INA DA HUJJA CHAPTER 1 By Ayshat Ɗansabo lemu_ ✍🏻

INA DA HUJJA CHAPTER 1 By Ayshat Ɗansabo lemu_ ✍🏻

 

_ASALIN LABARI_

******Zaune take ta tasa cup ɗin shayi ruwan bunu a gaban ta,wanda ko arziƙin sukari babu a cikin sa.Tsuran ruwan lipton ɗin ne kawai ta ke juya shi da cokali,ba tare da cewa akwai mahaɗin da xata haɗa dashi ta sha ba.Hawaye ne masu tsananin xafi ke sauka bisa kuncin ta ba tare da ta damu da ta tsaida su ba,daga gefen ta ƙanin ta Aliyu ne ke zaune yana faman shan ruwan lipton ɗin tamkar ya samu wani zuma.Sam bai damu da rashin mahaɗi ko rashin sukarin da babu a cikin sa ba.Burin sa kawai dama ya ji wani abu na ratsa cikinsa don rabon su da saka wani abu a ciki tun jiya da rana.Yanzu ɗin ma Khairiyyah ce ta tuno tayi ajiyan lipton ɗin cikin kayan ta ,shine harta samu ta haɗa musu suna sha.Kafin su ga dawowan Yayan su Ahmad da yace su jira shi ya fita ya dawo.Kanta ta ɗaga takai duban ta can ma’ajiyan kayan makarantan ta da ta ke ajewa,wasu hawayen suka zubo mata tana jin yadda zuciyanta ke sake ɗaukan tsananin zafi na tausayin kan su da halin da su ke ciki.Rabon ta da karatu shekara ɗaya kenan tuni qawayen ta sun jima da shiga SS1 na sakandiri.Amma ita tunda ta samu ta gama JS 3 shiga SS1 ɗin ya gagare ta.Gashi Allah ya ɗaura mata burin son karatu,tana matuƙan son ta ga ta zurfafa karatu har zuwa matakin gaba da sakandiri.Amma babu halin hakan wanda zai tallafe ta ta cinma gaci,babu tai masa katutu ƙarfin sa ya gaza.A shekarun ta na goma sha biyar ya ci a ce ta shiga matakin Senior Secondary school.Kaman yadda qawanyen ta suka wuce,sai dai ita a lokacin da sakamakon jarabawan JSCE ɗinsu ya fito alokacin ne iftila’i ya faɗawa Malam.Masu garkuwa da mutane sukai nasaran tafiya da shi, akan hanyan sa ta dawowa daga Zangon Aya.Yaje aikin ɗaukan Siminti da aka sauke sun kammala aikin ne za su dawo gida aka tare motan da su ke ciki akai garkuwa da su.Hakan ya zamo silan sake jefa rayuwansu Khairy cikin garari,har zuwa lokacin da Allah ya kuɓutar da shi da ƙarfin ikon sa ya dawo gida.Bayan sun gama cire rai da sake saduwa da shi,don koda wasa sun san in dai sai an biya kuɗin fansa ne xai dawo gare su to sai dai ya rasa rayuwan sa a hannun masu garkuwa da mutanan.Cikin ikon Allah su na xaune da maraicen wata ranan Laraba sai gashi ya shigo gidan wurjanjan.Bayan ya shafe sati bakwai a hannun su,tunda ya shigo gida a tsananin galabaice ya shigo.Wanda kallo ɗaya zakai masa ka san ikon Allah ne kawai ya kawo sa gidan,nan tsakar gida ya faɗi faɗuwan daya zamo silan samuwan laluran sa da har yau yake fama don saura kiris ya rage ya rasa sashin jikin sa na dama.Hawan jini yai masa mummunan kamu Allah ne ya taƙaita abun bai nakasa sosai ba.Tunda a yanzu an samu yakan dogara sanda ya fita zuwa masallaci amma baya ga masallaci baya nisa da gida sam,yana zaune a gida ne kawai yau ciwo gobe lafiya,sabida rashin samun shan magungunan sa yadda ya dace.Ga kuma tunanin halin da su ke ciki na ƙunci da talauci.Wanda hakan ke sake taka rawa wajen taɓarɓarewan lafiyan sa.Ba su da wani gata sai Allah sai kuma ɗan sana’an wankau da su ke yi idan sun samu,sai ko kitso da Khairiyyah ke yi da shine su ke samu su ci su sha,har su yi ɗan ƙananun buƙatu na yau da gobe,randa ba su samu ba su kwana da yinwa.Arziƙin su kenan gidan da suke xaune na su ne da wani abokin arziƙin Malam ɗin ya mallaka masa,wanda a halin yanzu ya rasu su ma iyalin sa sun tattara sun bar Zaria sun koma mahaifan mijin na su can Bauchi.Hakan yasa rayuwa ya sake tsananta ga Malam Lawal da iyalin sa dama Alhaji Harunan ne yake taimaka musu to shima gashi sun rasa shi.Khairiyyah ta sake juya cokali a cikin kofin shayin tunanin ta na katsewa a lokacin da ta jiyo muryan Aliyu yana faɗin”Yah Khairiyyah Inna na kiran ki.”

Wacce ya kira da Khairiyyah ta sauke manyan idanun ta a kan sa,sam ita bata ji kiran da Innan ke jero mata ba.Ta miƙe cikin sauri tana aje cokalin hannun ta da take ta faman juya shayin da tunani ya gagara barin ta ta sha,haka ta fice zuwa ɗakin Inna tana amsa kiran da take mata da faɗin.

“Na’am Inna gani nan zuwa.”

Da sallama ta shiga ɗakin bayan an bata izinin shiga,ta isa kusa da Inna Salamatu wacce take zaune a gaban Malam Lawal tana juye masa kokon da Yayan su Khairiyyah Ahmad ya shigo musu da shi a cikin kofi.Ahmad na zaune daga gefe guda shima yana shan kokon cikin cup,Khairiyyah ta dube sa tana faɗin “Yah Ahmad sannu da shigowa.”

“Yauwa sannu Khairy, Ba dai xaki daina yawan koke-koken nan bako?”

Ahmad ɗin ya faɗi tausayin su na sake mamaye zuciyan sa,yana sake jin cewa ya zama dole yayi anfani da lafiyan sa wajen dagewa da nema musu koda na abinci ne.Tuni ya jingine maganan Karatun sa shi ma,tunda ya samu ya kammala secondary da ƙyar ya aje batun karatun a gefe sabida rashin madafa.Yanzu haka gareji yake zuwa yana kanikanci ɗan abinda yake samowa ne ake samu aci abinci,har a sai maganin daya samu wanda Malam ke sha.

Tunanin sa ya katsene da jiyo muryan Malam dake ma Khairiyyah magana yana faɗin “Taho nan kusa dani Mamana kinji,don Allah Ummul-Khairy na ki cire duk wata damuwa,ki zama me juriya akan duk halin da xaki tsinci kanki a rayuwa.Sam bana jin daɗin wannan yawan kukan da kike akan irin jarabtan da muke ciki,karki manta Allah baya taɓa ɗaura ma duk wani rai abinda bazai iya ɗauka ba.Ubangijin mu yana sane da mu yana sane da halin da muke ciki Khairy,zai kuma kawo mana ɗauki da izinin sa.Na sani rashin karatun ku yana damun ki to amma kiyi haƙury ina ji a jiki na zakiyi karatu koba yanzu ba zaki cika burin ki na zurfafa karatu.Don haka karki cire rai da rahaman ubangiji ku cigaba da addu’a kawai Allah zai kawo mana mafita.Maza ɗakko wani kofin a zuba muku kokon ku ma ku sha ke da Aliyu kinji Mamana.”

Khariyyah ta share hawayen dake zuba mata tana me gyaɗa kai ta miƙe ta fice don ɗakko cup ɗin.Malam Lawal ya maida duban sa ga Ahmad yana faɗin “Amadu kana dai ganin yadda rayuwa take gara mana ko,nasiha ta a gareka a kullum shine ka sake dagewa da mai da hankali akan aikin garejin nan.Ka nemi sana’a ta halak kayi don ka rufa mana asiri da ƴan ƙannin ka da kai karan kanka.Ban yadda da yawon maula ko bin gida jen mawadatan mu ba,kunfi kowa sanin irin yadda kuka taso kuka ganni ina gudanar da rayuwata,ni me yawan zafin nema ne don kawai in tallafe ku in inganta rayuwan ku tare da kare mutuncin kaina.Ina da ƴan uwa mawadata kun sani amma baku taɓa ganin na je gare su da sunan naje maula ko bara akan ataimake ni ba,sai in su ne su ka ga dama su ka bani ɗan abinda su kai niyya.ba kuma komi yasa hakan ba sai gudun wulaƙanci.Allah ya gani nayi iyakan yina har kawo yanzu da ƙarfi na ya gaza lafiya ya kuɓuce min,duk da hakan kuma baka taɓa ji ko ganin na ɗauki sandata ina bin gidajen masu hannu da shuni da sunan naje maula ba.Don haka duk wani ɗa na da zai zama ɗan maula bazan taɓa yin alfahari da shi ba,ku tashi ku nemi halak ɗinku,kaine babba kaine kuma namiji don haka ka zama me kishin mu da sauran ƴan uwanka.Duk abinda zaka samu ka tuna dasu ka tallafe su musamman Mamana da take mace,ka kuma ji tsoran Allah a duk inda kake ka xama me riƙe amana da gaskiya,domin sune matakin nasara Allah yai maka albarka ya dafa maka a dukkan lamuran da xaka sanya gaba.”

“Ameen Malam insha Allah zaka sameni me aiki da dukkanin nasihohin ka,bari in tashi inyi shirin fita garejin zamu tafi da Aliyu shima.Abin da na samu sai na aiko shi da ɗan abinda xa’a ci da rana.”

“To shikenan tashi kaje Allah yayi albarka.”

Inna ta amsa da “Ameen ” ita kuma Khairiyyah data shigo riƙe da cup ɗin ta isa gaban Malam ɗin ta aje,ya dube ta da murmushi akan fuskan sa yana zuba mata kokon tare da tsare ta ta shanye a gaban sa,ana haka Aliyu ya shigo shi ma aka zuba masa ya sha,kafin Inna Salamatu ta sanar da shi zasu fita tare da Yayan sa Ahmad zuwa gareji.

Khairiyyah ne ta miƙe tana haɗa kufunan da suka gama shan kokon da su ta fice da su,don zuwa ta wanke ta maida su ma’ajiyan su.Ko da ta fito daga kitchen ɗin ɗakin da aka bar mata a matsayin mallakin ta ne,wanda yake falle ɗaya ne ɗan madaidaici me ɗauke da katifa sai drawern kayan sawan ta da sauran tarkacen ta,tsaf ɗakin yake cikin tsafta komi a kintse yake a kuma inda ya dace,wanka tayo ta dawo ɗakin don shiryawa ni dai kallon ta kawai na ke sabida yadda komi na ta ke birge ni,kyakykyawace na nunawa sa’a da alamu idan ta gama xama cikakkar budurwa za’ai kallon diri da kyawu.Color ɗinta me tsananin kyau ne sam ba fara bace sai dai akirata me hasken fata wanda turawa ke kira da (Brown skin) tana da hanci wanda ya tafi a miƙe zar tana da manyan idanu farare tas masu ɗauke da lashe’s gazar-gazar,ɗan ƙaramin bakin ta yafi komi ɗaukan hankali na,giran ta me cike da baƙin gashi cinkis tamkar anzana shi,shine abinda ya sake fiddo kyawun ta.Kaman yadda yalwataccen gashin ta da jelan kitson dake kanta ke reto bisa kafaɗun ta ya ɗauki hankali na.Doguwace amma tsayin ba irin can ɗinnan ba,tana da murjajjan jiki me ɗauke da lafiyayyan fata,kai kace a gidan hutu da jin daɗi take rayuwa.Cikin sauri-sauri take sanya kayan ta tana gamawa ta miƙe ta fice zuwa ɗakin Inna don tambayan Mallam zuwa gidan su Maryam Waziri da take son yi ta duba jikin ta,don kwana biyu kenan bata zo Islamiya ba.

So take tayi sauri taje ta dawo don kada azo yin kitso ko su samu wankau ya zam bata nan,ko da ta tambaye sa ta sanar dashi inda zata ya bata izinin zuwa,tare da sanar mata cewa da ta je ta dubo jikin Maryam ɗin tayi sauri ta dawo gida kada ta yadda ta zauna,daga haka taima Inna sai ta dawo ta fito ta sake komawa ɗakin ta,Hijab ɗinta wankakke tas ta ciro daga drawern kayan ta ta sanya,ta fito fes da ita ta sanya takalmin ta ta fice daga gidan.Bayan tayi addu’an fita gida kaman yadda ta saba,duk wadda ya ganta ya ga natsatstsiyan matashiyan budurwan yarinya da ta samu tarbiya me nagarta…..✍

DOMIN SAMUN CI GABA DUBA👇

https://arewabooks.com/book?id=62b735ad7f7fce1c0ba4d533

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE