JIDDATULKHAIR CHAPTER 11 BY KHALISAT HAIDAR

JIDDATULKHAIR CHAPTER 11 BY KHALISAT HAIDAR

 

 

Mai Anguwa na kallon Iliya dake maxurai yace “Kai yanxu Iliyasu baka da masaniyar inda wannan yarinyar take?” cikin murya irin ta ‘yan da6a yana nuna Hansai yace “Wllh wancan munafukar matar tasan inda take, kuma ni dama daga ita har wancan mutumin banxan na basu kwana daya su fito min da ita, matata ce fa, abinda har na bada sadaki me ya rage? Akuyar baabata fa na dauka na kai kasuwa na siyar na kai ma wancan mutumi da wasu kattin banxa a wajen kudin sadakina….” Mahaifin Iliya dai ba baki sai idanuwa, don kamar ma tsoronsa yake, Mai Anguwa yace “Toh yanxu idan ba a ga yarinyar nan har bayan kwana dayan da ka bada ba ya kake son ayi iliyasu?” Yace “Hansatu ta biyani duk hatsin da na dinga kawo mata a maimakon na kai ma baabata, ba hatsi kadai ba, lissafi xa mu yi tiryan tiryan ta biyani duk abinda na kashe sannan ta bani kudin sadakina dubu sha uku da kudin gaisuwa da sa rana da na kai, idan ba haka ba to wllh xan yi ta’asa, ai ba yau muka saba xaman kurkuku ba, banda yanxu da na fara gwangwan daga garin nan xuwa legas ai mu bama wata uku bamu leka gidan yan sanda ba daga nan mu garzaya kotu sannan gidan kaso, ko da mune da gaskiya ko mu ne bamu da gaskiya wannan ba sabon abu bane” Mai Anguwa ya kalli Hansai dake xare ido duk hankalinta a tashe sai xufa take yace “To ke kin ji Hansatu, lissafi yace xa ayi” kasa cewa komai tayi xufa sai karyo mata yake ta ko ina, yo ba gwara ya kasheta ba da ta ta6a kudin da Abuturrab ya bata, tabbb…. Mai Anguwa yace “Kai xuwa yaushe xa a baka kudin naka Iliyasu?” Ya gyara xama yace “Ae kafata kafar kudina, baxan bar wajen nan babu su ba, idan ko ba haka ba wllh wllh xan yi aika aika” Mai Anguwa ya kalli Hansai da jikinta ya dau rawa ta kasa cewa komai, Abuturrab ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yana kallon iliyan yace “Nawa ne gaba daya kudin naka?” Yace “Al-qur’an kudi na ya kusa dubu dari da wani abu, abinda duk xuwana legas sai na kawo mata garin alabo da gawayi ga hatsi da nake siya mata kwana biyu kwana uku… Sannan ga sadakina dubu sha uku na tinkiyar babaata, ga dubu biyar kudin gaisuwa da sa rana” Calmly Abuturrab yace “Kana da account?” Iliya yace “Aa amma abokina Kallamu na da shi, gaya can a xaune” Abuturrab yace “To ka kirasa ya bada account din” Iliya ya kwalo ma abokin nasa kallamu kira, Kallamu na karasowa Abuturrab yace “Account number dinka xaka bada” sai da ya dubo a waya sannan ya nuna ma Abuturrab, cikin few minutes Abuturrab yayi masa transfer din dubu dari da ashirin, sannan ya kalli Kallamu yace “Xa a maka alert na dubu dari da ashirin yanxu” Wani kara wayar yayi alamar shigowar alert din, Abuturrab ya amshi wayar ya duba sannan ya mika ma mai anguwa da sauran mutanen wajen duk suka ga dubu dari da ashirin, Hansai ta fashe da kuka sosai, Kawu Jibril kuwa Hamdala ya dinga yi a ransa yana sauke ajiyar xuciya, Hansai na kallon Abuturrab cikin kuka tace “Allah ya saka da alkhairi Alhaji, ka min taimakon da babu wanda ya ta6a min wllh a duniyar nan, nagode nagode, Allah ya kara maka budi da dukiya me yawa, wayyoo wani irin godiya kuma xan maka Alhaji” Abuturrab ya ki bata amsa dai a fili, Iliya ya mike yace “Toh amma fa duk ranan da jiddah ta bayyana wllh sai na aureta don na kwallafa rai, an kuma sa min ran ne, wllh wllh sai na aureta ko kuma in dauketa kawai in wuce legas in je a daura mana auren a can, so nawa aka yi hakan” Sake baki duk mutanen wajen suka yi suna kallonsa, ya kakkabe wandonsa ya kara gaba yana cewa “Sai in bani ne Iliya d’an me karfi ba” abokansa duk suka taso suka maya masa baya suna hailing dinsa, Mahaifinsa Malam Kabiru ya sauke ajiyar xuciya cikin sanyin murya yace “Abu me sauki da xa a samu wani ya auri yarinyar nan kawai, idan kuwa ba haka ba wllh xai aika abinda ya fada, kwakwalwarsa ya ta6u da dadewa mu kuma bamu da halin kai sa ko ina a dubasa, har cewa aka yi mu kai sa dawanau a kano to ina kudin?” Wani mutumi a wajen yace “Alhmdlh abinda xan fada kenan ka riga ni Malam kabiru, gwara kawai a aura mata wani tunda uwar ma tace ba ji take ba yarinyar, kun ga tana dawowa sai a kai ta dakinta kawai…” Abuturrab yace “Akwai wani yaro na, ina son nema masa aurenta yanxu” Kallonsa duk suka yi, Mai Anguwa yace “Toh in dai kasan halinsa ina ga wannan ba matsala bace amma kafin nan ya kamata ka gabatar mana da kanka…” Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace “Ni sunana Aliyu Usman Umar… An haifeni nan cikin garin kaduna, ni matukin jirgin sama ne” Sake baki duk suka yi suna kallonsa kamar ranan suka ta6a ganin me tukin jirgin sama, yace “Gidan iyayena na nan Malali…” Mai Anguwa yace “Maa sha Allah Aliyu, to amma a ina kasan ita wannan yarinya da ake magana a kai?” Hansai ta amshe tace “Wllh daga siyan awara muka sa6a da shi, customer na ne shi da dadewa, da motarsa yake xuwa yyi parking ya siya har na dubu biyar dubu goma yana siya, toh shine jin rasuwar mai gidana sai ya kawo mana kudi dubi hamsin dubu dari, ta haka muka saba muna mutunci sosai da shi” Mai Anguwa yace “Ikon Allah” Abuturrab dai bai ce komai ba, Mai Anguwa yace “Toh amma shi wannan yaron da kake son hada yarinyar da shi wanene, sannan a ina yake?” Abuturrab yace “A kano yake, yana aikace aikace ne a airport din kano…” Hansai tace “Shi ma jirgin yake tukawa?” Ya girgixa kai yace “Aa…” Wani datijo dake xaune wajen da baxai wuce shekara sittin da takwas ba yayi gyaran murya yana taunan goransa yace “Amma fa wata kusan ya fi wata kusan nake ji ai… Tunda haka ne ni yanxu xan bada sadaki sai a daura min aure da ita wannan yarinyar….” Da mamaki Abuturrab ke kallonsa, can ya girgixa kai yace “Haba Baba ai addininmu ma bai ce haka ba, da taxara sosai tsakaninku da yarinyar nan….” Dattijon ya hade rai ya katse sa yace “Toh kai idan taimako kake son yi ka aureta mana kai da babu taxara me yawa tsakanin ku, shi fa wannan yaron da kake son hadata da shi nasan ba kowa bane d’an goge gogen iyapot ne, ni kuwa kowa yasan babu rashin ci babu rashin sha a gidana, matana uku ko wacce kuma tana da yara shidda shidda, shi me anguwan ai yasan wanene ni, auren yarinyar nan da xan yi tamkar jihadi xanyi don ance bin maza take” Kallonsa kawai Abuturrab ke yi with disgust, Dattijon ya ja tsaki yana ci gaba da taunan goronsa da jajayen hakoransa yace “Idan tsakani da Allah ne kai ka aureta mana yaro xaka wani kawo ma mutane fi’ili a nan, kaga mai anguwa a yanke min sadaki yanxu in bada a wuce wajen dama ina da niyyar auren kwanan nan” Yana fadin haka ya fiddo yan dari biyar biyar a aljihunsa, lokaci daya tunanin Abuturrab ya kwance, Hansai ganin ‘yan dari biyar biyar tana d’an kame kame tace “Ai wllh tamkar taimako xaka yi Alhaji, wannan babban taimako ne, ni kaina da na haifeta bana shaidarta, kawai dai Allah ya shirya mana xuri’a” Alhajin ya murmusa yace “Babu komai ai tamkar jihadi xan yi, Ni mai anguwa ne waliyi na, ita kuma sai a samu wani….” Abuturrab ya rufe ido ya bude, yaji kansa ya fara juya masa ya dinga kallon tsohon nan da ya fara kirga kudin da ya ciro, rasa tunanin da xai yi yayi, he was totally lost, Hansai dake ta kallon kudin hannun tsohon tace “Kawai a daura tunda ga sadakin a kusa” Jibril yace “Wannan taimako ne me girma xaka yi Alhaji, Allah ya saka da alkhairi, tana dawowa daga gantalin da ta tafi sai a wanketa a kai maka gida kawai” Abuturrab ya kalli mai unguwa after gathering much courage yace “Ni xan aureta, sai ka xama waliyi na” Ba Hansai ba kowa na wajen sai da yayi mamaki, mai Anguwa wanda da alama dama bai yi na’am da daurin auren da wannan tsoho me suna Alhaji Saleh ba yace “Toh Madallah Aliyu” Tsohon ya d’an ja tsaki ya mayar da kudinsa aljihu, A nan take kuma aka daura auren Abuturrab da Jiddah a kan sadaki dubu arba’in, su kenan kudin jikinsa da ya ciro daxu bayan ya siya ma Umma drugs, Xaune kawai Abuturrab yake a wajen amma gaba daya he is absentminded and lost ga wani sanyi da yaji yana shigarsa kamar xai yi xaxxabi, har aka gama komai aka raba dabino da alawan da aka siya a nan cikin layi, Hansai dai ta kasa gane ko murna xata yi ko akasin haka, Ya xa ayi babban mutum kamar wannan gashi har yace jirgin da bata ta6a gani ba duk tsawon rayuwarta yake tukawa ace wai ya auri Jiddah maimakon Bibalo, tunanin hakan yasa taji wani bakin ciki ya tokareta a kirji, lkci daya hankalinta ya tashi sosai ba kadan ba ta dinga xufa daga inda take xaune, yanda take xufa haka Abuturrab ke xufan shi ma, tunda yake bai ta6a shiga rudani da confusion lkci guda irin wannan ba, wait!!! what did he just do now??? What have he done to his life?? A cikin lkci ba me tsawo ba aka gama komai, sama sama ya dinga jin albarkan da dattijan wajen ke sa masa na cewar ya rufa ma jiddah asiri duk da ga abinda aka ce tana yi amma hakan bai sa ya kyamaceta ba gashi ya taimaketa ya aureta domin nisantata daga cutarwan iliya, Abuturrab ya mika ma mutumin karshe hannu sannan ya mike a hankali ya nufi motarsa walking slowly kamar mara lafiya, yana shiga motarsa ya tada motar ya kashe Ac don sanyi yake ji sosai ya fara driving ya bar layin, ikon Allah ne kawai ya kai sa gida lafiya cause blurry ya dinga gani ga kansa dake juya masa ya dinga ganin komai double, ko parking din kirki bai iya yayi ma motar ba ya sauka ba tare da ya rufe ba ya shiga ciki mai gadi ya bi sa da kallo, direct dakinsa ya nufa ba tare da ya kalli kowa na parlon ba, duk suka bi sa da kallo, Aunty ta kalli Ummi, Ummi dai bata ce komai ba, Aunty ta mike ta bi bayansa da sauri, cikin bargo ta gansa ya lullube har kansa, da mamaki tace “Are you okay Aliyu???” Bai iya ya bata amsa ba, ta sauke bargon a hankali ganin he is shivering so much, da mamaki tace “Baka jin dadi ne?” Ya gyada mata kai kawai, tace “Subhanallah, let me switch off the Ac”

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE