JIDDATULKHAIR CHAPTER 14 BY KHALISAT HAIDAR
JIDDATULKHAIR CHAPTER 14 BY KHALISAT HAIDAR
Ko da Abuturrab ya koma gida bai bari stepmom dinsa ta san ya dawo ba don bai ma dawo da motarsa ba a gidansu Ahmad ya barsa, Ahmad yayi dropping dinsa kofar gida a nasa motar ya koma, yana shiga bedroom dinsa ya sa makulli hade da sauke ajiyar xuciya, wanka yayi ya sauya xuwa pajamas dinsa ya xauna gefen gado, yana son shan shayi but baya son fita duk da ko ya fita din kanninsa xai saka still, wayarsa ya jawo ya shiga dialing number din Ramlah, tana dagawa yace “Make me a cup of tea, an omelette with just two eggs” Bai jira cewarta ba ya katse wayan, ba a dau lkci ba Ramlah tayi knocking bakin kofar dakinsa, ya mike ya isa kofan ya bude ya bata hanya ta shigo, ajiye plate din hannunta na kwai dake rufe tayi da cup din shayin tana kallonsa tace “Yaya….” yace “Goodnight Ramlah” Shiru tayi sai kuma ta juya ta nufi kofa kafin ta fita yace “Thank you” Ta sake juyowa ta kallesa ta marairaice tace “Amma yaya me yasa…..” Hade rai yayi yace “Fita!!” Fita tayi ta kulle masa kofar ya karasa ya sa key. Washegari Friday Abuturrab na dawowa masallaci da asuba ya shiga bangaren Umminsa, da da ne bangaren stepmom dinsa xai fara shiga, kansa a kasa ya gaida Ummi ta amsa, a hankali ya soma bata hakuri, tace “It’s okay, ae kun gama magana da Hajiya Ramlah ko?” Ya gyada mata kai tace “Toh maa sha Allah” Yace “Amma Ummi don Allah kiyi ma Abba magana naji yana cewa baxan saketa ba…” Ummi tace “I don’t know… But seriously he is not to decide that for you, you just ignore him” Abuturrab bai ce komai ba, can yace “Toh shkkn Ummi” mikewa yayi ya fita dakin ya koma nasa, a masallaci ma dodging din mahaifin nasa ya dinga yi har ya shigo gida basu hadu ba. As early as 10 Abuturrab ya bar gidan ya tafi gidansu Ahmad, bayan ya gaisa da Umma dake parlor ya tafi dakin Ahmad, Ahmad na shiryawa ya samesa, Ahmad na murmushi yace “Welcome latest ango” Abuturrab yayi still ya dinga masa wani kallo, Dariya Ahmad yayi yace “Yanxu dai cikin ruwan sanyin kullum sai ka xo gidan nan ko?” Abuturrab bai tanka sa ba ya tafi ya xauna, Ahmad ya gama shiryawa yace “She’s getting better, jikin da sauki yau sosai” Nan ma Abuturrab ya sharesa, bai san shi abinda ya kawosa daban ba, Mikewa kawai yayi ya fita daki hoping Umma ta bar parlon yanxu, Ahmad ya bi sa da kallo yana murmushi, luckily ya tadda babu kowa a parlor ya karasa dakin da Jiddah take ya bude hade da sallama murya can ciki, tana xaune saman gado da wani drip din a hannunta ga pepper soup da Umma ta sa ayi mata, Huraira da Maman Abdallah ne dakin suna ta hira, ita dai sai dai tayi murmushi, ganin Abuturrab duk suka gaishesa, bai san suna ciki ba da baxai fara shigowa directly ba, ya amsa without looking at them, Jiddah ta kallesa tace “Ina yini?” Ita ma bai kalleta ba yace “Lafiya” Ahmad ne ya karaso dakin ya shiga ciki yana kallon jiddah yace “Alhmdlh jiki yayi kyau sosai ko Ummi?” Ta d’an yi murmushi amma bata ce komai ba, shi dai Abuturrab na tsaye, Ahmad ya kalli su Huraira da basu da niyyar fita a tunaninsu kawai dubata suka shigowa yi, yana murmushi yace “Maman Abdallah da Aunty Huraira a bamu waje mu duba patient pls” Duk suka mike, Huraira tace “Toh bari mu fita” Bayan sun fita dakin Abuturrab ya karasa gun window ya tsaya Ahmad dai sai kallonsa yake, Can yayi murmushi ya kalli Jiddah yace “Kin sha maganin ai ko?” Ta gyada masa kai tace “Eh” yace “Toh Allah ya kara lafiya” Tace “Ameen” Ya juya yace “Bari in kawo maki na karshen..” Daga haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita ya kulle kofar, sunkuyar da kanta tayi, Abuturrab ya d’an kalleta, he don’t even know where to start from, hada ido suka yi ya rungume hannunsa yace “Ya jikin?” Tace “Naji sauki” Ya d’an yi jim kafin yace “Iyayenki sun daura maki aure…” Da sauri Jiddah ta daga kai ta kallesa, yaki yarda su hada ido ya ci gaba yace “Amma ba da mutumin nan ba” Kallonsa kawai Jiddah take ko kiftawa babu, ya shafa kansa yace “Amma shi wanda aka daura maki auren da shi xai sake ki, sai ki ci gaba da xama a nan wajen Umma ko gidanmu wajen Ummina, amma fa sai kin amince babu ke babu Baabar nan taku don ba sonki take ba, kuma baxata ta6a sonki ba, neman kudi take da ke” Cikin sanyin murya Jiddah tace “Toh da wa aka daura min auren??” Yace “Fada maki ba amfani xai yi gareki ba, kawai dai abinda na sani xai sake ki, sai kiyi xaman ki a nan ko kuma ki xauna gidanmu, ki fara karatu islamiyya da boko, kinsan wacece ke, kinsan daga inda kike, kawai na shiga rayuwarki ne ba don komai ba sai don in taimakeki in samar maki yan cin ki, idan ba don haka ba, ni bana shiga abinda bai shafeni ba….” Kallonsa kawai Jiddah dai take a sanyaye, lkci daya hawaye ya kawo idonta, a hankali tace “Jiya Umma da daddare ta shigo ta tambayeni in gaya mata gaskiyan wacece ni, kuma ya aka yi na xo gidan nan” Cikin rawar murya ta ci gaba tace “Ni kuma baxan iya mata karya ba” Abuturrab na kallonta yace “Kin dai gaya mata ko?” Ta gyada masa kai yace “Good, xuwa gobe duk inda kika ce xa ki xauna nan xa a kai ki, ko gidanmu ko nan” A hankali tace “Toh idan na xauna nan xaka dinga xuwa?” Kallonta yake da kyau, ya hade girar sama da ta kasa yace “In xo in yi maki me??” Kasa cewa komai tayi tana wasa da fingers dinta, yace “Ae ba lallai ki gan ni ba, ki ma daina min kallon sani daga yanxu, ki kama Umma da su Siyama ki rike sosai, they will like you, ni ba lallai a shekara ma kike ganina ba” Kai kawai ta gyada masa hawaye cike idonta, yace “Sai ki tsaya kiyi karatu da kyau domin al’umma da wa enda suke tare dake suyi alfahari dake…” Nan ma ta gyada masa kai kawai, yace “Allah ya kara lafiya” Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita dakin, hawayen da bata san dalilinsa ba ya dinga sauka idonta, Abuturrab ya amshi medical report dinsa wajen Ahmad kawai ya bar gidan coz baya tunanin har ya koma aiki da akwai abinda xai sake dawo da shi gidan, he now felt relieved, yaji baya tare da duk wani damuwa. Da yammacin ranan Abuturrab dake bedroom dinsa ya dau wayarsa dake ring, ganin number Abbansa yaji gabansa ya fadi sosai, dagawa yayi ya kai kunne hade da sallama, Daga daya bangaren Abba yace “Ka sameni parlona ynxu” Kafin yace komai Abba ya katse kiran, lumshe ido yayi ya bude, bayan few minutes ya mike a hankali still holding to his phone ya nufi kofa ya fita, a main parlor suka ci karo da Aunty, yayi kasa da kai yace “Ina yini Aunty” Ko kallonsa bata yi ba balle ta amsa shi tayi wucewarta, ya bi ta da kallon gefen ido sannan ya ci gaba da tafiya xuwa parlon Abbansa cikin sanyin jiki, a hankali yayi sallama sannan ya shiga, sosai gabansa ya fadi ganin Abbansa da brothers dinsa biyu, a sanyaye ya karasa shiga cikin parlon ya xauna kasa sannan ya gaishesu, uncles din nasa suka amsa, ya kalli Abba amma bai ce komai ba, Alhaji Lawal yayan Abbansa ne yace “Mun ji abinda ke faruwa Aliyu, ko kuma ince mun ji abinda ya faru” kasa cewa komai Abuturrab yayi, Alhaji Ibrahim kanin Abbansa yace “What u did is something very good but ba ta yanda ya kamata kayi ba kayi, kada ka manta ba kai ka haifi kanka ba, kana da iyaye, no matter what ya kamata ka nemi consent dinsu, ya kamata ka basu girmansu su san abinda kake ciki, ba sae da abu ya kwabe ba…..” Daga kafada yayi yace “Anyway, wannan duk maida hannun agogo baya ne, tunda abinda ya faru ya riga da ya faru, sae dai a tari na gaba” Abuturrab bai iya yace masu komai ba, Alhaji Lawal yace “So what next now? Yarinyar tana ina?” A hankali yace “Tana gidan Umma” Alhaji Lawal yace “Wacece Umma?” Abba yace “Kanwar Hajiya Hauwa” Alhaji Lawal yace “Ohkk, am asking what ur next action is now” Abuturrab ya sunkuyar da kai yace “Abba sakinta xanyi sai ta yi xamanta tayi karatu that was my intention dama” Alhaji Lawal yace “Ka saketa a saboda me?” Abuturrab ya kallesa ya marairaice yace “Abba dama wllh niyyata kenan, ai baxai yiwu inyi aure iyayena basu sani ba, ni kawai na amince na aureta ne sbda kubutar da ita daga hannun matar babanta, amma ai ni baxan iya aurenta ba” Alhaji Lawal yace “Wannan ba magana bane Aliyu, ka aureta, ka aureta kenan, babu wani kwaskwarima, Allah ubangiji ya baku xaman lafiya, kada ka sake tunanin sakinta, kaddararku da ita ne a haka” Bude baki Abuturrab yayi yana kallonsa without knowing cewar yayi hakan, Alhaji Ibrahim ya gyada kai yace “Hakuri xaka yi son, ka xauna tare da ita, ka cike ladanka, ai Allah ya ga xuciyarka, idan ka saketa baka kyauta mata ba, akwai hikima cikin auren nan….” Abuturrab ji yayi kamar ya fara masu kuka gaba daya, Abba ya sauke ajiyar xuciya yace “Dama ni nace baxai saketa ba, cikin weekend din nan ya dauketa su tare, ai ba wani ya jawosa ya aura masa ita ba, sai yayi hakuri ya rungumi kaddara” Abuturrab was lost of words amma ganin musa masu baxai yi masa amfani ba yayi shiru duk yana sauraronsu, sai dai xufa kawai yake yi, to lkcn da ma xai saketa din sani xa su yi? Tunanin hakan ya saukar masa da relieve, Muryar Alhaji Lawal yaji yana cewa “Gobe asabar ka tare kawai da matarka, Allah ya sanya alkhairi, not too long sai ku shirya da ita ku tafi gaida mai martaba a bauchi” Abuturrab bai samu courage din ce masu komai ba, but he is boiling inside, dama taimako na iya xama fitina da tashin hankali haka bai sani ba??? Alhaji Ibrahim yace “Sai a kira Hajiya Hauwa ita ma aji ta bakinta tunda tana da right a kansa ko?” Abba ya dau waya ya kira Ummi, har da Aunty, Abuturrab ya ji dadi da Abba ya kira har Aunty don yasan she will stand for him, ba a dau lkci ba suka shigo parlon, duk suka yi ma ‘yan uwan mijin nasu sannu da xama don tun xuwansu gidan suka gaisa, Alhaji Lawal ne yayi masu bayanin shawaran da suka yanke, Ummi dai ta kasa cewa komai, ita babban tashin hankalinta asalin yarinyar nan ba wai tana kin auren bane, ba a san wacece ita ba gashi yace uwarta da ubanta sun rasu sai kishiyar uwar, Aunty ta mike tana girgixa kai cikin tashin hankali tace “Haba fisabilillah, an ta6a aure dole ne? Tunda yace bai so, yayi auren nan ne kawai don taimako to a barsa ya datse wannan kaddararren auren mana, ai ya gama taimakon da yayi niyya, to meye kuma xa ayi ta cusa masa yarinya kamar ku ka aura masa ita, wannan ai kamar neman suna ne ku ke yi, banda haka wllh ko mahaukaci baxai amince da irin wannan auren ba, yarinyar da bata da asali ku ke burin d’an ku ya xauna da?” Alhaji Ibrahim yace “Ke kinje kinyi bincike kinga bata da asali Hafsah?” A fusace tace “Banda yanxu da na kawo maganan asalin ai babu wanda ya damu da hakan, haka kawai xaku yi ma yaro dole kuce sai ya xauna da yarinya yana ce maku baya so?” Alhaji Lawal na kallonta da kyau yace “Tunda ni ko d’an uwana ko Ibrahim babu wanda ya ja Abuturrab ya kai sa aka daura masa aure he just have to dance to his music, ko yaki ko ya so haka xai hakura ya xauna da yarinyar, mu ba kananun mutane bane, yanda bai yi shawara da mu ba yaje yayi abu gaban kansa bai isa yace yanxu ma xai juya mu ba, Allah ya basu xaman lafiya” Abba ya gyada kai cikin gamsuwa, Aunty na masu wani kallo gaba daya tace “Ai ko baxan ta6a xuba ido Abuturrab ya cutu ba in dai ina numfashi…” Daga haka ta fice daga parlon fuuu, Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh Allah yayi abinda ya fi alkhairi, ya sa mu dace” Alhaji Lawal yace “Ameen Hauwa” ta mike ta fita parlon ita ma, Abuturrab dai kansa na kasa, Abba na kallonsa da kyau yace “Kafin gobe kayi duk abinda xaka yi a gidan nan ka tare da matarka, kamar yanda Alhaji Lawal ya fada maka, idan an kwana biyu kuma ka kai ta ku gaisa da mai martaba” Still Abuturrab ya kasa cewa komai, sai da suka yi masa ixinin fita sannan ya mike ya fita xuciyarsa na tafarfasa, Alhaji Lawal yace “This should serve as a lesson for him, next time baxai sake yin abu gaban kansa ba” A bedroom dinsa ya tadda Aunty tana ta jiransa tana girgixa kafa, a sanyaye yake kallonta, Tace “What next now?” A hankali yace “I don’t really know Aunty, but ni nasan baxan yi rayuwa da ita matsayin matata ba wllh” Aunty tace “Toh dama ina hakan xai yiwu, a ina xaka xauna da ita bayan ga Aneesah, uban me xaka ci da ita?? kuma idan ka saketa sani xa su yi?” Ya girgixa kai yace “That’s what i have in mind Aunty, xan saketa babu wanda xai san hakan sai ke a gidan nan, quite alright xan tare da ita gobe din amma ba matsayin matata ba wllh” Aunty tace “Ai xaman naku ne bana so kwata kwataaa Abuturrab” Yace “Aunty a hankali ake bin komai” Tace “Toh da dai ya fi, don wllh abun dariya xaka xama gun colleagues dinka da yan uwanka, wa ka ta6a jin yayi irin wannan auren? Auren ma na yar talaka” A sanyaye yace “Na sani Aunty” Ta nufi kofa tace “Ba dai tarewa suke so ba, xaka tare din da ita sannan ni xan san abun yi” Daga haka ta fice a fusace, ko ba komai Abuturrab na samun relieve tunda akwai warce ke supporting dinsa dai. Daren ranan Umma ta kirasa yana kwance sai tunane tunane yake yana imagine yanda lkci daya Jiddah ta shigo rayuwarsa tana neman tarwatse masa farin cikinsa da kwanciyar hankali, a hankali ya dau wayar ya kai kunne bayan ya daga, cikin sanyin murya Umma tace “Kana ji na Aliyu?” Yace “Ina ji Umma” Tace “Kayi hakuri ka bi abinda iyayenka suke so sai kaga haske sosai a lamarinka, Yaya ta kirani ta min bayanin komai, ka janye batun saki, kaga dai yau jiddah kwananta uku ko sama da haka a gidan nan, amma har yanxu ban ga aibun yarinyar nan ba wllh Aliyu, gata da hankali da nutsuwa da sanin ya kamata ga uwa uba kawaici da hakuri, baxa kuma a dau lkci ba xata waye don na lura tana da kwakwalwa, taka kaddarar ce a haka ka amsheta hannu biyu Aliyu, kada ka mance Allah ne ya tsaro maku hakan kayi hakuri ka yarda da kaddara my son, duk sanda xaka koma wajen aiki sai ka dinga kawo min ita nan ina gwada mata abubuwa, daga nan din ta dinga xuwa boko da islamiyya, wllh lkci daya xata dawo dai dai taste dinka, nasan damuwarka kenan, in sha Allah xaka yi mamakin wayewar da Jiddah xata yi” Abuturrab yaji baci ransa kawai yake da wannan shawaran da ake basa, ya ma rasa abinda xai ce mata, how on earth suke tunanin xai iya rayuwa da yarinyar nan matsayin mata idan ba cutarsa suke son yi ba, ina duk burinsa na auren wayayyiyar mace me tsafta 100%, ji yayi kamar ya fara mata kuka wannan wacce irin kaddara ce haka ake forcing dinsa ya amsa, a ransa yace no way sai dai duk suyi hakuri, he just have to disappoint them because no amount of their sugar quinted mouth will convince him to live with that girl as wife, he will only live with her as a guardian…. Jin shirun yayi yawa Umma tace “Are u there son?” Ya runtse ido yana jin ransa na dada baci, cikin dakewa yace “Ina ji Umma, nagode Allah ya kara girma” Tayi murmushi tace “Ameen my son, Yaya tace min Abbanka yace ku tare gobe ko?” Cijen lips dinsa yayi yana jin wani mugun takaici, amma ya daure yace “Ehh haka ne” Tace “Toh Allah ya kai mu goben lafiya son, may Allah reward u abundantly for this deed” Ya bude idonsa da ya kada sosai…. forcing his self yace “Ameen” Sallama suka yi ya jefar da wayar kan gado xuciyarsa na tafarfasa ya mike xaune ya rike kansa. Washegari Saturday Umma na xaune dakinta tana kallon Jiddah dake juya kayan hannunta ta kasa sawa, jira take ta sa kayan ta gyara mata gashinta da ta sa ta wanke, murmushi Umma tayi da ta lura kunya ce yasa take hakan, sabon kaya ne da ta dinka ma Ramlah, sae ya kasance Ramla bata xo gidan ba har sannan shine ta ba Jiddan ta sa, mikewa tayi ta fita dakin, Jiddah ta bi ta da kallon gefen ido, sae a sannan ta fara sa kayan da sauri, wani kunya na musamman Allah yayi mata ita kam, komai da Umma ta bata ta saka sabo ne, sosai riga da skirt din ya amsheta kamar don ita aka dinka, kallon kanta ta dinga yi a madubin dakin tunda take iyakar atamfar da ta ta6a sa wa na dubu biyu ce, lkcn ko Ahmad ya kawo mata atamfa me tsada sae Hansae ta amshe ta siya mata roba roba ko half cotton, yau kam ga tsadadden atamfa ta saka duk da bata san me tsadan bane ba ma, bayan wani lkci Umma ta dawo dakin, sosai hankalinta ya kwanta ganin powder kawai jiddah ta shafa a fuska sai kwalli, ta bar mata har kayan kwalliya kawai don taga irin kwalliyan da xata yi sae gashi alama ya nuna iyakar kwalliyarta kenan ba irin na yan kauye take yi ba a lafta ja gira da jan baki, ta madubi take ta kallon jiddah da ta kasa kallonta, Jikin Umma yayi sanyi ganin irin kyan Jiddah, wai ma tun bata waye ba kenan, kuma jikinta bai fara samun hutu yanda ya kamata ba, ae balarabiyan Africa xa ayi a nan, a hankali Jiddah ta juyo tana kallon Umma, Umma ta sakar mata lallausan murmushi tace “Kinyi kyau my daughter” Jiddah tayi murmushin karfin hali, Umma ta xauna tace “Taho ki xauna in gyara maki gashin” Jiddah ta karasa ta xauna ta janye hulan Siyama dake kanta, Umma tace “Idan kin wanke gashi bari ake ya bushe kafin a sa hula kin ji?” Kai kawai Jiddah ta gyada mata, Unma ta fara taje mata dogon gashin nata, murmushi Umma tayi ganin tsayin gashin Jiddah a ranta kuwa tunani take ko ruwa biyu ce dai ita, sosai gashinta ke da kyau da tsayi sai dai babu gyara, Umma ta xuba mata man kai me yawa a gashin da ya dinga sheki da kamshi sannan ta yi mata parking da ribbon, mikewa Jiddah tayi tace “Nagode” Umma tace “Ki daura dankwalin yanxu” Jiddah ta dau dankwalin amma ta kasa daurawa, Siyama Umma ta kira tayi mata daurin, Siyama sae murmushi take tace “Kinyi kyau” xuwa yanxu har Maman Abdallah tasan matsayin jiddah a gidan, sae kusan karfe sha daya Umma ta bar gidan xuwa gidan yayarta da Jiddah, well ironed Hijab ne nude colour har kasa jikin Jiddah, kasancewar akwai kalan a jikin atamfar jikinta, sanyayyen kyau tayi, Hijab din yayi matukar amsarta, Driver ne ya kai su gidan don Ahmad kin amincewa yyi he knows definitely Abuturrab will be mad at him wato da shi xa a kai masa mata……