JALILA CHAPTER 10

JALILA CHAPTER 10

Fitowa tai jiki a sayaye, abin duniya duk ya dameta ga tsoron abinda zai fito daga bakin Dady da takeyi. Tana sauka kasa taga Ummy, Ummy ta nuna mata hanyar falo tare da mika mata tiren dake dauke da juice da cup, Jalila ta amsa tare da yin murmushin dole sannan ta nufi falon. A gefen kofar da zata shiga da ita falon taga Sageer a tsaye, kallansa tai da idanunta wanda suka cika da taoro, yace “Jalila, menene wai?” Kai ta girgiza mai alamar ba komai, zata shiga yankara kasa da murya yace “Jalila?” Juyowa tai ta kalleshi, yace “Bakyasan ganin mahaifinki ne? Naga tunda na fada miki yazo naga fuskarki ta canza.”+ Murmushin yake tai sannan tace ” bakomai, nagode.” Kawai ta shiga, dan batasan me zatacemai ba. Abba na falon suna ta magana ta shiga bakinta dauke da sallama. Abba da Dady suka amsa, Dady ya kalleta cikin farin ciki yace “Jalila!” Jalia tace “naam sannan ta karasa ta ajiye tiren a gabansa ta gaisheshi. Abba ne ya mike yace “yanzu ba abin business kazo ba, uba ne yazo ganin yarsa, kaga bai kamata na shiga tsakani ba, later mayi magana.” Dady ya mike yana godiya har ya fita, kallan Jalila yai wacce ke tsugunne a inda ta ajiye juice din, Dady yace “zauna mana.” Ta gyara zamanta tana kallansa, gabanta sai faduwa yake. Dady ya zauna sannan ya kalleta yace “hmm ya gidan?” Tace “lafiya, wani abun ne ya samu Goggona?” Yace “wani abun? Kamar me kenan?” Tai shiru ta kasa magana, yace “dan uba yazo ganin yarsa sai ya zama sai akwai matsala?” Jalila ta kalleshi tace “a’a ba haka bane.” Yace “Jalila ni mahaifinki ne, ki daina dararewa da ni.” Ta kalleshi kawai bata ce komai ba. Matsowa ya danyi kusa da ita yace “jalila magana nakesan muyi.” Kallansa tai cikin tsoro, yace “Nikam ya kukai da mijin naki?” Tace “wani mijin?” Yace “wanda kukazo tare mana, badai wani abun kika fadamai ba ko? Naga kamar baiji dadi ba ranar.” Jalila ta kalleshi gabanta na faduwa ta kasa magana, Dady yace “amma yasan Goggo ce ta haifeki ko?” Jalila ta daga kai alamar eh, Dady yace “ya fadama wani ne?” Tace “ban gane ba?” Yace “ya fadama wani kamar mai gidan nan cewar Goggo ce ta haifeki?” Jalila tai shiru, yace “ba dai duk wani sirri na gida kin fadamai ba?” Jalila ta kalleshi yanzun ma batace komai ba, ya kalleta ransa a bace, badai duk wahalar da wulakancin da ya hadiye ba lokaci daya wannan yarinyar zata zo ta ruguzamai? Dan ya tabbatar in har Taura ya kwace kudin daya basu tabbas Inna korar sa zatasa ayi daga company din. Kallan Jalila yai rai a bace yace “Wai Habiba ba magana nake miki ba? Sai dai ki kalleni? Ko kema munafircin uwar taki zaki koya?” Jalila cikin tsoro ta kalleshi, hannunya daga a zuciye zai kai mata mari. Jiyai ance ” da alama sararka kenan?”1 Juyowa tai da sauri ya kalli mai maganar, Jalila ma kallansa tai kawai sai ji tai hawaye sun zubo mata. Karasowa yai cikin tafiyarsa ta isa sannan ya kalleta yace ” tashi.” Mikewa tai tana kallansa, yace “bakiji me nacemiki ba ne da zaki zo?” Tace “me kace?” Yace “sau nawa zan ce miki ki canza tone in zakiyi magana? Meyasa bakyayi da confidence?” Kallan juna sukai, hawaye ya gangaro mata, juyawa yai ya kalli Dady wanda yai tsuru tsuru. Hassan ya kalleshi yace ” gobe zanzo muje dakai asibiti inda aka kwantar da mahaifiyarta, a gabanka zakasa hannun sallama mu amsheta.” Dady yace “me kake nufi?” Yace “abinda zuciyarka ta baka, u don’t deserve to be a father nor a husband.”9 Kallan Jalila yai yace “wuce mu tafi.” Kallan Dady tai gabanta na ci gaba da faduwa, Hassan ya kalleta ya mata alama data fara fita, nan ta fita tana waiyaye. Tana fitowa daga bangaren falon taga Sageer a tsaye a jikin bango. Yana ganin ta fito ya matso da sauri yace ” Jalila” Hawayenta ta share sannan ta kalleshi, yace “menene?” Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta juya tai gaba, Sageer yace “Akwai abinda ya faru ko? Naga yaya ya shiga kuma shi bai fito ba.”5 Juyowa tai ta kalleshi sannan ta juya kawai ta hau sama da gudu. A falo kuwa Hassan ya kalli Dady yace “me ka samu, na saida yarka dakai?” Dady yace “me kake nufi?” Hassan yace “yanda kai da manyanka iyayen gidannka kuke nunawa, kunayi ne kamar kun samu wani abu sosai wanda yasa kuka bada yarku.” Dady ya kalleshi yace “Hassan ta ya zaka ce haka? Kana so kace rashin so ne yasa muka aurar da ita?” Yace “sosai, inba rashin so ba kun taba tambayar ya mijin nata yake? Wasu halaye gareshi? Me nene aikinsa? Ya mu’amalarsa da jama’a take? Duk kunyi wannan tambayar? A matsayinka na uban yarinya?” Dady ya kalleshi yace “Inna tayi bincike ita ce tasan mahai…….” Ya katseshi rai a bace “wacece ita? Menene matsayinta agun Jalila?”4 Dady yace “bangane ba?” Hassan yamai wani kallo yace ” karka manta gobe zanzo in banzo ba jibi zanzo, in kuma har kukai tunanin yin abinda bai kamata ba, zan baku mamaki.” Ya juya bai jira mai zai ce ba ya fita. 1 Dady haka ya fito gaba daya kansa yayi nauyi, Sageer ne kawai a falon yamai sallama ya fita, yana cemai ya gaida Taura. Mota ya shiga yai gaba. Sai daya je kofar gida sannan yai parking a gefen mota ya kashe motar ya fito yana tunanin abinda zai fi mai mahimmanci, danshi rayuwarsa itace gaba da komai, mai zaiyi dan cigaban sa? Hassan kam yana haura beni kansa na wani juyawa da kyar ya kai kansa daki yana shiga ya kwanta. Jalila na falo tana ganinsa ta taso dan dama ta kasa ko zama ne. Yana shiga a shiga dakin itama, akwance ta ganshi akan gado, taje kusa dashi tana san mai magana sai dai ganin idanunsa a rufe tasan bayasan magana, balle ya juya mata baya. Ta dan dade a tsaye kafin ta fito. Karfe tara tai shimfida ta kwanta, shikam tunda yai sallah ya sake kwanciya bai sake ko motsawa ba balle ta samu damar magana. Shikam takaicin abinda ke faruwa a gidansu ne yake damunshi, meke damun Abba? Meyasa ita wannan rayuwarta take a cude? Meyasa abubuwa ke faruwa haka? Yau ce rana ta farko dayai fada da magana mai tsayi haka, gaba daya kansa wani irin sarawa hakeyi, ya dade sosai kafin bacci ya daukeshi. Jalila kam ta dade a kwance kamar tana bacci, me suka fada da bata nan? Taya uba wanda ya haifeta zai dinga mata haka? Hawayenta ta share data tuno rayuwar da mahaifiyarta tai, lalai bazata bari Goggo ta cigaba da zama dasu ba. Juyawa tai saitin da Hassan yake, ta haska wayarta, ganinsa tai a dukunkune ta mike ta dan rage A.C din dakin sannan ta matso inda yake, kansa baya kan pillow din, in dagashi? Ganin yanda ya kwanta a takure. Hannu tasa a hankali ta daga kansa ta daura akan pillow din sannan ta juya ta kwanta. Shikam tana tabashi yaji ta, har sai data kwanta idanunsa na bude juyawa yai shima saitin da take kwance, duk da ta kashe hasken dakin ba ganinta yakeyi ba, sai dai ya samu kansa da tsurawa gun ido kafin ya maida idanunsa ya rufe. ************* A kasa kuwa, Ummy ce tasa kayan baccinta ta sa hijab tana neman fita daga dakin. Abba ya kalleta yace “ina zaki?” Tace “Dakin Ameera, ni kam kamar munyi kuskure da mun sani dakin can mun gyarashi.” Kallanta yai yanda take mai magana kamar bawani abu na sabani a tsakaninsu. Abba ya kalleta zaiyi magana wayarsa tai kara. Kallansa tai tace anama waya, ta juya ta fita. Zaliha ce, kashe wayar yai gaba daya sannan ya mike ya fito daga dakin. Dakin Ameera ya shiga, Ummy tana kade gadon ya bude kofar, kallansa tai tace “ya akai? Ko akwai abinda kakeso?” Abba ya kalleta sannan ya shigo ciki ya zauna akan gadon yace ” Kinsan gwara kiyi fada?” Tace “fada kamar yaya?” Yace “wannan abinda kikeyi it really scared me, gwara ki nunamin ranki ya baci in ma hakuri ne na baki.” Tace ” munyi fada dakai ne?” Kallanta yai, tace ” kai da Hassan ne kukai fada akai na wanda ni banaso, sai dai ya zanyi? Banaso naga kuna irin wannan akaina, tunda nake dakai na taba hanaka aure?” Yace ” kece kuwa kike da yanda zakiyi tunda akanki akeyi, ke kadaice kike da dama hana fadan, sannan maganar aure nasan tunda nake dake ban taba sha’awar kawo wata mace gidana ba, yanzun ma ni kaina bansan meke damuna ba.” Ummy ta kalleshi tace ” saboda kanasan ta shine ka hauni da fada waccan zuwa akan zaka koma Abuja, sannan yanzu kace bakasan meke damunka ba? Ni mubar wannan maganar, ni matsalata da damuwa ta akan Hassan ne, dan Allah ka daina barin yana sanin abinda ke faruwa a tsakaninmu, kafi kowa sanin halinsa in har yasan ina cikin damuwa, banaso Sageer ko Ameera ma susan wannan maganar, na rokeka da Allah, in aure zakayi kayi, wannan ra’ayinka ne sannan rayuwarka ce amma Please karka bari yarana su shiga wani hali a dalilin abinda kakeso.” Abba ya runtse idanu cikin takaicin abinda ya dade yana ginawa, wato farin cikin gidansa na neman wargajewa a dalilinsa. Ummy ya kalla cikin wani yanayi na tausayawa sannan yace “Maimuna ina cikin wani hali……..” Yanda yai maganar ne yasa ta tsaya tana kallansa sai dai tausayinsa ne ya kamata, dan bazata taba manta irin wannan muryar ba daya zo mata da ita a can baya shekaru masu yawa, a lokacin kalmar nan sai data sata kuka mai yawa, yanzun ma hannunta tasa akan nashi sannan ta zauna a gefensa tace ” In kanasan ta ka aureta, in dai shine matsalar, ni zanma Hassan magana, sai dai kafi kowa sanin baka isa ka zaunar da ita a gidan nan ba, in har baso kake danka ya mata illa ba.”1 Kallanta yai cikin rauni yace “ba santa ne matsala ba, ni gaba daya abinda ke damuna ne matsala, n rasa a yaushe na fara santa, a yaushe naji in banganta ba bazan iya rayuwa ba, na rasa a yaushene na fara amsa mata akan duk abinda tazomin dashi.” 4 Ummy ta kalleshi cikin mamaki tace “me kake mufi?” Ya kalleta yace “kizo mu kwanta, banajin dadin abinda mukeyi, me kike tunanin zai faru in Hassan ya ganki anan? D’a nane sai dai duk duniya nafi shakkarsa akan kowa, sannan shikuma indai akanki ne ba abinda bazai yi ba.”1 Ummy bata musa ba ta mike sukai daki, kwanciya sukai, tace “baka fadamin matsalar ba.” Yace “gobe zan gaya miki mike faruwa wanda na kasa ganeshi.” Ummy tace “Allah yaa kaimu.” Nan sukai bacci………… Sageer kam gaba daya ya kasa bacci, daga bayama mikewa yai ya zauna akan gado ya kunna fitila yana tunani, anya bashine sillar komai ba? Gaba daya tausayin Jalila ya hanashi rintsawa…… ****** A can gidan Inna kuwa, Inna sai kiran wayar Dady take bai dauka ba, yana kallan kiranta yaki dauka, sai data kira sau hudu sannan ya daga yace “gashinan zuwa.” Ajiye wayar yai ya koma mota, dan ya gama tunanin mafitarsa, yasan kuma yanda zai buloma abinda ke faruwa dashi………. Washegari…… Jujuya cokali kawai takeyi a cikin cup din tea din, jefi jefi tana kallansa ta kasan ido tanasan mai magana, shikuma yana zaune a kasan yanacin abincinsa kamar ba wani abu dake damunsa. Can dai ta tattaro dauriyarta tace “hmm yaya nace……” Kallan daya mata ne yasa ta maida bakinta ta rufe tare da kallan cup din ta cigaba da juya cokalin. Yana gama ci ya mike ya shiga toilet, wanka yai sannan ya fito. Kallansa tai ta ganshi daga shi sai towel dake daure a kasa, da sauri ta juya baya tare da rufe fuskarta da tafin hannunta bai bi ta kanta ba harya saka kayansa, sannan ya dawo gaban madubi yana shafa mai, yana gamawa ya fefesa turare. Jalila ta juyo ta kalleshi, matsowa kusa dashi ta danyi kadan tace “Yaya bakacemin komai ba.” Bai tanka mata ba ya dau wayarsa da makullin mota ya fita, tana tsaye ya rufo kofar. Kallan kofar tai cikin mamaki a fili tace “mekenan?” Takaici ne ya kamata ta zauna a bakin gadon dabas tama rasa me zata ce. Hassan yana sauko kasa ya sa hannu ya kwankwasa kofar dakin Abba. Bude kofar Ummy tai sannan ta kalleshi, tace “Hassan kaine?” Ya gaisheta sannan ya kafa leka dakin yace “Abba fa?” Tace “yanzun nan yadan fita waje gun garden waya zaiyi.” Waya? Waye ya kirashi? Ummy ta kalleshi tace “Hassan!” Kallanta yai fuskarsa ta fara canzawa, tace “Please Hassan ka dinga sama zuciyarka salama, ka dinga hakuri, Abbanka namiji ne yanada hakkin auran duk wacce yakeso………..”+ Juyawa yai bai jira ta gama magana ba yana neman tafiya, tace “Hassan magana nake.” Ya juyo ya kalleta yace “Yahkuri Ummy abu zanyi ne cikin gaggawa.” Kamar zata sake magana sai ta fasa, ta bishi fa kallo, Allah sarki Hassan tafi kowa sanin irin kaunar da yake mata. Garden ya nufa, Abba na tsaye yana waya ya karasa gun, kallan Abba yai kallan zargi, Abba yace “Hafiz Please ka barni tukunna.” Bai kara jiran yayi wata magana ba ya katse layin, Hassan ya kalleshi kamar zaiyi magana sai kuma ya gaisheshi. Abba ya amsa yace “Hassan.” Kallansa yai yace “kai da wanene haka?” Yace “business ne ba wani abun ba uban yan zargi.” Hassan ya juya kai sannan yace “me kaba iyayen Yarinyarnan a maimakon auranmu?” Abba ya kalleshi cikin mamaki yace “Hassan menene?” Hassan yace “bakomai, kawai dai so nake nasani, dan na tabbatar give and take kukai da rayuwar ta.” Abba yai shiru kafin can yace “Bakasanta ne ko me? Ko wani abun ne ya faru?” Shiru yai baice komai ba, kamar kuma zai saie magana sai ya juya zai tafi, Abba ne yace “Company dinsu ne ya ke neman yin Bankrupt shine na taimaka musu.” Hassan ya kalleshi sannan yace “yarinyar fa? Have u take care of her?” Abba yace “kamar ya kenan?” Hassan ya kalleshi yace “Abba ina dai sone a komai zakayi ga dinga tuna wacece Ummy a garemu.” Abba ya kalleshi yace “Hassan just pray for me, wlh nikaina bansan meke damuna ba.” Hassan yai shiru yana kallansa, Abba yacigaba “yanzu zan fada mata abinda ke faruwa itama, Hassan kafi kowa sanin family na are above komai na rayuwata ciki kuwa har da ni kaina, kasan yanda zan iya sadaukar da komai saboda su, sai dai i feel like there is definitely something wrong with me, na rasa yanda zanyi in cire yarinyar daga raina, as if samin ita akai a ciki.” Hassan kallansa yake, sai dai yasan mahaifinsa tabbas wannan kalaman daga zuciyarsa suke fitowa. Kallansa yai yace ” nafahimceka sai dai bansan meyasa zuciyata take blaming dinka ba, bawai baka iso kaso kowa bane sai dai Ummy doesn’t deserve this treatment.” Abba cikin takaici yace ” Ba so kadai bane a raina Hassan, mata nawa nake hulda dasu? Zance ba macen da ta taba burgeni ne? No kawai na riga nasa Ummynka ne beyond every woman, sai dai wannan karan it look like obsessed, inaji kamar dolene sai na sami yarinyarnan ko ta wani hali ne.” Hassan zaiyi magan, Ummy wacce hankalinta ya kasa kwanciya gani take kamar yanzun ma fada sukeyi yasa ta biyoshi, jin kalaman Abba ne yasa ta tsaya tana jinsu, sai dai yanzu kam idanunta ne suka zubo da kwalla, muryarta na rawa tace “it look like akwai babbar matsala a tare dakai” A tare suka juya suka kalleta, Ummy ta karaso tace “just one month, ka bamu one month, ka daina kiranta sannan mu dukufa da addu’a musa nalamai ma su maka, in har a wata dayan nan dukda haka bakaji santa ya ragu a ranka ba ni na amince ka aureta.” Ummy!” Hassan ya fada yana kallanta, tai murmushi tace “in har a wata dayan kaima ka amince dani, karka nemeta sannan ko ta nemika ko a wayyane karka daga ko ka canza number” Abba yace “na amince.” Hassann ya kallesu yana sanyin magana, Ummy tacee “Hassan please.” Idanunsa ya runtse, Abba yai murmushi tare da dafashi yace “Hassan bakasan dadin da nakeji ba, sauki ya fara samuwa da alama wannan auran rahama ne a gareka damu baki daya.” Hassan ya kalleshi sannan ya kalli Ummy, juyawa yai sannan yace “Shikenan Ummy tunda ke kikeso, sai dai ni ba one month ba ko shekara kikaba Abba bazan aminceba.”1 Ummy tai murmushi tace “nagode my eldest.” Juyawa yai yabar gun, mota ya shiga sannan ya fita daga gidan. Jalila kam ta dade a zaune kafin ta dauko tiren abincin. Akan dinning taga Sageer yana breakfast, da alama ma fitowarsa kenan dan tea yake hadawa. Yana ganinta ya kura mata idanu har ta iso inda yake, gaisheshi tai, idanunsa na kanta yana nazarin fuskarta ya kasa amsa gaisuwar. Kallansa ta sakeyi, yanzu kam ita kanta ta fahimci da abinda ke dakunsa dan duk fuskarsa ta canza, tace “Uncle bakada lafiya ne?” Flask din ya ajiye sannan ya zauna yace “a’a me kika gani?” Tace bakomai, wuceshi tai ta ajiye tiren abincin, kallanta yai yace ” Yaya fa?” Tace “ya fita.” Shiru yai sai binta da kallo da yakeyi. Jalila ta ajiye sannan ta fara dauraye kwanukan da sukai amfani dashi. *********** Hassan na fita ya hau titi yana tafe yana tunani, meyasa yarinyarnan bata iya fita a ransa? Ya rasa me yasa in yaji ko yaganta cikin damuwa hankalinsa baya kwanciya.4 Daren jiya ya tuno wajen karfe uku da rabi, kansa dake ta sarawa ya hanashi bacci, jin kamar ana kuka da magana, mikewa yai ya kunna fitilar gefen gado. Jalila ce da alama mafarki take, kusa da ita yaje ya zauna yana kallanta, alamar kuka takeyi tana magana kasa kasa, kunensa yasa kusa da bakinta dake motsi. “Dady, Mumy, Inna na kuyi hakuri karku kori Goggo dan Allah, na daina, na daina……” Abinda take cewa kenan, hankalinsa da tausayinta sune suka kara ratsahi, addu’oi ya mata sannan ya kamo hannunta ya rike yana kallanta. Ya rasa me yake tunani a sanda yake kallanta, meke faruwa dashi? Is he feeling guilty? Tunda yasan dalilinsa ne yasa aka mata auran dole? Sai dai abinda yakeji ya banbanta…… ya dade sosai har sai dayaji anata kiraye kirayen sallah sannan ya mike yai alwala. A kofar gidansu yai horn ya shiga, Mumy da Dady na zaune a falo, Yasmeen na gefe tana shan chocolate tana wasa aka sanar dasu zuwansa. Ba Dady kadai ba har Mumy sai da gabanta ya fadi, ta kalli Dady da sauri tace ” Dadyn Yasmeen meke faruwa? Cikin rawar baki yace bansani ba nima wallahi.” Yafada yana tuna kalaman Hassan badai zuwan dayace zaiyi yau ko gobe ba shine yai? Mumy ce ta bada umarnin akan a shigo dashi, ita kuma tai sama da sauri. Inna na zaune tana jiran Dady wanda tun jiya take sa ran ganinsa amma baizoba haryanzu. Shigowar Mumy ne yasa ta kalli kofar ta dauka Dady ne, ganin Mumy yasa tace “ya akai kuma?” Mumy da sauri tace “Inna yaran ya dawo.” Tace “yaro? Sultan?” Da sauri tace “bashi ba, mijin Jalila.” Inna ta kalleta da sauri tace “ya dawo ina?” Mumy tace “yana gidan nan, bansan dame yazo ba.” Inna ta mike hankali a tashe tace “gidan nan?” Mumy tace “yana falo.” Inna ta dau mayafi ta fito, mumy ta biyota a baya tana cewa “Inna badai wani abun ya sake faruwa ba?” Itadai Inna batace komai ba, har suka isa kasa. Dady na kasan beni da alama jiransu yakeyi, Inna na saukowa yace “Inna.” Kallansa tai tace “badai jiyan kwafsawa kai ba?” Dady yace “kwafsawa kamar ya?” Haushi ya kamata tace ” wuce muje, koma menene let’s hear it together.” Nan sukai falo? Hassan na zaune akan kujera suka shigo su uku. Kowa ya samu guri ya zauna, Hassan ya gaishesu sannan ya kalli Inna wace itama kallansa take, ya kalli Mumy da Dady wanda suma hanyace ” zuwa nai mahaifin Jalila ya rakani inda mahaifiyarta take, zai sanya hannun sallamarta.” Inna ta kalleshi sannan ta kalli Dady wanda a ransa yace Oh My God! Wannan wani irin yarone? Ya gama hargitsamin plan dina.2 Dasauri ya girgizama Inna kai alamar ba shi bane. Inna ta kalli Hassan tai dariya tace “Hassan taya za’a sallami mara lafiya? Bayan ba warkewa tai ba?” Yace “eh wannan damuwarmu ce, dan in aka sallameta hannuna zata koma.” Mumy d Dady da Inna a lokaci daya sukace mene? Hassan ya kallesu yace “menene abin mamaki? Ba mahaifiyar matata bace? Banaji cikinku akwai mai hakkinta.” Inna tace “mene?” Yace ” why? Bazai yiwu ba? In bazai yiwu ba bari na kira Abba na sanar dashi, ina tunanin kamar zamu amshi kudin mu.” “kudi?” Hassan ya daure dan kansa wani irin sara mai yakeyi, ya mike ya kalli Dady yace “ina mota.” Ya juya ya fita alamar wai yana jiran Dady a mota. Inna tabi kofar daya fita da kallo, sannan ta kalli Dady, takaici da bakin ciki ne suka kamata. Dady yace “Inna ya zamuyi?” Cikin takaicinsa da bakin ciki tace “dalla wuce kaje ka rakashi, ko so kake company dinmu ya mutu?”1 Dady ya mike ya fita. Inna takaici ya kamata tace “lalai ba yaran nan bane bashida hankali nice banda hankali dana kawo babban makiyi har cikin gidana da kaina……” Dady ya shiga mota Hassan yaja suka tafi. A asibitin premier sukai parking, ya zaiyi?Gashi bayasan asibiti, gashi yabar Jalila agida sabofa bayasan su nemi wulakantata. Tsayawa yai shi bai fita daga cikin motar ba sannan baiyima Dady magana ba, Dady kam wanda yake a zaune yana nazarin yaran ya kalleshi yace “muje?” Hassan ya fito daga motar sannan ya tsaya yana kallan asibitin, babban matsalarsa bawai shigar bane, zai iya shiga reception ko gun da ba marasa lafiya kamar office, sai dai daga yayi bangaren dakuna na marasa lafiya hankalinsa yake tashi, shiyasa kwanaki yana fara hawa saman beni yaji gaba daya hankalinsa da tunaninsa na neman gushewa. Da kyar ya daure suka nufi reception din, nan yamusu bayanin abinda sukeso, suka turasu wani office, nan ma sunyi cike cike, suka rubuta kudin da za’a basu, Hassan ya biya, suna fitowa ya kalli saman benin sannan ya kalli Dady dabara ce ta fadomai yace “kaje ka sanar da ita, ka kuma nemi yafiyarta sai ku fito tare ni ina mota.”7 Dady ya kalleshi a ransa yace “lalai wannan yaran bashida tarbiyya, ina sirikinsa amma ya maidani dan aike? Kamar wani masinjansa, ko driver? Yana tsaye har Hassan ya fita sannan yai kwafa ya hau saman. Goggo na zaune tana shafa mai a hannunta, yau kam jikin da sauki, lantana na tattare kwanukan da aka kawo abincin safe zata maidasu gida. Dady ya turo kofar ba ko sallama, Goggo ta kalli kofa, ganinsa sai dayasa gabanta faduwa, ya shigo fuskar nan a hade ya tsaya yana kallan dakin, kallan Lantana yai yace “ke dan fita.” Lantana ta mike tai waje, Goggo ta kalleshi tace “ina kwana?” Dady bai amsa ba yace ” hankalinki ya kwanta?” Tace “da me fa?” “A haka in aka kalli fuskarki ba wanda zaiyi tunanin zuciyarki akwai hassada, bakinciki da tsantsar munafirci.” Goggo cikin mamaki tace “me kake nufi?” Yace “sai ki taso ki zo kibi mijin yarki da kikasa ya daukeki daga gunmu.” Goggo cikin mamaki tace “mijin ‘yata kamar ya kenan?wace yar tawa?” Yace “ni banda lokacin munafircinki, ki taso ki fito, in kuma bazaki iyaba ki cigaba da zama.” Goggo gaba daya kanta ya daure ta kasa gane me yake nufi, kwallama Lantana kira yai yace “zo ki kwashe kayan nan an sallameta. Goggonta mike tsaye tadan dosana kafarta tace “Wai Abubakar me kake nufi ne? Ni na rasa me yasa kullum kai burinka ka jefeni da sharri.” Cikin takaici yace “sharri? Ai kece kike bina da sharri dan na tabbatar badadan ke ba da tuni Inna ta bani company dinsu, amma saboda tana ganin naci amanarsu na kawoki, daga ke har ‘yarki banda bakinciki me kuke tsinanamin? Da na dauka yanzu zan moreta sai gashi yau ta wargaza komai, ni ki wuce mu tafi dan ganinki ma bakin ciki yake sani.” Goggo kallansa kawai take zuciyarta na wani irin kunna, tace “nikam menene matsayina agunka? Ma dauka ni matarka ce.” Wata irin dariya yai wanda yasa ta kallansa cikin wani yanayi, yace “mata? Wa? Kedin? Kema kinsan ni ba sa’an auranki bane ko a can baya bare yanzu, ni ba wani aure ko makamancinsa tsakaninmu, ina zaune dake ne kawai saboda yarki da tazamarmin dole.” Goggo ta share kwallar ta tana neman yin magana ya fita yana cewa “kuma ki sauko yanzu.” Lantana ta shiga saukar da kaya kasa, dady ya nuna mata motar Hassan, nan aka bude boot din mota aka sasu, itakam Goggo ta dade tana kuka, nurse tazo ta kara dubata sannan ta taimaka mata ta sauko, shigowar Lantana na karashe suka sauka tare. Tsayawa tai tana kallan motar, Hassan ya taho da sauri gunta sannan ya kalleta. Kallansa tai cikin mamaki tace “wanene?” Hassan ya kalleta sannan yace “bari na kira kuyi magana da Jalila.” Dan baisan me zaice ba. Matsawa yai ya kira number Sageer. Sageer na daki lokacin da Hassan ya kirashi, yayi mamakin kiransa ya amsa da sauri yana cewa “yaya lafiya?” Hassan yace “Sageer ina Jalila?” Yace “tana sama dazu ta hau.” Hassan yace “please ka dan kai mata waya.” Yace to sannan ya mike ya fito. Jalila tafito daga wanka kenan ta zura wata doguwar rigar atamfa, dan dama kwalliya bata dameta ba saboda ba barinta ake tana yi ba, sannan bama wani iyawa tai ba, balle hankalinta ma ba’a kwance yake ba bare tai tunanin yi. Mai kawai ta shafa ta dan shafa hoda tasa turare, dan kwalimta kawai ta yafa akanta, ta zauna kenan ta dau wayarta taji knocking. Mikewa tai ta bude. Ganin Uncle ne yasa ta tsaya tana kallansa, shima kallanta yai sannan ya mika mata waya yace “Yaya ne.” Amsa tai bata rufe kofar ba ta juya zuwa ciki tana cewa “Yaya!” Yace “yauwa.” Tana jiran ya sake magana kawai taji sallamar Goggo, jikinta na rawa cikin rawar baki tace “Goggo.” Goggo tace “jalila?” Jalila hawaye ya zubo mata tace “Goggo kina ina?” Tace “gani a kasan asibitin ance wai wani ne ya zo daukana shikuma naga bansanshi ba, shine ya kiraki, kinsanshi ne?” Jalila tana kuka tace “ki biyoshi Goggo, ke kadai ce?” Tace “a’a mahaifinki nanan.” Jalila tace “Goggo dan Allah karki nuna bakinsanshi ba, ki bishi zai kawoki inda nake.” Cikin mamaki Goggo tace “inda kike? Kedin bakya gida?” Jalila tace “inkinzo zan sanar dake komai.” Goggo tace to, sannan ta kalli Hassan ta mikamai waya, baice ma Jalila komai ba kawai ya katse wayar. Jalila ta juyo inda Sageer yake tana hawaye, tace “Uncle!” Shikam hankalinsa ya tashi ganin tana kuka yace “menene? Wani abun ya faru ne?” Gani yai tana dariya tana kuka, tace “Uncle, Yaya ya daukomin Goggona.” Tsayawa yai sai dai yanzu baisan me zai kwatanta abinda yakeji ba, yai murmushi yace “duk da bansan meke faruwa ba, it look like abin farinciki ne, sannan alama ce ta shakuwa na shiga tsakaninku, tunda gashi har yasan abinda ba wanda ya sani, sannan lafiyarsa ma nasan samun kusanci dake ne yasa, uhm congratulation, Allah ya barku tare.” Ya juya jiki a sanyaye da kallo ta bishi zuciyarta na tausayamai, ta tabbatar Uncle na santa sosai bawai ya rabu da ita bane dan kansa sai dai zumunci da kaunar da ke tsakanin shi da yayansa. Hawayenta ta share sannan ta zauna abakin gadon tana tunanin me zata ce ma Goggo? Hassan kam Goggo na shiga mota ya kalli Dady yace “Allah yasa akwai kudi a jikinka” Dady yace “babu, menene?” Hassan ya sa hannu a aljihu ya dauko 1000 yace gashi ka hau mota dan gida zan wuce daga nan.”32 Dady yace “mene? Kai ni na haifi Jalila fa, bawai dan aikin gidansu bane, wai me yasa……” Ganin Hassan yai ya shiga mota kamar ma badashi yake ba yaja yayi gaba, ran Dady a bace yabi motar da kallo.4 Hassan kam jan motar yai sukai gaba, Goggo da Jalila na baya, suna fara tafiya Goggo tace “meke faruwa? Ya akai Jalila tabar gida?” Hassan ya dan shafi kansa dake ciwo yace ” Jalila zata miki bayani, zaifi cancanta ta miki bayani da kanta.” Goggo tai shiru tana addu’a aranta, Allah yasa Jalila ba wani mugun abu ta fada ba, sai dai kallan Hassan yasa wannan ya tafi daga ranta. Kallan tangamemen gate din da aka bude yasa Goggo ta kara cewa “tana cikin nan?” Yace “eh.” Kallan gida take har yai parking, da gudu Jalila wacce ke tsaye a waje ta taho bude kofar inda Goggo take a zaune. Kallanta Goggo tai sannan ta kalli gidan zatai magana Jalila ta rungumeta ta saki wani irin kuka. Hassan ya juyo ya kalleta, me yasa ta fita kuka ne? Shifa bayasan kukan nan. Kallanta yai yace ” kuka zaki tsaya yi ba zaki taimaka mata ku shiga ciki ba?” Ta share hawayenta tana cewa “Goggo muje.” Hassan ya fito ya wuce ciki bai jira su ba, a falo ya taradda Ummy da alama fitowarta kenan, kusa da ita yaje yace “Ummy ina Abba?” Tace “yana falon sa.” Yace “Ummy muje akwai maganar da zamuyi.” Kallansa tai cikin jin dadi tace “da alama Hassan dina yanzu bakinsa na kokarin yin magana akai akai.” Hassan ya juya ya kwankwasama Sageer kofa ya fito, yace “muje.” Nan suka shiga kofar falon Abba. Yana zaune rike da qur’ani dan suna shigowa Ummy ta dauko ta mikamai itakuma da bata sallah tadau littafin addu’oi. Shigowar su ne yasa ya kai aya sannan ya ajiye ya kallesu. Zama sukai Abba yace “lafiya?” Ummy tace “Hassan ne zaiyi magana.” Abba ya kalleshi yace “Hassan!” Zama yai sannan ya dansa hannunsa na haggu akansa dake ciwo yace “tare nake da bakuwa.” A tare sukace “bakuwa?” Hassan yace “eh, tunani nake boys quarters din mu zansa a gyara sai na maida ita can.” Abba yace “naji ba wai wannan bace maganar, wacece bakuwar? Itace tambayarmu.” Hassan yace “mahaifiyar Jalila.” Abba cikin mamaki yace “me kake nufi? Taya zaka dauko mata a gidan mijinta da arzikinta da komai ka kawota boys quaters?”” Hassan yace “bansan ta ina zan fara bayani ba, sai dai ita zatayima Ummy kudan bata lokaci kadan, abu daya zan iya fada, wacce kuka sani a matsayin mahaifiyarta ba ita ta haifeta ba, ban kyauta ba na kawota ba da saninku ba sai dai wannan ne kadai solution din da yazomin” Ya mike saboda kansa dake ciwo ya fita. Abba yace “meke faruwa takamaimai? Ni na kasa ganewa.” Ummy ta dafashi tace ” mu jira kamar yanda yace, na tabbatar yana da dalilinsa, kasan Hassan mutum ne da baya shiga abin mutane, tunda kaga ya shiga wannan i am sure da dalili.” Sageer ta kalla wanda yai shiru yana tunani, tace Sageer taimaka muje mu shigo da ita, sai mu sata a dakin Ameera inyaso gobe sai a gyara can din.” Nan suka mike suka fita.6 A waje sukaga Goggo ta tsaya tana cema Jalila, “nifa bazan shiga ba sai naji inane nan.” Jalila ta daure tace ” Goggo dan Allah mu shiga wlh zan fada miki.” Goggo tace “Jalila.” Jalila ta rike hannayenta tace ” Goggo gidansu mijinane.” Goggo tace “me? Miji? Miji kamar ya?” Sageer har zai fita ya tuna Goggo fa ta ganshi ta kuka san sunanshi, kallan Ummy yai yace “Ummy bari na dan shiga toilet it’s urgent.” Dariya tai tace “to a fito lafiya.” Ya juya da sauri, yana cewa gwara mu mata bayani kafin ta fada cikin mutane. Ummy tana turo kofar taji Goggo na cewa “Jalila aure kamar ya? Aure bansani ba? Auran dole aka miki?” Cikin mamaki Ummy a karasa tace “meke faruwa? Bangane aure mahaifiyarki bata sani ba, meke faruwa Jalila?” Jalila ta kalli Ummy idanunta fal tace “Ummy.” Ummy ta kalli Goggo sannan ta kalli kafarta dake ciwo, tace “muje ciki sai muyi maganar a nutse. Goggo bata musa ma Ummy ba suka shiga ciki. Ummy ta zauna akan gadon kusa da Goggo akwai abubuwan da takesan ji, sai dai ta tabbatar matarnan ba lafiya ce ta isheta ba, dan ga kafartanan. Kallan Goggo tai tace “ki kwanta ki huta dan Allah karkiyi tunanin komai har sai hankalinki ya kwanta.” Goggo ta kalli Ummy tace “Hajiya ta ina zan kwantar da hankalina, aure? Bansani ba?” Ummy ta kalli Jalila ta mata alama da ta fita, sannan ta kalli Goggo bayan Jalilan ta fita tace ” sai yanzu na fahimci me yasa yarki batada walwala duk kuwa da yanda naso ta saki jikinta da gidan nan, na fahimci an cutar dake, an munafurceki, sai dai bayanda za’ai a maida hannun agoggo baya, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, inkin huta anjima sai muyi magana, sai kiji abinda ya faru nima naji abinda ya faru, amma yanzu ko saboda ‘yarki da kwanciyar hankalinta kiyi hakuri, lafiyarki itace abin dubawa a wannan lokacin.”+ Goggo kallanta kawai take tana mamakin yanda mace mai kudi, mai aji, mai kyau haka take magana cikin sanyi da nutsuwa, da alama Matarnan macece mai tsananin imani, da kaunar jama’a da sanin darajarsu.5 Kasa musama Ummy tai ta daga mata kai alamar fahimta, Ummy tace “nagode, ga toilet nan in zakuyi amfani dashi.” Ta fada tana kallan Lantana. Goggo tace “Angode.” Ummy tai waje ta turo kofar. A waje taga Jalila a tsaye, murmushi ta mata tace “me kike anan?” Jalila ta kalleta da idanunta da sukai raurau tace “Ummy kiyi hakuri, sannan nagode….” Ummy tai murmushi tace “wanda zakima godiya daban bani bace.” Sannan ki barta ta huta zuwa anjima, amma meke damunta?” Tace “hawan jini da diabetes.” Ummy ta kalli kofar dakin cikin tausayawa sannan tace “shikenan mu barta ta huta.” Jalila ta daga kai alamar to sannan tai hanyar sama. Hannu tasa tana neman bude kofar dakin, tsayawa tai tana rike da hannun kofar amma bata bude ba, tana tunanin abinda zata cemai, da wani bakin zata fara mai godiya? A hankali tai ajiyar zuciya sannan ta tura kofar, a kwance ta ganshi kamar mai bacci, kusa dashi taje ta tsugunna tana kallansa, hawaye ne yazobo mata wanda batasan ya diga akan kuncinsa ba, a hankali ya bude idanunsa. Kallanta yai tana share hawayenta, a hankali ya ke magana yace “Menene? Wani abun ya faru ne?” Hawayenta ta karasa gogewa da sauri sannan ta girgiza kai tace “bakomai.” Yace “and why?” Tace “bansan me zance maka bane, kawai sai naji hawaye….” Idanunsa ya lumshe kansa na sarawa yace ” it looks like it’s ur hobby.” Tace “kukan?” Ya lumshe ido kawai, kallansa tai sannan tace “bakajin dadi ne?” Bai tanka ba sannan bai bude ido ba, hannunta tasa a kansa wanda ke mai ciwo kamar zai tsage, jin zafi rau akan tai, da sauri ta kai hannu wuyansa, nan ma zafi a rikice tace “Yaya bakada lafiya, zazzabi ne a jikinka, jikinka zafi.” A hankali ya bude idanu yace “why? Are u worried about me?”4 Da sauri tace “sosai ma, ka tashi muje asibiti.” Ta fada tare da mikewa tana kokarin dagashi, hannu tasa ta riko hannunsa tana neman dagashi. Jawo hannunta yai, ta fada jikinsa, shiru ne ya ratsa dakin, ita kuma zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, a hankali ta kalleshi, idanuwansa a rufe suke, sai cewa yai ” sai yaushe za’a daga ni?” Ta kalleshi ta kalli kanta data danneshi, neman dagawa tai sai taji hannunsa na rike da ita gam.11 Tace “to ai…..” Idanu ya bude a hankali ya kalleta, a hankali tai kasa da idanunta. Saketa yai ta mike ta zauna a gun, bata tashi ba tace “Yaya dan Allah muje asibiti.” Yace “bana zuwa asibiti, sannan ni nasan jikina kawai nayi abinda bansaba bane shiyasa, karki damu.”1 Idanu ta kuramai bayan ya maida idanunsa ya rufe, a hankali tana kallansa tace “Yaya nagode, ban taba tunanin wannan ranar ba.” Bai tanka mata ba, idanunta ne suka ciciko tace “Kayi hakuri Yaya nagode sosai har bansan ta ina zan fara ba.” Yace “hakurin me?” A ranta tace “da na dauka kai mutum ne mara tausayi da mutunci.” A fili tace “for everything.” Idanunsa ya bude a hankali sannan ya kalleta, itama kallansa takeyi, sai dai da sauri ta maida idanunta gefe. Yana kallanta yace “ya zakiyi?” Tace “name?” Idanunsa na kanta tana kallansa taga ita yake kallo ta dauke idanta da sauri, yace “ya zakiyi insu Ummy sun tambayeki?” Tace ” bansan ya zanyi ba, wata zuciyar na sanar dani in fadi komai, wata kuma na tunanin abinda zai faru da Dady dan na tabbatar Inna bazata barshi ba.” Kamar bazaiyi magana ba, dan harta mike zata nemomai maganin zazzabi ragowar tata wanda takaima Ummy taji muryarsa yace ” kiyi abinda ya kwanta miki a rai.” Juyowa tai ta kalleshi tace “In na tuno abinda yama Goggo tundaga haduwarsu zuwa yanzu, sai naji kome zai sameshi bazan damu ba sai dai bansan meke damuna ba, I wish nima inada dauriyar zuciya ko rabin taka ce.” Alama yamata da hannu akan ta matso, matsowa tai gunsa, ya mata alama data kara matsowa, nan ma ta matso takai kunnenta saitin bakinsa, a hankali yace “in fada miki sirrin?” Kai ta daga da sauri, yace “kisa Goggonki a saman komai.”6 Abinda ya fada kenan yai shiru tare da juya mata baya ya rufe idanunsa, tsayawa tai tana kallansa me yake nufi? Tace “yaya!” Shiru yai baice komai ba, itama shiru tai tana tunanin me yake nufi. Ta dade a tsaye kafin ta daukon mai maganin, ta dauko ruwa a karamin fridge din dake dakin, tazo kusa dashi tace “Yaya tashi kasha magani.”1 Bai bude idanunsa ba, ganin bashi da alama ne yasa ne ta kara cewa “Yaya Please, ko in fadama Ummy?” Idanunsa ya bude yace “wato kina neman kiyi amfani da weakness dina ko?”1 Dariya tai tace ” inkaki tashi yanzu sai na sanarma Ummy.” Yace “eh lalai kinga gadon bacci na…”4 Ta kuntse dariyarta tana nunamai gadan da yake kwance akai, harararta yai sannan ya mike zaune ya fizgi ruwan hannunta ya mikamata dayan hannun ta. Zubamai maganin tana dariya.1 Sha yai sannan ya kwanta. ********** Ummy na shiga falon Abba ya kalleta yace “meke faruwa? Nifa na kasa gane abinda ke faruwa.” Tace “ni kaina bansani ba sai dai na tabbatar Hassan yasan me yakeyi, kafi kowa sanin halinsa a da can inyai abu ma to akwai dalili, daga baya kuma da matsala ta faru gaba daya ma yadaina shiga rayuwar kowa inba tasa ba, kaga yanzu dayai abin nan kasan zuciyata dadi takeji dan na fara ganin Hassan dina na da na shirin dawowa.” Abba yai murmushi yace “na fahimta sannan nasan wanene Hassan, sannan ni koma menene ya faru ba wani abun dan ni dama ita na gani sannan ni ita na zaba, ko da a lokacin zasu nunamin wata ba lalai zuciyata ta amince da ita ba.” Ummy tai murmushi itama tace ” maybe suna tunanin sun cuceta ne da alama sunyi bincike akan Hassan……….” Karar wayar hannunta ne yasa ta kalleshi, kashe kiran tai sannan ta kalleshi, yace ” Sim dina na wayarki ne?” Tace “eh, da na cire sai kuma nai tunani kar san zuciyata yasa wasu dasuke nemanka ko na taimako ko na aiki suyi ta nemanka, shiyasa nasa Sim din a wayata.” Shiru yai tare da maida kansa gefe can yace “Kiyi hakuri.” Tace ” kadaina fadar haka, kaddara ce ta zo mana, sai dai mu roki Allah akan ya taimakemu yasa mu wuce kaddarar nan.”6 Abba yai shiru bai sake cewa komai ba…… ********* A can gidan Inna kuwa, Dady cikin takaici ya dawo gida, bakin cikinsa ko waya bai fita da itaba bare yasa a zo a daukeshi, rabansa da taxi haryamanta amma haka yahau ransa a bace.3 Yana isa gida ya wuce daki cikin zafin rai, Mumy dake kitchen tana bada umarnin abincin da za’ai ta taho da sauri ta shiga ciki. A tsaye ta ganshi tace “Abban Yasmeen lafiya?” Juyowa yai rai a bace yace ” kinsan yaran nan……” sai kuma yai kwafa. Ta matso da sauri tace “ya kukai? Yadauke Goggon Jalilan?” Yace “ya dauketa mana, yaran nan yana abu kamar shine gaba dani, kinga yanda yake wulakantani, amatsayina na uban matarsa?” Mumy tai shiru can tace “nikaina yaran nan yaban tsoro, wai garin yaya kukaba Jalila yaran nan? Bakusanshi ba? Na dauka kunyi bincike.” Cikin masifa yace “bincike? Abinda Inna ke bada umarni mu ina mukaga ta cewa?” Mumy tai tsaki tace “ai gashi nan ta ja mana masifa, ita kanta yanzu abun ya dameta, gashinan abinda take tunanin samu ma ba samu zatai ba, wanda take dashi ma yana neman wargajewa.”2 Dady yace “wai yaran nan ni zai kalla yacemin wai inada kudi a jikin? Sannan ya mikon wai 1000 wai na hau mota shi bazai kaini ba?”3 Mumy tace “mene?” Yai kwafa cikin takaici yace “ni nama rasa ma me zance, kamar ni????”6 Mumy ta rungumeshi tace “cool down Dadyn Yasmeen, zamu san mafita, bari Mu sanar ma Inna.” Yai tsaki cikin takaici, tace “Safeena ta kira, ta isa Paris lafiya.” Yace “Wai paris taje dama?” Tace “eh can Inna tasa a nemar mata skul.”4 Yai shiru baice komai ba…. Inna gaba daya tunda Hassan ya fita ta kasa tsaye t kasa zaune gaba daya ta kasa samo mafita, cikin takaici ta kira Sani tacimai mutunci akan kin yimata binciken daya kamata akan Hassan kawai yacemata bashida lafiya alhalin bai bincika wani irin ciwo na kwakwalwa yake ba…. 8 ************ Kuka Zaliha take sosai tana cema Yayarta ita wlh kome zata yi tayi amma itafa kawai ta aura mata Taura in ba haka ba wlh barin gidan zatai ta shiga duniya…9 Hankalin yayarta ya tashi tace ” kar ta damu dan dole zata koma Niger.”

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE