JIDDATULKHAIR CHAPTER 13 BY KHALISAT HAIDAR
JIDDATULKHAIR CHAPTER 13 BY KHALISAT HAIDAR
Mikewa Aunty tayi bayan Abba ya kai aya cikin tashin hankali tace “Ban gane ba Alhaji?? Are you for real? Shi Abuturrab din ne yaje ya daura ma kansa aure without our knowledge????” Abba yayi murmushin karfin hali yace “Dama mutum ya ta6a daura ma kansa aure, we just have to accept it Hafsah, it doesn’t make sense though, to amma ya muka iya da lamarin ubangiji, Allah ya riga da ya tsara hakan” Ummi kallonsu kawai take ko kiftawa babu, wanda da alama duk ta fi su shiga shock din, Aunty ta dage hannu biyu sama tana girgixa kai da karfi tace “No wayyy, mu ba gantalallu bane gaskiya, yanda aka daura auren haka xai saketa wllh wllh, me xai yi da yar hayi, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, yar hayi fa kace Alhaji?? To na rantse da Allah baxai yiwu ba” Wani kallo Abba ya dinga yi mata har tayi shiru tana huci kafin yace “Ja xa ki yi da lamarin ubangiji??” Aunty ta dalla masa wani harara ta nufi kofa rai bace tana cewa “Allah ya kiyaye, wllh sae ya saki wannan yarinya dai, banda fitinarsa ma ina shi ina shiga tsabgan talakawa mutan anguwan nan balle har wannan mummunan kaddararran ya fada masa, wllh saki kamar yayi sa….” sai kuma ta fashe da kuka ta fice ta rufe kofan, Abba ya kalli Ummi bayan kusan minti biyu da fitan Aunty jin taki cewa komai yace “Kinyi shiru Hauwa” Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh me xance, jin abun nake kamar a mafarki ai, an ta6a aure haka dama Yallabai?” Abba yace “Gashi nan dai d’an ki yayi, kinsan babu abinda taimako baya sa mutum yyi, to kinga inda nasa taimakon yayi leading dinsa to” Ummi ta girgixa kai tace “Toh yanxu meye abun yi Yallabai? Wannan ai ba abun ayi shiru bane ayi ta kiran taimako, wani irin aure ne wannan kamar a wasan kwaikwayo” Abba yace “Meye kuwa abun yi banda ya tare da ita yarinyar, ai an riga da an daura aure, kuma lamarin aure ba lamarin wasa bane” Da mamaki Ummi ke kallonsa tace “Kana nufin haka xai yi rayuwa da ita? Ya tare da ita fa kace” Abba yace “Kwarai, tunda har an daura auren, ai yanxu matarsa ce ita din, ko ke wani shawara xaki bada a nan?” Ta girgixa kai tace “Haba Alhaji, a ina aka ta6a irin wannan auren, ni dai tunda nake ban ta6a jin irinsa ba ma, me xa muce ma ‘yan uwa da abokan arxiki, me xa ace ma Hajja, ya kake ga xata dau lamarin nan? shi Abuturrab din shaye shaye ya fara da xai kai kansa ga irin wannan taimakon? Ba gwara ma ace yau kawota yayi gidan nan ba yace mana ga ta, ai babu wanda xai hanata xama gidan nan idan anyi bincike an gano gaskiyar lamarin, kuma baxa mu ki riketa ba, idan ma wani ya ki ni baxan ki ba ka sani” Abba yace “A takaice kema dai kin goyi bayan ya saki yarinyar kenan” Ummi tace “Toh idan bai saketa ba me xai yi, ai sakin kadai ne best solution a nan, ko a garin ga6a ga6a ba a irin wannan auren Yallabai” Abba yace “Toh duk kun yi kokari, amma ku sani auren nan bbu fashi tunda ba wani ya dau sadakin ya kai masa ba, da kansa ya aikata duk abinda ya aikata gaban kansa ba tare da ya duba cewa yana da iyaye da magabata ba, to don me xa ace sai yayi saki, tunda har ya amince aka daura masa aure da ita wllh dole ya amince ya xauna da ita, ba dai taimakonta yake son yi ba, gata nan sai ya taimaketa har karshen rayuwarta, nan gaba sai kiga ba shi ba har ke sai kiyi alfahari da ita a matsayin matar d’an ki, sannan a rayuwar nan there is reason for everything, Allah ya riga ya tsara hakan to mu a su wa da xa mu ce tsarin bai yi ba??” Mikewa Ummi tayi bata sake sauraronsa ba ta fice daga parlon, ya daga kafada yace “Yanda bai maku dadi ba nima lamarin bai min dadi ba ko kadan, but who am i to ask why tunda haka Allah ya tsara???” Aunty ce tsaye kan Abuturrab inda take shiga ba nan take fita ba duk ta hada xufa kai kace tayi wani tafkeken asara ne a rayuwarta, ko Salem ne yayi abinda Abuturrab yayi iyakan abinda xata yi masa kenan take ma Abuturrab, Abuturrab dai na xaune gefen gado ya rike kansa da yyi masa nauyi duk yana sauraronta ga wani bugawa da xuciyarsa yake, he just hate himself completely for this foolish mistake he made, me yasa bai yi duk wannan tunanin ba kafin ya aikata wannan shirmen, me yasa bai yi reasoning abinda xai biyo baya ba yayi abinda yayi?? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Da kyar ya dago kai yana kallon Stepmum din tasa da idanuwansa da suka kada cikin sanyin murya yace “Wllh xan saketa Aunty, ba da dadewa ba kuma xan yi hakan, ni ko ba ace in saketa ba ma dama ba sa’ar aurena bace dole xan saketa” Aunty na huci tace “Toh uban me kake jira har yanxu? Mu xaka kwaso ma abun kunya a dinga nuna gidanmu a gari, wllh baxai yiwu ba ko almajiri baxa ayi masa irin wannan auren da kaje kayi ma kanka ba, aikin banxa kawai, ko yar cikin gari wllh wllh kafi karfinta balle yar kauyen hayi, to sai ta shigo gidan mu gani ai….” Tana fadin haka sai ta saki kuka ta fice daga dakin. Abuturrab ya dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji’un a xuciyarsa, what has he done with his life, he wish he could wake up and see that all this is nothing but a dream, mikewa yayi a hankali ya karasa kofar dakinsa ya sa makulli don ma kar ta sake dawowa sannan ya dawo ya xauna ya dafe kansa hade da lumshe ido yana kiran Allah a ransa. Bayan azahar Abuturrab ya dau makullin motarsa ya fito daki, tun safe bai fito ba sai yanxu da yaje masallaci yayi sallah ya dawo, yana shigowa parlor ganin kallon da siblings dinsa ke masa yasan sun samu labarin kenan su ma, bai kuma kallonsu ba har ya fice daga gidan, ya hau motarsa ya bar gidan, gidansu Ahmad ya nufa, ko kallon matar mai gadi dake gaishesa bai yi ba ya nufi entrance din gidan, a yanxu dai komai haushi yake basa, underneath his breathe yayi sallama ya shiga parlon, Huraira ce da Siyama parlon, su ma bai sake kallon inda suke ba balle ya amsa gaisuwarsu, dai dai nan Ahmad ya fito daga wani daki dake nan parlon, ganin Abuturrab yace “I was planning on calling you now, welcome… Duk kayi scarce yau” Abuturrab bai ce komai ba ya nufi dakin Ahmad, Ahmad ya bi bayansa yana murmushi a ransa yana cewa the latest ango in town, xaune ya tadda shi gefen gado, Ahmad ya tsaya bakin kofa yana kallonsa yace “Ya ake ciki yanxu, hope it went well??” Abuturrab yace “Kamar yanda na fada, no much problem from Dad, but aunty took the matter tooo personal, Aunty tayi misunderstanding komai” Ahmad ya masa wani kallo yace “And so what? How about Ummi? Though she is here, daxu ta xo” Abuturrab ya xaro ido yace “Kana nufin Ummi na gidan nan?” Ahmad yace “Yea tana dakin Umma” Abuturrab ya lumshe ido ya bude, gaba daya abun duniya ya ishesa yanxu fisabilillah baxai farka yaga duk wannan abun mafarki bane, Ahmad yace “Amma Ummi tayi maka magana ne?” Abuturrab ya girgixa kai yace “Bata ce min komai ba har yanxu” Ahmad yace “Ka kwantar da hankalinka komai ya xo da sauki tunda Abba ya fahimce ka” Abuturrab yace “Ya fahimce ni?? Ai ni da abinda Abba ke ce min yanxu gwara ma ace bai fahimceni ba kwata kwata, Did you know that he is forbidden me from divorcing her?? Ce min yayi fa baxan saketa ba” Ahmad har xai ce dai dai kenan amma don kar ya sake provoking din d’an uwan nasa yayi fuskan mamaki yace “Toh fah, kar ka saketa kuma??” Abuturrab ya d’an ja tsaki a fusace fuskar nan tasa a murtuke, Can ya dago ya kalli Ahmad yace “Toh me Ummi ta xo ce ma Umma ynxu?” Ahmad yace “Don’t know…. And least i forget, Jiddah bata da lafiya fa” Daga kai Abuturrab yayi yana kallonsa, Ahmad yace “Yea, ina mata karin ruwa, shine kaga na fito dakin dake parlor da ka shigo yanxu” Abuturrab dai bai ce komai ba, Ahmad yace “Dakin mai gadin baxa a rasa sauro ba, it’s malaria symptoms….” Abuturrab na kallonsa yace “Kayi mata test ne? She just finished treating malaria few weeks ago” Ahmad yace “Yea it’s possible she is reinfected” Abuturrab bai sake cewa komai ba, Ahmad ya juya yace “Mu je ka dubata” Abuturrab yace “It’s not necessary” kallonsa Ahmad yayi yana ciro wayarsa dake ring a aljihunsa yaga Umma ke kiransa, ya kalli Abuturrab yace “Hmm Umma is calling” Daga kiran yayi ya kai kunne, bayan few seconds yace “Toh” daga haka ya katse kiran yana kallon Abuturrab yace “She’s calling me to her room now” Yana fadin haka ya fita dakin ya tafi bangaren Ummar tasa, tana xaune bedroom dinta tare da yayarta ko wannensu fuska babu annuri, Ahmad yyi kasa da kai ya xauna nan kasa yace “Gani Umma” Umma na kallonsa strictly tace “Ahmad wacce yarinya ce Abuturrab yaje ya aura without acknowledging how stupid that will be?? Yanxu kana matsayin d’an uwansa ka yi shiru ka barsa ya aikata abinda ya aikata Ahmad??” Ahmad yayi kasa da kai a hankali yace “Wllh i knew nothing about that Umma, i swear to God ban san komai ba…” Umma ta daka masa tsawa tace “You are lying, ya xaka ce baka san komai a kai ba, akwai wani abu da Aliyu ke boye maka?” ya kalleta da sauri yace “Billah abinda ya sanar da ni jiya ne kadai nasani game da lamarin nan, a jiya nima nasan abinda ya aikata Umma” Umma tace “Me ya sanar da kai jiyan?” Ya sauke kansa yace “Umma nima he didn’t tell me all, but he is around now, yana dakina” Umma tace “Abuturrab na gidan nan????” Ahmad yace “Ehh yanxu ya shigo” Umma tace “Call him” Mikewa Ahmad yayi ya fita dakin…. Abuturrab ya mike da sauri bayan Ahmad ya sanar masa kiran Umma yace “Me yasa xaka ce ina gidan nan Ahmad for God sake?” Ahmad ya daga shoulder yace “i didn’t say so, kawai kirana tayi tace i should call u, kilan ko su siyama ne suka gaya mata ka xo, aikena kayi da xanje in ce masu ka xo?” Abuturrab ya wani hade rai yana jin kamar ya dau car key dinsa ya bar gidan, but he just can’t, babu yanda ya iya haka ya fita dakin Walking slowly, Ahmad na biye da shi yana d’an murmushi, kasa ya xauna shi ma bayan ya shiga dakin Umma, tunda suka hada ido da Umminsa bai sake yarda hakan ya faru ba, ita ma small mum din tasa ya ki yarda su hada ido, su kuwa sai kallonsa suke kamar ranan suka fara ganinsa, Calmly Umma tace “Abuturrab, who is this lady that u went and tied the not with.. without the knowledge of ur parent??” Abuturrab kansa na kasa a hankali yace “I’m sorry Umma, i never knew it will happen this way, wllh it’s not intentional…” Ta dakatar da shi a fusace tace “Malam tambayarka nake wace yarinya ce?? Ba wani xance can ba” Abuturrab kamar baxai ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya yace “Tana gidan nan Umma” Ba Umma ba har Ummi bude ido tayi sosai tana kallonsa with shock, can suka kalli juna, Ahmad dai na tsaye bakin kofa ya rungume hannu, Umma na masa wani irin kallo tace “Wani gidan?” Abuturrab yace “Nan gidan?” Da wani expression Umma na kokarin calming kanta tace “Wacece ita?” Abuturrab ya kasa bata amsa, Umma ta kalli Ahmad, ya sauke idonsa murya can kasa yace “Yarinyar dake gun matar mai gadi yanxu” Umma ta xaro ido tace “Ban gane ba, wacce yarinya kenan?” Ahmad yace “Me sunan Ummi” Bude baki Umma tayi tana kallonsu gaba daya, Ummi dai duk sun gama confusing dinta sae bin su da kallo take, Cikin tsawa Umma tace “Baxa ku min bayani ba yanda xan gane???” Abuturrab ya dago yace “Ita ce Umma, da abun ya faru ne shine na kawota nan gun matar mai gadin gidan nan” Salati Umma ta saki har da tafe hannu tace “Kana nufin bakuwar nan Jiddah???” A hankali Abuturrab ya gyada mata kai yana kallonta da manyan idanuwansa, Umma ta hangame baki ta dinga kallon Abuturrab with shock, can ta kalli yayarta dake kallon ikon Allah tace “Yaya wai kinji yarinyar da mu ka shiga daki daxu a downstairs kika duba da jiki…” Ummi sai kallon Abuturrab take ko kiftawa babu, ya sunkuyar da kansa cikin sanyin murya yace “Ku yi hakuri Umma, i don’t know d words to use in asking for forgiveness, I’m truly sorry for all this, wllh it’s not intentional, Allah ne ya kaddaro min haka, amma in sha Allah nace xan saketa” Umma dake ta kallon yayarta da ta jinginar da kanta da gado ta kasa cewa komai, Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace “This is serious, Abuturrab? Why?? Why Abuturrab, dama ashe kai ka haifi kanka??” Kallonta kawai yake ruefully… ta girgixa kai feeling so disappointed tace “I am disappointed at u Aliyu, ka bani mamaki” Shi dai bai iya yace komai ba, Tace “Yanxu ita Jiddar ta sani? I mean tasan da wannan auren?” Ya girgixa kai yace “Bata san komai dake faruwa ba har yanxu…. And xaki iya samunta ki tambayeta ta gaya maki duk abinda ya faru da dalilin kawota gidan nan da nayi, sannan ni a lkcn da na kawota gidan nan ba a daura auren ba wllh” Umma was totally lost of words balle kuma Ummi da sai binsu kawai take da kallo, Umma tace “Daga bakin ka nake son jin labarin abinda ya faru ba ita ba” Abuturrab ya lumshe ido ya bude babu musu ya shiga bata labarin abinda ya faru tun daga farko ita ma bai boye mata komai ba har xuwa sanda aka daura masa aure da Jiddah, da tafin hannunsa ya rufe fuskarsa cikin breaking voice yace “Plss Umma ku daina ganin laifina, i only tried to help ne ban san haka abun xai kasance daga karshe ba, kice Ummi tayi hakuri ta yafe min wllh xan saketa na dau ma kaina wannan alkawarin, ban yi hakan don in bakanta maku ba Umma…” Umma ta rasa abinda xata ce tausayinsa ya cikata, cikin sanyin murya Ummi tace “Aa ni baka min komai ba, Allah ubangiji ya sa mu dace” Umma ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ta na kallonsa tace “Tashi kaje Abuturrab” Mikewa yayi ya juya ya fita dakin Ahmad ya bi bayansa, Umma na kallon Yayarta tace “Kiji wani babban lamari na ubangiji yaya, yanxu ke me kike ga xa ayi kan lamarin? What next?” Ummi ta sauke ajiyar xuciya a fili tace “Ban san me xance ba Ramlah” Bayan la’asar Abuturrab na fitowa masallaci tare da Ahmad, Ahmad yace “Ka shiga ka duba yarinyar nan pls, she was very sick yesterday night fa” Captain na kallonsa yace “Me dubata da rashin dubata xai kara mana ni da kai pls? Kai dai ba kana dubata ba me yasa xaka damu ni sai na dubata” Ahmad bai kulasa ba ya tsaya gaisawa da wani frnd dinsa a kofar gidan, Abuturrab ya shiga compound din walking slowly, babu kowa parlon ya kalli dakin da yaga Ahmad ya fito daxu da ya xo, kamar xai wuce sai kuma ya nufi dakin ya bude kofar a hankali ya shiga ya kulle sannan ya juyo yana kallonta, tana kwance saman gadon dakin drip a hannunta jin budewan kofa ya sa ta bude ido, ganinsa ta mike xaune da sauri, kana ganinta kasan she is very sick don har ta rame, lebbenta yayi ja, ya kalli drip din da har yayi rabi, da kyar tace “Ina yini” Bai yarda ya kalleta ba idonsa na kan drip din cikin calm voice dinsa yace “Ya jikin?” A hankali tace “Da sauki” Bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds ya d’an saci kallonta suka hada ido, da sauri ta sauke idonta, ya d’an hade rai, bude kofar dakin aka yi ya juya da sauri, Ummi da Umma ne bakin kofar, he wish hakan bai faru ba, ya ji kamar kasa ya bude ya shige kawai ya huta, kasa kallonsu yayi, Ummi dai sai kallonsa take ta karasa cikin dakin tare da kanwarta, Jiddah ta sunkuyar da kanta don sun gaisa daxu, Umma na kallonta tace “Ya jikin?” Tana jan fingers dinta tace “Da sauki Umma” Ummi dai sai kallon Jiddah take, Juyawa Abuturrab yyi xai fita amma ya kasa ce ma Umma ta basa hanya ita kuma ta ki basa hanyar, Ummi tace “Sannu Allah yakara lafiya” Jiddah na kallonta tace “Ameen” Umma tace “Kin sha shayin kuwa daxu?” Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace “Toh Allah ya sauwake” Daga haka ta kalli Captain tace “Meet me before leaving….” Shi dai bai dago kansa ba, Tana fadin haka ta fita Ummi ta bi bayanta, sai a sannan Abuturrab ya daga kai ya bi su da kallo, Umma ta kulle kofan, still yayi bakin kofar, can ya d’an kalli Jiddah, kallonsa take ita ma, suna hada ido tayi light smile tace “Kun yi kama da warce ke kusa da Umma” ya hade rai ya juya ya bude kofan ya fice ya kulle. Sai da Abuturrab ya tabbatar Umminsa ta bar gidan sannan ya koma dakin Umma, Kallonsa take xai xauna kasa ta nuna masa kujera ya mike ya koma saman kujeran tana kallonsa, cikin sanyin murya yace “Gani Umma” Tace “Tell me now son, what do u have in mind a kan wannan auren da kaje kayi ma kanka?” Ya girgixa kai yace “Taimakonta kawai nake son yi ba wani abu ba, but ban san things will turn out this way ba da ban fara ba…” Umma tace “So what’s ur next plan now?” Ya shafa kansa yace “Umma sakinta xanyi, since yanxu kun san abinda ya faru sai ta xauna nan ko kuma wajen Ummi, i know Ummi won’t say no” Umma dai kallonsa kawai take, can tace “Toh kilan hakan kadai ne mafita gareka, amma can su iyayen nata da suka baka aurenta fa?” Ya girgixa kai yace “Ba mutanen kwarai bane, ko da xata xauna da ke ko Ummi to babu ita babu su, ita din marainiya ce, she is staying with just her Stepmum, tace min iyayenta sun rasu, I don’t know of relatives amma da da akwai baxa su bari tana wahalan da take ba a gun Kishiyar Baabarta, beside that baxa su bari a aura mata shi wanda aka yi niyyar aura mata da farko ba, don duk anguwar babu wanda bai san tout bane shi, amma sbda yana ba ita stepmom din nata abun duniya wanda bai kai ya kawo ba shine take son aura mata shi, sannan tana da ‘ya ita ma sa’arta fa” Umma dake ta sauraronsa ta girgixa kai cike da tausayin Jiddah tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un….” Yayi kasa da murya yace “Ita ce me yin awaran da muke siyo maki a hayi, Ahmad yasanta… But bai ta6a sanin ina xuwa gunta a can hayin ba har sai da wannan abun ya faru” Umma ta buda ido tace “Ikon Allah, Allah sarki rayuwa, yanxu abinda nake so da kai shine you talk to her about all what happened tunda kace bata sani ba, ka sanar mata komai” Da sauri Abuturrab ya kalleta, ta gyada masa kai tace “Yes she needs to know kafin ma kayi sakin da kake cewa, after that kuma idan nan din xata xauna to, in kuma gun Yaya xata xauna shkkn” a hankali Abuturrab yace “Toh shkkn Umma, nagode” Umma tace “Amma ba yau xaka sanar mata ba tunda bata da lafiya, gobe ka xo we are hoping she will get much better sai kayi mata bayanin komai” Abuturrab yace “In sha Allah Umma” Tace “Maa sha Allah, you can go, Allah yayi maka albarka” Yace “Ameen” mikewa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya, tun bayan faruwan wannan lamarin sai yanxu ya ji magana da ya sa masa relieve a xuciya, he is happy Umminsa bata dauki wannan batun personal ba, just like his dad and small mum, but Aunty, wani sigh yayi yana tunanin yanda xasu yi da ita idan ya koma gida anjima….