IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 4 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 4 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Me zai hana tunda yana da kudi”
Nafisa ta bata amsa.
Safina ta tabe baki “Allah ya kiyaye
gaskiya ni bazan iya auren tsoho ba”. Nafisa ta
daga kafada “Sai dai in baki samu ba” Tana rufe
bakinta ta mike tsaye ta cewa Safina Tashi muje
wajen rawa”
“‘Ni bazan yi rawa ba, ke dai kije ni ina
nan ina jiranki”. Inji Safina. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba tare da ta matsawa Safina bata tafi
Filin rawa tana fatan inama itama tayi gamo da
katar ko a cikin abokan angon ne ta samu wani
yace yana yi itama ta yiwa yan mata fintinkau kamar yanda
Deezy ta yi musu.

Gidan amarya shi ne aljannar duniya, duk yanda Safina ta zata ya zarce nan, gidane na gani a bada labara, bai hadata da sauran matansa ba, suna can home town dinshi Albasu, ita kuma ya ajiye ta anan Gidado road, wani irin hadadden billa ne wanda ko ita Nafisa duk shige shigenta bata taba shiga irinsa ba, tsarin bungalow ne detached da aka kawata shi da shuke-shuke filawoyi da furanni gidan updated ne saboda komai na gidan lates ne wanda ake amfani dashi a duniyar yau. Safina da Nafisa suka ja baya suna ta zuzuta gidan da duk abinda ya kunsa ganin gidan suke yi kamar a mafarki Hafsat kawarsu na kusa da su tace “Ku dai wallahi you will never change har yanzu kuna nan da son kyale-kyalen duniya”.Nafisa ta dubeta kamar taga shashasha tace “To idan bamu so na duniya ba, Www.bankinhausanovels.com.ng
na lahira kike so ya burge mu? Duk abinki kema
baki isa kice gidan nan bai burge ki ba”. Lokacin da Amarya ta zo wajen su sai Safina ta tambayeta “Deezy wai ina kika hadu da


wannan kiciman gwaskan?”Tambayar ta zo wa Deezy da a bazata, ba zata so su san yanda ta hadu da mijinta ba domin tun asali tallan hotonta aka kai masa, dan haka dole ne tasan abinda zata fada musu tunda suka fara bincike da bin diddigi ce musu tayi “Kawai dai in mutum mijinka ne duk inda yake sai ya zo gareka amma babu wani meeting point special da ake hadawa da miji, kema na san lokacin da kika hadu da Sulaiman ai ba tsarawa kika yi ba”.
Karo na farko kenan da aka ambaci Sulaiman taja tsaki dan tasan sam bai dace da shiga sahun irin wadannan masu kudin ba, ta yatsina fuska tace “Ana maganar manyan gwasake wa yake sako irinsu Sulaiman masu neman na cefane?” Nan Amarya ta barsu suna ta zantukansu da sauran kawayensu masu hali irin nasu. Tunda aka gama biki abin ya tsayawa Safina a rai, tunaninta ga irinsu Deezy da bata kaita komai ba ta samu miji na kece raini, tafi Deezy kyau, diri da kuma wayewa to ya za ayi itama ta samu miji na nunawa tsara wanda zai zama talk of the town, ta zama tauraruwa a cikin dangi, idan kuma ta tsaya jiran sai ranar da Sulaiman ya yi kudi ta aureshi alhalin yanzu ya na karkashin wani lallai zata dade domin haka duk ta fara tunanin mafita bata samu wata mafita ba sai ta tafi gidansu Nafisa, ta tarar da ita tana shirin fita.Nafisa.
“Ina kuwa za ki je?” Safina ta tambayi
Nafisa tace “Online registration na Www.bankinhausanovels.com.ng
Jamb zan je na yi”. Dabara ta fadowa Safina itama kamata ya yi ta ci gaba da karatu, idan ta shiga jami’a zata kara wayewa da gogewa, yanzu ma samari na rububinta ina kuma ga idan tayi karatu mai zurfi ilimi ya ratsata, saurayi sai ta zaba ta darje, sai ta samo miji daya fin na Deezy domin ita ba zata auri tsoho ba komai kudinsa kuwa.
Sai da Sulaiman ya bari duk wata gajiyar jarrabawa da hayaniyar makaranta ta sauka daga kan Safina sannan ya tunkareta da maganar da ya lura cewar yanzu shi kadai ta dama, kafin ya isa sai daya biya ya siyo mata tsadaddun seti na kayan shafe-shafe da turaruka duk kan ya faranta mata rai, ya hada da alawoyi da sauran dangogin kayan zaki tunda ya san ita din ma’abociyar son zaki ce. Murna sosai ta yi saboda tasan Sulaiman din ta wannan bangaren bashi da matsala yana kula da ita kuma bukatunta, duk abinda tace tana so cikin rawar jiki yake yi mata.
Sai da suka dan yi hirarsu kamar yanda suka saba kafin daga bisani ya bijiro mata da muhimmiyar maganar data kawoshi “Tunda dai Allah ya sa kin kamala karatunki lafiya kuma nima na yi nisa a shirye-shirye na ina ganin ya kamata muje ga abu na gaba”. Cikin rashin nuna damuwa da zancen nashi tace.
“Haba Sulaiman da wuri haka?” Cike da
mamaki yace “To me za a jira?” “Na zata zaka bari na nutsu duk wani school tension ya sauka daga kaina, sannan muje ga principle dina na gaba”.Jikinsa ne ya yi masifar yin sanyi, duk
wasu kwarin gwiwar da yake dashi sai ya neme
shi ya rasa, muryarsa babu karsashi yace “To
mene ne principle din naki?”
Tambayar da ya yi mata ta yi mata dadi dan haka tace “Gaskiya a ra’ayin mahaifinmu yana son muyi karatu mai zurfi, dan haka ko zan yi aure nafi son sai na shiga jami’a”.
Dukkannin shirin Sulaiman ya wargaje domin basu taba yin haka ba, duk tsarinshi na yin aure ne yanzu amma Safina na yunkurin ta bata masa shiri, cikin sigar lallami ya tausasa murya
yace “Dam ainima ba wani abu nake so ba, ina son na turo manyana ne domin suyi Magana da iyayenki a samu matsaya, idan ya so lokacin da kika shirya sai ayi bikin”.
Da alama hakan bai yi mata ba tace “Duk da haka dai nafi son ko za ayi maganar a bari sai na fara karatun sannan sauran abubuwan su biyo baya, ka san fa ance taura biyu bata taunuwa”. Ganin yadda alamun damuwa suka bayyana a fuskar shi sai ta marairaice tace “Wai me yasa ka fiye damuwa ne? kodai har yanzu baka yarda da son da nake maka bane? Mahaifina ba zai taba yi min auren dole ba, wanda nake so za a bani, kuma ba wanda nake so sai kai, ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shima ganin ta sassauto sai ya dan sassauta fuskarshi yace “Ai dole ne na damu Safina, kinsa ina matukar son ki kuma ina gudun duk wani abu da zai iya rabani da ke, na san halin samarin wannan zamanin tsoro nake kar su bushe miki kunne”.
Cikin karyar da murya tace “Haba kada ka bani kunya mana baka yarda da kanka ba kenan? Be comfident with your self, kar ka bada maza mana, ai ba a san maza da tsoro ba”.”Ba dai a wannan fannin ba, ai duk cikar namiji dole ne ya ji tsoron mata”. Ganin har lokacin ransa a bace yake sai ta kwantar da murya cikin kissa ta kalallame shi, ta dauki lokaci mai tsawo tana rarrashinsa, wannan kisser tata ita ta wanke masa zuciya ya yarda lallai Safina tana son shi sosai tunda har take gujewa bacin ranshi, ya lura shalawar karatu kawai take yi dan haka ya biye mata yace “To wacce makaranta kike sha’awar yi?”
Ta dan jujjuya hannu “Gamu nan dai”. “Ki zaba mana, school of Nursing ko Polytechnic ko F.C.E?” Mamaki mai yawa ya kamata tace “Wacce irin School of Nursing kuma? Shekara goma sha biyu ina saka uniform tun daga primary sannan kuma naje higher insititution na ci gaba da sakawa? Allah ya kiyaye”.
Shima abinda ta fada ya yi matukar bashi mamaki yace “To mene dan kinci gaba da saka uniform? Tunda ba kya son School of Nursing din sai ki zabi F.C.E ko Poly din”.
Nan ma ta tabe baki “Ni gaskiya duk kwasa-kwasansu basu yi min ba karatu Jami’a nake sha’awa Jamb zan yi”.Sulaiman yace “Amma da kin zabi daya
daga cikinsu saboda duk ina da mutanen dana
sani amma samu admission a Jami’a abune mai matukar wahala”.”Ni dai gaskiya karatun Jami’a kadai
nake sha’awa” Inji Safina. “To wacce jami’ar kike so?” Sulaiman ya tambayeta. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Nafi son A.B.U Ko B.U.K”. PONTE Sulaiman yace “Gwara dai B.U.K domin bana son kiyi nesa da gida” Akan hakan suka rabu da Safina bayan ta amince ta zabi B.U.K a matsayin Jami’ar da zata ci gaba da karatu. Sai daishi Sulaiman kwata-kwata bahaka ya so ba, ya lura Safina kafiya gareta, duk abinda tanace haka za a yi, son da yake mata yasa yake biye mata duk abinda take so. Kwanaki biyu da yin maganar Sulaiman ya siyo mata scratch card na Jamb a wani cafe dake unguwarsu Gabari sun hada masa da wani tamporary form wanda mutum zai cike inda su kuma za su shigar masa da bayanan da ya bayar a cikin form din idan an zo online registration da ya so ya cike mata form din ba tare daya tuntubeta ba, amma daya tuna cewar ba komai ake yi mata a burgeta ba sai ya gwammace gara ya barta ta zabi ra’ayinta.  Koda ya kai mata sai daya kara jaddada mata burinsa yace “Ni kuwa nafi son ki cike Bsc Nursing ko Education”. Duk ta raina abinda ya fada tsayawa tayi sororo tana sauraren abinda yake fada, ta yi fakare ne kawai kafın ya gama fadar nashi ra’ayin in ya so daga baya sai itama ta fadi nata. Shi kuwa Sulaiman ya ci gaba da cewa “Kinsan me yasa nake yi miki sha’awar wadannan kwasa-kwasan?”. Safina ta amsa masa da “Aa”.» Nafi son kiyi karatun da za ki taimaki al’aumma”. Ai ko wanne karatun na taimakon al’umma ne”. Inji Safina.
Sulaiman yace “A i wani yafi wani, duk taimakonda za ki yi ba kamar aikin jinya ko koyarwa ba, wadannan aiyukan na da dimbin lada fiye da kowanne aiki”.  Tayi dariyar raina abinda yace inda ta kada baki tace “Ni ina zan iya wata koyarwa ko aikin asibiti? Wadannan ai duk aiyukan wahala ne kuma ba wani abin azo a gani gwamnati take basu ba nafi son aikin dazan zauna a office ga A.c tana sanyayani, ko banza na san ban sha wahalar karatu a banza ba”.
Tanata jawabinta shi kuma Sulaiman ya bar baki a bude don mamaki jin inda akalar tunaninta ta karkata, ita kawai dan kudi za ta yi karatu, wata kankanuwar ajiyar zuciya ya ja kana yace “Ke wane kwas kike ra’ayi?”
Safina ta jujjuya ido cikin murmushi tace “Ni gaskiya in dai ba computer science ba sai computer Engineering” Sai a yanzu ya fahimci inda ta dosa bai ja mata ba yace “Allah bada sa’a” A lokacin ya mika mata form din ta ciccike kafin daga bisani ta shiga gida ta dauko masa hotuna.
Ranar farin ciki a wajen Safina ba a Magana, hira da kulawa ba kama hannun yaro, ita ta shagaltar da shi har lokaci yaja sosai kafin daga bisani su yi sallama ya tafi gida abinsa. Kafin ya fito daga layinsu Safina ya yi karo da tsautsayi, karo yaci da wasu ‘yan daba suna ta shaye-shaye, gashi kuma lokacin sanyi ne unguwar tayi shiru babu kowa duk an kulle gidaje, da ganinshi suka mike tsaye tare da tare masa hanya, ko kallonsu bai yi baya yi kokarin ratse musu domin ya wuce abinsa daya daga cikinsu ya dawo da shi.Sai a lokacin Sulaiman yace “Lafiya kuka tsare min hanya? Me ye hadina da ku?” Yana rufe bakinsa ya sake Www.bankinhausanovels.com.ng yunkurawa da zummar ya yi tafiyarsa, tsautsayi wanda ba a masa rana, Sulaiman bai Ankara ba sai ji ya yi daya daga cikinsu ya daɓa masa wuka a kafada yana fadin “In dai har kayi gardama to zaka iya rasa ranka babu kuma mai kwatarka”.
Sulaiman dake rike da damtsensa inda aka yanke shi cikin rawar murya yace “Me kuke so a wajena?” Kudadenka da wayoyinka”. Wani ya fada daga can gefe.
Sulaiman yaga idan ya tsaya yi musu gardama shi zai sha wuya, domin za su iya halaka shi ko kuma su lahanta shi kamar yanda yaga somin tabi a yanzu, gashi unguwar babu kowa bare ya nemi dauki, babu musu ya sanya hannunsa a aljihu ya zaro kudi ya mika musu sannan ya ciro wayoyinsa guda biyu ya damka musu. Hakan bai sa sun rabu da shi ba saida suka cajeshi suka kwashe kudaden da bai ciro ba, hatta agogo da glass dinsa saida suka kwace, saboda tsiya ko hankici basu barmasa ba, hatta form din Safina da hotonta sai da ya yi musu magiya sannan suka dawo masa dashi suka

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE