INAAYA CHAPTER 10
INAAYA CHAPTER 10
Www.bankinhausanovels.com.ng
Washe gari sai karfe 10 suka tashi saboda gajiya suka tashi sukayi wanka sannan suka sauko kasa sukayi breakfast pancakes ne ba laifi inaaya ta dan sake ta ci sosai suka gama mamii tace suyi sauri karfe 12:00 ne waliman aleesha a gidan iyayen mijinta dake nan abuja dawaki extention layout, daki suka nufa suka daura dankwali inteesar tasaka wani voile purple da pink dinkin straight gown sai mimi ma irin voile din ne amma nata peach da blue dinkin doguwan riga cinderella style ne sai inaaya kuma nata wani black da blue dinkin doguwan riga A-line tasa wani blue veil mai kyau yasha stones sai sultaana wani atamfa tasaka dinkin straight gown kasa suka nufa suka tafi waliman tare da mamii a can suka tarar da ammah har ta je duk suka je suka gaida ammah inaaya duk sai taji tana jin nauyin ammah, dakin da aka ajiye ya aleesha suka nufa tayi kyau cikin wani lace dinta red mai kyau anyi mata makeup an daura mata dankwalin ta yayi kyau sai veil ta dora har kan kai suna zuwa sukayi hugging dinta tayi smiling tace “darlings nayi missing naku wlh shine jiya baku zo ba kuka tafi dinner ko” murmushi sukayi mata sai ta kalli inaaya cikin tsokana tace “Anty amarya an bar kukan” inaaya dai batace komai ba dan smile kawai tayi mata dan yanzu abun ya bar bata mamaki ta amince da haka
kaddarar tata take. Anyi walima an gama sai da yamma wurin 5:00pm zasu tafi aleesha tayi kuka tana cewa su zauna sai dare, haka suka samu suka tafi sultaana tace su sauke ta gida suka kaita har gida suka shiga gaida ummah suka gaisheta nan ta tsaresu tayi ma inaaya nasiha don jiya sultaana ta gaya mata abunda ya faru tayi mata Allah yasa Alkhairi sukayi bankwana da sultaana suka tafi gidan su inaaya suka koma sai mimi tace “nima yau fa zani koma gida tunda dai Alhamdulillah hidima is over” inaaya tace mata “ki kara kwana mana mimz” tace mata “no inee kinsan gobe ake komawa school and inada lectures by 4 so inaso naje gida nayi settling” kai inaaya ta gyada alamun gamsuwa sai tace ma mimi “please let the marriage stay between us I don’t want mutane suyita damuna da questions yan department din nan namu kinsan su” kai mimi ta kada mata sai inaaya tace “not even Ihsan please” ta amsa mata da to shiru ya biyo baya inaaya na tunanin ya rayuwar tata zata kasance a yanzu da auren wani a kanta. Bayan sallah magrib ne ya habib yazo zaya maida mimi gida yana ta insisting akan ta bari yazo yayi missing din ta he wants to see her su inaaya tace ma “to amarya natafi Allah ya tabbatar da Alkhairi, ya habeeb is here” kallonta inaaya tayi tace “mtsww wace amarya please ke dai wuce mu rakaki lover girl komai ya habeeb” murmushi kawai mimi tayi sai inteesar tace “wlh kuwa ni da su abbah sun gane ke suka aurar saboda naga kin matsu” mimi tayi dariya tace “rufamun asiri” hijab suka saka zasu rakata suka tarar da mamii da ya sa’id da twins a parlour tayi ma mamii sallama mamii tace “to mimi Allah ya huta gajiya ki gaishe da umminki sai mun shigo” ta amsa da to sai ya sa’id yace “to Aminatu sai aje a huta wannan rawa da aka sha” dariya mimi tayi tace “kai ya sa’id inteesar dai zakayi ma maganan rawa ta fi ni” tana fadan inteesar ya kalleta suka hada ido suka sakin ma juna Murmushi sai suka fita raka mimi har bakin mota suka je sannan ta shiga suka gaida ya habeeb ya amsa yace “inaaya ashe abunda ya faru kenan to Allah ya tabbatar da Alkhairi ciki ciki tace amin tana hararan mimi tasan ita ta gaya mishi sukayi sallama suka tafi su kuma suka shigo cikin gida parlour suka zauna nan ana ta fira mostly ya sa’id ne da inteesar sukeyi sai mamii kadan kadan inaaya dai tayi shiru tana ta tunani kala kala.
+
Aliyu ne zaune a parlour din part dinshi shi da fareed dake ta faman waya da khady, gajiya aliyu yayi ya fixge wayan ya kashe yace “kun wani ishi mutane da waya idan kun matsu kuce a daura maku aure mana kuntafi can kuyita maganan” dariya fareed yayi yace “please don’t disturb my life mana me kake so nayi maka? na zauna na maka fadan akan ka rungumi matarka da su abbah suka daura maka aure da ku zauna lafiya she’ll make the best wife for you but all in vain ya kakeso nayi maka ni ba sai naje ma rungumi tawa fiancée din ba” hararanshi aliyu yayi yace “to din anki a runguma wai i don’t know what everyone is thinking me kuke so naje gidan su nace mata that i love her and that I can’t do without her or what” dariya fareed yayi yace “hakan ma da zakayi daidai ne” haushi fareed yaba aliyu yace “you’re sick wallahi” sai fareed yace “but seriously aliyu you should be nice and not harsh on the girl wlh she’s scared of you ni na kula ka dinga sakin fuska koma me zaya faru nothing can be changed she’s your wife treat her how you intended to treat the one you’ll love to marry remember what you always say you’ll try hard to treat your wife how the prophet SAW treated his wives” shaking head aliyu yayi yace “may Allah forgive me but I can’t I can’t even look at her as a wife just a little younger sister” fareed yayi tsaki yace “kai kaima ka sani keep forming big older brother sanda zaka zo ka kamu da son diyar mutane ka rude babu ruwana na gaya maka ma” hadiye rai aliyu yayi yace “Allah ya sawake” fareed yace “shikenan lets see” ya karbe wayanshi ya sake dialing numbern Khadija yana bata hakuri akan kashewan da akayi shi kuma aliyu ya zauna a nan yana tunanin maganan fareed a zuciyan shi yace it can never be possible ma.
2
STORY CONTINUES BELOW
Washegari karfe 11 suka tashi bacci sun sauko yin breakfast mamii tace suje kitchen suyi abun su tace “kuna yara mata sai baccin tsiya bare ke inaaya yanzu haka zaki tare a kai ki gidan naki ki je kina bacci sai waye zaya ciyar da mijin bansan shirme fa” ita kuwa inaaya da anyi mentioning ita ke da aure sai jikinta yayi sanyi ta dinga tunanin wannan wace irin rayuwa ce ma haka sukayi making golden yam da kidney sauce suka ci sannan mamii tace su shiga kitchen su yi abincin rana suka shiga suka girka chicken biryani rice da wani peppered beef sauce inaaya ta hada zobo tasa cucumber sai kamshi yakeyi suka jera komai a kan dinning table sannan suka nufa sama suka sake wanka sukayi sallah inaaya ta saka wani riga a-line na wani fabric by ladies lounge black and white tayi kyau sosai ta yafa black veil sosai tayi kyau fuskanta daga kohl sai lip gloss a dakin suka zauna suka fara kallo a mackbook din inaaya suna kallon bahubali 2 har laasar yayi sannan sukayi sallah sai mamii ta kirasu suyi lunch. Aliyu tunda ya tashi yau yana daki saida abbah ya aika a kirashi yaje ya tarar da abbah da ammah a parlour din abbah yace mishi “aliyu kaje gidan daddy tun Saturday” yace aa sai abbah yace “to jira kakeyi na gaya maka kaje ko ya na?” Yace “abbah kayi hakuri dama yau zanije” abbah ya amsa mishi da to sai ya tashi ya koma daki hakanan ba dan yaso ba ya shirya cikin kananun kaya black jeans da wani shirt white mai rubutun black a jiki ya dauka makullin mota ya fita a hankali yake driving har yake isa gidan daddy cikinn 10minutes. Bayan sun gama lunch suna daki suna kallo kawai sai ga fauziyya tazo tace “yaya inaaya mamii na kiranku tana kitchen” amsa mata sukayi da to suka nufa kitchen din har suka wuce ta parlour basu kula da mutun ba saboda hankalin su baya nan suka shiga suka tarar da mamii kitchen tace “inaaya ga aliyu can parlour ki hada ruwa da drinks da abinci ki kai mashi” ji tayi kaman ta zuba ihu haka ta dauko tray tasa ruwa da drinks sai mamii tace “ki hada da zobon da kikayi dazu” ta gyade kai ta dauko shi ta daura sai ta samu wani babban tray ta sa kulolin abincin da plate da su serving spoon tace ma inteesar ta tayata mamii tace “aa ki yi da kan ki kar ki sake ki saka ta har hawaye ya taru idanunta sannan ta fara daukan karamin tray din a hankali take takawa har ta isa parlour tana shiga kamshin turaren sa ya bugi hancin ta tayi kasa da kanta zuciyanta na bugawa har ta isa gabanshi ta jawo side table a daura mishi a kai tana cewa “ina wuni” kaman mai koyon magana ba yabo ba fallasa ya amsa mata da “lafiya lau”yana kallonta briefly ya maida kanshi a wayan shi haka ta koma ta dauko dayan tray din tazo shima ta ajiye shi sannan ta koma kitchen tace ma inteesar suzo su je daki har sunyi hanyan fita kitchen mamii tace “ina zakuje ne” sai inaaya tace “mamii na gama kaiwa daman daki zamuje” kallonta mamii ta tsaya yi tace “ke kinada hankali ma kuwa anya? kinje kin jera mishi tray mi kikeso yayi ke ba ke yakamata kije ki zuba mishi ba sannan ki zauna a can parlour sai ki barshi ke ki kama gabanki kina wani behaving kaman bakisan mi akeyi ba, inaaya kinsan cewa aliyu in that parlour is your husband it can’t be changed so it’s better kiyi abunda ya kamata ba wai wannan attitude din ba” hawayen da take rikewa har sun sauko gogesu ta shiga yi taba mamii hakuri ta nufa parlour din inda yake zaune har lokacin wani kujera ta samu ta zauna gefen wadda yake shiru kusan 10minutes da kyar tayi mustering courage a hankali ta zame ta sauka kasa ta dauki plate zata zuba mishi ta bude kulan ta shiga zubawa serving spoon biyu tasaka taji yace “it’s ok” cikin wata murya mai sanyi da ta ratsa jikinta ta bar zubawa ta zuba masa sauce din shima kadan yace ta isa dago kai tayi a hankali ta mika mishi ya karba cup ta dauka kawai ta shiga zuba masa zobo instead of drink kallon hannunta ya tsaya yi tana sa zobon a hankali hannunta ya tsura ma ido da yasha lalle da wani bracelet mai kyau da sauri ya kauda kai yana mamakin yanda akayi tasan zobo yakeso at the moment ba drink ba, wuri ta samu ta zauna tayi kasa da kanta abincin ya fara ci a hankali yazata baza ya cinye ba amma ya samu kanshi da cinyewa tas! Ya mishi dadi ya dauka zobo yana kaiwa baki yafara sha ya lumshe ido a zuciyanshi yana cewa there’s something special about this zobo ya shanye ya kara zubawa ya sha sannan ya dago ya kalleta yanda ta takure a zaune daka ganta tayi wani iri sai tabashi tausayi yayi shiru for some seconds ya gyara murya yace “I’m sorry for what happened I know it’s not your choice but what can i do what can you do nothing we just have to pray to Allah and everything will be ok” a sanyaye take sauraron shi har cikin zuciyanta take jin muryan nashi ta gyade mashi kai a hankali sai yace mata “I’ll be going now ya tashi itama tashi tayi a tsaye taga yana matso inda take zuciyan ta yanata bugawa jinshi very close to her hannu yasa a pocket ya ciro wallet dinshi ya fiddo wani naira master card tana nan still kaman an dasa ta a wurin ga kamshin turaren shi da takeji sosai gashi tsaye gabanta zuciyanta bai bar bugawa ba ji tayi ya kamo hannunta a hankali runtse ido tayi saboda yanda takeji zuciyan ta kaman ba nata ba yanda yake bugawa card din ya dora mata a hannu ya kalleta yaga yanda ta rufe ido ga chest dinta yana beating da karfi sai ya saki hannun nata yace “you should take this you can use it for your needs the pin is ****” ya juya ya wuce yana wucewa ta bude ido tana bin bayanshi da kallo har ya fita sannan ta kalla hannun nata kusan 5minutes tsaye sannan ta kwashe kayan ta nufa kitchen ta kaisu sannan ta tafi daki ta tarar da inteesar ta cigaba da kallo tana shiga ta nufa wurin dressing mirror ta ajiye card din ta shiga toilet ai kuwa tana shiga inteesar ta tashi ta nufa mirror din don ganin me ta ajiye ai kuwa card din tagani ta jawo shi taga na ya aliyu ne sai ta ajiye tayi murmushi sannan ta koma taci gaba da kallon ta.