IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 7 BY ZAINAB LAWAN BIRGET
IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 7 BY ZAINAB LAWAN BIRGET
Mun tsaya
tace “Kamar ma yasan za mu yi wannan zaman shekaran jiya yake sanar min na dan kara hakuri akwai shirye-shiryen da yake yi kuma da kuma da zarar ya hada su zai turo ayi Magana”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Abba na su yace “To shikenan babu matsala, idan Allah yasa yagama shirin nashi sai ayi maganar, yanzu zan sa ranar auren Rahama in yaso ke ko bayan kin fara karatu ne sai asa duk da dai na so ace auren ne ya gabaci karatun amma tunda haka ne ya samu babu damuwa”. Da gama fadar haka ya mike ya bar musu falon ya tafi turakarsa.
Farin ciki ne bayyane karara a fuskar Rahama da Ummanta sabanin Inna wacce bata fuskar babu yabo babu fallasa, ita sam ba haka ta so ba, tafi son duk wani alheri ya tattara a dakinta da ‘ya ‘yanta, ta lura gaba daya ita kadai take abinta domin kuwa Ismail da Abba maganar suke tattaunawa babu wani abu tare da su.
Ita kuwa Safina kallon tsabar wauta take yiwa Rahama, kasa hakuri ta yi saboda yanda abin yake ci mata rai bata damu da idon Inna da Umma ba ta dubi Rahama tace “Rahama ke kika yanke wannan shawarar? Akan me za ki yi aure’ da wuri haka ba tare da kin yiwa rayuwarki wani kyakkyawan tanadi ba? Haka
kawai zaki hada kanki da wahala”. “Ke kika dauki aure a matsayin wahala, ni kuwa ba haka nake kallonshi ba, na fi son in yi aurena in huta da gararamba a titi”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Inna ta gallawa Safina harara tace “Tafi can, auren ne wahala? Tunda ta zabi auren ba shikenan ba,ai ra’ayi riga ne kowa da irin nasa”.
Ismail yace “Inna ai karatun ma yana amfani, itama Rahama da zarar an yi auren za mu yiwa mijin magana akan ya barta ta ci gaba da karatu”.Umma tayi farat tace “Anya kuwa Rahama zata ci gaba da karatun nan? Ni dai gara ta yi zamanta a gidan mijinta ta huta da yawon nan a rana”.
Rahama ma tace “Balle ma bana jin Idris zai barni na ci gaba da karatu”. Inna ta dubi Ismail da Abbas cikin gatse tace musu “To shishshigi in naku bai samu karbuwa ba, sai ku kama kanku”.
Umma da Rahama suka tashi suka tafi daki suka barsu anan. Inna tace “Gaskiya Safina ba zan bari a riga aurar da wata mace a gidan nan kafin ke ba, idan baki riga kowa ba to kamata ya yi ace an yi tare, dan haka dole ne kiyiwa Sulaiman Magana
domin ya turo ayi abin nan tare, so kike yi jama’a
suce kin yi kwantai an aurar da kanwarki a
gabanki?”. Safina ta marairaice “Haba Inna ya cefa bai shirya ba kuma sai nayita rokonshi akan ya turo? Ai sai ya dauka neman kai ake da ni”.Isma’il girgiza kai ya yi cike da rashin jin dadin halin mahaifiyar tasu, Abbas da Safina ne suka ci gaba da kalallameta har ta sauko.Duk da kasancewar yanda azumi yake
yiwa Sulaiman wahala kasancewar yana da gyambon ciki amma haka ya dage yana ta yin azumin nafila a jere duk dan neman nasara a kan admission din Safina, haka yake tashi cikin dare ya yi nafilfilu ga sadakar da yake rabawa duk dan neman biyan bukata a wajen Allah. Bai damu da ita ko tana addu’ar ko bata yi ba, shi dai yadage yana iyakar kokarinshi tunda ya san farin cikinta shi ne nashi.. Www.bankinhausanovels.com.ng
Allah maji rokon bawa, Sulaiman bai sha wahalar banza ba sai gashi abin nema ya samu, ana kafe first batch sunayen daliban sai ga sunan Safina Yusuf, sunanta ne na uku a computer science. Sulaiman da bashi zai yi karatun ba amma ransa inda zai saka kansa ya yi domin murna. Ita ma Safina murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha cikin idanunta ta tabbatar Sulaiman mai sonta ne na gaskiya, tana sane da duk irin fadin tashin da yasha wajen ganin ya nemar mata admission din ba tare dasa hannun kowa nata ba, bai yarda kowa ya sanya hannunsa bashi kadai ya jajirce sai da ya samo mata admission din duk da yanda yake wahala,ta san ba dan shi ba da wata kila burinta na shiga jami’a bai cika ba, ta san in dai dan ta mahaifinta ne sai dai ta shiga F.C.E inda yafi ido, yayyenta ma duk ba a kano suka yi jami’a ba kuma a
lokacin admission bai yi wahala kamar yanzu ba. Duk haka bai wadatar da zuciyar Sulaiman ba, gani yake duk abinda ya yiwa Safina ai ba gwaninta ya yi ba kansa ya yiwa a matsayinsa na wanda yake burin aurenta. Sai daya ware makudan kudade cash domin ya fito da ita a ‘yar jami’a sak, shi ya biya mata registration da duk wasu abubuwa da ake bukata badan mahaifinta ya gaza ba, hasalima shi ya hana kowa ya saka hannu, sai ma ya riga ya yi suke sani.
Bayan ya kamala da registration sai ya koma kan suture, suture na kece raini masu tsada ya diddinka mata duk domin zuwa makaranta, kayan masu yawa kamar mai hada lefe har da takalma da sauran kayan kyale-kyale, a matsayinta na sabuwar daliba yasan zata hadu da dalibai iri-iri daga gidaje daban-daban, ba ya so a raina masa Safinarsa ko taga wani abu a wajen wata da bata dashi, ya fi son sai dai aga abu a wajenta, hatta waya sai daya sake mata tsadajjiya ta shiga jama’a a karshe kuma ya sai mata laptop kirar zamani saboda ya san wahalar dalibai saida research.Safina ta yi murna sosai saboda yanda Sulaiman din ya yi mata abubuwan da bata zata ba, ya fito da ita ta zama babbar yarinya ta wuce raini.
Burin Sulaiman a kullum bai wuce na ganin farin cikin Safina ba, yana jin dadin kala manata na kissa a duk lokacin da ya faranta mata rai. Www.bankinhausanovels.com.ng
To Safina dai ta fara karatu cike da dogon buri da daukar kanta da nisa, gashi sun kara jonewa da Nafisa kawarta dake kara izata tare da dorata akan layi mara bollewa, itama ta samu admission a B.U.K tana karantar English Education wato (B.ed English). Haduwar tasu ta kara basu damar kara rura wutar dogon burí da suke da shi, a kullum sun fi son ace su wasu ne ko kuma sun fi kowa, sai dai kuma dik da haka Safina ba ta wasa da karatunta, burinta shi ne fintinkau a kowanne fanni, burinta shi ne samun sakamako mai kyau da zata rika alfahari da shi kuma ta farantawa ‘yan uwanta rai dashi kansa Sulaiman yasan ba a banza ya kashe mata kudi ba, hakan shi ya janyo mata jama’a maza da mata da kawaye kala-kala a department dinsu harda ‘yan maths da pysics saboda yanda ta iya calculation.
Cikin semester daya kawai Safina tayi bala’in sauyawa ta goge sosai, ta kara samun gogewa iri-iri ta zama babbar yarinya kamar yanda take fata, iyayi da sanabe suka karu hatta maganarta ma ta canza, ko hausa take yi cikin salo da sarrafa harshe.
Kwalliya da ado sun karu musamman da Sulaiman ya tsaya mata da suturu na kece raini, ta murje kyawunta ya dada fitowa da ainihin fatarta, ta kara koyar kyale-kyale a wajen ‘yan matan jami’a. Duk wanda yaga Safina zai zaci ‘yar wani hamshakin mai kudi ce ko wani wanda yaci ya tada kai ya isa fada aji, gashi bata da yawo da ‘ya ‘yan talakawa sai ‘ya ‘yan manya classic babies wadanda hutu ya riga ya ratsa su..
Sulaiman kuma ya karawa kansa hidimar dauko Safina daga makaranta saboda korafin da take yawan yi masa akan wahalar da take sha wajen dawowa gida kasancewar kullum lakcarta sai karfe shida na yamma take karewa, tana samun matsalar abin hawa ga traffic congestion, dan haka sai magariba take isowa gida kuma a gajiye. Da yake Sulaiman mai yaki da damuwarta ne, nan da nan ya dauki matakin lekawo karshen abin, kullum sai ya baro kasuwa da wuri misalign karfe biyar ya karbi motar Iliyas ya tafi daukota. Safina kuwa tana jin dadin zuwan da s
yake yi daukarta saboda tana ganin ana zuwa daukar sauran dalibai a motaci itama kuwa kamarta bata dace da hawa motar haya ba.Misalign karfe biyar da rabi ya isa jami’ar Bayaro domin ya saba sai dai shi ya jirata ba dai ita ta jira shi ba, kullum kafin su gama lakca yake zuwa ya jirata har su kammala. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daya gaji da zaman mota sai ya fito ya jingina a jikin motar ya dauko wayarsa yana dannawa, kyawunsa, yanayinsa, wankansa da kuma tsayuwarsa sun tafi da hankalin wadansu yan mata guda hudu da suka fito daga library daya daga cikinsu ta kasa jurewa tace WATabarakallah ahsanulkhaliken, gaskiya wancan gayen ya hadu, hala ko sabon dalibi ne?”. “Ko kuma wata ya zo dauka ba”. Inji daya daga cikinsu.
Har suka zauna a wani waje ta farkon bata daina bin Sulaiman da kallo ba, dayar biyun da basu ce komai bata daga mata duka a cinya tare da fadin.”Ke kuma meye haka? Wannnan ai
zubar da mutuncine, sai kija ya rainamu”.Ta karshenma ta tofa tata “Da ma ai naka shike bada kai, kuma irin wadan can nan mazan da kike gani basu da mutunci, basu ki su tsinkaki ba, wulakancinsu yawa ne da shi, suna ganin yanda Allah ya haliccesu babu wata mace da tafi karfinsu”.
Ta biyunsu tace “Ai dole suja aji domin kuwa irin su ake so, kyawawan samari masu kudi yan hutu, kin san ai kowa yana son jin dadi yanzu dazan samu irin wannan a matsayin miji ai ba Magana”.
Ta karshen ta yatsina fuska “Kwadayi mabudin wahala, ai ni wallahi babu ruwana da kudinka ko kyawunka, burina shi ne in auri wanda yake sona tsakani da Allah, niba zan iya auren wanda ba ya sona ba komai kudinsa”.
Ta farkon tana shirin yin Magana Safina ta isa inda Sulaiman din yake, a daidai lokacin kuma dukkansu sun kai hankalinsu wajen, akan idanunsu Sulaiman ya zagaya ya budewa Safina Kofar motar ta shiga ya maida kofar ya rufe ya zagaya ya shiga motar yaja suka tafi.
Sai a lokacin ta farko ta samu damar yin Magana “Ashe dai wannan ya zo dauka”. Ta ukun su tace “A perfect match, babu laifi itama ta hadu, gaskiya sun dace da juna”.Ta hudun su dake da ra’ayin soyayya tace “Kuma da alama ta same shi yanda take so,
ko daga kallon da yake mata an san yana tsananin sonta”. Itace kuma ta kawo karshen tsegumin nasu da fadin “Muma Allah ya bamu maza na kwarai masu kaunar mu”.Suka amsa da “Amin”.
Suna hawa titi Safina tace “Ni aida farko ban zaci kai ne ka zo ba, daga nesa na dauka gizo kake yi min kamar yanda ka saba zuwa min a cikin bacci ko a farke”.
Ya ji dadin maganar tata sosai yace “Nima haka nake fama da tunaninki a koda yaushe, tunda naje kasuwa ban samu sukuni ba sai yanzu dana dora idanuna akan kyakkyawar fuskar nan taki mai dauke da annuri”. “Ai gwara kai tunda babu jarrabawa a
gabanka”. Inji Safina. Sulaiman ya rike baki “Yanzu abin har ya kai ina hanaki karatu? I am so flattred, amman dai bana son tunanina yasa ki fadi jarrabawa, ya kamata dai ki daure bature ma yace nothing good comes very easy”. Kafin tayi magana sai ya kara cewa.”Koda yake ma naga alama karatun baya baki wuya tunda gashinan kullum kara kyau kike yi”.Safina tace “A hakan? Ni da duk na rame saboda fama da rana”.
“Ai duk da haka babu wata ramar da kika yi, ni kuma baki ga yanda kewarki ta busar da ni ba? Ko wadataccen barci bana iya yi, dana rufe idanuna ke nake gani”.
Safina tayi murmushi tace “Kai ka ma iya fadar halin da kake ciki, ni kuwa bakina ba shi da kalmomin da zan iya yin amfani da su wajen sanar maka yanda nake jinka a cikin raina”. Murmushi suka yi gaba daya, a daidai Www.bankinhausanovels.com.ng
lokacin Sulaiman ya karya kan motar ya shiga school of management studies domin daukar Iliyas. Tunda suka gaisa da Iliyas tayi shiru bata kara cewa komai ba sai kalle-kallen titi. Ta rasa dalilin daya saka Iliyas din yake yi mata kwarjini, sam bata iya sakewa matukar yana tare da su.
Hira sai ta koma tsakanin Sulaiman da Iliyas, sai dai duk rabin hankalin Sulaiman yana kan Safina wacce yake lura da yanayinta ta madubi, bai so shirun da tayi ba, ya so ace sun ci gaba da hirar da suka faro da ita, ya fahimci yanayinta ya sauya sabanin yanda suka tawo.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG