudi ce, ta saba da
rayuwar hutu’ a gidansu, a Badawa layout suke
zaune, sai dai duk da kudin manaifinta amma ita
zuciyarta sam bata wadayta ba, wadannan
kudaden basu isheta ba, wadan da suka fisu take Www.bankinhausanovels.com.ng
honkoro. Safina tana yawan yi mata zancen
Sulaiman a lokacin da soyayyar su tayi. karfi, ita
Nafisa ta dauka cewa shi Sulaiman din wani ne k0
kuma dan wani musamman ma data ga hotonsa,
lallai ya amsa sunansa, shi yasa take sakar masa
fuska har suka saba das hi sosai domin duk sati
biyu yake zuwa visiting, ga kudaden da yake
kashewa, yana kai musu kayan masarufi masu
yawan gaske kuma kafin wani ya kare ya kawo
wani.
Sai da tafiya tayi nisa sannan Safina ta
fahimci cewa ashe mamallakin katafaren kantin
nan ba mahaifin Sulaiman bane, ba dangin iya
bana baba a tsakaninsu da duk a tunaninta mai
kanti Baban Sulaiman ne, duk da haka bata damu
ba tunda dai yana iyakar kokarinshi akan ta, babu
abinda ta nema a wurinshi ta rasa, kuma ta san a
shirye yake ya yi mata komai domin faranta
ranta. Wata matsalar kuma ita ce yanda Sulaiman
yake dan dangi, kuma rankata kaf dinsu a gidan
Suke da yayye da kanne har su goma sha uku,
manyan yayyensa da suka yi aure ma duk a cikin
fungun suka yi gidajensu, daya ma a cikin gidan
baban nasu yake zaune, Sai dai, duk wannan bai
dameta ba domin ko kyan Sulaiamn kadai aka
barta da shi ya isheta tayi alfahari da shi balle ma
yanda yake matukar kaunarta, tasan idan suka yi
dure duK abinda ta tsara ya zauna Da bazai yarda
da duk wani gutsuri tsoma da Danginsni za su
kawo ba.
Tun kafin Safina ta dawo Sulaiman ya
fara shirye-shirye aurensu, s0 yake da Zarar tayi
Canay sai ya tura manyansa domin a sanya rana,
Baya son a dauki lokaci mai tsawO, SO yaKe a
sanya takaitaccen lokaci shi ya sa yake ta shiri
babu kama hannun yaro.
akan gyara gida da zai zauna ya fara,
anan unguwarsu gidan yake, babu’ laifī gidan ya
yi kyau sosai, katon falo ne sai bedroom guda
biyu, a farfajiyar gidan kuma akwai kicin da
bandaki, a nan yake so su fara zama kafin ya
gina nashi filin. Bayan yagama da wannan sai ya
fara hada kayan aure, kar kas0 kaga doki wurin
Sulaiman domin har yafi masu jarrabawar
Zumudin suyi su gama dan ya mallaki Safina.
Biki na farko daya tashi bayan sun yi
candy shi ne bikin Khadija Tahir wata classmate
dinsu Safina. Tun daga ganin katin bikin Safina ta
fara zumudin. bikin datake so kenan wanda ya
amsa sunansa biki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bata kara saki da al’amarin ba sai da
suka je ganin lefe, lefe ta gani irin wanda bata
taba gani ba, ilahirin kayan lefen odarsu aka yi
babu wanda aka siya anan Najeriya, dadin
dadawa kuma ga mukullin tsaleliyar mota kirar
matrix da aka zubo akwatunan goma sha biyu
rigis a cikinta, saboda rudewa saida Safina ta
rasa me zata kalla. Haka ta koma gida tana ta
mafarkin wadannan kaya, baki daya tunaninta ya
kwance, banda burin ta samu irin lefen nan babu
abinda take yi.
Babu shagalin data bari ya wuce ta,
babu abinda bata halarta ba, ranar Laraba aka yi
kamu, aka yi walima’ ranar Alhamis, Ranar Jumaa
kuma suka yi ladies launch, abu na karshe shi ne
dinner ranar Asabar da daddare bayan an daura
aure da safe, wannan karo dinner har da ango da
abokansa. ‘yan matan amarya ankon leshi light
purple da gwaggwaro silba suka yi wanda duk
ango ne ya raba musu kyauta an ce mijin Khadija
tsohon dan majalisa ne hakan kuma ya rike
mukamai daban-daban na siyasa, sai lokacin da
ya bayyana Safina taga ashe babba. mutum ne
dan shekarunsa Sun dan tura, matansa uku ne
Khadija cikon ta hudu, kudi ne kawai amma bashi
da kyau ko na sisin kwabo, baki ne wulik sai naira
data haska shi, banda kyalli da shuni babu abinda
yake yi a hasken fitilun da suka haske hall din,
dashi da abokan na shi babu waida bai haura
shekaru hamsin ba.
Safina ta kasa hakuri sabida tsegumi
daya cika mata ciki ta tabo Nafisa tace “lta kuwa
Deezy me zata yi da wannan shirgegen tsohon?
Yanzu duk cikin masoyanta ta rasa Wanda zata
zaba sai sa’an Babanta?” Nafisa ta kalleta galala
To tsoh0 ba mutum bane? Ko bakisan tsoho da
kudi yaro bane?” Cikin mamaki Safina tace Ke
yanzu idan aka ce ki auri wannan sai ki aure shi?”
Me zai hana tunda yana da kudi”
Nafisa ta bata amsa.
Safina ta tabe baki “Allah ya kiyaye
gaskiya ni bazan iya auren tsoho ba”. Nafisa ta
daga kafada “Sai dai in baki samu ba” Tana rufe
bakinta ta mike tsaye ta cewa Safina Tashi muje
wajen rawa”
“‘Ni bazan yi rawa ba, ke dai kije ni ina
nan ina jiranki”. Inji Safina. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba tare da ta matsawa Safina bata tafi
Filin rawa tana fatan inama itama tayi gamo da
katar ko a cikin abokan angon ne ta samu wani
yace yana yi itama ta yiwa yan mata fintinkau kamar yanda
Deezy ta yi musu.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE