IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 9 BY ZAINAB LAWAN BIRGET
IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 9 BY ZAINAB LAWAN BIRGET
Mun tsaya
Har kullum matsalar Safina ita ce dogon buri, zarmiya da kuma son abin duniya, gata da daukar zugar kawaye ko yaushe ba ta da ra’ayin kanta, duk son da take yiwa abu da zarar an zugata nan da nan sai ta sauya ra’ayi, mace ce mai raunin gaske.
Haka al’amarin karatun Safina ya ci gaba da mirginawa cikin nasara, babu abinda ke gagararta, kwakwalwarta na da yalwa fahimta duk abinda ake koyar dasu kuma tana da kishin karatu, bata fashi saida wani dalili mai karfin gaske, yanzu haka sun yi nisa a second semester suna dab da fara jarrabawarsu ta end of session.
Ranar wata lahadi ta shirya ta je gidan su Rahama acan unguwa uku, gidane madaidaice mai matsakaicin falo da dakuna guda biyu ga kichen da bandaki, gidane daidai zaman mutum daya da yake Rahama mace ce mai tsafta ko ina kal-kal gashi kuma an kawata gidan da ‘yan furanni.
Gidan ya burge Safina sosai, rabonta da gidan tunda aka kai amarya kuma lokacin da daddare ne bata kare masa kallo kamar yanzu ba, bata taba tunanin karamin gida zai taba burgeta ba sai wannan, sai bin gidan take yi da kallo cike da sha’awa.
Rahama kuwa dan murna rasa inda zata saka ‘yar uwarta ta yi, cikin kankanin lokaci ta cika mata gaba da kayan ciye-ciye iri-iri, dambun nama, fish cake da spring roll da fruits kala-kala.
Ba wannan ne yafi baiwa Safina mamaki
ba illa sauyawar da Rahama ta yi, sauyi na ban
mamaki kuwa, ta yi kiba, ta yi fresh, fatar jikinta
luwai-luwai sai sheki take yi da annuri, lallai aure
rahama ne ba kadan ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Safina tace “Irin wanna dadin da Idris yake baki anya kuwa wata ran zamu gane ki?”. Rahama tayi murmushi tace “BaNana son zolaya”.
“Babu wani zancen zolaya”. Inji Safina a cikin ranta tana mamakin irin abubuwan da idanunta suka gane mata, ashe dai abin ba dukiya bane zuciya ne, irin abinda ta gani ko a gidan hamshakin mai kudi sai haka.Rahama tace “Akwai farfesun kayan ciki
bari inje in kawo miki”. “Barni ma haka, ina zan kai shi?”. Suna
cikin hira Idris ya yi sallama ya shigo gidan, hankalinshi na kan Rahama sai jifanta yake yi da wani irin murmushi shima ya yi kiba ya yi haske kamar ba shi ba
“Ango barka da zuwa”. Safina ta fada
Sai a lokacin ya lura da bakuwar tasu murmushi. Yayi yace
“A ai ban kura dake ba, ashe yau babbar bakuwa
garemu, mu da har mun gaji mun yi fushi”. “Banda abinka wa yake zarya zuwa gidan amare, “Dariya suka yi suka ci gaba da hirar inda Idris yace “Ai zumunci dai bai ce haka ba”, hira suka sha sosai tare da ango har yamma kafin daga bisani ya maida ita gida da kansa a motar abokinsa.
**
Karshen shekara lokacine
na musamman ga yan, kasuwa, lokacin da akan zauna ayi karatun baya ta hanyar yin lissafin abinda ke kasa domin ganin ribar da aka samu ko kuma akasin haka, daga nan kuma sai asana bin yi ta hanyar tsara yanda za a fuskanci sabuwar shekara. A bisa wannan tsarin kantin su Sulaiman na zainab Brigede bai zamo daban ba, suma sukanyi Www.bankinhausanovels.com.ng
makamancin haka a duk shekara. Rana suka ware musamman suka gudanar da nasu lissafin karkashin jagorancin maigidansu Alhaji Nasidi, sai dai ma iya cewa an kwata ‘yar gidan jiya, ma’ana dai lissafin bai zo musu da dadi ba, an samu ɓatan makudan kudade fiye da wanda aka rasa bara, bama ta batun riba ake yi ba batun uwar kudin ma bata hadu ba.
Wannan al’amarin ya daure kan Alhaji Nasidi matuka da gaske amma duk da haka sai ya boye damuwar tashi har saida ya salami sauran yaran shagon, ya rage daga shi sai Sulaiman wanda alhakin gudanar da shagon kacokan yake a hannunsa.
Alhaji Nasidi ya yiwa Sulaiman duk tambayoyin da yake da su akan abinda ya faru shekaru biyu a jere amman Sulaiman ya gaza amsa masa, ko ido ma kasa hadawa ya yi da shi, bai san kuma abinda zai iya fada ba domin bashi da wata madogara akan kudaden da suka bata. A bara da aka samu haka Alhajin kauda kai ya yi ya dauki abin a matsayin sha’anin irin na kasuwa, wata rana a samu wata rana kuma a rasa, sai dai abinda ya faru a bana yasan akwai lauje cikin nadi, babu shakka yana ganin kudaden sun salwanta ne ta sanadiyyar Sulaiman ko kuma ta dalilin sakacinsa, domin Sulaiman ya sukurkuce tamkar bashi ba kuma baya baiwa kasuwa muhimmanci da yake bata a baya, sai Alhaji yaita zuwa shagon baya samun shi, ba da shi ake bude shagon ba kuma ba da shi ake rufewa ba.
Sulaiman mutum ne mai himma da kwazo, ga kuma tsantseni da taka tsantsan, bashi da almubazzaranci ko barnatar da dukiya, gashi da gaskiya da rikon amana, jajirtaccene akan duk wani abu da ka sakashi. Amma yanzu ma iya cewa himmarsa da kwazonsa sun zama tarihi in dai ba akan Safina ba ko kuma al’amarin da suka shafeta bane, batun tsantseni kuwa babu shi a yanzu domin kuwa duk abinda Safina tace masa cikin rawar jiki yake yinsa ba tare da la’akari da karfinsa ba. Shi kanshi bai san a lokacin daya zama haka ba, gaskiyar da aka sanshi da ita kuwa bai iya fadinta in dai akan abinda ya shafi Safina ne, al’amaransa gabaki daya sun tabarbare kowa ya rasa kanshi, wannan shi ne abinda Iliyas yaketa kokarin fahimtar da shi amman idanunsa sun rufe sun gaza gani.Jin bashi data cewa sai Alhaji Nasidi
yace “Sulaiman a gaskiya ka bani mamaki, ka sauya daga yanda nasanka, cikin ‘yan shekarun nan al’amarinka sai tabarbarewa suke yi, a niyyata na so ace shekara mai zuwa na yi maka freedom kaima kaci gashin kanka amma haka ba zai yiwu ba a halin da kake ciki”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Shekaru takwas da muke tare da kai bahaka na sanka ba, duk kokarina na son ganin abinda ke damunka ya ci tura na lura akwai abinda kake boyemin wanda bai cancanci haka daga gareka ba. Sulaiman ba zan iya cewa ka biyani kudadennan ba domin idan na yi haka ban yi maka adalci ba, sai dai zamanmu a haka ba mai yiwuwa bane kar azo ayi haihuwar guzuma da kwance uwa kwance, ya zama wajibi na dauki . matakin dakatar da kai har zuwa lokacin da zaka koma Sulaiman din dana sani a baya, dan haka kaje na sallameka har sai lokacin dana nemeka”. Bai jira abinda Sulaiman din zai ce ba yafice ya barshi anan durkushe.
Sulaiman kuwa rasa abinda yake yi masa dadi ya yi, sam bai ga laifin Alhaji ba sannan kuma bai ga laifin Safina ba wacce a hidimominta kudaden suka zurare ba, laifinsa kawai yake gani ba tare da wata hujja ba. Ya dade anan a durkushe kafin daga bisani ya tashi jiki babu kari ya tafi gida.
Yau da gobe sai Allah kuma karfen nasara bashi da tabbas, a hanyar shita zuwa daukota a makaranta tayar motar tayi faci, ya tsaya domin ya sauya taya ya karasa ya daukota, sai da yagama kwance ya dauko safayar sai ya lura itama faci gareta, ba karamin tashin hankali ya yi ba, rasa yanda zai yi ya yi, bashi da wani zabi dan haka ya dauki tayoyin biyu ya tafi wajen da zai bayar da su faci.
Bayan fitowa Safina daga lakca sai ta nufi wurin da Sulaiman yake parking, domin harta saba kullum sai dai ya jirata,tayi mamaki da taga babu motar da yake zuwa daukarta a wurin da ya saba yin parking din. Bata kawo komai a ranta ba ta nemi wuri ta zauna domin jiransa, zamanta ke da wuya kiran shi ya shigo wayarta inda ya bata uzurinsa tare da bata tabbacin yana nan zuwa da zarar an kammala masa facin.
Sauke wayarsa ke da wuya taga wata tsaleliyar mota baka ta faka a inda Sulaiman ya saba tsayawa, ba ka gano kowa dake cikin motar saboda bakin gilashin da take da shi kuma a rufe take ruf babu gilashin da aka sauke duk da irin zafin ranar da ake yi a lokacin, haka na alamarta cewa wanda yake cikin motar rabar A.c kawai yake kwasa, tsawon mintina uku wanda yake cikin motar bai fito ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Safina uwar dogon buri da zarmaya, tuni ta fara santin motar a cikin ranta da zuciyarta mai cike da burin samun daula na ta fama raya mata tunane-tunane iri-iri ina ma ace irin wannan mota ake zuwa daukarta lallai da ta kara martaba da kima a tsakanin kawayenta ko babu komai dai ta san wannan motar ta haura naira miliyan uku.
Sallamar da aka yi matace ta dawo da ita cikin hayyacinta da sauri ta amsa tare da dago kanta ta dubi mai sallamar duk a lokaci guda, yawun bakinta ne ya yi mata wuyar hadiya saboda abinda ta gani wani hadadden saurayi ne dan kwalisa tsaye a gabanta fuskarsa dauke da murmushi mai kara haskaka nutsuwar dake tare da wannan saurayin. Tayi gaggawar kauda kai daga gare shi gudun kada ya fahimci kallon da take yi masa. Da alama shi ne wanda ya zo da wannan makekiyar motar duk da dai bata ga sanda ya fito ba ta tsammanci haka ne kasancewar babu jama’a a wurin, bencin da take zaune ya dafa yace “Ko zan iya zama anan?”.Safina ta dago ta kalle shi “Mai zai hana”.
“Na gode”. Ya zauna yana karkada makulin mota tunda ya zauna bata sake kallon wajen da yake ba, shi kuma babu abinda yake yi sai satar kallonta a cikin ransa yana yaba kyawun da Allah ya yi mata, bai taba haduwa da yarinyar data dauki hankalinsa ba irinta. Haka nan yana son jin muryata, akan haka ya fara kokarin janta da hira amma sai taki biye masa, duk kokarinsa na ganin ya sa tayi Magana sai yaci tura, ko kadan hakan bai dame shi ba saboda yana matukar son mace mai aji irin Safina sai dai ya lura nata ajin har yana neman ya yi yawa. Duk maganar da yake yi babu abinda take binshi dashi sai “Eh ko A,a” Su dinma ta hanyar amfani da kai ba fada da baki ba.
Bai yi aune ba ya hangi kanensa su Laila tsaye a jikin mota suna kallonshi, da alama su ya zo dauka, nan ya yiwa Safina sallama ya taho wajen motar domin su tafi, tun kafin ya karaso kannen nashi suke yi masa dariya, basarwa ya yi kamar bai lura da dariyar da suke yi masa ba. Yana karasowa Laila tace “Yaya Kamal ya ka taho daga hango mu, ai kamata ya yi ka tsaya ka karasa abinda kake yi in yaso ma
jiraka”. Murmushi ya yi yace “Ke dai kin fiye sa
ido, mu tafi kawai domin naga kamar bata yi
na’am da ni ba, domin ko maganar arziki bata yi
min ba, watakila ko ban yi mata ba ne”.
Laila tace “Yaya kenan, ai Safina haka take, baka ga babbar yarinya bace? Daurewa ya kamata ka yi ko za a dace domin naga kunyi matching”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kamal ya murmusa “Kika ce sunanta
Safina?”. In Ta girgiza masa kai da alamar tabbatar
da abinda ta fada masa.Ku tsaya ina zuwa”. Ya fada tare da juyawa ya koma wurin wacce aka ce masa sunanta Safina.
Tana ganin ya sake dawowa taji gabanta ya yanke ya fadi, kafin ya karaso tayi saurin tattara nutsuwarta dan gujewa raini. Sunanta daya kirata yasata saurin dagowa ta kalle shi, bata yi mamakin jin sunanta a bakinsa ba domin ta san kannensa zasu fada masa “Na san dai jira kike azo a dauke ki, amma idan ba za ki damu zan so ki bimu sai mu kaiki gida”.Kallon shita sake yi ba tare data ce dashi komai ba, kiran Sulaiman ya sake shigowa wayarta, bayan ta dagane yake sake bata hakuri akan cewar bayan ya yi faci motar ta kuma. samun matsala amman yanzu ya tsaya a wani gareji domin a duba masa, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sauke wayar.”An samu matsala ko?” Inji Kamal.Safina ta kalleshi tace “Waya fada maka?”Murmushi ya yi yace “Fuskarki ceta
fada min ki yi hakuri ki biyomu mu kai ki gida”. Rashin sanin ainihin lokacin da Sulaiman zai karaso domin daukatarne yasa ta sauke girman kai ta amsa bukatar Kamal din ta amince ta shiga motarshi, mikewa tsaye tayi ta dauki Jakarta ta rataya a kafada ya yi gaba ita kuma tabi bayansa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Gaban motar ya bude mata ta shiga su kuma su Laila suna baya. Hakan ne ya bashi damar ci gaba da neman kan Safinar, babu laifi ya samu lambar wayarta. Sun kusan zuwa gida Sulaiman ya sake kiranta a lokacin aka gama yi masa gyaran ya kirata ne domin ya sanar da ita ya kusa karasowa a lokacin take fada masa cewar tana tare da kawayenta sun ma kusa zuwa gida.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG