JALILA CHAPTER 9

JALILA CHAPTER 9

Abba yaje shiga falon ya tsaya yana kallanta, meke faruwa dashi? Me yasa baya iya controlling din kansa? Juyawa yai da sauri yana neman fita, hannunsa yaji ta kamo. Kallanta ya juyo yai cikin bacin rai sai dai yana kallanta yaji ya kasa cewa komai. Tace “Tafiya zakai?” Yace “a’a.” Haka taja hannunsa har cikin falon sannan ta zauna a gefen da yake. Tace ” Sai naga kamar na takura ma.” Yace “kamar ya kenan?” Ta dan shagwabe fuska tace ” gashi nan ka hade rai.” Da sauri yace ” ba hade rai nai ba, kiyi hakuri.” Murmushi tai sannan ta zubo mai juice a cikin cup ta mikomai tace ” gashi.” Amsa yai yana kallanta yana sha, can yace “Zaliha inaji ya kamata na tafi.”1 Kanta ta kwantar akan kafadarsa ta sakala hannunta cikin nasa tace “da wuri haka? Ni anya ka damu dani kuwa?” Taura bakinsa na rawa yace “damuwa dake din danai shiyasa kika ganni anan garin, nabar tarin aiyukan dake gabana.”1 Murmushi ta saki sannan tace ” nikaina mamakin yanda zuciyata ta kamu da kaunar ka nakeyi.” Washe baki yai yace ” nikaina ban taba tunanin hakan zai faru dani ba.” Haka tai ta jansa da hira tana kara dirkamai juice din abarba da kwakwa da suka hada wanda suka hadashi da rikaken maganin da aka basu.7 Sai dare sosai ya tafi shima harda wani kwallarta wai batasan ta rabu dashi. Haka ya lalabata ya tafi, da yaso barin garin washe gari amma dole ya hakura sai jibi. Yana fita ta shiga dakin Yayarta da gudu tace “Aunty !” Kallanta tai ta mata alama da tai shiru, nai tai shiru ta matso kusa da ita tace “Aunty gaskiyar malamin nan kinga yanda ya mato kuwa?” Auntyn tai dariya tace ” an fadamiki barno gabas take? Sanda malamin yace mu koma gida zaizo da kansa me nace miki?” Tace “ai ni ban dauka abin zaizo da sauki haka ba.” Tace ” kedai kiyi abinda malam yace karki kuskura ki nemi jin rayuwarsa da matarsa ko ‘yayansa har sai mun amso dayan maganin.” Tace “To Aunty zan kiyaye.” Nan ta fito tana murmushi, dolene ta fara rubuta abubuwan da take bukata intayi aure da irin wayar da takeso, da motar da takeso da gidan da takeso. Dan bataso a wuce wata daya basuyi aure ba. Taura kuwa yana shiga hotel dinsu yai sallah sannan ya kwanta akan gado yana kara tunano abinda ya faru dashi, yaushe zuciyarshi ta koma budurwar zuciya? Me zai cema Ummy? Sagir? Ameera? Has……… goshinsa ya dafa dan ya tabbatar akwai gagarumar matsala babba in Hassan yasan halin da ake ciki, dan tabbas shikansa tsoron abinda zai biyo baya yake. Baisan sanda ya dau waya ya kira Zaliha ba, nan ya baje sukai ta hira har sha biyu sannan ya kwanta. ********* Jalila kam batai baccin safe sosai ba dan karfe takwas ta sauko danyima Ummy abinci, dankali ta fara firewa bayan ta saka tafashen naman kaza, tana suya tana dan kara gyara kitchen din har masu aikin gidan suka iso. Bayan ta gama suya ne tadan tafasa indomie tai awara da ita sannan ta jera akan dinning. Dakin Ummy ta nufa ta kwankwasa. Ummy ta taso ta bude mata, Jalila ta rusuna ta gaisheta sannan tace “Ummy ya jikin?” Ummy tai murmushi tace ” Jalila na warke, na barki da aiki ko?” Tace “kai Ummy wannan ne aiki?” Ummy ta riko hannunta suka fito falo tana cewa “Hassan fa?” Tace “bacci yake sanda na fito.” Ummy ta dan tsaya sannan tace “Jalila haryanzu a kasa kike kwana?” Jalila ta sunkuyar da kai saboda kunya sannan tace “Ummy yaya ya fara canzawa, yanzu yana amsawa in namai magana.” Ummy ta jinjina kai cikin jin dadi tace “na gani Jalila, ai tunda ya fita dake a mota nasan Hassan ya fara canzawa, ko Ameera bai taba fita da itaba a motarsa.” Jalila tai murmushin jin dadin yanda taga Ummy na farinciki. Ummy ta kara rike hannunta tace “Jalila nagode sosai, nagode har bansan yanda zan miki godiya ba, nasan kina shan wahala da kuka da Hassan.” Jalila ta sunkuyar dakai tace “Ummy ki daina fadar haka dan Allah.” Ummy ta jawota ta rungume tace “Jalila mu dauki junan mu a matsayin uwa da yarta, mu ajiye surukantaka a gefe.” Ta dagota tana kallanta tace “Ameera bata fiya zama muyi hira ba, saboda makaranta in ta tafi tun safe sai uku da rabi sannan islamiya karfe hudu, tana dawowa assignment da gajiya su hanata zama ayi hira, Sageer kuwa shine ma muke hira dashi shikuma kinga namiji ne, balle kuma ince Hassan.” Tai ajiyar zuciya tace “inaso mu dauke junan mu da mahimmanci.” Jalila ta daga kai cikin jin dadi tace “To Ummy insha Allah.” Haka suka karasa dinning, Ummy ta bude kulolin sannan tai murmushi tace “inama Hassan zai sauko muci abinci dukan mu?” Jalila ta kalleta, Ummy tace “later, mu bi abin a sannu, kar san zuciyata yasa mu rikita komai.” Jalila ta daga kai tare da cewa to Ummy. Ummy tace kizo ki kaimuku naku, Jalila tace “ke fa? Ke kadai zaki yi breakfast?” Tace “Sagir na nan nasan ya kusa fitowa.” Jalila ta zo ta zuba musu ta hau sama dashi. Tana tura kofar yana kokarin saukowa daga kan gado da alama tashinsa kenan, Jalila ta ajiye tiren sannan tace “Yaya ka tashi? Ya jikin?” Kallanta yai sannan yace “Ummy fa?” Ta dago tana cewa tana falo, ya mike ya nufi toilet. Tana gyara gado ya fito, dayan bangaren ya karasa yana tayata gyarawa, kallansa tai tace “yaya barshi, ka zuba abinci.” Bai tanka mata ba har ya gama sannan ya zauna ya mike kafa yace “zo ki zubamin, tunda kin damu sai naci yanzu.” Jalila tana murmushi ta matso ganin zata wuce yasa ya shiga kokarin janye kafarsa daya mike, ita kuma da sauri ta taho yana kokarin janye kafar ita kuma bata kula ba tai tuntube, tahowa tai zata fadi ta gaba, da sauri yasa hannu dan tareta, duk da haka sai da shima ya kai kasa, ta fada kansa kif. Hannunta na hagu ya bugi bango, da dan sauri tai kara, da sauri ya kalleta yace “Jalila? Menene?”4 Kallansa tai tace ” bigewa nai.” Harararta yai yace ” raguwa, shine harda wani kara haka? Ni da kika danneni fa?”1 Ta dan dago ta kalleshi, yace “sai yaushe za’a dagani?” Da sauri ta murgina gefe sannan tadan hade rai kadan, ya kalleta yace ” karki ma fara shirin yin pretending I won’t fall for it twice, ki zubamin inci ko ki dauke abincinki.” Jalila bata san sanda tai dariya ba tace “au in ban zuba ba sai kaki ci?” Yace “Ehem, kina wasa ne?” Tace “a’a ina na isa in hana dan Ummy abinci?” Ta fada tana zubamai a plate, kallanta yai bayan ta gama zubawa sannan ya fara ci. Itama ta xuba taja gefe tana ci, batai auni ba taji yace ” yaushe zaki koma?” Kallansa tai tace “Ina…..?” Sannan ta kara fadada dariyarta tace ” Gun Goggo?” Bai kalleta ba, da sauri ta tsame hannunta ta matso inda yake tace “Yaya da gaske?” Kallanta yai sannan yace “me kike shirin yi? Yanzun ma pretending din faduwa zakiyi dan in tare ki?”1 Kallansa tai tana dariya sannan ta matsa daga matsowar da tai tana cewa “wlh dazu faduwa nazo yi.” Bai kalleta ba, ta jawo kwananta kusa kadan tana cewa “Yaya yaushe zamu? Yau? Gobe?” Tea yadan kurba sannan yace ” yanda kika damu da Mahaifiyarki me yasa kike tsoro?” Har tayi shiru kamar bazata amsa ba kafin tace “a haka na taso, daga ni har Goggo bamu da daraja bare matsayi.” Idanunsa na kanta yana dan nazari kafin yace “ki binciki mahaifinki, banaji akwai igiyar auranta akanshi.”2 Jalila ta kalleshi tace ” To yaya, ni tsoro nake karma su kara dauke Goggon.” Kamar bazai tanka mata ba sai taji yace “sai ke ki dauketa kafinsu su dauke ta.” Da sauri ta kalleshi tace “kamar ya?” Abincinsa ya cigaba da ci, yana gamawa ya mike yai toilet, shiru tai tana nazari kalamansa wanda bata fahimta ba sam……… ******* Inna ce ta kalli Mumy tace ” waccen sokon yaje gun Jalilan?” Mumy tace “Inna wai dan Allah meyasa kike haka ne? Karfa ki manta mahaifin jikokinki ne.” Tai dan tsaki tace “ni tambayarki nake yaje ko baije ba?” Tace “wai tayaya zaije gidan sirikansa yana namiji?” Inna tace ” ta yaya zaije? Ki tashi ki sanar dashi in har shi ya kasa zuwa ya ja mata kunna ni zan yi abinda ya dace, tun kafin zance yakai gun matar Taura har yaje gunta” Mumy tace to ta mike ta sauko fuskarta a hade. ******* Zaliha zaune a cikin mota tana jiran Abba wanda ya fita siyo musu abu ya dawo, ta sa hannu ta dau wayarsa, ba security hakan yasa kawai ta bude ta shiga gallery tana kallan hotuna, ba wasu pictures bane a ciki yawanci na aikinsa ne, sai Matarsa da ta gani wace ta riga dama ta santa, sai Ameera data gani daga baya wace taga tsantsar kamar matarsa a fuskarta. Maza biyu ta gani sunsa kaya iri daya da alama basu ma san sanda aka musu hoton ba saboda kallon wani gun da sukeyi, dayan fuskarsa a hade ba alamar dariya da alama labarin ba burgeshi yai ba, dayan kuwa fuskarsa a sake take. Kurama wanda ya hade fuskar ido tai, waye wannan haka? Waye haka?????? 2 Nace kece inaji kika koma haka😏8 Ajiye wayar tai tare da kallan titi, ita ba tsarin soyayya a ranta ba kuma ta tunanin soyayya shine abunda ya dace da ita, abu daya ta sani a rayuwa ta ganta a katan gida a katuwar mota da waya mai masifar tsada, to komai ya biyo bayan wadannan….. Ameera ta kalli Aina’u tace “dan Allah kizo mu tafi tare.” Aina’u ta maida kanta ta kwanta kan gado tace “dan Allah kimin uzuri, kema kinsan bazan iya zama a gidan ku kamar da ba.”4 Ameera ta dan hade rai tace “kin san da haka me yasa ke da kike yar uwa har kika bari bare ta aureshi in har kinsan kina sanshi?” Aina’u ta mike ta zauna akan gado tace “Ameera ni kike so in kai kaina gunsa?” Tace “daga baya kenan, kema tun farko kinso rigima kinfi kowa sanin Halin Aunty Nana da yanda ta daura buri akanki, me zaisa ki wani fito da zancen wai kinasan yaya?” Aina’u ta kafe ta da ido cikin rashin jin dadin kalamanta, Ameera ta mike tace ” in ba so kike zumuncinmu yai rauni ba ki cire wannan zancen, ki ajiye shi a cikin dakin nan, na rokeki da Allah.” Ta karasa maganar tare da shiga toilet. Aina’u ta bita da kallo tasan gaskiya ta fada mata amma duk da haka sai dataji zafinta. Komawa tai ta kwanta cikin takaici.+ Ameera na fitowa ta kalleta sannan ta bude kofa ta fita falo ba tare da ta mata magana ba. *********** Jalila tana zaune a falo tana kara tunanin kalaman Hassan, haka ta sauko tana girkin rana amma tana kara maimaita kalaman a ransa, me yake nufi? In ta dauketa ta kaita ina to? Batama san Ummy ta shigo kitchen din ba sai ji tai ta tabata. Kallanta tai da sauri tace “Ummy!” Ummy tai murmushi tace “tunanin me kike haka? Kin kunna fanfo yanata zuba?” Jalila ta kashe fanfon da sauri tana cewa “wlh ban kula ba sam.” Ummy ta karaso ta dau cabbage ta fara yankawa tana cewa ” Hassan ne?” Da sauri tace “ba shi bane.” Tace “Nice?” Jalila ta tsame hannunta tana cewa “ke kuma Ummy?” Tace “eh mana, kinsan dan Adam ajizine, to ko Sagir ne?” Tace “wlh ba kowa Ummy kawai abu nake tunani.” Tai murmushi tace ” to ki rage yawan tunani haka, in kin kasa fahimtar abu ki tambayi wanda ya saki a duhu ko kuma ki nemi wanda zai fahimceki.” Kai ta daga cikin jin dadi tace “nagode Ummy.” Sannan ta ce “ina zuwa.” Da gudu tabar kitchen din ta haw sama, tana hakki ta shiga cikinn dakin, yana kwance kamar me bacci ta shiga. Kai ya girgiza kawai ba tare da ya kalleta ba, dan yasan in ba ita ba waye zai banko mai kofa haka? Jalila ta isa kusa dashi tana hakki tace “Yaya!” Idanunsa a rufe sai dai yadan yi motsi da hannunsa daya yake kan goshinsa, ta kara gyarawa sannan tace “Yaya dan Allah me kake nufi? Naga ni ba gida ba, ba yan uwa ba, in na dauketa in kaita ina?” Ta karasa maganar tana hakki. Bai bude idanunsa ba yace “ni zaki tambaya?” Ta sa gwiwowinta a kasa sannan ta sunkuyo jikin gadon tace ” yaya tunda kai magana na tabbatar da abinda kake nufi,, shiyasa naketa tunani har Ummy ta bani amsa.” Yanzu kam jin an anbaci Ummy yasa ya bude idanunsa ya dan kalleta, yace “tace me?” “In tambayi wanda ya sani a duhu in har bangane ba.” Ya gyara kwanciyarsa tare da juya mata baya yace ” ni ai banine na saki a duhun ba.” Mikewa tai ta dawo ta bangaren daya juya tace ” Yaya kaine fa kace in dauketa kafin su dauketa.” Yace “sosai haka nace.” Ya fada yana kallanta. Tace “to ai shine ban gane ba.” Yace “baki gane ba ko kwakwalwarki bata aiki yanda ya kamata?” Baki tadan turo jin wannan bakar maganar, ya kalleta yace “na nawa kike ci a skul? Na tabbatar double number kike dauka.” Fuskarta a dan hade tace “double din ai kala kala ne, ni na farko farko nake dauka.”2 Yanzu ma bai san bakinsa ya dan murmusa ba, sai kallanta dayai yace ” what’s the difference?” Tace ” mai daukan double number akwai yan 10’s akwai 20’s akwai 30’s har 50’s ma akwai kaga kuwa ba daya bane.” Kai yadan jinjina kadan sannan ya sakala hannayensa tare da maida hankali kanta yace ” and?” Tace ” mene?” Yace ” u.” Shiru tai tana dan kumburo baki sannan ta mike tace “Yaya ni danazo magana daban ka canza ta zuwa wani.” Hannunsa yasa yadan bugi gefen sa wajen saitin cikinsa, kallansa tai sannan tace “in zauna?” Da ido ya mata alamar eh, nan ta zauna tana kallanshi, ganin yanda ya kafeta da ido ne yasa tai saurin dauke nata idanun. Hassan ya kalleta yace ” me yasa kika aureni? Bayan baki sanni ba?” Dagowa tai ta kalleshi, yanayin idanunta suka canza, yace “am sry let me change the question, me yasa kika bari aka miki auren dole? Last time da na tambayeki baki bani amsar da ya dace ba.” Jalila idanunta ne suka ciciko tana kallansa tana wani murmushin wanda kana gani kasan na damuwa ne ta dan rangwada kai gefe kadan tace ” ya zanyi? Bayan rayuwar mahaifiyata na hannunsu.” Yace ” kin taba ganin rayuwar wani a hannun wani dan Adam irinsa?” Bakinsa tasan rufe da labanta kafin ta kalleshi tanna share hawaye tace “she is too sick, wanda hakan ya tsoratani, sunce in ban aminceba bazasu taimaketa ba, how can i…….” Hawaye ya cigaba da zubo mata, idanu ya zuba mata kafin yace “sai yaushe ne zaki gama?” Ta kalleshi tana hawaye tace “mene?” Da kai ya mata alama da fuskarta. Ta share hawayenta tana cewa ” na gama.” Gani tai ya mike ya zauna, sannan ya sa kafafunsa ta daya bangaren ya saukar kasa kamar mai shirin sauka sannan yace ” sai a fara canza mata asibiti, inda suma bazasu ganta ba kafin ta samu lafiya cikake.” Da sauri ta kalleshi, tace “Yaya!” Cikin wani yanayi ta kira sunan wanda kana ji kasan kira ne na jin dadi da ba zata.” Mikewa yai tare da bude wardrobe, gaba daya ita kam ta kame a zaune tana mamakinsa, a yanda ta ganshi bata taba tunanin mutumin nan zai mata rana ba, ta dauka itace ake san ta taimakeshi batasan itace wacce za’a taimaka ba, sannan batasan zai ata rana a dan karamin zaman da sukai ba, sai gashi tana ganin side na halayensa kala kala, wanda ta tabbatar zaman taren da sukai, su kwana tare su tashi tare shine yasa ta fahimci hakan, lalai taga hallaci daga gunsa, da gun Ummy. Batasan tayi nisa a tunani ba sai jitai yace “sai yaushe zaki fadama Ummy?” Tace ” bansan in kara mata damuwa…….” Da sauri tai shiru tare da juya kai, takowa yai a hankali zuwa inda take, yasa hannu ya juyo da fuskarta yace “Damuwarta?”1 Yawo ta hadiya sannan ta mike da sauri ta matsa daga inda yake. Hannu yasa a gefen cikinta ya jawota yana kallanta da idanunsa wanda suka canza. Gabanta ne ya shiga faduwa, tana kallansa. Dayan hannun yasa ya juyo da fuskarta saitinsa yace ” tambayarki nake.” Jalila idanuna suka firfito tace ” hmm.” Saketa yai yana neman fita, da sauri tasha gabansa tace “Yaya Please!” Kallanta yai yace ” in bakyasan in tambayeta ki fadamin meke faruwa?” Jalila ta kalleshi tace ” wlh bansani ba nima, ranan nan ne na fita naji Abba nadan fada.” Yace “yace me?” Jalila tace “Yaya dan Allah…..” Cikin zafi yace ” bani hanya” Jikinta ne yai sanyi ta kalleshi sannan ta sanar dashi abinda ya faru, ta daura da cewa “Yaya dan Allah karka nuna ka sani, dan Allah.” Gani tai a hankali idanunsa sun rikede, a hankali tadan matsa baya kadan, tana tsoron kar ya mazge ta. Gani tai ya dau key din mota a zuciye yayi waje. Biyoshi tai da sauri, sai taga ya fita waje. Komawa tai kitchen gun Ummy tana cewa “Ummy yahkuri na dade.” Ummy tai murmushi tace “bakomai, dama kinyi zamanki, Hassan ne ya fita?” Tace Umm kawai dan batasan me zata ce ba daga nan…… Haryasa key ya ta da motar sai ya kashe motar ya kwantar da kansa jikin kujera tare da rufe idanunsa. Idanunsa ya bude wanda yanzu ya kara kadawa yai jaa sosai, wayarsa ya dauko ya kira number Abba. Bayan sun gama yawo shi da ita yai parking din motarsa a gaban gidansu. Zaliha ta kira number yayarta a waya tace “Aunty mun dawo.”+ Tace “to bari in fadamai ya fito.” Hafiz ta kalla wanda ke faman hada takardu tace mai “Taura yana waje.” Wasu takardun ya dauka ya fita, Taura na ganinshi ya kalleta yace “ki shiga ciki bari muyi magana.” Tace “a’a ku gama magana ni ina jiranka anan, banasan rabuwa dakai yanzu.” Taura yai murmushi sannan ya fita, tsayawa sukai da Hafiz suna tattauna wani abun. Ringing din waya ne yasa ta kalli inda ya ajiye wayarsa, Eldest Son abinda taga an rubuta kenan. Eldest? Tuno hoton maza biyun nan tai, ta tabbatar wanda ya maze din nan shine babban, murmushi naga tayi sliding ta daga wayar, a kunnenta ta kara. Hassan shiru yai kafin can yace “Abba?” Zaliha tadan sake murmushi tace “Bayanan.” Gani nai Hassan ya bude kofar motar ya fita yace “waye” Gaban Zaliha ne ya fadi dan batasan ya akai ta tanka mai ba. Cikin tsawa yace “waye nace?” Bakinta ta shiga motsawa dan ta kasa magana, raban dataji tsawa ace ita akema har ta manta. Hassan cikin tsawa da karfin gaske yace ” kin fadamin ke wacece ko sai nazo nan na fasa miki baki.” Zaliha ta kalli inda Taura yake a rikice tace “Bari ba……..” Yace “ina mai wayar?” Da sauri ta bude motar ta taho inda Taura yake jiki na rawa ta mika mai wayar. Yana ganin sunan Hassan gabansa ya fadi, kallanta yai cikin takaici yace “Meyasa kika dagamin waya?” Tace “bansani ba nima….” Matsawa yai daga gun sannan ya kara wayar a kunnensa yace “Hassan!” “Hassan? How can u call my name as if ba abinda ke faruwa” Abba yace “Ya akai? Ina wani meeting ne Secretary gun ce ta dauka.” Hassan fuskarsa ta kara hadewa yace ” Wacece wannan? Abba me kakeyi a garin Abuja? Ba dai……” Kasa karasawa yai saboda kansa da yaji yamai nauyi, Abba a rikice yace “Hassan? Hassan jikin ne?” Idanunsa ya runtse cikin takaici yace ” Abba ko ka manta wacece Ummy a gareka? Ta yaya zaka yi mata haka?” Abba a rikice yace “Hassan ba haka bane ka tsaya kaji.” Cikin takaici yace ” Wallahi Wallahi Abba in dai ina numfashi a doron kasa bazan taba bari ka tozarta Ummy ba, sannan kayi gaggawar gayawa wannan yarinyar dan na tabbatar muryar yarinya naji, wallahi in har bata shiga hankalinta ba har cikin gidan ubanta zanzo in lahantata, in yaso a kamani.”4 Ya kashe wayar cikin takaici sannan ya saki wayar kasa cikin wani irin bakin ciki ya saki wani irin kara tare da tsugunnawa. Jalila da Ummy dake kitchen suka fito da gudu saboda karar da sukaji, da sauri Ummy ta karasa kusa dashi tace “Hassan! Menene?” Idanunsa na runtse bashi koma da alamar dagawa, Ummy ta kalli Jalila a rikice wacce itama gaba daya hankalinta ya tashi, tace “Jalila kira Sageer a daki.” Da gudu a juya, bata kwankwasa kofar ba saboda rikicewar da tai itama ta bude kofar. Yana kwance daga shi sai singlet da gajerar wando, yana ganinta ya mike zaune da sauri, juyawa baya tai da sauri tace “Uncle kazo, yaya…..” Ai yanajin tace yaya ya sauko da sauri ya zari goduwar riga ta fito, shima ya fito bai ma karasa sa kaya ba sai a falon. Yasan nanan a tsugunne duk yanda Ummy tai ta dagashi yaki, Sageer na zuwa ya dagashi da kyar, kallan Ummy Hassan yai idanun sa jawur kai kace garwashi. Ummy batasan hawaye na zubo mata ba tace “Hassan lafiya?” Idanunya rufe kawai dan takaici, wato ita tana nan ta dauka mijinta na aiki ashe mata yake bi? Tun yaushe ya fara? Badai zina yake ba? Sageer ya kalleta yace “Ummy akaishi daki.” Ta matsa tana share hawayenta, hannunsa ya zare daga jikin Sageer sannan yace “take care of Ummy zan karasa da kaina.” Sageer ya kalleshi har yai gaba, Jalila tabi bayansa da sauri. Ummy kam jingina tai da motarsa tana share hawaye, Sageer yace “Ummy muje ciki.” Kallansa tai tace “Sageer kaji karar da ya saki? Bai tabayin irin haka ba, ina murna ya fara samun sauki, Sageer meke shirin faruwa?” Sageer yai shiru tausayin Yaya da Ummy ya hanashi cewa komai, ta share hawayenta sannan tace ” Sageer kaje gun Dr kajii ko da matsala.” Sageer yace “To Ummy, amma muje ciki ki zauna tukun na.” Hassan na shiga ya zauna a kasa jikin gado ya jinginar da kansa a jikin gado. Jalila ta tsaya a bayansa ta rasa ta ina zata fara mai magana, ta dade a tsaye dan tayi wajen minti ashirin kafin ta juya jiki a sanyaye, hannu yasa ya riko hannu ya riko hannunta ta baya. Juyowa tai da sauri tana kallansa, haka suka tsaya hannunsa na rike da nata ba kuma wanda yana wani magana, har na tsawon minti goma sha biyar, kafin ta tsugunna jin kafarta na dan zafi, ji tai ya saki hannunta. Kallansa ta sakeyi sannan tace “Yaya jikin ne ko wani abun ne ya faru?” Bai kalleta ba, sai dai yanzu ya mike daga kasan da yake ya zauna akan gado. Sannan ya kalleta, idanunta na kansa ta kara cewa “yaya!” Kallanta yai sannan yace ” are u worried about me? Or are u scared?” Ta kalleshi tace “Yaya dan Allah kadaina min tambayar nan, dan bansan me zance ba.” Yace “okay, jeki to.” Tace “naam?” Yace “ba fita zakiyi ba na tsayar dake?” Kallansa ta sakeyi tace ” Yaya.” Kallan daya mata ne yasa ta mike tai waje jiki a sanyaye. Zama tai a falon tana tunanin abinda ya faru yanzun nan, ya riketa sannan yace jeki, mekenan? Itakam tana kasa ganeshi wani sa’in. ********** A Abuja kuwa Abba na gama waya ko kallan Hafiz baiyiba ya fada motarsa yai gaba hankali a tashe, kayansa kawai ya dauko a dakinsa sannan yai check out ya fito tare da ajiye motar. Airport ya nufa dan hankalin sa a tashe yake, yana zuwa yai sa’a akwai jirgin da zai tashi karfe 3:00pm zama yai yana jira sai dai zuciyarsa ta kasa nutsuwa. Lokaci nayi kuwa ya mike da sauri, ba nisa daga Abuja zuwa kano a jirgi kan kace me sai gasu sun sauka. Bai tsaya neman Mamman ba kawai ya hau taxi zuwa gida. Ummy na kwance a falo, tayi shiru tana tunanin Hassan, tana jiran dawowar Sageer daga gun Dr. Jin an taba kofa ne yasa ta mike da sauri dan ta dauka Sageer ne. Da sauri ta bude kofar tana cewa “Sageer me Dr din ya…….” Ganin Abba yasa ta tsaya da maganar tana kallansa, kafin tace ” Sannu da zuwa.” Kallanta yai jiki a sanyaye yace “Yauwa, sannan ya fara kokarin shiga ciki.” Hannu tasa ta amshi jakarsa tai gaba fuskarta ba walwala. Kallan falon yai sannan ya kalli hanyar sama, kafin yace “ina mutanen gidan?” Tace “Ameera tace sai jibi zata dawo, Sageer ya fita.” Yace “Jalila fa?” Tace “Tana sama.” Yace “Hassan fa? Ya jikin nashi?” Kallansa tadanyi kamar zata fadamai sai tace “da sauki.” Sannan tai gaba. Ba abinda yakesan ji ba kenan, so yake yaji ko wani abun ya faru dashi, sai dai baisan ta ina zai fara ba shiyasa yai shiru. Ummy tana ajiye mai jaka ta juya zata fita, har takai kofa yai sauri yace ” kinje taron kuwa?” Kallansa tai tace “banje ba.” Yace “Naga kamar bakya farinciki da dawowata.” Wani murmushin takaici tai kafin tace “banasan musu ko fada dakai daga dawowarka, mu bar maganarnan, kai wanka kafin ma shiryama abinci.”1 Kallanta yai hartabar dakin, zama yai a bakin gadon sannan ya sa hannayensa ya rufe fuskarsa. Jalila kam ganin hankalinta ya kasa kwanciya yasa ta mike ta kara turo dakin a hankali. Yana zaune yasa farcensa yana karzar bayan hannunsa, idanunsa nakan bango yana tunani, idanunsa da fuskarsa a hade suke. Jalila ta shigo ciki, har taje kusa dashi bai san tazo ba, hannunsa ta kalla taga yana ta karza har yaji ciwo ga jini nan. Kallan tsoro tamai sannan tasa hannunta agun dayake karza, tana kallansa. Dagowa yai ya kalleta sannan ya kalli Hannunta sannan ya kalli nasa hannun, sake kallanta yai sai dai yanzu idanunsa sun canza. Idanunta ne suka ciciko tace “Yaya wani abun ne yafaru ko? Menene dan Allah? Ko akan abinda na fadama ne?” Hannunsa ya janye sannan ya mike daga kan gadon zai nufi toilet. Tace “kayi hakuri dan Allah, laifinane dana sani ban tsaya naji abinda suke cewa ba, sannan dana sani ban fadama abinda ke faruwa ba, kayi hakuri dan Allah, it’s all my fault.” Tafada tare da share kwalla. Juyowa yai ya kalleta kanta na kasa, tana share hawaye, ya dade yana kallanta kafin yace ” ba akanshi bane, sannan in ma shine ba laifinki bane laifinane tunda ni na matsa miki sai kin fadamin.” Kallansa tai sannan tace ” akansa ne ko?” Kai ya girgiza mata alamar a’a sannan ya shiga toilet. Kallansa tai sannan tai ajiyar zuciya tace “Goggo ya zanyi? Inaji nayi laifi ga wanda zai taimakeki, na tambatar da ban fadamai ba kila yau zai dauke ki daga asibitin sai dai da alama wannan bakin nawa ya ja min…….. ************** Inna ce ta kalli Dady tace “Abakar!” Kallanta yai sannan ya amsa, tace ” sai yaushe zaka gidan Jalila?” Yace “so nake sai Taura ya dawo, naji ance yayi tafiya.” Tace “meye damuwa ta da haduwarka da Taura?” Dady yai kasa dakai yana cewa “ai kinga ya kamata mu sake mai godiya da taimakon daya mana.” Inna tace “wace godiya bayan abinda muka aikata yana neman wargajewa saboda shirmanka.” Dady yace “Inna ni……” “Dalla rufemin baki, so kake kace ba laifinka bane? Ka tabbatar ka lalabata da mijin nata, dan kafi kowa sanin dayan plan dinmu da mukesan sake bude wani branch dinmu, ka kuma tabbatar inba da taimakon Taura ba abin nan bazai yiwu ba, ya kamata kasan abinyi, kafin ni insa hannu, kasan in nasa bazata ma kyau ba.” Dady yace “To inna.” Ta kalleshi sannan tace “tashi kaje, ka kuma tabbatar kaje gun Jalila, dan a yanda na ganta da yaran nan ina tsoro karta fadamai komai, wannan yaran idanunsa kadai zaka kalla zaka fahimci ba kara a idanunsa balle ya mana.” Yace “to sannan yai waje. Shiru tai tana sake wani tunanin, yanzu me ya dace tayi??????2 (Nace ” kya tambaye ni😏”) ********* Sageer ne ya kalli Dr yace “kana nufin hakan alamu ne na samun nasara? Dr ya kalli Sageer sannan ya jinjina kai yace “Sageer kasan Hassan yana dauke da trauma ne wanda shikadai yasan abin da kuma faruwar abin, tunda abin ya faru ka taba gani yayi ihu ko fada da karaji?” Sageer yace “a’a sai dai zafin rai, rashin magana da kadaicewa, sai kuma rashin nuna emotion na farin ciki ko na tsantsan bakin ciki a fuskarsa, a koda yaushe fuskarsa a hade take wanda yake nuna alama ta bakin ciki ba alama na canji.” Dr yace “Good, yau kuma fa?” Sageer yace ” yau yayi kara sannan kana kallansa kasan ransa a bace yake wanda bacin ran ne da alama yasashi yin karan.” Yace “Very Good, ka gano improvement?” Sageer yace “na fahimta Doctor, a da yana fada sai dai bawai da jikinsa yakeyi ba, ko zuciyarsa yanayi ne da fuskarsa da bakinsa.” Yace “Very Good ka fahimceni yanzu?” Sageer ya daga kai cikin gamsuwa da jin dadi yace “nagane Dr, na kuma gode sosai. Saukowa kasa tai, tana matatakalar karshe, taha an bude kofar dakin Ummy, tsayawa tai tana jira Ummyn ta fito sai ta karaso. Ganin Abba tai ya fito daga dakin, mamaki ne ya kamata da sauri ta karaso dan yana fitowa suka hada ido, tsugunawa tai ta gaisheshi. Kallanta yai bayan ya amsa yace ” Jalila Hassan yana sama ne?” Tace “eh.” Da sauri ya wuce ta ya nufi sama, bata kawo komai a ranta ba kawai ta wuce falo. A kitchen taji Ummy nan ta nufi gunta, tanashiga tace “Ummy ashe Abba ya dawo?”+ Ummy ta juyo tace “eh, ya jikin Hassan din?” Jalila tace “da sauki.” Ta fada tare da karasawa gunta tana neman taimaka mata gun rufe kullar da ta gama zuba ma abinci.” Ummy tace “dauki abincinku la’asar har tayi ba wanda yai lunch.” Ta amsa da to. Abba kam dakin ya karasa yai knocking din kofar, Hassan daga ciki ya fito daga toilet kenan daure da alwala ya bude kofar. Tsayawa sukai yana kallansa hannunsa rike da kofar, fuskarsa kuwa ya kara hadeta tamau, Abba ya kalleshi yace ” Hassan baka ganni bane?” Hassan ya saki hannun kofar baice komai ba ya wuce ciki. Abba ya shiga dakin sannan ya maida kofar ya rufe, yace “Kayi mamakin ganina ko? Bayan dazu mukai waya.” Hassan bai kalleshi ba balle yai magana, Abba ya zauna akan sofa sannan yace “Hassan!” Hassan ya juyo ya kalleshi da jajayen idanunsa, yace “How can u? Of all people?” Abba ya runtse idanunsa cikin takaici sannan ya mike ya kamo hannun Hassan suka zauna akan kujerar. Hannayensa na cikin na Abba yake kallansa, Abba yai shiru kafin yace “Hassan.” Hassan ya kalleshi cikin takaici sannan ya zare hannunsa daga nashi yace “Zina kake?”2 Abba cikin mamaki ya kalleshi yace “Hassan wani irin magana kakeyi haka? Taya zaka cemin ni mahaifinka? Ka kalleni kace zina nake?” Hassan ya mike tsaye tare da dan matsawa daga inda yake yace ” Ni kaina ina fatan hakan ya zama laifi ne na aikata.” Abba yai shiru yana kallan Hassan, gaba daya ma ya rasa ma mai zaice. Muryar Hassan yaji yace “wacece?” Abba yai shiru tare da shafar fuskarsa, Hassan ya juyo ya kalleshi cikin bakin ciki yace “Budurwarka ce?”1 Abba yace “Hassan ni kaina ina mamakin kaina, wai nine nakesan……..”1 So? Hassan ya kalleshi ya sake cewa, so? Abba so kace?”2 Abba yace ” Hassan wai me yasa kake kokarin juya kalamai na zuwa abinda ranka ya raya maka?” Hassan cikin dan daga murya yace “ta ya bazan fassara ba? Ta yaya Abba zaka kalleni kacemin wai so? Ta yaya zaka furtamin kalmar so, sannan kalmar san bawai akan Ummy kake yinta ba, ta ya……..”1 Kasa karasawa yai saboda numfashinsa dayaji yana seizing. Abba ya mike da sauri yazo kusa da shi yace “Hassan menene?” Hassan ya zare jikinsa daga rikon da Abba yamai ya dan ja baya cikin takaici yace “ni danka ne, banida ikon hanaka abinda kai niyya, sai dai wlh Abba kamar yanda na fada in dai had ina numfashi bazan taba bari ka tozarta Ummy ba.” Kofar dakin aka bude, Abba ya kalli kofar shikam Hassan kai ya juya cikin takaici dan yayi tunanin Jalila ce. Muryar Ummy yaji tace “Hassan!” Juyowa yai da sauri ya kalleta, Ummy ta share kwallarta data zubo mata sannan ta matso kusa dashi dariya yaga tanayi tana share hawayenta, tace ” Hassan yanzu Sageer ya kirani, Dr yace sauki ne ke samuwa a gareka, ya gama min bayani naga bazan iya hakuri ba sai na ganka.”1 Ta kara share hawayenta tace “Hassan bansan yanda zan kwatanta maka dadin da nakeji ba.” Cikin takaici ya kalli Abba sannan ya kalli Jalila wacce ta juya ta fita, Hassan ya kalleta yace ” Ummy?” Tace ” fadanku da Abbanka a kaina?” Ya kalleta cikin tausayawa, tai murmushi tace “karka damu Hassan bakomai, ko ka manta ba mace daya aka halarta ma namiji ha aura ba? Ta yaya zaka nemi mahaifinka ya zauna da mahaifiyarka ita kadai? In mukai haka bamuyi san kai ba? Ko baka ga na fara tsufa bane?” Idanunsa ya rufe cikin takaici yace ” ya wani irin zance kikeyi Ummy? Waye zai ga Ummy yace ta tsufa?” Ummy tai dariyar takaici tace “ba wani kai dai sankai zakai, Hassan gashi nan na fara gani.” Yace “me?” Tace “samun saukinka mana, rabon da kayimin magana mai tsayi haka har na manta, yau gashi nan kana min magana.” Shiru yai kawai yana kallanta, Ummy cikin jin dadi tace “Kar kasa komai a ranka, ka manta da maganar da kukai yanzu, kayi kokari ka dawo Hassan dinka ma da, I really miss that Hassan.” Baice komai ba sai kallanta kawai da yakeyi, Abba ne ya share kwallar data dan zubo mai, sannan yai waje da sauri. Ummy ta kalli Hassan tace “Please ka kula da matarka, wannan shi kadai ne abinda ni nakeso, kaji?” Hassan yai shiru, ta juya tai waje. Jalila na zaune a kasa a falo ta sa kanta akan gwiwowinta, gaba daya abinda ke faruwa ya sa tausayin Ummy ya sa ta zubar da kwalla, wannan wace irin macece? Ita lafiyar Hassan ce a gabanta bawai abinda taji ba? Tana kallan Ummy ta fita, mikewa tai ta shiga dakin, gani tai har ya tada sallah. Nan itama ta wuce tai alwala tai sallah, ganin bashida niyar mikewa daga kan sallaya yasa ta fito daga dakin. Abba kam daki ya shiga ya shiga zagaye dakin cikin takaicin abinda zuciyarsa take sashi aikatawa, wani irin butulci ne hakan yake shirin yi? Ummy ce ta shigo dakin tacemai, yallabai ka fito kaci abinci, ko in kawo ma nan?”5 Jiki a sanyaye yace “muje can din.” Ya zauna akan kujera ta zubamai sannan ta turamai abincin gabansa, sannan ta juya tai daki. Da kallo ya bita dan baisan ta ina zai fara magana ba, shi yanda takeyi kamar ma batasan me ake ciki ba shine ya kara tsoratashi, dana sani ya kara kamashi.2 Jalila kam, sai yamma liss ta samu taci abinci kadan, sam ba fuska agun Hassan, dan ko kallanta baiyi ba bare ta samu damar yi mai magana. Haka tai tayin abinda zatai har dare, shikansa Abba har dare bai samu damar yi mata magana ba. Bayan sallar Magrib ne Sageer zai shigo yaga motar Dady. Nan yasa aka budemai yai parking din motarsa, Dady ya fito suka gaisa, Sageer ya jashi ciki. Yau gidan tsit ba dadi, Hassan na daki, Jalila na falo a kan carpet a kwance tana latsa waya, Ummy na falo shi kuma Abba yana daki. Sageer ne ya shigo ya kalli Ummy yace “Ummy dadyn Jalila me yazo.” Mikewa tai da sauri tace “ka shigar dashi falon Abba” Nan Sageer ya shigo dashi yai bangaren Abba. Ummy ta bude dakinsu ta kalli Abba dake zaune yayi shiru abin duniya ya dameshi tace “Abban Ameera ka fito Baban Jalila ne yazo.” Abba ya mike tare da cewa to. Ta juya ta fita, Sageer ne ya karaso yace “Ummy na kaishi.” Tace “Sageer dan hau sama kama Jalila magana, bari na shirya abin sha.” Yace to, sannan ya hau sama har zai kwankwasa kofar yaji motsi a falon, nan ya juya ya falon, a kasa ya ganta tana ta latse latsen waya, tv din ma ba’a kunne take ba. Kallanta ya tsaya yana yi cikin tausayawa, sai dai ya taya yayansa murna ta fara samun lafiya, sai dai shikam tausayin kansa yakeyi, anya zai iya san wata kuwa? Jalila ce ta juyo, ganinsa tai a tsaye ta mike zaune tana kallansa, yace “ashe kina nan?” Ya dan sosa keyarsa. Tace “Eh.” Yace “Uhmm dama Ummy ce tace nazo na fadamiki Dadynki yazo.” Kallansa tai cikin mamaki tace “Dady?” Yace “eh, yana fallon Abba.” Ya fada tare da juyawa. Jalila ta mike gabanta na faduwa, me yazo yi? Badai wani abin bane ya samu Goggon ta? A rikice ta shiga dakin tana neman hijab dinta, gashi a gabanta wanda ta ninke bayan tayi sallah amma tsabar hankalinta baya jikinta sam ta rasashi. Hassan dake zaune yana kallanta shine yace “menene?” Matsowa kusa da shi tai kamar dama jiran kiransa takeyi, tace “Yaya! Dady ne yazo, baka tunanin ko wani abun ne ya faru da Goggona? Ko kuma wani abun suke shirin yimata?” Ganin yanda ta rikice ne yasa yace “Dan yazo shine kika rikice haka?” Tace “Yaya bansan……..” Tai maganar cikin wani irin murya mai raunin gaske, da yatsarsa ya nuna mata hijab din sannan yace ” a haka zaki?” Ta kalleshi alamar rashin fahimta, yace ” bazaki daidaita kanki ba?” Tsayawa tai tana ajiyar zuciya wai tana calming din kanta, baisan yanzun ma bakinsa ya motsa ba saboda yanda takeyi. Yace “yimin magana naji.” Tace “Yaya!” Yace “sake.” Tace “Yaya.” Yace “bai yi ba.” Baki tadan turo tace “dazu amma inasan maka magana ai hade rai kayi.” Ya kalleta yace ” ni yanzu inaji damuwar dake gabanki tafi tawa, ke mahaifiyarki zaki ceto wace take hannunsu, ni kuma i am confidence akan I will protect mine.” Tace “ni ma…….” Sai kuma tai shiru dan tasan she is not confident.1 Yanzu ma bakinsa sai da ya sake motsawa yace “jeki, bari na jira naga yanda zakiyi.” Ta kalleshi tace “yaya zakazo?” Yace “ina kenan?” Tace ” gun Dady, tsoro nakeji kar ya sani abunda banzan iya bijerewa ba.” Kafada ya daga mata alamar ba ruwansa. Jalila tai raurau da ido tace “Yaya Please!” Samun kansa yai da kallanta cikin wani yanayi sannan yace “ki wuce kije ko?” Ta dau hijab jiki a sanyaye ta fita………. Da kallo ya bita har ta fita daga dakin, yabi kofar da kallo.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE