JALILA CHAPTER 8
JALILA CHAPTER 8
Kallanta kawai yake baice komai ba, ta dago tace ” Yaya Goggona……” Sai ta kasa karasawa saboda kukan daya kwace mata, kallanta yake baida niyyar tanka mata, balle ya lalasheta. Sai dai yanayin kukan da takeyi ya fahimci lalai she is desperate. Yace “in kuka zakimin zan iya tashi in fita.” Ta share hawayenta tace ” bansan ta inda zan fadamaka halin da Goggona take ciki ba.” Yace “ban tambayeki wannan ba, abinda kawai nakesan naji me kike tunanin yi, sannan me kikeso nayi miki?” Ta mike da sauri tace “Yaya zaka taimakeni?” Kallanta yai sannan ya juya kansa, shiru tai kafin tace ” Bansan me zanyi ba.” Yama rasa mai zaice hakan yasa ya sa hannu zai dauki littafinsa, da sauri ta rike littafin. Kallanta yai tace “Please!” Yauce rana ta farko a rayuwarta da take roko da neman taimako akan ‘yancinsu, aduk lokacin da aka musu abu a da sam bata kawo komai sai takaicin yanda ake wulakantasu, amma bata taba tunanin zata kwaci kanta ba, itadai kullum fatanta tai aure ta dauke Goggonta. Hassan yace ” in bakida abin cewa ki bari sai kin samu sai kimin magana, bance zan taimaka miki ba bare kisa ran zanyi, na dai ce ki fadamin ne kawai inji ko zan iya, i hate meddling in someone’s life.”2 Bata saki littafin ba tace ” Ban taba tunanin nima har akwai lokacin da zan nemi taimakonka ba, ganin halayenka, sai dai kai kadai ne a duniya a yanzu da zaka iya taimako na, Yaya dan Allah.” Yace ” bai dameni ba, Ita mamar taki haryanzu suna tare da wanda ya haifeki ne?” A ranta tace “ina laifin kace mamanki da babanki?” Amma a fili tace “eh sai dai bansan wani irin zama ake ba wanda maganar mutunci bata hadasu.” Littafinsa ya kwace yace ” to meye matsalar?” Tace “naam?” Yace menene matsalar ta koma gidansu mana.” Jalila ta kalleshi jiki a sanyaye, kallanta kawai yai wanda hakan ya nunamai can din ma dai ba magana. Ya dade baice komai ba wanda har jikinta yai sanyi kafin taji yace “ki shirya gobe muje ki dubata.” Da sauri ta kalleshi sam hankalinsa baya kanta ya maidashi kan littafi, kamar bashi yai maganar ba, Tace “Bansan asibitin da suka canza mata ba.” Bai tanka mata ba, tace “Yaya in mun dubata sai me zamuyi?” Yace “later.” Tana shirin magana ma sai taga ya mike ya wuce toilet, ajiyar zuciya tai tace “kai wannan matarka ta shiga uku.” Sai tai shiru tace au ahh ashe fa nice ko? (Nace kila nice…….lol)3 Mikewa tai ta fito tana cewa “da alama bai fahimci ina na nufa ba, ni ba dubata nakeso ba, darajarta nakeso su sani balle har su kara tunanin rainata.” Haka ta fito ta sauka kasa, tana san yima Ummy saida safe. Tasa hannu zata bude kofar taji muryar Ummy tace ” wai meke damunka ne? Bansan me yasameka ba yanzu komai sai ka fara neman yin fada, scammers ka hadu dasu ne ko me?” Yace ” ke ce yanzu bansan meke damunki ba, bansan yaushe kika fara takura haka ba, dolene sai naci abincin……? Jalila ta juya da sauri a ranta tana cewa ” mekenan?” Komawa tai sama da sauri, bayan sunyi sallah sannan taga yadanci abinci kadan, a ranta tace “in mace tayi ba wani abu amma namiji?” Hassan ya hau kan gado ya zauna ya dau jornal dinsa, a ranta tace “wai baya gajiya? Daga zama da karatu sai fita?” Wayarta ta dauka tana dan lalatsawa, lalai ta kosa gobe tayi ta nunama Goggo wayarta, amma zasu ganta kuwa? Bayan basusan sunan asibitin ba? Kallansa tai tanasan kara mai magana amma ta kasa. Meya faru tsakanin Ummy da Abba? Ta fada mai? Can tace “hmm wannan mutumin? Salan yace gulma naje yi?” Kafa yasa ya tura bargon dake kan gadon zuwa kasa. Jalila ta kalleshi, ganin ba alamar shi yayi yasa ta dauko bargon ta na neman maidawa kan gadon, yace “in kinaso kiyi amfani dashi.” Da sauri ta kalleshi tace “dagaske?” Bai tanka kata ba, ta dauka tana murmushi ta shimfida, ta hau ta luluba da bedsheet ga pillow yaukam kwanciyar ta mata dadi, wayarta ta dauko tana kara latsawa. Haka tai ta latsa wayarta har tai bacci. Juyowa yai ya kalleta, gani nai ya kura mata ido daga inda yake, kamar yana nazari akan wani abu. Can sai naga ya gyara ya kwanta, bai dade ba bacci yai gaba dashi. Washegari ma Alhamdulila anyi sa’a abin nasa bai tashi ba, bayan yayi alwala yasa kafa ya dan buge ta dan dama haka yake tashinta. Idanu ta bude ta kalleshi, kallanta yai sannan ya mata alama data mike, Jalila ta tashi ta dauke da bargon daga gun, ga fili nan a dakin amma shidai anan yake sallah. Toilet ta shiga shi kuma ya tada sallah. Sai wajen karfe 7 ta tashi ta kasa ma baccin saboda ta matsu ya tashi su tafi gun Goggo, saukowa kasa tai dan fara aikin abinci saboda yana tashi itakuma ta gama komai sai tafiya. Ganin dakin Ameera tai a bude, a ranta tace “ta dawo ne?” Dakin ta nufa ta kara tura kofar, me zata gani? Ummy ta gani a kwance tana barci. Meke faruwa? Badai fadan da sukai jiya bane haryakaisu ga haka? Gyara kofar tai ta juya a hankali tabar gun ta nufi kitchen. Aikin breakfast take amma sam hankalinta nakan Ummy, ta rasa meyasa batasan wani abun ya bata mata rai sam. Tana aiki har masu aikin gidan suka zo, suna fara kwankwasawa ta fita da sauri ta bude musu kofar, bataso a tashi Ummy. Gaisheta sukai sannan suka fara aikin shara da gyare gyare, saboda girman kasan. Sagir ne ya fito ya hangota a kitchen tana ta aiki, tsayawa yai yana kallanta inama matarsa ce? Da yanzu zuwa zaiyi kawai ta bayanta ya rungumeta. Da sauri ya fara a’uziyya saboda neman tsari daga shaidan, komawa ciki yai da sauri ya zauna a gefen gado sannan ya kwantar da kansa kan pillow.1 Ummy kam sai wajen takwas da kwata ta farka, kallan agoggo tai cikin mamaki, wani irin bacci tai haka? Shiru tai tana tunanin abinda ya faru itada Abba a daren jiya. Bayan ya dawo tanemi ya fito falo yaci abinci, tunda haka suka saba. Kallanta yai yace mata “bayajin yunwa.” Tai murmushi tare da ajiye jakarsa tace “haka ka koshi a waje ne da alama.” Ganin sun saba irin wannan abin bata daukeshi a komai ba, sai cewa yai ban gane na ci a waje ba? Me kike nufi? Gun wata naje ta bani ko me? Mamaki ya kama Ummy tace “meye hakan? Ai kafi kowa sanin ba hakan nake nufi ba.”1 Ai kuwa ya kara hawa wai ta rainashi, nan ya fara masifa ta inda yake shiga bata nan yake shiga ba.2 Haushi yasa ta fito tabar mai dakin, ajiyar zuciya tai sannan ta mike, ta fito falo. Tayi mamakin ganin masu aikin har sun gama shara suna mopping. Can tai tunanin Sagir, murmushi tai sannan ta nufi kitchen. Jalila ta hango tana aiki, da sauri ta karasa tace “Jalila?” Jalila ta juyo tace “Ummy ina kwana?” Ummy tace “Jalila? Yaushe kika tashi haka?” Jalila tai murmushi tace “kije ki zauna Ummy na kusa gamawa ma.” Tace ” banyarda ba bari naje na dawo dai.” Ta juya ta nufi dakinta. Shikansa bai samu barcin arziki ba, dan bayan ta tafi abin duniya ya dameshi, ya rasa mai yasa yake saurin hawa akan kome ta masa wanda ya tabbatar basai wani abin bane, ya rasa meke damun zuciyarsa da yanzu duk abinda Ummy tai matar da yake ganin kimmarta a rayuwarsa bata birgeshi yanzu. Zaliha……. Duk sanda wannan sunan yazomai saurin mikewa yake yana girgiza kai, bai isa ba, ta ina zai fara yima Ummy butulci? Yasan bazata taba hanashi aure ba dan macece mai class da sanin rayuwa wacce sam batasan fada balle musu, to amma yarinya sa’ar danta? How can he?1 Yana kallanta ta shigo ko kallansa batai ba ta shiga toilet, can ta fito ta bude wardrobe ta dau abu zata fita. Yace “Hajiya! Ina tunanin zuwa Bauchi gobe.” Tace “Adawo lafiya.” Ta fita. Adawo lafiya? Ita kuwa tana fita tai kitchen gun Jalila, tare suka karasa aikin. Jalila tace “Ummy bari na hau sama.” Ta fada tare da saurin yin saman. Hassan ya farka ta turo kofar dakin, kallansa tai tace “ina kwana?” Bai amsa ba, tace “bari na shirya.” Ya daga kai alamar to, juyawa tai tadau towel tai cikin bandakin sanye da kayan jikinta. Kallansa tai bayan ta fito cikin zumudi tace “Yaya na fito ka shiga wanka.” Yace “in nayi wanka me zan miki? Ko dama ke kike sani yin wanka?”3 A ranta tace “hmm wannan mutumin?” Amma a fili tace ” a’a gani nai zamu fita.” Yace “zuwa inafa?” Ya fada yana gyara gadan daya kwanta dan shi kam badai gyara muhalinsa ba.” Jalila da sauri ta fara tayashi ta dayan bangaren tana cewa “jiya fa kace yau zamu.” Yace “yau din ta kare ne?” 1 Baki tadan turo mai mutumin nan yake da ita? Hassan ya matso kusa da inda take a tsaye, hannu yasa ta bayanta ya dauko wani littafi sannan ya koma kan kujera ya zauna. Jalila ta tsaka sakato tana kallan ikon Allah, amma mutumin nan…. Cikin takaici ta fita waje tana wata irin tafiya, bugo kofar tai sannan tabi kofar da kallo, dama ita tasan ba lalai ya taimaketa ba. Da alama Uncle kawai zata fadama, haka ta zauna a kujera ta kuna Tv. Shikuwa tunda ta fara cika tana batsewa yake kallanta ta gefe ido, da ta fara wata irin tafiya kuwa tsayawa yai yana kallanta harya banko kofar. Mai zan gani? Hassan naga ya murmusa sannan ya girgiza kai. Shikansa bai fahimci murmushin yai ba saboda rabansa dayai murmushi ko dariya har ya manta. Amma tabas yau kam da saninsa ya kular da ita, dan ya fahimci wani sabon zumudi da takeyi.4 Ajiye littafin yai sannan ya mike ya shiga toilet, yana fitowa ya dauko jeans da shirt yana shirin sawa, baisan msi ya tuna ba sai naga ya cire ya dauko farin yadi mai shara shara ya sa. Bayasa hula dan haka ko dubata ma baiyi ba. Zama yai ya bude tiren data ajiye. Kallan plate biyun dake gun yai, kenan bataci abinci ba?6 A falo taji yunwa ta kamata ta turo kofar daki fuskarta a hade, kallanta yai sannan ya dauke kai kamar bai ganta ba. Ganinsa a gaban abinci yasa ta tsaya turus tana kallansa. Kallanta yai yace ” Kin fasa zuwa ne?” Da sauri tace “zamu?” Kallan abinci yai sannan ya kalleta, da sauri ta matso tana dariya, duk yanda taso ta boye farin cikinta ta kasa.1 Shikam ya hade rai yana kallan ikon Allah, shi ta fara zubama sannan ta zuba nata. Dan kadan taci ta fara neman mikewa, kallansa tai taga shima kallanta yai fuskarsa a daure. Da sauri ta koma ta zauna tana kara cin abincin.4 Yana mikewa kuwa itama ta mike, gani tai ya koma ya zauna akan gado. Tace “Yaya na……” Kasa karasawa tai sai ta wayance tace “Yaya naga bakasha tea din ba, ko na kawoma ruwa?” Yace “later.” Juyawa tai ta fita, kallanta yai sannan ya mike ya dau key din mota ya dau wayarsa. Sannan ya sauka, bata falon sama shiyasa ya wuce kasa. A kitchen ya hangota, ita da Ummy da alama wanke wanke suke. Tsayawa yai yana kallansu, bai san me take cewa ba yaga Ummy na dariya. Matsowa yai yana san yi mata magana, kuma bazai iya ba. Juyawa kawai yai yana neman komawa sama, Sagir yace “Yaya kaine a falo?”1 Hassan ya kalleshi sannan ya juya zai hau sama, Jalila najin ance Yaya ta juyo da sauri tana hangoshi ta tsame hannunta a ruwan dauraya tai gunsa da sauri. Ko bi takan Sagir batai ba tasha gaban Hassan tace “Yaya ina zaka?” Kallanta yai yace ” fita ma inzanyi sai an tambayen?”1 Tace “au yahkuri, in fito?” Juyawa yai ya fita waje bai bata amsa ba, da gudu ta haura sama ta dauko hijabinta, da wayarta. Da gudu ta fito ta sauko, Sagir kallanta kawai yake, Ummy da mamaki ya sa ta tsaya tana kallansu, Jalila ta karaso gunta tace “Ummy zamu fita, na tafi karya fasa.”1 Ummy mamaki yasa ta kasa ma magana, yau Hassan ne zai kai wani unguwa? Kallan Sagir tai da sauri wanda yai shiru yana kallan Jalila wace yaga ko kallansa batai ba tana zumudin fita da miji.7 Ummy tace “Sagir ka ga Hassan?” Kallanta yai ya kakaro murmushi yace “naganshi Ummy, ni kaina mamaki nake.” Ummy ta fadada murmushinta tace ” Sagir da alama Hassan ya fara canzawa, ko?” Sagir ya jinjina kai yace “sosai Ummy.” Ummy ta juya cikin tsananin farin ciki. Jalila kam da sauri ta bude gaban mota inda yake ta shiga. Tana hakki, Hassan ya kalleta yace “meye hakan? Gudu kikai?” Tace ” tsoro nake karkai zuciya.” Hassan ya tada mota ya ja, suna tafi motar shiru ba komai sai sanyin AC din da ya kunna, ita ta dinga nuna mai hanya da suka shiga unguwar. Suna zuwa kofar gidan tace “nan ne, amma yaya kana tunanin zasu nuna mana inda Goggon take?” Bai kula taba yai horn, mai gadin gidan ya fito da sauri ya leka ganin Jalila yasa ya koma ya bude. Shiga sukai yai parking, sannan ya kashe motar ya kalleta yace “ki shiga.” Juyowa tai ta kalleshi tace “in shiga?” Yace “ko ni zan shiga?” Tace “a’a ban dai fahimceka bane, ba tare zamu ba?” Yace ” a yaushe mukai hakan dake?”1 Jalila ta tsaya tana kallanshi tace “Yaya kaifa kace zaka taimaken.” Yace “a yaushe kenan?” Jalila yanayin fuskarta ya canza tace “Amma…..” Yace ” ki shiga ku gaisa, in kuka bakida niyya mu juya.” Kallansa tai tama rasa me zatace ” Hassan ya dau wayarsa yana duba abu.” Idanunta ne suka ciciko ta bude motar ta fita, ta nufi gidan zuciyarta a dagule. Amma mutumin nan anyi mara mutunci. Shikuwa yana kallanta har ta shiga. Dady na zaune yana hada wasu takardu yana waya ta tura kofar tare da yin sallama. Dady ya juyo jin muryar Jalila. A daidai lokacin Mumy ta fito ita da Yasmeen, Mumy na rike da plate dake dauke da kayan marmari. Da yake yau asabar ba aiki. Kallanta sukai sai suka zubo mata ido, Yasmeen ta rugo da gudu ta rungumeta tana mata oyoyo. Jalila ta kalleta tace “My Yasmeen ya makaranta?” Yasmeen ta rike hannunta tana zuba mata shagwaba, nan Jalila ta dauketa. Dady ya kalleta yace “Jalila! Kece?” Mumy ma tace “Jalila shigo mana.” Jalila ta shigo jiki a darare ta zauna a kasa, tana gaidasu. Mumy ta amsa sannan tace “banyi tunanin ganinki ba daga aure.” Jalila ta kalleta sannan tai kasa dakai ita duk ta rasama me tazo yi. Knocking din kofa sukaji, Dady ya kalleta yace ” bake kadai bace?” Kallan kofar tai da sauri tana cewa “eh tare muke.” Mamaki tai dataga Dady ya mike da sauri yana kallan Mumy yace “yi maza kinsanar ma Inna.” Mumy tai sama da gudu. Jalila ta tsaya kallan ikon Allah, Dady ya bude mai kofa. Hassan ya kalleshi sannan yace “sannu.” Dady ya washe baki yace “shigo mana.” Hassan ya shigo tare da zama akan kujera.2 Dady ha zauna a dayar kujerar yana cewa “ai bamu san tare kuke ba, ke kam Jalila bakyaji akan me da kika shigo baki sanar mana ba?” Hassan ya kalleshi sannan ya kalli sama wanda yaji alamar saukowar mutane. Matan biyu daya gani a gidan su yau ma su ya gani. Kallan Dady yai yace ” tanata damuwa akan rashin lafiyar mahaifiyarta shiyasa nace bari muzu.” Turus Inna da Mumy sukai akan kasan beni, Jalila ma da sauri ta kalleshi, Dady yace “naam? Me kake nufi?” Hassan ya zubawa su Inna ido yace ” Jalila a ina Goggon take? Dan nasan bata cikin su.” Ya fada yana nuna su Mumy da kai.12 Inna wace ranta yakai koluwa gun baci, ta kalli Jalila tana jiran me zatace, Jalila kuwa tayi mamakin kalamansa dan bata taba tunanin haka zai bulo musu gatse gatse ba.2 Hassan ya kallesu yace ” Ina wuni?” Inna bakinta na dan rawa tace “Lafiya.” Hassan ya mike ya kalli Dady yace ” dan Allah a ina take? Ina sauri ne.”1 Dady baki na rawa ya kalli Mumy da Inna yace “tana primer.” Yace “wani dakin?” Dady ya kalli Mumy yace “wani dakin ne ma?” Tace “hmm….” Hassan ya kalli Jalila yace “muje ko?.”2 Jalila tai sakato tana kallan ikon Allah. Ganin yana neman fita yasa ta mike da sauri kar a rufeta da duka tai waje. Suna shiga mota ya ja yai gaba. Jalila ta zubamai ido tana nazari akansa, can tasa wata dariya tace “Yaya kaga idon Inna kuwa?” Kallanta yai yace “wacee hakan?”7 Jalila tace “kaka ta? Ahh ba kakata ba kakar su Yasmeen.”1 Hassan bai kula ta ba ya juya yana tuki, ita kuwa in ta tuno yanda sukai sai ta kara sa dariya. A haka har suka isa, suna shiga ya nemi a duba musu sunan Goggo. Nan wata nurse ta wuce dan nuna musu dakin, Hassan ya kalleta yace “ina mota.” Da sauri ta riko rigarsa ta kasa tace “mota?” Kallanta yai, tace “dan Allah kuje ka gaidata. Batasan anmin aure ba fa?” Ta fada tare da canza fuska xuwa tausayi…… Hassan ya kara kallanta yace “kina nufin in shiga ciki?” Ta daga kai, ya kara kallan asibitin, batasan nan ma dakyar ya shigo ba? Jalila ta kalleshi tace “Yaya!” Kallanta yai sannan ya fizge rigarsa ya juya. Binshi tai har jikin motar ta tsaya a jikin kofar inda yake tace “Dan Allah yaya kazo muje.” Kallanta yai yace ” wai meke damunki? Ana abu dole ne?” Tace “i am really scared” Kallanta ya sakeyi, tace “bansan a wani hali zan sameta ba, bansan me zance mata ba in ta tambayeni, Yaya dan Allah kazo muje.”+ Oh God! Wannan wace irin yarinya ce? Yace “to in naje ta tambayeki wanene ni me zaki ce?” Kallansa tai sannan tai shiru, yace “ki je ki fito in kuma in barki anan ne sai ki zauna sai dare.” Jalila ta kalleshi tace “zan zauna anan din.” Yace ” ur choice.” Sannan ya kalleta yace” zan rufe kofa.” Jiki a sanyaye ta matsa daga jikin motar, ya ja yai gaba, ta glass din mota ya hangota tana tsaye inda ya barta. Bazai iya shiga ciki ba dan shikadai yasan memory din da yake dawomai in ya shiga cikin asibiti gun marasa lafiya. Jalila ta juya jiki a sanyaye, tana shiga nurse din ta tareta tace “ina yayan naki?” Jalila ta kalleta tace “a ina Goggon take?” Nan tai gaba Jalila ta bita a baya. Goggo na zaune akan gado, ba laifi kafar tata ta samu sauki sosai, tana shiga tai gunta da gudu ta rungumeta ta saki wani irin kuka. Ita ma Goggon kuka ta saka, sun dade a haka kafin Goggon ta daure tace “Jalila ina kika shiga?” Jalila ta dago ta zauna kusa da ita tace Goggo na. Goggo tasa hannu ta share mata kwalla tace ” kukan ya isa hakanan, me ya faru? Ko jikin naki ne?” Jalila ta kalleta tana girgiza kai tace “ba komai Goggo na, ya jikin naki?” Goggo ta kalleta kallon tuhuma tace “Jalila kin tabbatar? Dan nikam tsoron mutanen nan nakeyi.” Hassan har ya fara tafiya naga yayi kwana da motarsa ya dawo asibitin, bude kofar motarsa yai ya fito sannan ya nufi asibitin. Nurse din tana ganinshi ta taho inda yake, tace ” ka dawo?” Hassan yace tana ina? Nan Nurse din ta fara tafiya yana binta a baya. Suna taka steps din gaba daya kawai takawa yake, suna zuwa second floor yaji kansa ya fara juyawa, da sauri ya rike bango, sannan ya tsaya ya rike gefen zuciyarsa. Wani irin numfashi yake fitarwa, juyawa yai da sauri ya sauka kasa, nurse din ta juyo kawai taga bayanan. Hassan ya sauka da sauri ya shiga mota ya ja ya rufe ya fita da gudu. Sai da yai nisa sannan yai parkin ya kifa kansa akan sityarin motar yana maida numfashi. Jalila tai murmushi tace “Allah Goggo ba komai, kawai dai ina bakin cikin laifin dana miki ne.” Goggo tace “laifi?” Jalila ta kwantar da kanta akan cinyarta tace ” ni dai ki yafemin Goggo na.” Goggo ta shafi kanta tace “ba abinda kika min Jalila, na tabbatar ko da kin min ba daidai ba sai dai a rashin saninki ko kuma tirsasaki akai, kawai dai inaso kisan ke kadai ce dani a duniya” Jalila ta share kwallar data gangaro mata tace ” tsoron sanar dake nakeyi.” Goggo tace “ko menene ki fadamin.” Jalila tai shiru can tace “zan fada miki amma sai kin warke an sallameki.” Goggo tai murmushi tace ” shikenan, da alama akan Sagir ne.” Jalila tai murmushin yake batace komai ba. Haka ta zauna makale da Goggonta, Lantana na gefe tana kallansu gwanin sha’awa. ************* Su Hassan na fita Inna ta matso kusa da Dady ta daga hannu ta sharara mai wani wawan mari, da sauri ya kalleta dan sam baiyi zatan abinda zatamai ba kenan.10 Mumy ta matso da sauri ta tsaya agan Inna tace ” Inna menene hakan?” Inna cikin takaici tace “Uban wa yace ka fadi inda take?” Dady ya kalleta ransa a bace takaicinsa agaban Yasmeen dan wulakanci. Mumy ta kalleta tace “Ta ya bazai fada ba bayan yaran yasan komai, da alama Jalila ta gama sanar dashi duk abinda ke faruwa?” Inna cikin kunar rai ta zauna akan kujera tace “Akace bashi da hankali?” Mumy ta zauna kusa da ita tace “dama Bakiyi bincike ba?”2 Inna tai shiru kafin tace ” muna cikin tashin hankali, idanun yaran nan ba tsoro ko fargaba a ciki sannan da alama baya ragama wanda ya tabashi, me kuke tunanin zai faru in yasan abinda akama matarsa? Sannan canjen da mukai muka bashi Jalila a maimakon Safeena?” Mumy ta kalli Dady tace “Dadyn Yasmeen!” Dady ya kalli Inna wacce ke kallansa yace ” hakan bazai faru ba, ni da kaina zan sanar da ita karta kuskura ta sanar dashi komai, kuskuren sanar dashi Mahaifiyarta datai ya isa.” Inna ta jinjina kai tace “u have to take care of her, in ba haka ba ni zan bulo mata ta bayan gida, zan sata dana sanin da bata gaba yi ba daga ita har uwarta.” Dady yace “insha Allahu baza’a sake ba.” Mikewa tai ta hau sama. Tana tafiya ya mike a zuciyd ya shiga dakinsu. 1 Mumy ta bishi da sauri tare da rungumeshi ta baya tace “Darling.” Hannunsa ya zare yace “meye hakan? Kina abu kamar yarinya?” Ta kara kankameshi tace “Dadyn Yasmeen am sry…….” Kallanta yai kamar zaiyi fada, da sauri ta sumbaceshi……….. ************* Ummy ce ta kalleshi tace ” ina zakaje da har kake san in wakilceka akan taron da yake da mahimmanci?” Yace “Abuja zan koma dan akwai abu mai mahimmanci da nake sanyi.”7 Ummy ta kalleshi tace “yafi wannan mahimmanci?” Abba yai shiru yana duba abu a computer sa. Ummy tace ” ni na kasa gane abinda bazaka iya fadamin ba” Cikin zafin rai yace “wai meke damunki ne? Dolene ko wani abu na rayuwarta sai na sanar miki?” Da karfi ya budo kofar wanda ya sa suka kalli kofar a tare, kallan Abba ya shiga yi idanunsa sun canza sosai. Yanda yake kallan Abban ne yasa Ummy ta matso da sauri ta sa hannu ta riko hannunsa tace “Hassan meye hakan? Taya zaka banko kofa haka bako sallama?” Idanunsa na kan Abba haryanzu wanda gaba daya Abba ya gama shan jinin jikinsa. Hassan ya daure yace “mekenan?” Ummy tace ” mekenan kamar ya?” Hassan bai kalli Ummy ba idanunsa nakan Abba yace “me Ummy tai da har kake mata fada haka?” Ummy tasa hannu da karfi ta turashi waje sannan ta fito itama, ta rufo kofar sannan ta kalleshi tace “muje.” Ta fada tana jan hannunsa, dakyar ya hau saman sannan ya kalleta cikin takaici yace “Ummy me kika mai yake fada haka?” Tace ” ba abinda yamin nice namai lefi shiyasa yakemin fada akan abinda nai.” Kallan ta yai dan shikam bai yarda ba, to ko laifin ma tamai taya zai hauta da fada haka? Ummy ta kalleshi tace “Ina Jalilan?” Yace “Ummy kin tabbatar ba abinda ya miki?” Tace “sau nawa kake so na fada ne? Ina tambayarka Jalila, badai ajiye ta kai a hanya ba?” Yace “Tana nan, kawai ya wuce dakinsa.” Zama yai a bakin gado yana tunani, dolene ko wani abu na rayuwata sai na sanar miki? Kallaman Abba ne ya sake dawo mai, meke faruwa? Ummy tana sauka ta koma dakin, Abba ya kalleta yace “me kika cemai? Tace ” kome nacemai bana tunanin nima ya zama dole in sanar dakai.” Abba ya matso kusa da ita yace “Ciwon sa fa? Ya tashi?” Ummy ta kalleshi tace ” kaje ka duba.” Ta matsa daga kusa dashi. Abba yai shiru yana tunani sannan ya koma ya zauna agefen gado. *********** Bayan magrib yana zaune yana karatu, naga ya rufe littafin ya sauko zuwa mota. Kallo daya zakamai ka fahimci yana cikin bacin rai tsantsa. A asibitin yai parking sannan ya fito, duk yanda yaso ya duba Nurse din a reception din bai ganta ba. Kawai komawa yai mota ya zauna, ya kwantar da kansa akan kujera. Jalila kam sunata hira da Goggo taga isha’i tayi. Wayarta ta dauko tana dubawa ko zai kirata, ta ina zai kirata? Bayan bashi da numberta? Itama haka. Ajiyar zuciya tai sannan ta ajiye wayar. Goggo ta dau wayar tana kara kallo tace “gaskiya wayar nan tayi kyau ta birgeni, mahaifiyar Sagir ce?” Tace “Hmm.” Goggo tai murmushi tace ” karki damu ina warkewa zansa ya turo ai auran.”2 Wani film akeyi a tv dake dakin, saurayin ta na waje yana ta jiranta ita kuma bata sani ba tana cikin gida suna ta hirar su Mikewa tai ta dau hijab dinta tace “Goggo ina zuwa.” Ta fito, tana tafe tana cewa kai inaa…. ta ya zai zauna jirana? Au ko bai san inda nake ba na tabbatar zai sa a nemi ni. Tana fitowa kawai ta hango motarsa, mamakinne ya kamata ta karaso gun motar a ranta tana cewa ” kai…. ba shi bane, kanta tasa tana leka motar.” Hassan na kwance ya bude idanunsa, gani yai ana leko cikin motar, tunda akwai haske fitulun waje. Hassan ya zuge glass din motar yace ” meye hakan?” Tace “kai!!!! Kaine da gaske, me kake anan?” Yace ” me nake kuwa, bakisan wannan shine hubby dina ba?” Tace “zama a mota?” Bai tanka mata ba yace ” muje?” Tace “bari nama Goggo salama, Yaya bazaka shiga ba?” Kansa ya kawar gefe. Ta fita ta ma su Goggon salama, goggo ta bita da kallo tana tunanin tabbas akwai wani abun, Jalila bazata taba zuwa ta tafi a aranar ba. Jalila ta shiga mota ya tada suka fara tafiya, yanda taga yanayin fuskarsa ne yasa tai shiru dan taga ba alamar wasa. Can ta kasa daurewa tace “Yaya nagode.” Bai kalleta ba yace ” 4 wat?” Tace ” taimakon da kamin.” Shiru sukai sai tafiya kawai da yakeyi, can tai murmushi cikin sanyin murya tace ” at first tsoronka nakeyi, later sai na fara fahimtar ka, yau kuma na ga wani side naka na daban.” Hassan bai kulata ba sai da aka dade yace ” kina tunanin adan karamin kwanakin da mukai ne kike tunanin kin fara sanina?” Tai murmushi tace “a’a bansanka ba, sai dai na fahimci abu daya.” Juyowa yai ya kalleta, yana jiran abinda zatace. A ranta tace u are kind, amma a fili dariya tai tace “na fahimci kana matukar san Ummynka.” Kansa ya dauke daga inda take ya cigaba da tukinsa. Tana san sanar dashi matsalar Ummy sai dai tana tsoro……. Yana tafe yana tunanin kalaman Abba har suka iso gida, parking yai sannan ya maida kansa ya kwantar a jikin motar. Jalila ta fita daga cikin motar, sannan ta juyo ta kalleshi, ganinsa tai bashida alamar ma fita. Komawa tai cikin motar ta zauna tace “Yaya! Bazaka shiga ba?”+ Bai kalleta ba bashi kuma da alamar bata amsa, Jalila ta kalleshi tace “Yaya?” Idanunsa ya bude ya kalleta yace “Nikam bakinki baya shiru ne?” Kallansa tai ta rufe bakinta da labanta, yace ” jeki, ko dole sai tare zamu shiga?” Jalila ta mike sum sum tai waje, ita kanta mamaki take, tana da surutu sai dai ba’a ko ina ba, a gaban Goggonta kadai take magana san ranta, amma ta rasa me yasa yanzu ta saki jiki da Hassan har take magana haka dashi, duk kuwa da dizgatan da yake. Rufe masa motar tai ta tako zuwa cikin gida, tana kokarin bude kofa shi kuma ya turo kofar zai fita. Tsayawa sukai suka kalli Juna, Jalila ta matsa ta bashi hanya. Sagir ya kalleta yace ” ki shiga.” Ya fada tare da rike da matsa mata, kallansa tai sannan ta tako ta shiga. Har zata wuce taji yace ” kinga Goggon?” Ta kalleshi ta daga mai kai alamar eh, murmushi yai tare da cewa “Alhamdulila.” Bata amsa mai ba ta wuce ciki, dakin Ummy ta nufa ta kwankwasa mata kofa.4 Ummy na kwance dan zazzabi ke neman rufeta tace “shigo.” Jalila ta murda kofar dakin ta shiga, Ummy na kishingide akan gado Jalila ta shiga. Tace “Ummy ina wuni?” Ummy ta kalleta tace “kun dawo?” Jalila ta matso tace “eh, amma Ummy lafiya dai ko na ganki a kwance” Kallanta tai tace “kai na kemin ciwo.” Da sauri Jalila ta matso tace “Sannu Ummy, kinsha magani?” Murmushi ta sakar mata tace “kar ki damu daga nayi bacci zai ware.” Jalila ta tsaya tana kallanta cikin tausayawa, tabbas abinda ya faru jiya ne kila yake damunta. Daurewa tai tace “Abba fa?” Ummy tace “dazu ya tafi Abuja.” Jalila tace “Ummy ko dai in kira Yaya akaiki asibiti?” Hannunta ta kamo tace “Jalila karki fadama Hassan banajin dadi.” Jalila cikin mamaki tace “Ummy me yasa?” Tai murmushi tace “Tun yana karami bayasan yaga ko ya ya ne banda lafiya, in kuwa ya sani to ya dinga kuka kenan, yanzu kuwa da ba lafiya gareshi ba inya sani abin nashi karuwa yake.” Jalila tace “to a kira Ya Sagir.” Ummy tace “Jalila karki damu, daga na kwanta shikenan.” Jalila tai shiru kafin tace “bari nai sallah.” Nan ta fito zuwa sama, baya dakin nan tai alwala tai sallar isha’i sannan ta sauko zuwa kitchen. Duk da batajin dadi Ummy sai data musu jollof din taliya wacce tasha kayan ciki. Jalila ta dau nasu takai sama sannan ta dawo gun Ummy. Hassan kam ya dade a mota kafin ya fito, kofar dakin Ummy ya murda dan yana san ya tabbatar da gaske Abban yayi tafiyar? Ummy na kwance da alama bacci take, ita kuma Jalila na zaune a kasan carpet ta daura kanta akan gado, itama da alama bacci ya fara dan daukarta. Tsayawa yai yana kallansu, yanayin kallan da yake musu ba irin kallan daya saba bane, yau kallo ne yake na jin dadin ganin Ummy da Jalila. Yana neman juyawa yaji Ummy tace “Hassan!” Juyowa yai ya kalleta, tace “zo ka dauki matarka ku tafi.” Yace “in dauketa kamar ya?” Tace ” Badai dan rashin tausayi tashinta zakayi ba?” Yace “Ummy tanada kafa fa?” Ummy ta mai alama da hannu akan yai shiru sannan ta mai alama da dayan hannun akan ya shigo. Shigowa yai fuskarsa a daure, a hankali tace “dauketa, da alama baccin yanzu ya dauketa, kuma da karfi ya dauketa.” Hassan ya kalli Ummy sannan ya kalli Jalila dake bacci, ta karamai alama da hannu akan ya dauketa. Cikin takaici yasa hannu ya dauketa kamar yarinya.8 Jalila kam yana daukanta taji alama sai dai muryar Ummy dataji tace “to sai da safenku.” Yasa ta fahimci Hassan ne sai ta kara rufe ido dan batasan ta ina zata fara kallansa ba.1 Hassan ya juya ya fita, Ummy ta kallesu cikin farinciki sannan ta kalli gefen gado, Abinci Jalila ta ajiye mata da ruwa da paracetamol wanda ta tabbatar a cikin magungunanta ta dauko mata. Murmushi tai sannan ta hadiye maganin kawai ta kishingida. Hassan haka ya hau da ita steps din har yaje kofarsu, kallanta yai yaga tana kif kif da ido, hannu yasa ya bude kofar sannan ya shiga ciki. Gani nai yayi hanyar toilet da ita ya bude kofar, yana neman shiga, Jalila kam jin ya sake bude kofa yasa ta bude ido ta kalleshi. Ganinshi tai yana neman shiga toilet da ita, da sauri tace “Yaya ina zaka kaini?” Yace “au kin tashi?” Tace “ina zaka kaini?” Yace “kamar Ummy cewa tai in kaiki bandaki in taimaka miki kiyi wanka.”12 Da sauri ta fara kokarin kwace kanta tana cewa “wlh banji tace haka ba. Sauke ta yai a ciki sannan yace ” me tace to?” Yafada tare da tare hanyar toilet din. Jalila ta kalleshi tace ” cewa tai sai da safenku.” Hassan yace “hmmm bakiji farkon ba kenan, ni kuma na ji.”5 Kallansa tai batace komai ba, fitowa yai yasa hannu yana neman rufe kofar. Da sauri ta rike tana cewa “yaya menai? Naga lafiya muka dawo.” Yace ” idanki biyu kikasa ma daukeki?” Tace ” ba idona biyu ba Allah daga baya na farka.” Yace ” da kika farka fa?” Tace “yahkuri wlh ni kunya naji.” Kallanta ya tsaya yanayi. Kanta ta maida kasa tana kara rike kofar, can ta saki dan kara ta rike hannunta tace “wayyo hanuna.” Kallanta yai yace “hannu?” Jinginna tai da bango tana dan murza hannun, sakin kofar yai ya shigo yana cewa “menene?” Da sauri tai waje da gudu tana dariya. Tsayawa yai kawai yana kallan ta, lalai yarinyar nan. Dariya ta shiga yi tana cewa “yaya wai harka shiga?” Hassan ya hade rai ya fara nufo ta, ganin yanda idanunsa suka canza yasa ta tsaya cikin tsoro tanayin baya. Sai dayaje daf da ita sannan ya zauna akan gado bai ce mata komai ba ya dau littafinsa. Kallansa tai jiki a sanyaye tace ” Yaya bakai dinner ba.” Kallanta yai yanzu ma baice komai ba, tai shiru ta zauna a gefen gado daga karshe. Shiru ne ya ratsa dakin kafin can yace “Jalilah!” Kallansa tai da sauri, yauce rana ta farko da ya kirata da sunanta cikin wannan muryar, murya ba mai dauke da zafi ko fada ba.2 Idanunta na kansa yace ” Jalilah Please take care of Ummy.” Idanunta na kansa tana kallansa ta daga mai kai alamar fahimta sannan tace ” Insha Allah.”1 Haryanzu idanunsa na kanta yace ” Nagode.” Kanta ta sunkuyar sannan tace “nima na gode Yaya da taimakon da kamin.” Yace ” me kika ce ma Goggon taki?” Ta kalleshi da raunanan ido tace ” ban iya cemata komai ba, bansan ta ina zan bulo ba, bansan me zan ce mata ba.” Ta karasa magana tana share kwalla, kallanta yai yanasan lalashinta sai dai bai san ta ina zai fara bama. Kansa ya dauke daga gunta, wayarsa ya dauka ya dubo sunan Abba. Rabon daya kirashi harya manta, sai dai shi Abban ya nemi shi. Dialing yai yana kallan agoggo, goma saura. Yanajin wayar har ta gama ringing bai dauka ba, idanunsa ne suka kara canzawa ya sake kira, tana daf da katsewa Abba ya daga cikin mamaki da shakka. Kallan Abokinsa yai sannan ya mike daga falon ya fito waje. Ya daga yana cewa “Hassan!” “Abba kana ina?” Jalila ce ta kalleshi da sauri, Abba yace “nayi tafiya ne, baka tambayi Ummynka ba?” Hassan yace ” na dauka akan tafiyarne kukai fada?” Abba cikin mamaki yace “Haka tacem?” Yana mamakin kiran da Hassan yamai da kuma mamakin yanda yake tambayarsa, duk da Hassan na tsananin san Ummy bai taba shiga maganarsu ba, me ke faruwa?” Hassan harzai sake magana sai kuma ya kashe ya cillar dawayar gefen gadon. Jalila tai shiru tana kallansa, mikewa tai tai shimfida dan yanda ta ganshi tasan da matsala. Bata dade da kwanciya ba bacci yai gaba da ita. Hassan kam ya dade kafin ya mike ya sauko kasa. Sai daya leka Ummy yaga tana bacci sannan ya juya ya koma sama. Jalila ya kalla wacce ke bacci, daga gefen gado ya kwanta har bacci ya daukeshi. Yanda jikinsa ke kadawa da yanda yake abu kamar maiyin kuka yasa cikin baccinta ta farka. Da sauri ta kunna wayarta sannan ta kunna fitilar dakin. Bakinsa sai kakkarwa yakeyi, da sauri ta karasa kusa dashi ta kamo hannunsa. Ganin yana neman fadowa daga kan gadon yasa ta rungumeshi tana hawaye tana kiran sunansa. Idanunta a runtse, hawaye kawai ke zuba. Ta kankameshi, sun dade a haka kafin nimfashinsa ya fara daidaituwa. A hankali ya bude idanunsa ya zubasu akanta, hawaye kawai take tana kiransa. Yanda ta rungumeshi ne yasa ya kara kallanta sannan yace “Jalila!” Idanunta ta bude ta kalleshi, bakinta na rawa tace “Yaya?” Yace “wannan rikon fa?” Sakeshi tai tana kallansa, ya kalleta yace “baki iya addu’a bane sai kuka da kiran sunana?” A hankali tace “banyi islamiya ba.”2 Kallan mamaki ya mata da tausayawa, sannan yace ” kukan fa? Are u worried about me? Or are u scared?”4 Kallansa tai bata iya cewa komai ba. Agoggo ya kalla, karfe biyar saura, mikewa yai ya nufi toilet har zai shiga sai yace ” forget what I just said.” Sannan ya shiga, ajiyar zuciya tai sannan ta sa hannunta shafi fuskarta. ********** A abuja kuwa, Abba ya kalli Abokinsa Hafiz yace ” sry muna magana yarona ne ya kira.” Hafiz yace ” to yaya? In sanar da ita ne ko ka fasa?” Abba yai shiru kafin can yace “bari dai sai zuwa gobe, in na sake yin nazari.” Hafiz yai dariya yace “nazarin me? Bayan abinda ranka ke so ne sannan ba haramun bane?” Abba yai shiru yana tunanin yanda idanun Hassan sukai alokacin daya shigo, can yace “sai dai goben.” Hafiz yace shikenan Allah ya kaimu. Nan Abba ya fito, yana neman fita gate yaji muryarta tace “Ba gaisuwa?”1 Juyowa yai da sauri ya kalleta, gani nai ya hadiye wani yawo, Zaliha tayi kyau iya kyau kamar mai shirin zuwa dinner doguwar riga ce a jikinta ba dankwalli balle mayafi. Gashin kanta kawai ta saukar wanda yasa gyara. Bakinsa na rawa yace “Zaliha ko?” Ta dan kashe mai ido sannan ta matso inda yace tace “badai sunan ma an manta ba?” Yai dariya yace ” ina zan manta?” Tace “muje ciki mu gaisa, bana iya jurar tsayuwa.” Nan yaga ya juya tana gabe yana binta a baya, komai na jikinta motsi yakeyi.