INAAYA CHAPTER 11

INAAYA CHAPTER 11

Www.bankinhausanovels.com.ng 

three weeks later

Inaaya ce zaune a cikin office din Dr anwar yana mata explaining programming language daya koya bata ganeba, zuwa yanzu sun saba sosai da Dr anwaar har ce wa ihsan take he’s her favorite lecturer yanada kirki ita kuwa ihsan saidai tayi ta jin ta tana cewa uhmm dan ita a ganinta soyayya ce tsakanin inaaya da Dr anwaar, bayani yake mata ya kura mata idanu ita kuwa tayi kasa da kai tana kallon dan book din dayake koya mata dashi sun shafe kusan 1hour kafin ya gama koya mata Murmushi tayi tace “thank you so much sir” shi kuwa anwaar idanu ya zuba mata kaman baza ya ce komai ba sai yace “hope kin gane” kada mishi kai tayi sai kawai wayanshi dake kan table yayi kara yasa hannu ya dauka yace “hello” bataji me akace dayan bangaren ba sai taji yace “I’ll make it InshaaAllah” sannan ya kashe inaaya kuwa wondering takeyi shi haka yake just serious babu wani wasa, tattara books dinta inaaya tayi tasa a backpack dinta red ta kara mishi godiya zata fita taji muryanshi yace “fatima” a hankali juyowa tayi sannan taga ya miko mata wayanshi yace “can i have your number” kallon wayan tashi tayi ta dan kalleshi tayi hesitating kafin ta karba zata saka

mishi hoton dake jikin wallpaper dinshi ta tsaya kallo wata ce kyakyawa tayi wani murmushi daya kayata fuskan nata sosai dauke take da wata yarinya da bata wuce 5years yarinya itama kyakyawa ga gashi anyi mata kitso an saka beads na yara ya sauko gashin nata abunda ya raba yarinya da Dr anwaar shine kawai ta fi shi haske kaman balarabiya inaaya ta ma manta abunda zatayi ba ta san ta tsaya tana kallon picture din ba sai taji an fixge wayan sannan ta dago taganshi ya shiga call log yana cewa “ki gaya mun number din na saka” haka ta karanto mishi yace mata thanks hade da yi mata murmushi sannan itama ta kara mishi godiya ta fita tana tafe tana mamakin ko su waye a jikin screen din yarinyar tayi kama da diyar shi kodai yana da mata haka tayita tunani a ranta ta shiga mota ta nufa gida. Mamii da daddy da su aneesah da twins ne zaune a parlour da ta shigo gida gaishe su daddy tayi ta zauna tana cewa “nagaji wlh mamii” dariya daddy yayi mata yace “kai mamana tun yanzu ke da kikeda hacking a gabanki” dariya duk sukayi mamii tana ce mata “wuce ki je kiyi freshening up ki sauko ki ci abinci sannan kizo kiyi selecting wasu kayan kitchen da hajiya mariya ta kawo daga dubai kuloli ne masu kyau ki zaba color” inaaya kuwa turo baki tayi dan mamii ta tabo abunda bataso cux idan akwai abunda bataso shine maganan aurenta don ita mantawa ma take da akwai wani aure a kanta, amsa ma mamii tayi da toh dan tasan halin mamii idan ta kuskura tace other wise, aneesah tayi dariya in a dramatic way tace “wow! Mamii I seriously can’t wait for someone to finally leave our house” murmushi kawai mamii tayi wani irin harara inaaya ta sakin mata tana bata fuska tace “daddy kaga yarinyar nan ko” daddy ma dariya yayi yace “anee babu ruwana idan ta kama ki” dariya aneesah tayi ammar ne ya fara hawaye ya taso ya rungume inaaya yana cewa “ya inaaya please don’t go anywhere and leave us kinga ya aneesah use to bully us” kaman hadin baki ayman ma ya taso yana rungumeta shima da hawayen nashi yana cewa “yess ya inaaya please don’t go we’ll be good boys” nan take kwalla suka ciko a idanun inaaya mamii na ganin haka ta tashi ta jawo twins tana cewa “ammar, ayman me haka she’s not going anywhere” tashi tayi da gudu tayi sama jikinsu duk yayi sanyi harda aneesah da lokaci daya itama idanuwanta suka cicciko ita ma tayi sama hanyar da suka bi mamii tabi da ido sai kuma ta juyo ta kalli daddy a sanyaye itama kaman zatayi kukan, daddy ya kalla twins yace “haba my big boys stop crying big boys ba sa kuka go to your room and play game” lallaba su daddy yayi suka tafi dakin su sannan ya matsa kusa da inda mamii take yana dafa ta kadan kan ta ta kwantar a jikin kafadan shi single tear na escaping daga idon ta tace “daddy she’s in pain i can see it but she is trying to hide it and be strong are we really being fair on her” dan shiru daddy yayi kafin yace “i know and i can also see how hard she’s trying to hide it but I’m sure it’s for the time being Aliyu is our son also and I’m very sure he’ll treat her right and make her happy, think of it she’ll never get a husband with his qualities and you know that” mamii tace “yes i know ni banda fargaba kan Aliyu I’m just feeling like we’re not being fair we just got her married without even knowing she must be in so much pain” daddy yayi consoling mamii sosai ya nuna mata she’s their loving and obedient daughter ta masu biyayya and there’s no doubt she’ll be happy by Allah’s grace haka ya dinga kwantar ma mamii da hankali.Tunda inaaya ta tafi daki key tasa ta rufe kofan ta fada kan gado tayi kuka sosai she cried out the pain she has been carrying nan da nan idanunta sukayi jajjawur tafi 30minutes kafin ta daidaita kanta ta bar kukan ta tashi ta rage kayan jikinta ta daura towel zata shiga wanka taji wayanta na kara ta duba taga inteesar ke kiranta face time dauka tayi amma sai ta kashe camera dinta don kar ta ga idanunta ta gane tayi kuka, inteesar tayi appearing a jikin screen din da murmushinta tace “anty inaaya ina wuni” inaaya tace “you’re not serious intee wace anty” dariya intee tayi tace “you mana matan yaya ai dole na yi mata biyayya” shiru inaaya ta dan yi wasu hawaye suka kara sauko mata tayi sauri ta goge sai taji intee yace “inee are you there meya sameki ne and miyasa kika kashe camera dinki” daidaita kanta tayi tace “it’s nothing intee na dawo school ne fa na gaji” intee tace “turn on the camera I don’t believe you” kin kunna cameran inaaya tayi ita kuwa intee bata hakura ba tayita insisting har inaaya ta gaji wasu hawayen sun sauko mata kawai ta kunna camera din intee ce take kallonta tana zare ido “innalillahi inee meya faru? What is wrong with you ne? are you alright? wani abun ya faru ne?” Duk a tsorace take mata tambayoyin dan hankalinta ya tashi ganin bestyn tata na kuka gashi idanuwanta sunyi ja shiru inaaya batace komai ba hankalin inteesar ya kara tashi tace “ina zuwa let me call mamii” da sauri inaaya ta goge hawayen idanunta tayi tace “no intee don’t call her nothing happened kawai kai na ne ke ciwo” inteesar tace “no inee you’re lying to me tell me what is wrong please I’m worried” tana fadan haka itama bata san hawaye ya sauko mata ba nan inaaya tace “i am sorry intee don’t get worried I’m ok it just hurts sometimes to remember how my life took a turn in just few minutes” sai lokacin inteesar ta gane me take nufi nan ta shiga lallashin kawar ta ta har ta dan sake sukayi fira kadan sannan ta kashe ta fada toilet ta sakin ma kanta hot bath sannan ta fito ta saka wani riga peach maran nauyi sleeveless tasauko kasa taga ba kawo ta nufa dining taci lunch dinta ta koma parlour taga mamii ta sauko Murmushi tayi mata tace “mamii I’m done”, kallonta mamii tayi da burgewa ta zauna gefen diyar ta ta ta jawo waya sukayi ta selecting kayan kitchen har mamii ta sanar mata next week me gyaran jiki zatazo yanda sukayi agreeing, Murmushi kawai tayi ma mamii tace to.

Aliyu ne zaune parlour da Ammah tasashi a gaba kan bikin nashi dake matsowa tana cewa “Aliyu inaso da kai ka kira ta ka tambayeta sizes dinta saboda kayan lefe su shoes, innerwears and all” Aliyu yace “kaii Ammah you can just ask inteesar that am very sure she knows” bata rai Ammah tayi tace “aliyu bansan shashanci fa ai nasan da inteesar din nace ka tambaye ta, wai ni kana ko kiranta kaji lafiyar ta aliyu kaji tsoron Allah wlh she’s your wife” nan Ammah tasashi ya fara feeling guilt yace “Ammah kiyi hakurii zanyi yanda kikace” tashi yayi ya nufa dakinshi ya zauna yana tunanin yanda zayayi shi ko numbern ta baya da shi sai idea ta fado masa ya jawo wayanshi ya kira inteesar tana dauka yace “meet me in my room now” a ranta tayi mamakin yanda ya kirata dan bayayi tana zuwa yace “i want you to call her right now and ask her sizes for me and don’t you dare tell Ammah what happened” kallonshi tayi cikin rashin fahimta tace “her? Who ya aliyu” hararanta ya danyi sai kuma yace “inaaya” yanda ya fadi sunan a bakin nashi so perfect Murmushi inteesar ta danyi sai ta kira inaaya a facetime tayi saa ta dauka shine ta ganta tana kuka nan ta manta ma tambayan da zatayi mata ta shiga lallashin ta duk a kan idon aliyu sai yaji ta bashi tausayi baa kyauta mata ba amma babu yanda zaya yi, suka gama wayan ta kashe sai tace “ya aliyu am sorry I can’t ask her but I’ll text you her sizes ka nuna ma ammah i know it yace mata ohk kawai sannan ta bar dakin nashi ta nufa nata.

Sai bayan sallah magrib inaaya ta fito daga daki ta sauko parlour duk ta tarar da family din nata su duka suna zaune amma duk ba wani fira sukeyi kowa na zaune duk jiki a sanyaye itama inaaya zama tazo tayi suna kallon tv kowa idan nashi a tv sai daddy ya gyara murya yace “to inada wani albishir da zanyi muku amma naga duk kun yi wani iri ko baku san ji” duban su suka maida ga daddy inaaya ta kirkiro Murmushi tace “kaii daddy haba mana muna sonji sosai ma” yayi dariya yace “to ranan sunday sa’id zaya dawo ya gama masters gaba daya” inaaya har da ihun dadi ta rungume daddy tana cewa “wow daddy this is like the best news ever” duk sauran kannen nata ma sunyi murna sosai yayan nasu zaya dawo gaba daya, fira suka ci gaba dayi har lokacin sallah yayi duk sukayi jam’i a gida daddy ya ja su suka gama sukayi dinner sai wurin 10 kowa ya tafi daki, inaaya na shiga dakin nata kan gado ta zauna taga mimi tayi mata 8missed calls nan da nan ta kirata tayi picking tace “hello mimz sorry kin kirani bana kusa” mimi tace “yess hold on” ta kashe sai bayan 10minutes ta kirata tana dauka tace “meya faru kina wani hold on” mimi tace “dummy! Babu komai, ina kika shiga ayita kiranki kaman me wani kula da gida” dariya inaaya tayi tace “haa an to mi kike nufi ban isa kula da gidan ba” dariya taji duk anyi harda muryan sultaana da inteesar taji tace “ku useless girls miyasa kukayi shiru ashe conference ne mtsww” saida suka gama dariya sannan inteesar tace “Anty inaaya ina wuni ya gida da shirin biki” tsaki inaaya tayi su kuma sukayi dariya tace “kai zan kashe wayana idan abunda kuka kira kuce mun kenan” sultaana tace “sorry sorry babes yanzu dai let’s talk about abunda ya kamata, inaaya 2months kawai ya rage har yanzu baki ce komai ba wane events zakuyi ke kanki ko dinkin gowns dinnan na brides baki yi ba ya ake ciki mu muna son fitarda anko” inteesar tace “yess that’s right ki gaya mana yanda ake ciki” mimi ma tace yesso inaaya kuwa dan tsaki tayi tace “uhh don’t disturb me oo ni babu wani event din da za ayi I’m not inviting anyone one just family ku kadai idan mamii or ammah zasuyi event that I can’t say no but ni babu wani event din da zanayi” mimi tace “kutt wlh baki isa ba inaaya yanzu sai in taro maki su ya khady da ya leesha suji abunda kike cewa” inaaya tace “I’m serious fa me zanayi da wani event the nikah have already taken place so what next ai komi ya kare” inteesar tace “wlh kuwa even though it’s not love marriage baki isa ba sai anyi event fa saidai kice baki zuwa idan kin isa” sultaana tace “tell her please” insisting sukayi tayi amma fir inaaya taki ta yarda daga karshe ma cewa tayi “girls no event we’ve already decided that with him” mimi ta fashe da dariya tace “ikon Allah inee who is him” dariya duk taba su inteesar suka sha dariyan sannan inteesar tace “please let’s switch to video call so i can be seeing your faces all” haka suka koma video call sukaci gaba inteesar tace “please inee bawani deciding yanzu sai naje na tambaya ya aliyun ba nisa yayi mun ba” rolling eyes inaaya tayi tace “sai kije din” ai kuwa intee ta kashe camera din ta basa ganinta sai magana kawai suke ji ashe dakin aliyu ta tashi ta nufa tana zuwa ta bude a hankali da siriiriyan sallama yanda duk basuji ba sai ya aliyun dake a dakin sai ta mika mishi wayan ta shi kuwa kallon lafiya yake mata pleading tayi da idanu sai ya karba inaaya na cikin cewa “ke intee better open your camera yanzu nasan ki dai ba iya zuwa zakiyi wurin ya aliyun ki tambayeshi ba kuma as it is it’s a husband and wife something so munyi deciding ni da sh..” bata karasa maganan ta ba kawai taga fuskan aliyu ya bayyana a jikin screen din cikin tashin hankali zuciyan ta kamar zata bar kirjin nata ta fara dum! Dum! Aliyu kuwa tunda ya karba wayan saida gabanshi ya fadi ganinta ya kura mata ido yanda take ta magana yana jinta kawai bata ida ba mistakenly ya kunna camera din fuskan shi ya bayyana kaman freezing inaaya tayi dan ko motsi ta kasa sai kuma dip! Ta dauke ta kashe call din sai su sultaana da dariya ke cinsu suka gaida shi ya amsa masu harda tambayan su makaranta yayi suka ce lafiya qalau sannan ya mika wa inteesar dake tsaye tana rike dariya wayan nata juyawa tayi ta fita ta koma daki tana shiga daki ta fashe da dariya sai su sultaana ma kaman jira sukeyi inteesar tace “wai ni kadai naga kaman freezing inee tayi” cikin dariya mimi tace “wallahi kuwa kaman statue ta koma” sukayi ta dariya sannan inteesar ta yi adding inaaya a call din har ta kusan katsewa sannan inaaya ta dauka ta rufe cameran ta saida ta gansu su uku suna dariya sannan tace “intee Ban yafe ba wlh” dariya inteesar tayi tace “habaa inee is it not a husband and wife something” haka sukayi ta tsokanan ta har dai suka gama wayan nasu bayan sun sa ta amince da zatayi only kamu kuma a gida zatayi haka suka yarda sannan mimi da sultaana sukace to this weekend zasu dauke suje tayi checking out bridal fabrics ta bada dinki suma zasu fitar da anko nasu bayan sunyi reaching agreement din ne sukayi sallama inaaya ta kashe wayanta sai inteesar tace “babies I have an idea” a tare sukace “what is it” tace “only ya fareed can make ya aliyu yayi dinner and only ya aliyu can say za ayi dinner inaaya won’t object and then only ya khady can make ya fareed do it you know love birds da tace abu yana kyarma za yayi mata” dariya mimi tayi tace “wow intee excellent you’re a genius” sultaana ma tayi dariya tace “so basically we just have to tell ya khady tayi ma ya fareed magana and then ya fareed yayi convincing ya aliyu and ya aliyu will tell his wife there must be a dinner” dariya sukayi mimi tace “exactly! But babu ruwana idan inee taji wife part din nan” da jin dadi suka kashe wayan bayan sun san sunyi sorting komai kowa ya kashe wayan ya kwanta bacci akan gobe zasu yi conference call su uku sai da Khady su sanar mata.

+

STORY CONTINUES BELOW

          Yau ta kama ranar Friday ranar da anty bee ta turo mai gyaran jiki daga maiduguri zuwa garin abuja by flight ko da ta sauka dama mamii ta sa inaaya sunje da driver su dauko ta, basu wani wahala ba suka ganeta suka dawo gida tarba mai kyau da mutunci mamii tayi mata inda aka sauketa a dakin kasa dake cikin gidan, matar gashi tana da kirki da fara’a da bada Labarai nan da nan suka saba da mamii suka dunga fira mostly na aikinta ne take bawa mamii labari da irin amare daban daban da tayi ma wa, har tace ma mamii “hajiya ai banga amaryan ba ma saboda inga yanda zamuyi deciding na safe da dare za a dinga mata ko safe da rana ko rana da dare kinsan su kamshin da sauransu sun fi kama jikin mutun idan anayi so biyu a rana” Murmushi mamii tayi tace “habaa yagana ai ita ta dauko ki a airport ko” da mamaki yagana ta kalli mamii tace “kaii hajiya yo ai nazata kanwar amaryan ce naga wannan bata wuce shekaru 16 kuma kinsan masu kudin abujan nan ban taba ganin amarya karama ba duk daga 25 sama zakiga amaran” dariya mamii tayi tace “ai kuwa shekarun ta 16, habaa ba wani masu kudi mu ai ba yan abuja bane yan gargajiya da al’ada ne” dariya matar tayi tace “gaskiya hakane kuma MashaaAllah wanda zaya aureta ya dace mata yarinyar ki akwai natsuwa gashi baki ganinta kice tana yarinta dan kamar yar shekaru 20 haka nima dan inada diya me shekarunta yasa na gane” nan ma mamii tayi dariya tace “kai yagana kin ji ki, Allah ya tabbatar da Alkhairi dai” ta amsa ma mamii da amin sannan mamii tasa aka kira mata inaaya tazo suka tattauna da yagana tace na safe da dare yafi haka sukayi deciding akan gobe za a fara sannan yagana ta ce masu zata kwanta bacci sukayi mata Allah huta gajiya ta nufa dakin da suka bata domin yin bacci, suma duk kowannensu daki ya nufa inaaya har ta kwanta taji wayanta na kara har bazata dauka ba saboda sabuwan number ne sai ta dauka tayi shiru a dayan bangaren taji sassanyar muryan Dr anwaar yace “assalam alaiki” nan da nan ta gane shi ne ta amsa tana gaishe shi suka gaisa shiru ya dan biyo baya sannan yace “fatima natakura miki ne” Murmushi inaaya ta danyi tace “no not at all sir” shima yar dariya yayi mai dan sauti kadan sannan yace “MashaaAllah I’m glad, so can you tell me more about your self if it’s ok with you” ta amsa mashi da eh nan ta dan bashi brief abu a kanta complete name,family,state da komai save for the fact that she’s married, yagama sauraronta yayi murmushi yace nice you know I’m anwaar abdullah and i am from yola my parents live here in abuja we’re just four in the house i have an older sister her name is haseena she’s 35years old and she’s married and live in abuja with her husband and three kids, then follow by me I’m 33years old and my younger brother abdulhafiz he’s 28years old he’s married he also lives in abuja with his wife and a child and the last born khalida she is 18years old she’s in her semi final year at nile university studying architecture” Murmushi inaaya tayi tace “MashaaAllah that’s so nice, but how comes your younger brother is married and you’re not” wata yar dariya yayi mai ciwo yace “I actually don’t like talking about it but with you I’m feeling secured” ita dai inaaya kawai tana jin shi yaci gaba “i got married when i was 27years old to the love of my life, sarah we dated for 5years before we finally got married we were so happy together until destiny decided to separate us, 9months after our marriage she gave birth to the most adorable baby girl  the love i have for her increased and i love the baby with all of my heart too we named our baby after sarah’s late mother zakiyya and called her umaymah we loved our daughter with everything we have before you know it she was all grown up tayi 5years she was  my carbon copy life continued sarah got pregnant again she was 5months pregnant one day i was going to work in the morning and sarah was down and doing things very slow she told me she’s  feeling too bad having a bad feeling i consoled her and assured her nothing will happen and left for work and she took our daughter to school, just after zuhr prayer i called her to check up on her how I always do she picked and we talked for more than 30minutes she kept telling me how much she love me and our daughter and i was teasing her that she’s emotional today and she’ll just smile it was 2:00pm time to pick up umaymah from school we ended the call and she went to pick our baby she went to the school ta dauko ta saboda hold up she parked the car in the other side of the road kawai sun zo tsallake titi umaymah’s friend called her name irin abun yaran nan sai kawai ta juya zata koma wurin friend din da gudu ita kuma sarah was calling her tana cewa “umaymah why are you stubborn itama zata bi umaymah unknown to them wani trailer yana tafiya da gudu and It hit both of them! SubhanaAllah sarah sarah she died at the moment” muryan shi har wani rawa yakeyi yana gaya ma inaaya da itama hawaye sun jike mata fuska tace “I’m sorry sir you don’t have to finish” yayi Murmushi yaci gaba “she died and i recieved a call that my daughter had an accident she’s at the hospital I rushed like a mad man with tears in my eyes on reaching the hospital I sighed sarah’s body covered to her head i loose it all a family doctor was there so he called my parents and they came in no time we were all broken it was so hard for me but with prayers i began to heal and then everything got spoiled again after my source of happiness umaymah died a week after, i was depressed and crazy it took me a year to heal and start acting normal then I got a job at the uni cux i wasn’t interested in anything from my old life even the job that was how I become a lecturer” inaaya tasha kuka da ta ji labarin shi tace “i am sorry sir they’re in better place InshaaAllah” yayi smiling yace “yes Fatima InshaaAllah but please call me anwar” amsa mashi kawai tayi da to sannan ya dan canza topic din don baya son wani pity yace “so Let me be straight forward to say the first day i saw you I just felt we can connect just some type of feeling you know i like you fatima and I’m so serious about it! ta ma rasa mi zata ce mishi tana zare ido gabanta na bugawa dum! Dum! Kaman bazata ce komai ba sai kuma muryanta na rawa ta bude baki tace “subhanAllah I’m sorry sir we can’t have any relationship except the teacher and student i am unlikable” sai yace “habaa Fatima please don’t get me wrong I don’t mean anything bad please do accept me and who wont like you after seeing you and observing your behaviors, wlh after sarah’s death I’ve never felt anything for any lady but with you it’s different please accept me kar ki mun haka” hawaye ke fitowa daga idanuwanta ta rasa me zatayi a zuciyarta takejin ta tsani kanta saboda wannan kaman cin amanan ya aliyu take da aurenshi a kanta ta ba wani numbern ta kuma tana magana dashi dukda ba love marriage bane, shiru batayi magana ba anwar yace “fatima talk please say something” rufe idanunta tayi ta bude tace “please i am sorry sir, but don’t call me again you’re my teacher and i have respect for you but i am unlikeable and haraam to any guy except my husband I’m sorry for not mentioning i am a married woman so please you can even delete my number right now i am feeling guilty inaji kaman ina cin amanan mijina” har firgita anwar yayi jin abunda tace sannan yace “habaa fatima ba gaskiya kike fada ba bakiyi kama da me aure ba dan haka you can reject me politely no need to lie” hawaye sun taru idanunta suna zuba ta rasa me zatace tace “please sir goodbye don’t call me again it’s hard to believe but i am married” bata jira cewanshi ba ta kashe wayanta hannunta na kyarma tayi blocking numbern nashi ta kwanta kan gado hawaye sai zirarowa sukeyi ta rasa dalili. Kusan one hour tana kwance shiru sai taji wayanta na ringing ta duba taga Ihsan ce ta goge idanunta ta dauka wayan tana cewa “hello ihsan” a dayan bangaren muryan ihsan da bacin rai tace “habaa inaaya ke ba karaman yarinya ba miye haka kikeyi just because dr anwar said he likes you shikenan zaki wulakantashi habaa inaaya miye laifinshi Wlh he’s even confused cikin daren nan ya nemo numberna wurin class rep ya kira yana gaya mani ya tambayeni wai kinada aure habaaa mana fatima you’re not young think sosai mana miyasa zakice mashi you’re married dan kawai baki san shi ko miye” inaaya tayi ajiyar zuciya tace “ihsan you won’t understand kawai ki kyaleshi” ihsan abun ya fara bata haushi tace “understand what inaaya the fact that you despise him shine kikayi karya to get rid of him wlh babu kyau ki bar wulakanta mutane hakanan bawan Allah just because kinga lots of people wants you doesn’t mean ki dinga wulakanci” yanda ihsan ke ta accusing dinta da wulakanci ta fusata “what do you want to hear ihsan seriously? Wulakanci you won’t even ask me my reason for doing that in a calm way and you’re accusing me huh? How is doing what is right wulakanci? He’s my lecturer and i am his student it’s all my fault that i gave him my number and even became free with him cux i am not suppose to and by trying to mend everything you’re now accusing me? What did you know ihsan you want me to be cheater so kike na zama mutuniyar banza dan na faranta ma wasu so kike Na yi abunda Allah zaiyi fushi dani na zama mai cin amana?” Yanda take magana yasa jikin ihsan yayi sanyi tace “what are you talking about inee” inaaya da kuka yaci karfinta taci gaba da cewa “ihsan so kike na faranta ma wasu na zama mai laifi wurin Allah ohhk fine let me tell you what you don’t know today I didn’t intend to tell you but this is the real and bitter truth I AM A MARRIED WOMAN” muryan ihsan na rawa tace “me kika ce” inaaya tace “yess ihsan what you heard i am married you want me to cheat my husband by talking to another man huh?” Ihsan tace “what habaa inaaya you know I won’t just buy that story of yours kina zaune a gidanku kice mun you’re married it doesn’t make sense” murmushi mai cin rai inaaya tayi tace “its upto you to believe ihsan you can call mimi for confirmation or even sultaana or inteesar it won’t change the fact that i am married even tho the wedding haven’t taken place the nikkah took place months back I’m married to ya aliyu inteesar’s brother you can enquire from anyone close to me goodnight!” Kit ta kashe wayanta hawaye na ci gaba da zubo mata ita kuwa ihsan shock ya kamata tabi wayanta da kallo babu yanda ta iya bata sake kiran inaaya ba ta kwanta bacci da tunani kala kala a ranta har bacci ya dauketa, inaaya kuwa kasa bacci tayi bayan tasha kuka har ta godewa Allah ta dauro alwala ta fara nafila ta dunga rokon Allah ya yafe mata a kan prayer mat bacci ya dauketa.

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE