JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI
JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI
JARUMI DAN BAIWA
Yaro ne da bai fi shekara tara ba ya
ratso ta tsakiyar kasuwa a guje yana
ihu yana waigen bayansa kai da
ganinsa kasan gudun ceton rai yake yi,
amman ko da mutane suka ga wanda yake biyo bayansa
aka rasa wanda zai čeceshi.
Wanda ya biyo yaron wani makeken kato
ne mai kira mutanen farko rike da wata zabgegiyar
takobi tsirara, babu komai a jikin wannan katon ila
bujen wando gami da takalmin fata farde a kafarsa a
kanshi kuma akwai karamin zagayayyen rawani a
goshinsa kuma an masa bule da zabibi kana ganin
wanan katon kasan ba indiye ne. Www.bankinhausanovels.com.ng
Badakaren na gidan sarki, haka ya rika baje
hajojin mutane yana bangaje jama’a yana kuma tattake
musu dukiya yana bi takansu amma sabi da tsoron
masarauta da ake yi an rasa wanda zai yiwa katon
magana. Haka suka ci gaba da zagaye kasuwa shi
yaron yaki kamuwa haka kuma katon bai daina binsa
ba su kurda nan su kurda can su fita su shiga wannan
sakon haka sukaita yawo a cikin kasuwar suna yiwa
jama’a barna da dukiya da suka kasa.
Shi dai wannan yaron da wannan katon
yake bi ba wani abu ya aikata ba face satar gurasa a
gidan sarkin kasar ta Hindu saboda yunwa da take
damunsa
yaga ana rabawa bayin gidan sarki gurasa a hannu su
kuma sun kafa wani dogon layi suna bi daya bayan
daya ana basu.
Da wannan damarya bi ya daki idanun
masu rabawa ya kuma kai cikin gidan ya faki idanun
mai raba gurasar ya suri guda daya, ashe sarki yana
zaune a gefe guda yana kallon shigarsa da lokacin
daya dauki gurasar da ake rabawa bayi kuma a kirge
take ta bayi dari uku ce daidai babu dadi babu kari
kuma an kawo ne domin a ciyar da bayin da suka yini
suna aiki a gonar sarki.
Kuma an basu da zumar suna gama cin
gurasar dai-dai da aka basu a maida su gonar sarki su
ci gaba da aiki, ai kuwa koda sarki Mazwan yaga
wannan yaron ya suri gurasa daya ya zura da gudu
zuwa wajen gidan sarautar sai ya dakawa wannan
katon tsawo yace masa Www.bankinhausanovels.com.ng
Maza ku bi wannan yaron ku saro min
kansa kuma ku daddatso sassan jikinsa a kawo min zan
ciyar da kadojina Kafin sarki Mazwan ya gama rufe
akinsa tuni wannan katon ya zare takobinsa.şuka kasa
tsere da wannan yaron.
Haka suka ci gaba da gudu yaron yana
gudun ceton ransa a cikin kasuwa da zarar ya tsagaita
ya waigo sai yaga katon ya kusa cin masa sai ya kuma
azama wajen gudu.
ana cikin
haka sai yaron ya yi tuntube da wani kututturen gunki
ya fadi kasa kafin ya mike tsaye ya ci gaba da gudu
tuni katon ya cin masa ya zo ya kansa ya raba
Rafafunsa biyu.
Ya kalli yaron cikin tsantsar rashin iman ya
tofa masa yawu a fuska sannan ya daga takobinsa
sama zai datse masa kai kwatsam babu zato babu
tsamani sai narkeken katon ya ji an daki kirjinsa
saboda karfin dukan sai daya yi tsalle sama ya fado
kasa akan wata rumfar kara a cikin kasuwar.
Rumfar ta ruguje ya baje akanta a fusace
narkeken katon ya mike tsaye zumbur koda ya waiga
don ganin wanda ya yi masa wannan dukan sai
mamaki ya turnukeshi ya kuma sake fusata ainun.
Ba kowa ya gani ba face wata yarinya yar
kabilar indiyan daji tana tsaye ta rataya kwari da
bakanta a bayanta kuma ta dunkule hannayenta alamar
a shirye take ta fafata da katon duk da cewar shekarun
yarinya basu haura takwas ba.gaba daya mutanen da
suke cikin kasuwar sąi wannan al’amarin ya daure
musu kai suka cika da mamaki kuma suka taru waje
daya suna kallon ikon Allah. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kuma narkeken katon ya taso mata, da
dukanin karfinsa ya kawo mata sara akan kafadarta da
Zumar ya tsargata gida biyu amma sai ta gocewa saran
cikin bakin zafin nama takobin tasa ta sari iska.
Nan ya kuma juyowa ya KawO Wani
saran tuni tayi tsale sama ta dawo ta dake shi da
gwiwar hannunta ta baya, take kashin kafarsa ya karye
ya kurma wani ihu ya durkushe a kasa, ai kuwa sai
gaba daya jama’ar da suke wajen suka bushe da
dariya.
Ko da wannan narkeken katon yaga ana
masa dariya kuma gashi wannan karamar yarinya ta
karya shi sai ya yi wuf ya dauko wani kaho daga cikin
aljihun bujen wandonsa ya soma busawa da karfi,
faruwar hakan ke da wuya sai ga wasu dakaru kimanin
irinsa su arba’ in sun shigo cikin kasuwar da gudu suna
rike da goruna da takuba a hannunsu nan suka hau
dukan jama’a suna tattake dukiyoyinsu.
Koda ganin haka sai wannan yarinyar
indiyan daji tayi wuf ta kama hannun wannan yaron
barawon gurasa ta jashi da gudu suka nausa zuwa cikin
daji shi kuma yaci gaba da binta ba tare daya san inda
za su ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka suka ci gaba da gudu a cikin dokar
daji yaron yabi ya gaji kawai yana gudu baya sanin
wajen da yake saka kafarsa, ita kuwa yarinyar indiyan
daji sai tsale-tsale take daga nan zuwa can kana gani
kasan tasan sirrin daji, haka ya hakura ya daure yaci
gaba da binta duk ya galabaita yasha wahala ya fita
hayaccinsa.
sunansa Salhim ya kasance maraya tun yana jariri aka
kashe iyayensa a wata rana da sarki MaZwan ya turo
dakaru karban haraji a hannunsu koda dakarun suka zo
suka iske iyayen salhim basu da kudin da za su iya
biyan haraji sai suka rufe su da duka har da suka sumar
da su.
A lokacin salhim yana ta tsala kuka irin na
jarirai an ajiye shi akan harawan doki amma saboda
rashin imani na dakarun ko kallonsa basu yi ba. Da
haka ma sai ci gaba da dukan iyayen salhim sukayi
suka shiga cikin gidan suka kwashe duk abinda yake
cikin
gidan suka kuma cinnawa gidan wuta suka yi
tafiyarsu.
Kafin iyayen salhim su farfado daga suman
da suka yi tuni wuta ta kama ko ina a cikin gidan babu
ta wajen da za su iya bi su fita har su tsira haka suka yi
ta dawurwura a cikin wajen har hayakin’ wutar ya
kuma bugar da su suka fadi a wajen wuta ta kama su
suka babbake suka cinye. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kuma salhim wani ikon Allah da yake
ciyawar danya ce; kuma a jike take da ruwa sai taki
kamawa da wuta, bayan komai ya lafa shima yaci gaba
da tsala kuka abinsa.
A waje mutane sun taru jingim suna ji suna
gani haka gidan ya cinye kurmus ya zama toka amma
ba a samu wanda yaje dan kai musu dauki ba domin