JALILA CHAPTER 11

JALILA CHAPTER 11

Inna tana zaune tananin mafita Mumy ta banko kofa da sauri, Inna ta kalleta tace “naga sanda hankali zai ratsaki ki daina buga kofa haka, yarki ta kai a mata aure amma haryanzu inkina wani abu kamar karamar yarinya.”+ Mumy ta zauna da sauri tace “ni Inna ki bar fadanki zuwa anjima yanzu akwai matsala.” Gaban Inna ne ya fadi ta kalleta tace “Abakar ya dawone?” “Ya dawo sai dai yaran ya dauke Goggo” Inna tai shiru hankalinta ya tashi, ta kalli Mumy tace “yanzu kenan da alama sunsan komai ko?” Mumy tace “me zai hana? Shiyasa Inna ni dama na kasa gane dalilinki na…….” Wani kallo data mata ne yasata yin shiru, Inna tace “kinsan menene yake bakantamin rai?” Bata jira amsartaba tace ” rashin wayau da auna tunaninki, daga ni har mahaifinki munada saurin tunani da kwakwalwa amma ke ni bansan ina kika dauko ba, da farko kince yaran ubanki zaki aura yaran da ko A bai sani ba lokacin, dole da ganin bamuda wani da bayan ke yasa muka jure, sannan kikasan wannan yaran ya munafirceki ashe har aure gareshi, amma tsabar rashin kwakwalwa kika dage ke sai shi, sannan abin bakin ciki duk yanda nai dake akan kiyi aiki a company din da muka gina nida mahaifinki amma kinki, kin dage sai dai mijinki yai, sannan yanzu kice me?”1 Mumy tai kasa dakai sannan tace “Inna wai dan Allah sai yaushe ne zaki amince da Abakar daro bisa dari? Mutumin nan na miki ladabi wanda ko ni bana miki, sannan ya a sona san da ba wanda yakemin irinshi…” Inna tai tsaki tace “ni tashi ki bani guri nasan mafitar data dace damu dan zamanki anan bakomai yake karamin ba sai bakin ciki.” Mumy ta mike tai waje rai a bace…. Inna tai shiru tana tunani kafin ta dau waya ta kira Abakar. Yana zaune a falo Mumy na gefensa itada Yasmeen, Sultan na daki yana ganin kiranta gabansa ya fadi ya kalli Mumy yace da alama Inna tagama shawara. Mumy tace “muje tare.” Yace “karki damu ki zauna bari naje.” Nan ya mike yai sama……… ********** Inna ta tashi tayi wanka, Ummy ta kawo mata kayanta tace ta saka, dan itakam ta kula kayan dake jikinta da wanda aka dauko a leda san ba magana, itada Jalila ne sukaje BQ dan ganin yanayin gun. Jalila ta kalli Ummy tace “Ummy kije ciki zan gyara.” Ummy tai murmushi tace “Jalila ko dai ince masu aiki gidannan sundinga kwana ne?” Jalila tace “saboda me?” Tace “da alama aikin gidan ya karu, sannan zai yi yawa, tunda akwai bangarensu ina tunani gwara mu tambayesu, in zasu dinga kwana to, in kuma bazasuyi ba kinga sai mu samo wasu.” Jalila tai shiru can tace ” Ummy gani, ga Lantana ina tunanin ba wani abu.” Ummy tai murmushi tace “baki fahimceni ba kenan.” Jalila ta mata kallo mai alamar tambaya tace “ban…..” Ummy tai dan dariya tace “so nake kibama Hassan kulawa 80% dan na kula ina hanaki kula dashi.” Jalila da sauri ta juya tana tattare kaya dan kunya, Ummy ta sake dariya tace “ko nayi sankai?”4 Jalila tace “a’a kawai ta cigaba da aikinta. Ummy ta kalleta tana murmushi, Lantana ta kira suka gyara gun, Ummy tace “gobe sai a siyo gado da kayan bukata a sa a ciki, wai gadan ciki ya tsufa, da Jalila zatai magana Ummy ta harareta wanda yasata yin shiru. Sageer kuwa a daki hankalinsa duk ya tashi tabbas Goggonta ganshi a lokacin dan har gaisheta yayi, to amma tagane tsakaninsu? Malam Sagir ashe da raban zan ganka. Kalaman Goggo ne suka dawo mai, ajiyar zuciya yai cikin tashin hankali yace ” ba zama bane ya dace dani.” Mikewa yai ta budo kofar dakinsa a hankali ha sako kai, yana leke.1 Bakowa a falon, komawa yai ciki ya zauna yana tunanin abinyi, can ya daure ya fito a hankali yai falo, Ummy na zaune rike da littafin addu’oi ya shigo. Ta kalleshi tace “Sageer fitowarka kenan, tun rana sai yamma?” Yace “Ummy ina matar Yaya?” Tace “Jalila? Tana BQ suna aiki, ta dage sai na taho, ya akai? Nemanta kake?” Yai murmushin dole sannan yace “eh, bari naje can.” Ummy tace “to, amma Sagir karka tambayeta maganar mahaifiyarta, da magrib in anyi sallah za’a zauna a falon Abbanka.” Yace “to Ummy sannan yai waje. Tana kwashe shara ya tsaya a bakin kofar yana kallanta. Kallansa tai sannan ta matso inda yake jiki a sanyaye. Kallan dakin yai, ya kalli Kofar Toilet inda Lantana ke wankewa. Yace “Jalila!” Yace “Uhmm” Shiru suka danyi dan they are uncomfortable in suna tare ba kamar da ba. Can ya daure yace “Goggonki, sanda mukaje asibiti…..” Sai a lokacin itama abin yazo mata, ta kalleshi da sauri tace “Ta ganka ko?” Yace “kin manta har gaisawa munyi?” Tai shiru tana kallansa, yace “Jalila, zaki iya mata magana? Dan banasan kowa yasan abinda ya faru a baya.” Jalila ta kalleshi tace “ince me? Ince Goggo yayan Uncle nake aure? Ko ince Goggo karki fadama kowa irin san da nakema Kanin mijina? Ko ince Goggo da naso Uncle ashe kanin mijinane?” Yace “Jalila ya kikesan juya maganar da na fada ne? Me yasa bakya yima kalamai na kyakyasar fahimta?” Idanunta ne suka ciciko tace “Uncle ni to ya zanyi? Me zance? Kamar yanda kake tsoron matsala ta afko a dalilinka, matsalar da zata sa hankalin iyayenka su tashi ni kaina a yanzu bana san ace nice silar wargaza farinciki Ummy da Abba, dakai kanka da yayanka, Uncle bansan…..” Kasa karasawa tai saboda kuka dake neman zuwa mata dan muryarta ta fara rawa. Sageer yai shiru yana kallanta cikin tausayawa yace “Nafahimceki Jalila, na kuma gode da kaunar da kikema Family na, Please ko Goggonta tambayeki kawai kice mata sunane yazo daya, mu barshi kawai a haka.” Ta daga kai, kawai dan batasan itakam me zata kuma cewa ba… Bayan sun gama aiki tai wanka a toilet din ta maida kayan jikinta ta hau sama. Yana kwance yana bacci ta shiga a hankali ta dau kaya ta saka, sannan ta matso kusa dashi ta sa hannunta akansa, jin ba zafi yasa tai murmushi. Da alama yau ma ciwon nasa da sauki, dan bacci yake hankalinsa a kwance.1 ********* Bayan magrib kuwa Ummy ta kalli Jalila bayan sun gama girki tace “Jalila inkin kaima Goggon ki ajiye sannan ki kaita falon Abba zamuyi magana.” Tace to, sannan ta dauki Abincin Goggo, tana shiga dakin ta zauna kusa da Goggo tare da kwanciya a kafadar ta tace “Goggona!” Goggo ta kalleta tace ” kin gama gudun?” Jalila tace “gudun me?” Goggo ta tureta daga kafadarta tace “kindauka bansan guduna kike ba? Kar na miki tambayoyi? Shiyasa tunda kika fita kikaki shigowa?” Jalila ta tuntsire da dariya tace “ni? Wlh ba haka bane aiki mukeyi ne bakiga Lantana ma batanan ba?” Goggo tace “ba wani.” Jalila fa kara kwanciya a kafadarta tace ” Ummy tace inkaiki falon Abba, anan zakiji komai.” Tace “kaini dan ni kaina so nake naji.” Nan suka fita tare, sai data kusa kaita falon, suna tafe tare sai ga Ummy tace ” Jalila barta zamu shiga tare.” Ta matso kusa da kunnenta tace “ki je ki lalabo mijinki.” Jalila ta kalleta, Ummy tai murmushi sannan ta nuna mata sama da kanta. Jalila ta kalli saman sannan ta nufi matatakalar, anya zai fito kuwa? Gashi bashida lafiya. Kofar dakin ta tura ta shiga, yana kan sallaya yana karatun kur’ani. Zama tai a bakin gado tana jiransa, bai dade ba yakai ayar karshe ta cikin suratul maryam, yana neman dauko wata surar ne dan izu daya yake yi a duk tsakanin sallar magrib da isha’i tai saurin cewa “Yaya!” Tsayawa yai bai fara wata surarba sannan bai juyo ya kalleta ba, tace “Yaya za’ayi maganar.” Ya juyo yace “magana?” Ta kalleshi tace “maganar nan…. ba Abba yace sai anjima ba?” Yace “and so?” Tace “shine za’ayi yanzu ka sauko.” Yace “in me?” Tace “ka sauko, muje tare.” Yace “kinsan me kike cewa? Nine zan sauko inje inda kowa zai zauna ayi magana?” Kallansa tai tai raurau da ido, yace “ki tashi kije, ni ba nayi nawa part din ba? Saurab ya rage naki.” Haryanzu kallansa take da idanun kafin tace “Yaya Please” Juyawa yai ya bude kur’ani zai dora daga inda ya tsaya. Da sauri ta sauko ta bayansa ta rike gefen rigarsa ta kafadarsa. Juyowa yai yace “wai……..” Bata jira me zaice ba tace ” yaya dan Allah ka taimaken, ba wai wani abu zakace ba, inka zauna agun ma ya isa.” Yace “in zauna?” Tsugunawa tai ta gefensa tace “Dan Allah yaya.” Hade rai yai ya juya, tace “kan ne?” Ya mata shiru, tace “yahkuri yaya, na sani ina takura maka, sannan ina takura maka da neman yin depending akanka akan komai na rayuwata, kayi hakuri nasan bana kyautawa.” Ta mike tai waje, a falo ta tsaya tai ajiyar zuciya sannan tace ” who do u think u are?”1 A hankali ta fara sauka daga matatakar, jiki a sanyaye. A falo kuwa Abba da Ummy na zaune daga bangare daya, Goggo na dayan bangaren Jalila ta shigo. Tana shigowa Sageer ya shigo, tunda ya shigo Goggo ke kallansa, inata san fuskar nan? Abba ne ya katseta da cewa “yaki saukowa?” Ta daga kai alamar eh. Jiki a sanyaye ta zauna a kasa kusa da Goggo. Sageer ya zauna a kasa kusa da Abba. Falon ya dan yi shiru kafin Abba yai gyaran murya yace “Sannu da zuwa mahaifiyar Jalila, muna baki hakuri akan abinda ya faru wanda mu kanmu bamusan takamaimai abinda ke faruwa ba, sai dai ina neman sanin dalilin dayasa ba wanda yasan da zamanki a gidan, sannan dalilin dayasa aka munafircemu mu dake akan auran nan, Jalila yar muce a yanzu shiyasa nake san sanin menene ke faruwa takamaimai.” Goggo tace “nagode da karamawa, sai dai a yanda nasan mutanen nan ba damuwa sukai damu ba ina mamakin yanda akai suka kawo Jalila cikin gidan karamci irin wannan.” Abba yai murmushi yace “mun gode da karamawa, Jalila inaso ki sanar damu abinda ke faruwa.” Jalila ta kalli Abba, ta kalli Ummy sannan ta kalli Sageer. Ummy tace “duk wani abunda kika sani muke sanji, wannan shikadai ne abinda zaisa musan abinda ya dace muyi, kada ki munafurcemu, kada ki munafirci mahaifiyarki.” Jalila ta kalli Goggo. Turo kofar da akai ne yasa suka kalli kofar, Hassan ne ya shigo. Kallan Jalila yai wacce itama kallansa takeyi, a hankali wani murmushi ya bayyana a fuskarta wanda yana ganin haka ya dauke kansa daga kallanta sannan ya nufi can gefe ya zauna akan kujera shi kadai. Goggonta kalleshi, wannan shine na dazu…… ******** Inna ce ta kalli Dady tace “take all the blame.” Kallanta yai cikin mamaki yace “ban gane ba?” Tace “kace kaine kai komai, dama matarka ce da yarka, kaga kome kai dama kaine me hakki akansu, wannan shikadaine hanyar dazamu kwaci company dinmu.” Dady yace “ni na kasa fahimta, kenan nine na shirya duk abinda ke faruwa?” Tace “eh ko dama nice na shirya? Ina naga matsayi? Matar data tsufa???? Dady yamata wani kallan tsantsan mamaki…….. Jalila tai ajiyar zuciya sannan ta kalli Goggo tace “sanda na sameki a bangaren su Dady akwance ba lafiya…………………….” Haka ta kwashe komai ta sanar dasu, gaba daya falon yayi tsiy saboda tsananin tausayin abinda kunnuwansu yakeji, Hassan na zaune ya kwantar da kansa a saman kujera, idanuwansa na lumshe kai kafe bai san me ake cewa a falon ba, sai dai gaba daya zuciyarsa a karye take da abinda kunnuwansa keji, wannan wace irin rayuwa yarinyar nan tai? Wani irin rashin imani ne hakan? Hannunsa ya matse guri guda cikin tsananin takaici.+ Jalila ta karashe maganar tana kuka tace Goggo banasan wani abu ya sameki shiyasa na kasa fadamiki, sannan suma sunce min karna sanar dake….. Goggo tana kallanta idanuwanta na zubar da kwalla ta jawota jikinta ta rungume Jalila ta saki wani kuka mai ban tausayi, Goggo tana hawaye tana shafa bayanta tana cewa “kiyi hakuri Jalila duk nice na ja miki abinda suka miki.” Ummy ma gaba daya hankalinta ya tashi, tausayin su ya kamata. Sageer kam ba’a magana dan baima san hawaye yana gangaromai ba, sai dayaji ruwa a kuncinsa, ya goge da sauri yana kallanta. Ummy ta kalli Abba wanda yai shiru yana nazarin abinda ke faruwa, kenan bayan yaga Jalila yace yanaso su bawa dansa a matsayin matar Hassan shine sukai bincike akan Hassan, da sukaji bashida lafiya shine suka hadashi da ita, to ina asalin yar tasu? Dan ya fahimci akwai wata. Kallan Jalila yai yace “ya isa haka Jalila, su ne suke tunanin sun cutar dake suna ganin sun yaudare mu, amma ni da matata basu yaidaremu ba ko kadan dan ni dama ke nagani sannan ke kika kwantamin a rai, haka itama ke ta gani sannan ke kika kwanta mata a rai, anci mutuncin mahaifiyarki a matsayinta na wacce ta haifeki ta shayar dake sannan ta reni bai kamata ko menene ba a aura da ‘ya bada sanin mahaifiyarta ba.”2 Ummy cikin zafin rai tace “ai muma sun ci mutuncinmu taya zasu nuna mana sune suka haifeta bayan mahaifiyarta daban, tayana dan rashin imani zasu aurar da yarinya mahaifiyarta na kwance ba lafiya? Sannan suyi amfani da rashin lafiyarta gun sata tayi abinda sukeso?” Goggo ta share hawayenta tace ” duk nice suka raina, nice suka maida abin zuba shara, nice basa ganin mutunci, nagode sosai da kaunar da kuka nuna ma yarinyar nan, ko ba’a fada ba na san akwai kulawa mai karfi datake samu a gidannan fiye da gidan da za’a kirashi da sunan gidan mahaifinta.” Abba yai ajiyar zuciya yace “yanzu tunda nasan meke faruwa bazan barsu haka ba.” Ummy ta kalleshi da sauri tace “me zakayi?” Ya mike cikin takaici yace “don’t u understand what’s happening? Sun daukemu a matsayin joke ne, kenan sun maidamu fools, duk abinda suka tsara shi muke bi.” Ummy ta kalli Hassan wanda kamar ma baisan abinda ake a falon ba, sannan ta kalli Abba tace ” ni kuma ina ganin ka kyalesu kawai.” Abba yace ” In mun kyalesu kina tunanin zasuyi dana sani?” Goggo ta kallesu tace “amma dan Allah inada tambaya, me ka musu ne da harsuke tunanin ko za’a mutu sai sun kawo Jalila cikin gidan nan?” Sageer ya kalli Abba yace “Abba ni kaina ina wannan tunanin.” Abba ya kalli Ummy yace ” kasuwanci…….” Ummy tamai alama dayai shiru, yace ” yanzu ke Jalila kiyi hakuri, nasan an shiga hakkinki, sannan an shiga hakkin mahaifiyar data haifeki, kuyi hakuri wannan harda laifin mu.” Goggo da sauri tace “ba laifinku bane, masu laifin daban, zan iya yafe duk wani abu da za’amin ko na wulakanci ko na tozarci amma bazan yafemusu ba akan abinda sukama Jalila, tayaya zasuyi amfani dani wajen ganin sun sata abinda sukeso? Yanzu da ace mugun hannu ta fada fa???? Ta fada cikin raunaniyar murya. Hassan ya bude idanunsa ya kalli Jalila wacce ke kuka tana zaune kusa da Goggonta. A hankali ya mike kawai yabi ta bayan kujera yai hanyar waje. Jalila ta kalleshi, shima kallanta yai sannan ya dauke idanunsa da sauri. Ummy ta mike tace “Hassan ya akai?” Yace “bakomai….” Kawai yai kofa, kallan Abba tai cikin wani yanayi, hannunta ya yadan dafa alamar ba komai. Sannan ya kalli Goggo wacce gaba daya ita da Jalila tausayi suke bashi, yace “Sageer kai dasu Jalila ku shiga ciki, ni zanyi magana da mahaifiyar Jalila.” Sageer ya mike ya fita, Jalila ta mike ta fito. Abba ya kalli Goggo yace ” garin yaya kika bari aka maidake kamar baiwa? Ko bakida yan uwa ne?” Tace “inadasu sai dai a matsayin babu suke.” Ummy tace “kamar ya?” Tace “bayan anmin auren dole da Abakar aka umarceni da karna kara tako garin sai dashi tin daga lokacin ban sake zuwa ba, dan banida darajar da zai kaini.” Ummy tace “kamar ya? Baki sake neman mahaifiyarki da yan uwanki ba?” Tace “ina zan nemisu bayan umarni mahaifina ya bani…..” Abba yace “wani umarni ne hakan?”2 Ummy tai saurin cewa “Auranki fa?” Dan ta fahimci rashin ilimin addini ne ya sa ta dauka biyayya takeyi. Goggo tace “ban sani ba nima dan rabona dashi tun ranar da aka kaini, lokacin Allah yai dabon Jalila.”4 A tare sukace “me?” Goggo tai kasa dakai tana murmushin takaici. Ummy tace “Goggo muje kici abinci ki kwanta.” Abba ya kalleta cikin mamaki dan akwai tambayoyin da yake san jin amsarsu.1 ******** Jalila na fitowa ta nufi hanyar sama, Sageer da sauri yace “Jalila!” Tsayawa tai bata juyo ba tana share kwallarta, Sageer ya matso ya mika mata handkerchief kallansa tai kamar zata karba sai kuma naga ta fasa, kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa tace “nagode.” Kawai tace ta juya ta hau saman. Tsayawa yai yana kallanta cikin tsananin tausayi, har saida tai kwana sannan ya juya zuwa dakinsa, yana shiga ya zauna a bakin gado yana tunani, haka rayuwarta take? Shiyasa ashe ake barinta a makaranta ita kadai? Shiyasa sukasata a government? ******* Ummy ta taso tazo kusa da ita, suka fita tare, ina saurayin Jalila? Ta tabbatar Jalila………. tunowa datai a inda tasan Sageer ne yasa ta kalli Ummy da sauri tace “ya sunan mijin Jalila?” Ummy tace “Hassan!” Goggo tace “wanda na gani dazu fa?” Ummy tace “Sageer? Kaninsa ne.” Goggo tace “kaninsa?” Ummy ta daga kai alamar eh, Goggo a ranta tace “to ko ba shi bane?” Dakin Ameera ta kaita sannan tace “kici abinci ki kwanta, dan Allah karkiyi tunanin komai, Jalila yanzu ‘yatace bazan kara bari wani abu ya sameta ba, sannan mu zamu san abinyi, ke dai ki kwantar da hankalinki ko dan lalurarki.” Goggo ta riko hannun Ummy tace “Nagode, nagode har bansan iya godiyar daya kamata nai miki ba.” Ummy tai murmushi tace “muma mungode, da kika fahimcemu, yanzu sai kisama auransu albarka.” Tace “insha Allah.” Nan ta shiga ciki….. Ummy ta bita da kallan tausayi. Jalila kam kamar zata shiga ciki sai kuma ta fasa, zama tai a falo kawai tana kuka ko kwanwutar bata kunna ba. Shima zama yai a kasa ya kwanatar da kansa akan kujerar dakin, wace irin rayuwa yarinyar nan tai? Amma duk da haka akwai laifinsa a ciki, ya tabbatar dabadan shi ba da baza’a mata auran dole haka ba, wadan nan tunani sune suke tayimai zirya a ransa, tarinta yaji hakan yasa ya kalli kofar falon. Mikewa naga yayi ya jingina kansa da jikin kofar, sheshekar kukanta yaji wanda yasashi rufe ido cikin tausayawa. Jin kukan yake har zuciyarsa, a hankali ya bude kofar.2 Dayake makunin fitilar falon a kusa da kofar take kawai sai ya kunna ta. Haske ne ya baibaye falon, da sauri ta dago. Jingina kansa yai da jikin kkatangar falon yana kallanta tare da sa hannunsa na hagu cikin aljihunsa. Kallansa itama takeyi, sun dade a haka kafin ta sauke idanunta kasa. Yace ” yau ma hobby din naki ya motsa ne?”5 Ta kalleshi da idanunta da suka sha kuka, yace “a rana kuka nawa kikeyi?”1 Baki tadan motsa tanasan magana, yace ” in zakiyi kuka kiyi a gurin daba kowa, dan ni ba hobby dina bane sauraransa.” Ya juya bai rufe kofar ba ya zauna akan kujera, me yasa yace haka? Shi dayaje dan ya lalasheta? Mikewa yai yai sallar Isha’i, ganin batada niyyar shigowa yasa yaki mikewa daga kan sallayar, yana jiranta. Kofar yake lekawa, yaga ba alama. Pillow ya janyo yasa kansa akai yana kallan kofar. Abincin su ya kalla, bataci abinci ba, shiru yai yana tunanin shigowarta. Yana nan a kwance har karfe 10, baisan sanda bacci yai gaba dashi ba. Jalila kam bayan ya juya kawai ta kwanta akan kujerar tana yan mitoci, kasan baka damu da hawayena ba me yasa dazu kazo? Nikam Yaya me yasa baya magana mai sanyi? Tadan turo baki ta kwanta tana tunanin rayuwarsu. Batasan bacci ya dauketa ba, sai karfe 11 ta farka, batai isha’i ba ya akai bacci ya dauketa? Da sauri ta sauko daga kan kujera ta nufi dakin, a kwance ta ganshi a kasa, batai mamaki ba dan taga yanayi, kawai ta wuce toilet. Tai alwala tazo tai sallah, jitai cikinta na karar yunwa, ta zo ta bude abinci zataci, gani tai ba alamar taba abincin, baici abincin dare ba kenan?3 Kadan ta zuba a plate ta faraci. Lomarta uku taji kakarinsa, wani sankamewa yakeyi, da sauri ta ajiye abincin ta matso inda yake. Gaba daya ya sai juye juye yake, yana girgiza kai alamar a’a, ga zufa tanata keto mai. Hannunsa ta riko tana tabashi, Yayah! Yayah! Gaba daya ba alamun yanajinta, kansa ta kwantar a kan cinyarya dan murkususun dayake yasa kansa ya sauka daga kan pillow din, tasa hannu ta rike kansa dayan hannun kuma tasa a saman kirjinsa tana dan tabashi tare da kiran sunansa. Can kuma sai tadanyi kulhuwalahu da falaq da Nasi sai tadan tofa mai. A hankali taji ya daina motsumutson. Idanunta na kansa ya ciciko saboda da tausayinsa, wannan wani irin abu ne ke damunshi? Me ya sameshi abaya? A hankali ya bude idanunsa, daidai lokacin kwalarta ta zubo ta zubu saiti idanunsa, wanda yana rufe ido ta zubo a bayan idansa. Idanunsa ya sake budewa ya kalleta, dayan hannun data rike kansa dashi ta saki ta share hawayenta sannan ta kalleshi tace “Yayah!” Idanunsa ya lumshe yana kallanta kamar yanda take kallansa cikin sansanyiyar murya mai kamma da rada yace “sai yaushe ne zaki daina saurin kuka?” Tace ” kukan ne bakaso nayi?” Itama a hankali tai maganar tana kallansa. Mamaki ne ya kamata dataga ya daga kai alamar eh, tace “meyasa?” Ya dan girgiza kai kadan yace “ban sani ba nima, sai dai I don’t like it.” Kallansa tai tare da neman zare hannunta daga kan kirjinsa. Hannu yasa ya tsayar da hannu yana kallanta yace ” yanzu kukan me kikeyi?” Tace “meyasa kakesan sani?” Yace “Hmm kawai, saboda sai naji ne zansan abinda ya dace nai.” Hannunta ta nemi janyewa tana cewa “me ya faru dakai? Duk sanda kake abin nan kamar wani abu kake tunani.” Shiru yai bai bata amsa ba, kafin can yace ” izinki nawa?” Tace “mene?” Yace “tambayarki nai, so nake nasan karatunki, na kula kamar bakiyi nisa ba.” Tadan sosa wuyanta da dayan hannun tace “bankai izu ko daya ba, a gida Goggo tadan koyamin na sallah.” Idanu ya kura mata, wanda yasatai saurin juya kai yace “bakyajin zafin mahaifinki?” Tai shiru kafin tace “inaji, inaji sosai da har wani sa’in ganinsa ma banaso.” Yace “kenan ko me ya faru bazakiji haushi ba?” Tace “me zakamai?” Mikewa yai daga kan cinyarta sannan ya saki hannunta yahau kan gado…. Da sauri ta taso tace “me zakayi?” Yace “bakomai, fada kawai nai.” Jalila ta kalleshi alamar rashin gamsuwa……… ******** Dady kuwa yana saukowa daga gun Inna ya shiga daki kawai ya hau hada kayansa, Mumy ta shigo da sauri zatai magana taga yana hada kaya, a rikice ta rike hannunsa tace “Dear menene?” Ture ta yai yace ” menene? Da alama karshen zamana dake yazo.” Da sauri ta rungumeshi tace “menene? Kafi kowa sanin bazan iya rabuwa dakai ba, Inna ce? Itace?” Yai shiru wai shi a dole ransa ya baci. Da sauri ta fito ta nufi dakin Inna da gudu rai a bace……… Da karfi ta banko kofar dakin Inna, lokacin Inna na zaune tasa hannu tayi tagumi tana tunanin abinyi, yanda Mumy ta banko kofar ne yasa ta zabura ta kalleta tace “Lafiya?” Mumy cikin bacin rai ta zauna a gaban Inna tace “Inna so kike kiyi ajalina?” “Ajalinki kamar ya kenan?” Tace “in ba so kike in mutu ba taya zaki nemi halakamin aure? Sanin kanki ne yanzu kinsan bazan iya rayuwar ba Abubakar ba, a da ma da ‘ya’ya basu hadamu ba na kasa rabuwa dashi bare yanzu.” Inna ta katseta cikin fada tace “me ya fadamiki?” Tace “ba damuwa ta bace da duk abinda kike tunani sai dai kiyi abinki ke kadai, dan wallahi bazan bari wani abu ya sameshi ba, in kuma so kike mu bar miki gidan to…..”6 Mamaki ya kama Inna ta kalleta cikin wani yanayi tace “Fatima ni kike fadama haka? Ni wacce ma sadaukar da komai dan ganin farincikin ki?” Cikin masifa tace “kika sadaukar dame? Me kika sadaukar? Duk abinda kikeyi ba saboda kanki kikeyi ba? In har saboda nine ai da kin daraja Abakar kin bashi company din kamar………” Marin data kifa mata ne yasa Mumy yin shiru, ta kalleta tare da rike kuncinta. Inna ta kalli Hannunta dake rawa, dan ita kanta batasan ta mareta ba, cikin dana sani tace “Fatima……” Mumy ta mike tsaye tana kallanta, hawaye sun cika mata ido tace ” in har bakyasan in bar gidan nan ki ajiye duk abinda kike shirin yi.” Ta juya tanaji tana kiranta bata amsa ba tai waje.1 Inna ta bita da kallo jiki a sanyaye….. Shikam Dady tana fita yai wata dariyar mugunta yace “Inna i am sry sai dai kin riga kin makaro akaina ‘yarki da kikafiso a duniya zata iya juya miki baya.” Yanajin alamun bude kofar ya shiga kokarin zuge jaka, Mumy na shigowa ta sa hannu da karfi ta fincike jakar sannan ta rungumeshi tace “Dadyn Yasmeen me yasa baka tunani na in zaka aikata abu?” Yace “tunanin naki ne yasani yanke wannan hukuncin, taya zan zubarma kaina mutunci? Bayan nasan ina zubar da mutunci na naki na zubar? Da ace kome zai faru zai tsaya akaina ni kadai bazai shafeki ko yaranmu ba wlh ba abinda bazan iya ba, amma ta yaya zan yarda in zubar da mutuncinki dana ‘ya’yanmu.”4 Dagowa tai tana kallansa tace “to kamin alkawari ko me zai faru bazaka sake tunanin rabuwa dani ba.” Yace “na miki, yanzun ma ba’a san raina nake shirin tafiya ba.” Ta kara kankameshi tace “barni da Inna bazan kara bari ta wulakantamin kai ba” Ya shafa kanta yana wani murmushin mugunta yace ” taya zan yarda na zama sillan fada tsakaninki da mahaifiyarki?”3 Tace ” ba kaine silla ba dan dama na gaji da yanda take ma kamar wani bawanta.” Nan ya sumbaceta a kunci yace “i luv u Zarah.” Ta sakarmai murmushin so…… Nace ansha kauna😏4 Inna kuwa Mumy na fita ta ture littatafan dake kan tabir din gabanta cikin takaici tace “Abakar how dare you!” Kwafa tai tace ” kana tunanin ka samu abinda kakeso? Inji wa?” Ta sakeyin wata kwafa…….. ******** Zama tai a kusa dashi a kan gado yana kwance yana tunanin Zaliha, ji yake zuciyarsa kamar zata fashe da rashinta. Ganin baimasan ta zo bane yasa tasa hannu ta tabashi. Kallanta yai sannan ya kakaro murmushi yace “Yaushe kika shigo?” Tace “me kake tunani?” Kallanta yai jiki a sanyaye, murmushi tamai sannan ta kauda kai, a hankali yace “I am sry, i am really sry.” Kallansa ta sakeyi tace “me kake tunani game da mutanen nan?” Ya mike ya zauna yace “amsar kudinmu zamuyi, inyaso company din nasu ya nukushe.” Tace “ayi haka kuwa?” Yace ” baki kula da rainin hankalin da suka mana ba? Sannan yarinyar nan da mahaifiyarta, gaba daya ba tausayi a harkarsu, Hajiya taban mamaki duk da nasan macece wace kanta yake a waye amma i didn’t expect that from her.” Tace “na sani sai dai in muka duba abin ta wata fuska zamuga mu taimakonmu sukai, da farko dabadan sun yaudaremu ba da bamu san wacce zamu aurana Hassan ba, in muka duba saukin da muka dade muna nema akansa yanzu gashi abinda likitoci da dama suka kasa yi yarinyarnan a ciki wata daya ta mana, duk da bawai ya warke ne ba sai dai canjin daya samu nada yawa.”2 Abba yai shiru yana kallanta zuciyarshi na dana sanin abinda ya aikata mata, yace “yanzu me kike tunani?” Tace “just live them.” Yace “kina nufin duk abinda sukai ya tashi a banza?” Tace “ko daya sai dai ina tunanin mu barma Allah, yanda suka cutar da Jalila da mahaifiyarta Allah bazai barsu ba, mu murikesu, gatan da basu samu ba mu basu, mu jira hukunci Allah akan su.”5 Abba yai shiru sai kallanta kawai da yakeyi, tace “kallan fa? Shawarar batai ba?” Yace “akoda yaushe in kina abu sai na dinga yin wani tunani, sau dayawa akance mata basukai maza zurfin tunani ba, sannan sai kaji namiji na ta aibata mace, in naji haka a koda yaushe sai insan Allah yamin baiwar da ba ko wani namiji yama ba, samunki a matsayin matata yana daya daga cikin abubuwan da nake alfahari dasu a rayuwata.”1 Kallansa tai sannan tai murmushi tace ” Kasan abinda yaban mamaki? Ban taba tunanin Hassan zai sauko kasa ba wlh, kasan kawai nama Jalila zancen ne amma a raina nasan bamai yiwuwa bane?” Abba ya kalli yanda taketa farinciki yace “ni kaina nayi mamaki, kinsan rabon da Hassan ya shigo falona kuwa harya zauna ya dade haka?” Tace ” kasan ya sauko ya gaida baban Jalila ran nan?” Abba yai murmushi yace “da alama yanda nai dace da mata haka Hassan yai dace, sai muyi addu’a Allah yaba Sageer mace shima ta gari.” Tace “insha Allah.” Washegari. Dakin Sageer ta nufa tasa hannu tai knocking. Yana kwance akan gado ya taso ya bude mata. Kallansa tai cikin kulawa tace “Sageer lafiya? Naga baka fito ba.” Ya kalleta yace “Ummy….” A rikice ta kalleshi tace “menene? Bakajin dadi ne?” Yace “a’a kawai dai…” Tace “na kula ma gaba daya yanzu kadan canza, Sageer menene ke faruwa?” Yace “kai Ummy wacce canzawa?” Tura kofar tai ta shiga dakin, binta yai ciki da sauri yana cewa “Ummy.” Hannu tasa ta zuge labulen dakin ta zauna akan kujera. Ya matso yana cewa “Ummy!!!” Cikin shagwaba ya kirata, ta harareshi tare da hard’e hannayenta tace ” In baka fadaminba ba inda zani.”7 Dariya ya saka sannan ya zauna a kasa kusa da ita yace “shikenan sai muyi hira.” Tace “Sageer dan Allah meke damunka? Sai yanzu na fahimta sam da yake banda nutsuwa ban kula da canzawar dakai ba.” Yace “Ummy wlh ba komai, muje na tayaki aikin kitchen kafin sirikarki ta sauko.” Kallansa tai sannan tai murmushi ta mike ta fito, yabiyo ta. Dakin Ameera ta kalla tace “bari in nakai musu breakfast sai mu gaisa.” Shima dakin ya kalla sannan ya matso yace “Ummy me kukai da Abba akan su?” Tace “Goggonta zata zauna anan kamar yanda Hassan yace, su kuma su suka sani.” Sageer yai murmushi zaiyi magana ya hangota a kitchen. Tsayawa yai yana kallanta, Jalila ta juyo jin motsin mutane, kallan Ummy tai sannan ta matso fuskarta dauke da fara’a tace “Ummy ina kwana?” Ummu ta kalleta cikin jin dadi tace “Jalila kin tashi lafiya?” Tace “lafiya kalau Ummy.” Sannan tadan kalli Sageer a hankali tace “Ina kwana?” Sageer yace “kin tashi lafiya?ya yaya?” Lafiya kawai tace. Ummy tace “Jalila naji dadin ganinki haka kamar ba abinda ya faru.” Jalila tai kasa dakai tana murmushi, a zahiri itakam ganin Goggonta yasa takejin kamar duk wani abu daga baya kenan, sannan ta rasa me yasa takejinta haka. Sageer ya zauna a falo su kuma suka nufi kitchen, suna aiki suna yar hira, Ummy tace “Hassan abin nashi na tashi sosai yanzu?” Jalila tace “ba sosai ba sai yai kwana biyu zuwa uku lafiya.” Ummy tai murmushin jin dadi ta kalli kular data suko dashi ta bude, kallan Jalila tai tace “jiya bakuci abinci bane?” Tace “yayane baici ba, inaji bacci ne ya daukeshi.” Ummy tace “ba matsala tunda ya fara bude zuciyarsa nasan komai zai daidaita a hankali.” Jalila ta kalleta cikin rashin fahimta tace “bude zuciya?” Ummy ta dauko kukar tana cewa ” eh mana akanki ba.” Jalila tace “ni?” Ta fada cikin mamaki da alamar tambaya, Ummy bata tanka mata ba ta cigaba da aiki. Jalila tai shiru tana nazarin abinda Ummy ke nufi, ba dai so take tace wai Hassan ya fara santa ba? Tab shi wannan har akwai zuciyar soyayya ma a ransa?lalai Ummy. Haka suka gama ta kaima Goggo ya zauna suka gaisa da dan hira, Ummy na shigowa ta mike ta dawo kitchen ta dau nasu. Sageer na zaune kan dinning shi kadai yana cin abinci, waya yakeyi da alama da Ameera yake waya dan yana cewa “In bazata biyoki ba sai ki dawo kindai san ran monday zaku koma makaranta.” Jalila ta wuce ta hau sama, a hankali tasa hannu tadan murda kofar, tadan fara kokarin budewa a hankali. Jitai an jawo kofar da karfi har ya hado da ita data rike kofar, ta taho ciki da dan gudu ga tire a hannunta. Da sauri ya rike tiren yana kallanta. Daidaita tsayuwarta tai sannan tace “yaya irin wannan fizgar kofar fa?” Yace “ke kuma irin wannan bude kofar fa? Kamar wata munafuka? Ko laifi kikai?”yai maganar da alamar tuhuma. Da sauri ta ajiye abin hannunta tace “laifin me? Ni wlh ba laifin danai.” Baisan yanzu ma bakinsa yadan motsa ba yace ” kin tabbatar?” Ya fada tare da matsowa. Da sauri tai baya tana cewa “ni wlh banyi komai ba, kawai dan na murdo kofa a hankali.” Yadan kalli idanunta yace “why do i have this kind of feeling?” Tace “ikon Allah, dama dai fada kakesan yi, daga shigowata?” Ya zauna akan gado yana cewa ” ramawa nai.” Tace “me nai da zaka rama?” Bai tanka taba ya dau littafinsa tare da gyara zama, ido ta kuramai a ranta tace “so? Hahh lalai Ummy wannan mutumin nan?” Bai kalleta ba yace “kallan fa?” Ta dauke idanta da sauri tace “sauko kaci abinci.” Yace “banaci.” Tace “bakaci jiya da daddare fa?” Yace “shiyasa ai bazanci yanzun ba.” Tace “ban gane ba???” Ya shareta. Ta matso tana neman amsar littafinta, wani kallo ya mata yace “littafin kike san amsa ko rikeni kike sanyi?”1 Da sauri ta matsa baya tace “rike ka kamar ya?” Yace “kamar yanda kika saba.” Mamaki ne ya kamata tace “kaima ai kana rike ni.” Wai meke damun mutan nan? Jiya da daddare kamar bashi ba. Kallanta yai kamar bazai yi magana ba sai jitai yace “inma na rikeki ai ke matatace.”3 Mamaki me ya kamata ta saki baki tana kallan ikon Allah, shikuwa kamar baiyi maganar ba ya cigaba da karatunsa. Tace “dan Allah ka sauko kaci abinci.” Yace “Allah bazan ci ba.” Tace “bangane hakan ba.” Mikewa ma taga yayi ya ajiye littafib ya nufi toilet, mamaki ne ya kamata ta bishi da kallo. Haryaje zai shiga toilet sai taji yace “inkin gama ki shirya muje a siyoma Goggo kayan dakinta da abin bukata.” Ya shiga ciki yana cewa jiya dana jira kizo muci ai shareni kikai kema kiji ko da dadi……14 Duk da taji dadin abinda yace sai dai wulakancin daya mata yasa tama rasa abinyi. Da kyar tasha ruwan tea, duk kuwa da tanajin yunwa amma takaici ya hanata, wai Allah bazanci ba, kalmar nan ta bata haushi. Tana nan a zaune ya fito daga wanka daure da towel, da sauri ta juya baya. Ko kallan inda take baiyi ba ya fara shiryawa. Yana gamawa ya dau key yace “ina jiranki a mota.”yai waje. Da kallo ta bishi tai tunanin jiya bayan ya warke, kamar ba shiba yana mata magana a hankali, to yanzu me ya sameshi kuma? Ramawa? Me tamai? Haka ta mike tai wanka duk ranta ba dadi, ta fito tana kokarin sa bra a saman towel din jikinta ya turo kofar. Idanunsa ne ya sauka a kanta, zaro ido tai tana kallansa, da sauri tasa hannu ta rufe kirjinta. Ganinsa tai ha fara matsowa inda take, idanu ta runtse tana tsoron abinda zai biyo baya, sai dayazo daf da ita har tana jiyo numfashinsa yasa hannu cikin wardrobe ya dauko abu, kallanta yai yace “Wallet.” Ya fada tare da nuna mata wallet din, ya juya ya futa.4 Wani nanauyan numfashi ta saki…….. Hassan na saukowa kasa ya nufi hanyar fita da sauri “Hassan!” Juyowa yai da sauri kamar mara gaskiya ya kalleta. Karasowa yai inda take sannan ya gaisheta, fuskarta dauke da murmushi tace “fita zakai?” Yace “eh ni da….” sai kuma yai shiru, murmushi ta sakeyi tace “ya zaka fita baka gaida sirikarka ba?” Yace “sirika?” Nunamai dakin Ameera tai da hannu, Hassan ya kalleta alamar rashin fahimta, tace “badai bazaka ba?”2 Kallan dakin ya kuma yi sannan taga ya nufi dakin, da kallo ta bishi cikin jin dadi. Hassan ya kwankwasa kofar dakin, daga ciki Lantana ta mike ta bude. Tsayawa yai yana tunanin me ma zaice inya shiga? Goggo dake zaune a kasan carpet tana ganin shine ta mike tace “Hassan? Shigo mana.” Shigowa yai ya zauna daga gefe yace “Ina kwana?” Kansa na kasa. Goggo tace “ka tashi lafiya? Ya dawainiya da mu?” Hassan yai shiru dan bai san me zaice ba, Goggo tadanyi shiru haryana shirin mikewa. Tace “Hassan.” Komawa yai ya zauna tare da kallanta, Goggo tace “in ba damuwa magana nakeso muyi.” Yace ” ba komai, menene?” Tadanyi shiru kafin tace “da farko dai nasan kafi karfin Jalila, saboda ita ba gata gareta ba, ba kudi gareta ba sannan ba ‘yan uwa dake santa take dashi ba, yarinyar tasha wahala agidan mahaifinta wanda har bata iya cewa ko kawo kawarta da sunan gidansu, tunda nake da ita bata taba kawo kawa ba, bata taba zuwa gidan kawa ba, nasan bawai dan batada shi bane sai dan tana gudun wulakancin dazai biyo baya, dan Allah Hassan ga amanar yarinya ta nan, ka taimakeni kamar yanda Allah ya taimakeka ya baka iyaye na gari ya baka duk wani abu da ya dace ka kularminn da ita, ba marainiya bace sai dai tafi wasu marayun rashin gata, dan garasu a kalla sun san mahaifinsu ba rai gareshi ba akanta, wacce tana ganinsa sai dai yafi karfinta.”1 Tai shiru kafin ta daura da cewa “nagode sosai da kaunar da kuka nuna mata, da kuma kaunar da kuka nunamin sai dai kuyi hakuri bazan iya zama a gidan ‘yata ba.”7 Cikin mamaki Hassan ya kalleta yace “meyasa?” Tace ” taya zan iya zama a gidan ku? Bayan kudin sirikainane? Wani irin zama zamuyi?” Hassan yace “wlh bakomai.” Tace “nafi kowa sanin ba komai, dan kaunar da kuka nunamin a kwana dayan nan yasa na fahimci hakan, sai dai kuyi hakuri bazan iya zama a gida daya da sirikaina da yata ba, abinda yasa ban fadama kowa ba sai kai bakomai bane sai dan kaidin kaine ka kawoni gidan sannan inaso inbaka girmanka na mijin ‘yata tilo.”1 Hassan yai shiru dan baisan me zai kuma cewa ba Goggo tai murmushi tace ” ka sanar dasu ra’ayina, zan koma inda na fito.” Yace “ina kenan?Goggo?” Tace “karka damu kauye nake nufi bawai gidan Babanta ba.” Hassan yai shiru yana nazari, jiyai tace “jeka dama abinda zan fadama kenan kar na tsayar dakai, zuwa anjima ko gobe zan tafi in Allah ya kaimu.” Hassan yai shiru kafin ya mike ya fito, mota ya shiga yana nazarin kalamanta, bazai takura akan ta zauna ba dan hakan ita kuma zai iya zama takura ne a gareta sai dai ya kula ganin mahaifiyarta shine zaifi sata farinciki…….. Kofar da aka bude ne yasa ya kalli kofar, shigowa tai ta zauna. Yauce rana ta farko data taba saka doguwar rigar abaya, shima a cikin kayan lefenta yake ta dade tanasan ta saka amma kunya ta hanata, yau ma daurewa tai ta saka, dankwali baki ta daura a ciki ta yafa dankwalin abayar. Tana shigowa idanunsa suka kalli kirjinta, da sauri ya dauke ido daga kanta, meye hakan? Abinda zuciyarsa ta tambayeshi kenan. Tada mota yai baice komai ba, itama tai shiru ranta a bace wai ita a dole ya bata mata rai, bazanci ba, kalmar nan ta bata haushi. Ina zaije? Bayan Goggon tace bazata zauna ba? Sai dai ya rasa meyasa ya kasa fada mata, da alama san fitar yakeyi da ita.+ Bayan sun hau titi ne yadan gangara bakin wani shago yai parking. Fita yai bai dade ba ya dawo, yana shiga ya bude leda ya dauko robar yoghurt ya mika mata bayan yaja motar. Jalila ta kalleshi tace “nima banasha.” Yace “ce miki nai naki ne?”2 Tace “nawaye to?” Yace “budemin zakiyi yunwa nakeji.”7 Wani kallo tamai tace “yunwa?” Yace “bazaki budemin ba?” Ta kara hade fuska ta fizgi robar yoghurt din da karfi daga hannunsa ta budemai sannan ta mikamai. Amsa yai sannan ya kurba. Takaici yasa tace “yunwa kakeji amma kaki cin abinci?” Yace “dama dan mutun najin yunwa sai ya zama dole sai yaci abinci?” Tace “ba dole tunda cikin mutum ne.” Yai shiru tare da cigaba da tukinsa, meyasa nace haka? Ahh meke damuna? Abinda zuciyarsa ke fadamai kenan. Jalila kuwa ta kara kumbura, kallanta yadanyi kadan sannan ya mika mata yoghurt din, tace “me zanyi kuma?” Yace “sha?” Tace “nace banasha.” Yace “ke da kikejin yunwa meyasa bakici abincin ba?” Ta kalleshi sannan tace “Yaya wai dan Allah me yasa kakemin haka?” Yace “me?” Tace “yau sai ka min magana cikin sanyi, anjima sai kamin cikin zafi, wata anjimar kuma amsa ma ban isa samuba.” Yace “haka kike gani?” Cikin wata irin murya da ita kanta bata sani ba tace “hakan ne mana.” Da sauri yai gefen titi dan jiyai wani abu ya tsirgamai, kallanta yai sannan ya kalli kirjinta, da sauri yamaida kansa titi ya hade rai, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, fizgar motar yai da karfi. Haushi ne ya kara kamata, ta juya tana kallan titi. Can dai ta daure tace ” ina zamu siyo kayan?” Yai shiru kafin yace ” me kike tunani akan nemawa Goggo wani gidan? Ko a cikin gidajen Abba ne dan yanada na haya.” Jalila tace “Goggo tace wani abun ne?” Yai shiru, ta dan yi ajiyar zuciya tace ” dama tunda naje gaisheta da safe naji tana cewa ina ita ina zama gida daya da sirikai? To ni ban gane me take nufiba, dana tambayeta kuma sai tace bakomai.” Hassan ya kalleta yace “me kike tunani?” Ta kalleshi tace “Yaya nikam tsoro nake, kar Goggo ta zauna inda mutanen nan zasu sani, dan wlh Inna bazata barni ba tunda na bata mata plan.” Hassan ya kalleta yace ” karki damu dasu, ba abinda zasu iya.” Jalila tace “Yaya bakasan Inna bako?” Yace “me zai sa na santa bayan banida hadi da ita?” Jalila tai murmushi tace “ya kake gani?” Yace “yanzu muje ki siyo mata kaya, da abinda zata bukata sannan sai ki mata magana akan gidan da zata zauna kiji.” Jalila tai shiru tana kallansa, juyowa yai ya kalleta yace “kallanfa?” Tace “wani sa’in rasa abin cewa nakeyi.” Yace “kin huce kenan?” Tace “ai ba fishi nai ba, kaine fa kacemin wai bazakaci ba.” Yace “bazanci ba so kike nace zanci?” Tace “ba haka nake nufi ba.2 “To me kike san ji?” Shiru tai tare da tambayar kanta, me nake sanji? Hassan bai kalleta ba ya cigaba da tukinsa. Can Jalila tace “Yaya nagode sosai harma bansan ta ya zan yi godiya ba, yaushe Ameera zata dawo ne?” Yace “Ameera batanan?” Kallan mamaki tamai tace “bangane ba?” Bai tanka mata ba, ta cigaba “dan Allah bakasan bata gida ba? Ta dade fa batanan.” Nan ma baice komai ba. Haka suka isa ya zauna a mota yace ta shiga ta siyo kayan, ya mika mata Atm dinsa. Kallan mamaki tai tace “wai ni kadai zani?” Yace ” badai kina tunanin dani zaki shiga ciki ba?” Jalila cikin mamaki ta kalleshi tace “Yaya ni wlh tunda nake bantaba zuwa irin wannan gurin ba, sannan bantaba siyo abu ma da Atm ba bare nasan ya akeyi.” Kallanta yai kamar zaiyi magana sai ya fasa. Kallansa itama tai tadan shagwabe fuska tace “Yaya Please!” Shiru yai yana kallanta kafin ya bude kofar ya fito, yana fitowa itama ta fito da sauri ta matso inda yake. Can gefe yaje ya tsaya yana kallanta wai ta gama zaba, tsayawa tai a gun atamfofi tana tunanin wanda zata dauka tare da duba kudin da aka rubuta a jiki. “Bakya tunanin wannan yafi kyau?” Abinda taji an fada kenan, muryar daga bayanta ta fito. Da sauri ta juyo, baya tadanyi kadan ganin mutum a bayanta. Murmushi ya sakar mata yace “Sunana Al-Ameen Abbah.” Dan baya ta sakeyi tace “Malam…….” Ganin Hassan tai a bayanshi, hannu yasa ya dan bugi kafadarsa, mutumin ya juyo rai a bace yace “Malam meye hakan?” Hassan yace “zaka tafi abinda ya kawoka ne ko kuwa?” Yace “mene? Kai.”2 Wani kallo daya bugama Jalila ne yasa tai saurin matsowa kusa dashi, kallanta yai yace “wuce muje.” Gani tai ya nufi kofar fita tace “bamusai kayan ba.” Yace “banasan shagon.”5 Jalila ta bishi fa kallo, tare da binshi mota.1 Waya ya dauko ya kira Ameerah. Yauce rana ta farko data fara ganin kiran yayanta a wayarta, cikin mamaki ta daga tace “Hello.” “Kina ina?” Tace “Yaya? Ina gidan Aunty Nana.” Yace ki shirya zanzo in daukeki.” Mamaki ya kamata bayan ya kashe wayar tabi wayar da kallon mamaki. Da sauri ta mike ta hau shirya kayanta. Aina’u tace “Ameera tafiya?” Tace “eh yaya ne zaizo ya daukeni yanzu.” Aina’u tace “Kice yau akwai zolaya gun Yaya Sageer?” Tace “Yaya fa ba yaya Sageer ba.” Mamaki ne ya kama Aina’u bata dade da shiryawa ba ya kira wayarta yace ta fito yana waje.” Aina’u tace “Ameera tafiya zakiyi ga Mamana batanan?” Tace “inta dawo kya fada mata.” Cikin hanzari tai waje. Mamaki ne ya kama Aina’u ta biyota waje dan tabbatar ma idanta, aikuwa shine a zaune matarsa na gefensa. Aina’u kishi da takaici ya kamata ko fita daga gate din batai ba ta koma ciki ta fada gado tana hawaye, itafa ya kamata ta zauna a kusa da Hassan ba wannan yarinyar ba.8 Ameera ta shiga baya bakinta yaki rufuwa, yauce rana ta farko da yayanta zai fita da ita guri a motarsa. Jalila sai murna take taga Ameera tana ta neman jan ta da hira, Hassan yai gyaran murya sannan yace “maganar ta isa, inkunje gida kwayi.” Jalila tai gum da bakinta. A kofar wani store ya ajiye su ya kalli Ameera yace “Ameera kuje tare kaya za’a siyoma mahaifiyarta, sannan ya mika mata Atm dinsa.” Tace to yaya, ta fita. Jalila na neman fita ya riko hannunta, juyowa tai ta kalleshi yace “yanzun ma inkin je ki kara bari wani katan ya miki magana.”11 Tace “wancan din ma ni na bari? Sannan bafa komai yace min ba cemin kawai yai wannan yafi…….” Wani kallo ya maka mata, ya rufe bakinta tace “to.” Ya saketa ta fita. Da kallo ya bita har ta shiga cikin shagon na Jifatu. Meke damunshi? Meke damunshi???? Abinda yaketa tambayar kansa kenan…..

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE