IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 5 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 5 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Sulaiman yaga idan ya tsaya yi musu gardama shi zai sha wuya, domin za su iya halaka shi ko kuma su lahanta shi kamar yanda yaga somin tabi a yanzu, gashi unguwar babu kowa bare ya nemi dauki, babu musu ya sanya hannunsa a aljihu ya zaro kudi ya mika musu sannan ya ciro wayoyinsa guda biyu ya damka musu. Hakan bai sa sun rabu da shi ba saida suka cajeshi suka kwashe kudaden da bai ciro ba, hatta agogo da glass dinsa saida suka kwace, saboda tsiya ko hankici basu barmasa ba, hatta form din Safina da hotonta sai da ya yi musu magiya sannan suka dawo masa dashi suka

barshi anan rike da dantsensa dake zubar da jinni, ga radadi da zogi daya addabeshi banda jinin da yake dibarsa, haka ya lallaba ya fito bakin hanya ya tare mai adaidaita sahu, ya kaishi chemist mafi kusa mai adaidaita sahun ya razana da halin da yaga Sulaiman, dan haka ya yi hanzarin garzawa da shi chemist domin ya samu taimakon gaggawa.
Yankan ya yi zurfi sosai saida aka yi masa dinki da chromic gadgut aka yi masa allura TT da sauran Analgesics. Bayan da aka gama dan adaidaita sahun ya dauke shi ya kaishi har gida, Sulaiman ya ji dadin taimakon da mai adaidaita sahun ya yi masa, saida ya shiga gida ya dauko kudi ya sallame shi tare da yi masa ihsani.

Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan ya kwanta sai hannun yace bai yarda ba, azabar zugi da radadi suka hadar masa, kasa kwanciyar ya yi ya tashi tsaye ya fara kewaye dakinsa ko zai samu dama-dama amma ina, haka ya kwana cikin azaba ba tare da ya rintsa ba, ji yake kamar ya cire hannun daga jikinsa ya huta.
Washe gari da safe yana kwance Iliyas ya yi sallama ya shigo daki shi kuma ya amsa sallamar kafin ya rufe bakinsa Iliyas yace “Me ya samu wayarka na jita a kashe ina ta…” Bai iyakarasa maganar ta shi ba saboda lura daya yi da ciwon dake hannunsa “Subhanallahi, Sulaiman me ya sami hannunka?”. Ya matsa tare da zama kusa da shi.
Sulaiman ya labarta masa yanda abin ya faru. Iliyas ya girgiza kai yana duban shi cike da tausayawa yace “Abokina Allah ya sa kaffarane amma gaskiya kana yin soyayya da wahala, da fatan Allah yasa kaci ribar wannan wahalar”.”Amin abokina dama kasan shi so haka yake, there is no love without shedding tears”.
Iliyas yace “Ai niba zan iya irin wannan
wahalar ba, bazan iya zuwa zance da wannan
sanyin ba”. Sulaiman yace “Ka daina cika baki, dan dai baka kamu da son wata bane, lokacin da zakaje ba wanda zaka fadawa”.”Ina fatan dai ita gimbiyar ta zo dubiya?” Inji Iliyas.
“Bata ma sani ba kuma bana son ta sani saboda bana son ta tashi hankalinta”. Sun dade suna hira Iliyas na tausayin abokinsa, yana jiye masa kar ya yi wahalar banza akan Safin, har yanzu hankalinsa bai kwanta akansoyayyar tasu ba, Iliyas digirinsa biyu, yanzu haka koyarwa yake a kwalejin fasaha wato Kano State Polytechnic, shakuwarsa da Sulaiman ta kai matuka, shakuwarsu daya kuma ra’ayinsu daya, akan Safina ne kawai suka sha banbam sam bata yiwa Iliyas ba. Kuma yana ganin bata dace da abokinsa ba, yana ganin tafi karfin arzikin Sulaiman.
Safina dai an yi jamb an gama kuma an samu gaggarumar Www.bankinhausanovels.com.ng nasara, makin data samu ya zarta cut of mark din da jami’o’in kasarnan ke bukata, dama Sulaiman baya shakkarta domin ya santa akwai kwakwalwa, matsalarta daya dogon buri da son fantamawa, wannan kuma baya da mun shi, shi dai ko yaushe burinsa Allah ya kara masa budi ta tsawon kwana yaci gaba da daukar hidimominta.
Bayan fitowar jarrabawa sai ya fara tunanin abinda ya kamata ya yi tunda dai hausawa na cewa da zafi-zafi ake bugun karfe kuma da sanyin safiya ake kama fara, bai ma jira sun yi post-utme ba ya fara tunanin inda zai yi kamun kafa domin ganin Safina ta samu abinda take so. Bashi da kowa a can B.U.K da zai iya tunkara da batun sai mutum daya abokin babbanwansu ne wanda suka yi karatu tare a jami’ar Sakwato yawanci ma babansune ya dauki dawainiyar abokin mai suna Sale Sale Sa’id yanzu haka malami ne a B.U.K kuma Sulaiman na sa ran zai taimaka.
Sulaiman bai yi kasa a gwiwa baya hado takardun Safina ba tare ma da sanin yayan nashi ba ya nufi Office din Mallam Sale Sale Saida misalin karfe tara ya isa jami’ar sai dai ya tarar da office din nashi a garkame alamun.bai zo ba, ya tarar da wasu mutane suna jiransa dan haka shima ya hau layin jiransa.
Mutanen sun kai goma suma ga alama alfarma suka zo nema, domin ga alama da takardu suma hannunsu, har kusan sha biyu Mallam Sale bai zo ba, koda wani a cikin su ya kira shi yace yaje wajen taro amman yanzu yana hanya. Shiru-shiru har lokacin Azahar bai iso ba, suka yi sallah suka dawo a lokacin ya zo kuma bayan zuwan nashi ma ya shafe fiye da mintuna talatin bai fara sauraron mutane dake jiran nashi ba, in takaice muku zance Sulaiman dai bai samu ganin Mallam Sa’id ba sai bayan karfe uku na yamma faram-faram suka gaisa da Mallam Sa’id sannan ya yi masa bayanin abinda ke tafe da shi, nan ya karbi form din Safina ya duba ya yaba dasakamakon nata tare da baiwa Sulaiman tabbacin cewar Safina zata samu gurbin karatu tare da cewar ya dawo bayan sati biyu yaji abinda ake ciki sannan kuma yace idan ya koma gida ya gaida Baba.
Sulaiman ya baro Office din cike da kwarin guiwa marar misaltuwa har ya manta da haushin dadewar da ya yi, ji yake kamar Safina ta samu gurbin karatu ta gama, murna a wurinsa a wannan ranar kamar wanda akaiwa albishir da aljanna.
Cikin zumudin mai zai tarar sati biyu na cika ya koma kamar yanda Mallam Sa’id ya umarceshi da ya yi, wannan karon ma saida yasha jira kafin ya samu ganinshi. Bayan sun gaisa ne Mallam Sale yake Www.bankinhausanovels.com.ng
tambayar Sulaiman “Yarinyar nan da kake
nemarwa admission ya kuke da ita? Na ga ita
bada sunan Baba take bearing ba?”.
Sulaiman ya sosa keya cikin jin kunya yace “Ita nake son aure”. “Oh baka ma aureta ba?” Inji Mallam Sale, a ranshi kuwa cewa ya yi “Sannunka da
kokari”. shirye”. Sulaiman dai shirye
yace “Muna”Allah ya taimaka” Inji Mallam Sale.
Sulaiman ya amsa da “Amin” A karshe Mallam Sale yace “Sulaiman
zaka ci gaba da hakuri saboda ka san yanda harkar tamu take sai a hankali”.
“Babu komai”. Inji Sulaiman, ya yi godiya ya baro ofis din.
Wasa-wasa haka Sulaiman ya yi ta jelen zuwa B.U.K ba tare da ya samu wata cikakkiyar maka ma ba, domin kuwa tuni su Safina suka yi post-UTME kuma har sakamakon ya fito yanzu haka mafi yawan ‘yan alfarma sun soma sanin matsayin su duk da cewar jami’a bata saki admission ba, hakan ne ya kara tada hankalin Sulaiman yana gudun kar ashashi basilla ayi masa sakiyar da babu ruwa, gashi dai kullum yana faman zaryar ofis din Sale Sa’id Sale amma babu abinda yake yi sai dai ya cikashi da dadin baki, kullum akwai abinda zai ce masa , tun Sulaiman yana kamawa har ya fara wasi-wasi akai, gashi kuma Safina ta kara hura masa wuta, kullum ba ta da wani zance sai na admission din.
Zuwansa na baya-bayan nan ne ya kawo karshen zaryarsa zuwa B.U.K a zuwan ne Sale Sa’id Sale ya kawo karshen batun inda yace Sulaiman sai dai kayi hakuri, na yi iyakarkokarina amma abin nan bai samu ba, babu yanda ban yi ba amma Deparment din sun tabbatar min cewar sun kamala dibar wanda za su diba har ma sun mika wa hukumar makaranta kasan yanda abubuwan nasu suke, idan ba bangarenka bane sai dai abinda ka gani, amma in da ace a bangaren da nake ne da babu matsala, duk da cewar ba field dinta bane amma idan tana son public administraon sai ta zo wanna ba zai yi wahala ba”.
Sulaiman ya girgiza kai, ya dube shi kamar bai yarda ba, wai ace H.O.D guda a kasa yi masa alfarma, amma sai ya duka yace “Na gode yallabai, yanzu zan je muyi shawara abinda muka zartar to zaka ganni” Ya fice abinshi ransa a bace. Sulaiman na zaune a Kasuwa ya yi tagumi abin duniya ya yi masa zafi yana ta tunanin wata mafitar sai maigidansa ya zo, sam bai lura da zuwan sa ba sai da Alhaji yace “Kwana biyu Sulaiman baka zuwa kasuwa sosai, koda yaushe idan na zo sai ace min baka zo ba, gashi yanzu ma ka yi tagumi, akwai wata matsalar ne?”
Sulaiman ya daure ya ce “Wallahi Alhaji ina ta faman fafutukar nemawa kanwata admission ne a jami’ar Bayaro shi yasa bana samun zama a kasuwa sosai”.”To yanzu an dace?” Alhiaji ya tambaya.Sulaiman ya girgiza kai “Aa”.Me suka ce maka?”. Alhaji ya sake tambaya. Dama wurin wani abokin yayana naje,
a duk lokacin da naje sai ya yi ta yi min hanya hanya, sai a jiya yace min wai department din sun ce masa sun gama diban dalibai”. Alhaji yace “To sun saki admission dinne?”.Aa suna dai dab da saki  Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kyalesu akwai wa ni wandazan hadaka da shi a can, shima babbane na san in Allah ya yarda zai taimaka. Bari ma in fara kiranshi a waya in sanar da shi”. Nan da nan Alhaji ya kira shi a waya suka gama mag’anganunsu sannan ya baiwa Sulaiman lamabar. Alhaji Nasidi kenan, mutumin kirki kuma mai kyautatawa wadanda ke karkashinsa, a kullum burinsa shi ne neman hanyar da zai taimakiawa Sulaiman kamar yadda shima Sulaiman din yake dawainiya da dukiyarsa. Kamar an yiwa Sulaiman bushara da aljanna yake ji,bai tsaya wata-wata ba washe gari ya tattara takardun Safina sai Ofis din Mallam Adamu Galadanci.Bai samu wata matsala ba saboda tuni Alhaji ya riga ya yiwa Adamu bayanin. Bayan Mallam Adamu ya dudduba takardun Safina sai yace “Karka samu damuwa, ai Alhaji ya fi karfin komai a wajena, za a taimaka”.
Sulaiman ya risina sai godiya yake yi kamar zai tsinke harshen shi domin yana sa ran anan za a dace. Mikewa ya yi zai tafi sai Mallam Adamu Galadanci yace “Alhaji bai baka sako ka kawo min ba?”.Cikin rashin ganewa ya girgiza kai yace
“Aa bai bani ba”. “Kace masa ina nan ina sauraron shi, ka gaishe shi idan Alhaji ya zo zai ji ko me ake ciki”.
Sulaiman ya sake yin godiya ya tafi.Tun daga nan yake jin farin ciki yasan duk wahalarshi ta zo karshe musamman ma idan
ya yi la’akari da alakar Alhaji da Mallam Adamu Galadanci.
Kwanaki biyu a tsakani Alhaji Nasidi ya kewayo Shago tare da tambayar Sulaiman yanda suka yi da Adamu Galadanci, babu abinda ya rage bai fadawa Alhaji akai ba shi ne jin cewar wai idan ya je zai ji komai, shi yana ganin ba sai ya je ba tunda dai rubuce-rubuce ne da turancin iska za a yi wanda ko ya je ba iya su ya yi ba, take ya kira Mallam Adamu Galadanci inda shi kuma ya waske yace kada su damu ba sai kowa ya sake zuwa ba, da kanshi zai kira Sulaiman din a waya idan komai ya kamala, bayan sun gama waya Alhaji ya yiwa Sulaiman bayani shi kuwa ya yi ta godiya.
Tun Sulaiman yana jiran Mallam Adamu ya kira shi a waya har aka share makwanni biyu shiru dan haka ya yanke shawarar shi ya neme shi domin sanin halin ake ciki tunda gashi lokaci yana kurewa. Zuwa ya yi ya tarar da mutane a bakin ofis din suna son ganinsa, layi shima ya bi ya samu waje yasa takalmansa ya zauna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Koda layi ya zo kansa sai ya tashi ya shiga da sallamarsa, kafin ya samu wurin zama Mallam Adamu yace “Ba nace zan nemeka da kaina ba? ko ba kaine yaron nan na wajen Alhaji ba?” Cikin girmamawa Sulaiman yace “Eh ni ne” Mallam Adamu yace “Ai na shaidaka, kaje ni da kaina zan nemeka da zarar abin ya tabbata”.
Sulaiman ya fito a sanyaye jikinsa babu kwari, gani yake yanda jama’a suka yiwa Mallam Adamu yawa zai iya mantawan da shi, wani sashe na zuciyarsa yace “To kai me zai dameka tunda

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE