JIDDATULKHAIR CHAPTER 22 BY KHALISAT HAIDAR

JIDDATULKHAIR CHAPTER 22 BY KHALISAT HAIDAR

Bude ido Abuturrab yyi ya tashi xaune yana kallonta da mamaki, ta mike tsaye hannunta a goshinta, ko ina na jikinta rawa yake, duk ta daburce, xata bude kofar cikin tsawa yace “Me ya kawo ki nan??” Kin juyowa tayi hannunta na rawa ta bude kofar xata fita, wani tsawan ya kuma yi mata yace “Kar ki kuskura ki tsallaka bakin kofar nan” fashewa tayi da kuka amma taki juyowa kuma bata fita dakin ba, ya sauka daga saman gadon ya dau jallabiyansa ya saka sannnan ya nufeta, tana jin alamar ya sauka gadon ta juyo da sauri, ganinsa tayi tsaye gabanta, fuska daure yace “Me ya kawo ki bangarena?” Cikin rawan murya ta durkusa tace “Wllh kara naji shine na xo in ga meye, ban san ka dawo ba Allah” Ya rungume hannunsa yace “Wato har nan kike shigowa kenan idan bana nan kenan?” Ta fashe da matsanancin kuka tana girgixa kai tace “Aa bana shigowa, ni ba shigowa nake ba wllh” Yace “Toh ina ruwanki da koma me kika ji da xaki shigo min daki?” Hawayen dake makale idonta ya sakko ta girgixa masa kai kawai bata ce komai ba, yace “Toh tafi ki dauko abun shara, ki share tun daga cikin dakin har parlor sannan ki goge, ki wanke bandakin….” Ta sunkuyar da kanta don har ta ji hankalinta ya kwanta xatonta har marinta sai yyi yau, kofar balcony din dakin ya nufa ya bude yana nuna mata yace “Har nan xaki share kiyi mopping” Gyada masa kai kawai tayi, ya dau wayarsa har ya nufi kofa ya tsaya, ya juyo yana kallonta yace “Kar ki ga na kyaleki yau, billah idan kika sake shigo min bangarena ko da wasa xaki sha mamaki” Kai kawai ta gyada masa a sanyaye, ya juya ya fita, sai da ya fita parlon gaba daya sannan ta juya a hankali ta fita ita ma, downstairs ta sauka ta gansa xaune parlor ya kunna TV, ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, abun sharan ta dauko da mopping bucket tare da mop with duster sannan ta wuce sama, aikin ta shiga yi babu ganda, har xanin gadon sai da ta sake shimfidawa, bayan ta gama da bedroom din ta tafi balcony, kallon inda taga mutumin ranan tayi duk da babu kowa wajen sai kujera amma sai take ganin kamar shi a wajen, ta fi minti biyu tsaye tana ta kallon wajen kafin ta fara share balcony din ta yi mopping ta dawo dakin ta kulle kofa, parlor ta tafi nan ma ta share ko ina ta goge har kayan kallon, tana gamawa ta koma bedroom din ta bude kofar da take tunani bandaki ne, kallon bracelet din hannunta me kyau tayi wanda yau ya kai kwana uku da ta saka shi, ta tafi gaban mirror dinsa ta cire sannan ta ajiye tana kallon turarrukan da ke gaban madubin, kwalabensu ne ya burgeta sosai, they look so unique, ta dau daya daga ciki ta bude ta kai hanci, rufe ido tayi sannan ta bude, da wannan kamshin ta sansa, babu kuma abinda ya fado mata sai lkcn da yake xuwa can wajenta a Hayin rigasa, ta dau murfin xata rufe turaren ya subuce daga hannunta duk kokarin ganin ta kama turaren kan ya kai kasa hakan ya faskara don tuni yayi landing kan tiles sbda irin faduwan da yayi kuma lkci daya ya tarwatse, a tsorace ta ja baya ta dafe kirjinta da ya hau bugawa, lkci daya ta fara yarfe hannu murya can kasa tace “Na shiga uku” hankali tashe take kallon turaren, ta ma rasa abun yi, can ta nufi kofa sai a sannan ta fashe da kuka ta fita part din, downstairs ta sauka ta makale jikin bango tana kallonsa gabanta na faduwa, jin footstep kuma bai ji ta karaso cikin parlon ba ya sa ya juya, sunkuyar da kanta tayi, ya mike yana kallonta ganin hawaye a idonta, satan kallonsa tayi ganin kallon da yake mata ta fashe masa da kuka tace “Don Allah kayi hakuri” kasa daina kallonta yyi, can yace “Me kika min a sama?” Ta kara rushe masa da kuka tace “Don Allah kayi hakuri nace” Ya wani hade rai yace “Me kika yi nace?” Kin cewa komai tayi, ya nufeta, da gudu ta bar wajen ta wuce sama, ya bi bayanta, tuni ta shige dakinta ta rufe kofan da karfi, part dinsa ya nufa tun bai shiga parlon ba ya soma jin kamshin turarensa, ya shiga parlon sannan ya bude kofar dakin, tsaye yayi bakin kofa ya rungume hannunsa yana kallon tsadadden turaren nasa a kasa, Jiddah dai sai zare ido take tana jiran jin ya shigo dakin amma bai shigo ba har sha daya na safe, sai a sannan ta fara jin yunwan da ya dameta, lamo tayi kan gado kamar xata yi kuka tana tsoron fita, tana nan a haka har kusan sha biyu, mikewa tayi daga karshe ta nufi kofarta ta bude a hankali, cikin sanda ta sauka downstairs bayan ta tabbatar baya kasa sannan ta wuce kitchen, indomie ta dauka ta fara dafawa a kitchen din, ko kadan bata yrda tayi making noise da xai sa a san tana kitchen din ba, yanda taga Ramlah ta dafa masu indomie jiya take yi, with ingredients, tana duba indomie da har ya dahu kamar ance ta juya ta gansa tsaye bakin kofa, sake murfin tukunyar tayi a rikice tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” end din kitchen din ta tafi ta tsaya tana kallonsa a tsorace kamar xata yi kuka, ya karasa gun gas din ya kashe na indomien, da kuma na kwai dake tafasa, tana ganin haka xata fita kitchen din da gudu, ya tare hanyar, hade hannunta tayi waje daya ta marairaice tace “Don Allah kayi hakuri” yana mata wani kallo yace “Laifi nawa kenan kika yi yau a gidan nan?” Ta hadiye abu da kyar tace “Biyu” yace “Wanne da wanne?” Tayi narai narai da ido ta ki cewa komai, ya hade rai yace “Ina jin ki” Cikin rawar murya tace “Na fasa maka turare” yace “Ehen, sai me?” Tace “Na ji kamar radio na magana shine naje sashinka ka kamani” Ya gyada kai yace “Good, kinsan nawa turaren nan da kika fasa min?” Ta bude ido tana kallonsa amma bata ce komai ba, yace “Toh ki sani cewar tara ki nake, turaren nan kuma sai kin biyani duk yanda za ki yi ba ruwana” a hankali tace “Toh ae ni bani da kudi” yace “Ehh nemosu xa kiyi duk inda xa ki nemo su” ta sauke idonta kasa, kallonta yake daga sama har kasa, ya sauke idonsa kan fingers dinta yaga babu farce alamar tana cirewa a kai kai, ya kalli fararen toes dinta, kallon fuskarta yyi yaga har sannan kasa take kallo, yace “Cire hular ki” sae a sannan ta daga kai ta kallesa amma taki cirewa, ya hade rai yace “Magana nake maki” a hankali ta xame hular, ya dinga kallon bakin gashin nata wanda sak na Fulani, amma duk ya takure waje daya duk da da ribbon ta dauresa a tsakiya ya sauka kasan wuyarta, tun gyaran gashin da Umma tayi mata har ranan bata ta6a gashin ba, ya yamutsa fuska yace “Meye wannan din?” Ta kallesa bata ce komai ba, ya mata tsawa yace “Ba tambayar ki nake ba” Cikin sanyin murya tace “Gashina ne” Yace “Ke kaxamar wace gari ce, gashin ki ne kika bari haka kamar na mahaukaciya?” Ita dai bata ce komai ba, ya koma baya yana sake kare ma gashin kallo da mamaki, satan kallonsa tayi ya mata wani shegen kallo yace “Sae na tsokale idonki kika sake kallona, kina mace da ke dubi ynda gashin ki ya koma kamar gashin jikin tinkiya?? What nonsense” Lkci daya hawaye ya kawo idonta, strictly yace “Ki gama cin abincin kiyi sllh ki jirani a parlor” Bata ce komai ba ya juya ya fice daga kitchen din, Jiddah bata wani ci abincin ba sae hawaye, daga karshe ta mayar kitchen ta rufe taje sama ta wanke bakinta ta dau gogaggen hijab dinta ta saka ta dawo parlor ta xauna fuskarta babu walwala, sae da ya dawo sallahn Juma’ah sannan ya dau makullin motarsa, ya isa bakin kofar fita sannan ya kalleta yace “In xo in dauko ki ne” mikewa tayi a sanyaye ta bi bayansa, gaban motar ta xauna don bata mance abinda yace mata ba last time da ta xauna a baya, wani saloon ya kai ta, yana xaune mota ya jira har aka gama sannan daya daga workers din ta fito ta sanar masa an gama ko xa ayi mata lalle, yace “Aa, nawa ne kudin gyaran gashin naku?” Ta fada masa ya ciro kudin ya mika mata tayi masa godiya ta koma ciki, ba a dau lkci ba sai ga Jiddah ta fito daga saloon din, walking slowly ta iso gun motar har sannan fuskarta babu walwala, ta bude gaban motar ta shiga, ta rufe bata ce komai ba, kallonta kawai yake da mamaki, gani yake kamar da kyar ta iya rabuwa da halin gidadanci, ya daga kafada don yasan yana magana xata fara hawaye abinda bai shirya gani ba kenan, ya tada motarsa ya bar saloon din, suna tsaye traffic ganin yanda take kallon me tallan Apple a bakin glass din motar yace “Xa ki ci ne?” Sauke idonta tayi bata ce komai, yace “Ba magana nake maki ba?” Ta girgixa masa kai fuskarta a tamke tace “Baxan ci ba” hade rai yyi yace “Keee” Juyawa tayi ta kallesa tace “Nace A’a” Wani mugun kallo ya dinga mata ta dauke kanta, har suka isa gida bata sake kallon inda yake ba, yana gama parking ta sauka amma tana tsoron ta fara tafiya yyi mata masifa, Matar Mai gadi ce tsakar gidan daga kofarsu ganin Jiddah tace “Sannunku da dawowa Hajiya, Ina wuni…., duk yau shiru baki fito ba” gaban jiddah ya fadi sosai, Abuturrab ya dinga kallonta, Jiddah ta yi murmushin karfin hali tana kallon matar tace “Ina yini” daga haka ta fara tafiya da sauri, bin bayanta Abuturrab yyi, sai da ya shiga parlor ganin har ta isa stairs xata wuce sama yace “Dawo nan” juyowa tayi sannan ta dawo gabanta na faduwa, yace “Ta ina kike fita har take ce maki yau baki fito ba?” Ta xaro ido tace “Ai kofar a rufe kake barinsa, ni bana fita ko ina, ban ta6a ganinta ba ni sai yau” kallonta kawai yake ta Sunkuyar da kanta, ya xauna saman kujera, ita dai bata yadda ta sake kallonsa ba, yace “Ina gyaran gashin da aka maki?” Cire Hijab din jikinta tayi sannan ta sauke hular tana kallonsa, da mamaki yace “Daga nan xan gani” A hankali ta duka kasa ta matsa kusa da kujeran da yake xaune ta juya masa kan nata, kallon bakin gashin dake ta sheki yake, yace “Ta haka xan ga gyaran an daure gashin?” Ta juya ta kallesa sannan ta xame ribbon din gashin ya sauka kasa, bayan few seconds jin bai ce komai ba ta juya ta kallesa suka hada ido, hade rai yyi yace “Tashi ki tafi” Tashi tayi ta mayar da hulan sannan ta wuce sama dakinta. Mikewa yayi ya dau makulli ya fita don xuwa can gida ya gaida su Ummi, Tana jin an bude gate ta mike ta isa bakin window ta tsaya tana lekan compound din har ya fita da mota, turo baki tayi ta koma bakin gado ta xauna, can ta kalli wrist dinta sai kuma ta mike ta fita dakin ta tafi can bangarensa da sauri, a hankali ta bude kofar parlon ta shiga ta karasa bedroom da sauri ta isa gaban madubin tana duba bracelet dinta bata gani ba, bin dakin ta shiga yi da kallo bata ga alamarsa, juyawa tayi ta fita ta koma dakinta ta kulle kofa ta kwanta. Da daddare Abuturrab na bedroom dinsa yana operating laptop wayarsa ya fara ring, dauka yyi ganin me kiransa ya katse ya kirata, daga daya bangaren tace “Hi ya Abuu, Grandma want to vid call with u, na kira naga baka online” Yace “Ohk, how about zoom?” Tace “Aa ta WhatsApp dai” katse wayar yyi ya bude datansa ya hau online sannan ya kirata vid call din, Hajja ta hakikance gaban screen da katon eye glass dinta, yyi dariya yace “Ina wuni Hajja” Tace “Aa ba ruwana, meye kuma ina wuni, kai baka kiran mutane sai dai a kiraka kawai don kana matukin jirgin sama, baka da wani bambanci fa da me jan motar haya wllh, naga kamar wani jin kanka kake, ga Saleem kullum sai ya kira Farida ya ga fuskata, haka ma Bashir, ko daxu sai da Bashir ya kira muka ga fuskar juna, to kawai don bana kasar sai kayi watsi da ni, sai kace ba ni nayi wahala da kai ba, ko uwarka ce tace ka fita harkata, don dai har yau bamu san xuciyar matar nan ba” Abuturrab na shafa kansa yana murmushi yace “Ya gidan Hajja” Tace “To lafiya lau, ai naji Baban farida xai taho Nigeria ni dai nace tare xa mu taho don na gaji, babu wani abinci a nan banda gurasar alkama, to ina dalili duk na kanjale na xata wajen arxiki ne ashe ba haka ba, basu da komai sai alkama da madara” Abuturrab yace “Yaushe xa ku taho kenan?” Tace “Aa ni dai kawai ji nayi xai taho, amma ban san yaushe ba” Yace “Toh Allah ya kai mu” Tace “Kana nan kana tukin jirgin har yanxu dai ko? Don duk na sanar ma abokan arxiki da nayi a kasar nan cewar jikana tukin jirgin sama yake, bbu kamarsa duk Nigeria” Abuturrab yyi murmushi kawai, tace “Aa ba batun murmushi ba, ko sun koreka a aikin ne nake nan nake ta tsuga karya?” Yace “Ke fata kike a koreni” kiran Aneesah ne ya shigo wayar, hkn yasa vid call din yyi still, ya daga kiran, daga daya bangaren cike da fara’a Aneesah tace “Guess what My captain?” Ya jawo pillow ya kwanta ya lumshe ido cikin calm voice dinsa yace “I am not a good guesser u know….”

Hansai ce xaune kan takalmanta da kawarta Zulai da ita ma ta xauna kan takalman nata a karkashin bishiyar wani tsakar gida, Mata ne sun fi talatin a d’an tsakar gidan, ko wacce da hijabinta yarkace yarkace, wasu da goyo wasu da ciki, Hansai tace “Anya Zulai xa mu samu ganin mutumin nan yau kuwa, ni d’an cinikin awaran yau ma nake ji, don wllh Bibalo ba yi xata yi ba ta gwammace in ma kwantai ne awaran yyi, nan gaba fa sai na koma xan fara tuya, ga layi kamar baxa a xo kanmu ba, to ko wacce da matsalarta a kugunta” Zulai ta gyara xama tace “Shi sa nace maki mu fito da sassafe Hansai, amma kika tsaya dafa awara, mutumin nan aiki yake kamar yankan wuka shi sa ake masa layi wllh, idan ba da asuba mutum ya shigo ba sai ya kai magariba ma bai gansa ba, don ma mutumin baya tashi sallah kenan” Hansai tace “Toh ko dai mu je mu dawo goben da asuba Zulai? kinga fa uban layin yaushe aka xo kanmu” Zulai tace “Kin ji ki, mu kashe kudin mota kusan dubu daya kice mu tafi mu dawo Hansai??” Hansai tace “To ni ya xance? Wllh kwantai awarata xata yi yau, Allah ma yasa ta yanyanka min in dai bibalo ce, kinga idan ya so gobe sai in sake xaran dubu daya cikin kudin awaran mu taho” Zulai ta mike tace “Toh shhkn, mu tafi” Mikewa Hansai tayi tana sa6a bak’in gyalenta da duk ya takure suka fito waje tana cewa “Ni dai fatana Allah ya sa na xo gun karshen wahalata” Zulai tace “Ahaf ai fada ma 6ata baki ne wllh, in dai kika saki kudi rass xai maki aiki bbu algus, kina xaune rana tsaka xaki ga Jiddah har gida kamar an korota, wnn ai karamin aiki ne a wajensa, shi fa mutumin nan har haukata mutane ance yana yi” Hansai ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Ae ban san amfanin shegiyar yarinyar ba sai da ta tafi, ashe ita ce rufin asirina ban sani ba, gaskiya idan Allah ya dawo min da ita auren ma wllh baxata yi ba har ta mutu, tun bayan bacewarta har yau banyi cinikin awara da yafi na dubu biyu ba, shi ma da kyar, snn xan ce ma malamin ya sa mata bak’in jini yanda bbu wanda ma xai yi sha’awan aurenta a bar min a bata kawai” Zulai tace “Da dai ya fi wllh, kinga bbu ma saurayin balle yace xai aureta” A haka suka isa bakin titi Hansai tace “Allah dai ya kai mu goben, in sha Allahu komai ya xo min karshe, wahalata ta kare”

Abuturrab na tsaye balcony misalin karfe takwas na safe wayarsa kare a kunnensa yana sauraran wani abokinsa, sai da ya jira abokin ya kai aya snn yace “I thought xa a samu mata ne, in dai ba a samu matan ba kawai a bari, i will think of another alternative” Daga daya bangaren abokin nasa yace “Amma wa kake nema ma lesson teacher din?” Ya xauna saman kujeran dake balcony din yace “Wata daughter na ne” Abokin nasa me suna Farouq yace “Ohk in dai an samu matan i will let u know Capt, kasan maxan ne sun fi juriyan koyarwan” Abuturrab yace “Eh haka ne, nagode da kulawa” Daga haka suka yi sallama, ya koma parlor ya xauna, daukan wayarsa da yyi haske yyi, ya dinga kallon screen din ganin El-Basheer ke kiransa, it’s been a while da suka yi magana, duk da shine baya daukan kiran nasa, can dae ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren El-Basheer yace “Sai aka yi yaya da baka daga kirana?” Abuturrab ya jinginar da kansa da kujera yace “How are you doing?” El-Basheer yace “Saboda baka da bayanin da xaka min kan auren da kayi ma kanka ne yasa baka picking call dina??” Abuturrab ya gyara xama yace “Babu xancen wannan auren ne yanxu, shi sa ma na samu kwarin gwiwan daga kiran ka” El-Basheer yace “Ohh really? amma few days ago mun yi magana da Ahmad kuma yace min kana gidan ka da matarka….” Abuturrab ya daure fuska yace “Matar da ya aura min?” El-Basheer yace “But wait…. On a serious note Captain don kaje ka yi ma kanka aure babu shawara da kowa shine kake ignoring mutane, why are u avoiding good frnds? mu baxa mu hanaka xama da matarka ba ae no matter who she is” Abuturrab yace “Look Bashir, am serious babu xancen wannan auren yanxu, kasan ni bana karya, i don’t have any god-damn wife now…. amma this is just between i nd u don ‘yan gida basu sani ba har ynxu” El-Basheer yace “Ban gane ba, sakinta kayi?” Abuturrab yace “Ba sa’ar aurena bace ita ae, kawai tsautsayi ne da kaddara ya fada min” El-Basheer yace “Then why are u still hiding it from people at home in har da gasken ka saketa?” Abuturrab yace “Bcos we are staying under same rood with her har ynxu, and Abba won’t take it likely if he finds out na saketa, i think we should change topic now dude….” El-Basheer yace “Anyway… Ina kaduna, turo min address din gidan naka, i will be leaving in two days time in sha Allah” Abuturrab yace “Really? Yaushe ka shigo, kuma me ka xo yi” El-Basheer yace “Forward to me ur address now” Abuturrab ya d’an yi shiru, sae kuma yace “Ohk” daga haka ya katse wayar….. Ya d’an yi jimm, bayan kusan 5 minutes kawai ya tura masa Address din sannan ya mike ya wuce sama, dakin Jiddah ya bude ya ganta tana faman shafa man gashi a dogon gashinta da ya cika ko ina na kanta, atamfa ce jikinta, ta daga kai tana kallonsa, fuskarsa bbu yabo bbu fallasa shi ma yake kallonta, a hankali tace “Ina kwana” yace “Idan da abinda xa ki yi a kasa ki sauka ynxu kiyi, xuwa anjima bana son ganin ki a kasa” Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya bar bakin kofar. Mikewa tayi bayan tayi parking gashin ta saka hula ta sauka parlon, xaune ta gansa parlon yana rike da remote, ta sunkuyar da kanta ta wuce kitchen, dankali ta shiga ferewa ta soya da kwai, sannan ta fito kitchen din rike da plate din Irish da egg din, ya bi ta da ido ganin xata wuce sama yace “Ina shayin?” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Koma” Ba musu ta juya ta koma kitchen din ta sa ruwan xafi sannan ta hada shayin a cup ta kara fitowa kitchen din, still yana kallonta yace “Wani ruwan kike sha gidan nan?” Tana kallonsa tace “A bandaki nake sha, ko a pampon kitchen” Bude baki yyi yana kallonta with shock, can ya mike yace “Ruwan bandaki?” Sosai gabanta ya fadi ta fara komawa baya, ya lura da hakan gudun kar ta saki ruwan shayin hannunta tunda ya san ba setin kirki gareta ba, calmly yace “Je ki ajiye abun hannunki ki dawo” A sanyaye ta wuce sama bayan ta ajiye plate da cup din ta mike ta fito a sanyaye, lkci daya hawaye ya kawo idonta, tsaye ta gansa har sannan yana jiranta, ta makale jikin stairs bayan ta sauko cikin rawan murya tace “Gani” Juyawa yyi yana kallonta, ta sunkuyar da kanta da sauri, daga sama har kasa yake kallonta, riga da skirt na atamfa da ya kamata, babu abinda kayan ya boye na surarta, ya rungume hannunsa yace “Daga yau kada ki sake sa atamfa a gidana” Ta d’an kallesa, sae kuma ta kara sunkuyar da kanta, yace “Idan baki son Abayan da nake siyo maki kiyi yawo ba kaya kawai” Ita dai bata dago ba balle tace komai, yace “Sannan kika ce ruwan bandaki kike sha?” Ta marairaice ta girgixa masa kai, strictly yace “What??” Tace “Sae cikin dare ne nake shan na bandaki, amma da safe da rana da yamma na pampon kitchen nake sha” Gani tayi ya nufota ta juya da sauri xata koma sama yace “Allah idan kika motsa daga nan xan maki abinda ban ta6a maki ba, wato xan gaura maki mari” Kuka ta fara yi, tana hawa stairs din da daddaya da daddaya cikin rawan murya tace “Don Allah kayi hakuri” Yana isa ta fasa kara, ta durkushe wajen tace “Kayi hakuri don Allah” Bai karasa kusa da ita ba yace “Shi ruwan fridge din na waye?” Ta boye fuskarta tace “Naka ne” yace “Ni nace maki nawa ne?” Ta girgixa masa kai, yace “Toh daga yau kika sake shan ruwan pampo a gidan nan Allah sae na mareki” Ta gyada masa kai da sauri, yace “Tashi ki bar nan” mikewa tayi da sauri ta haura sama, sae a snn ta juya tana kallonsa a downstairs, yana tsaye yanda ta bar sa, da sauri ta shige dakinta. Bayan azahar El-Basheer ya iso gidan, Abuturrab ya fita ya shigo da shi, Abuturrab ya sakala hannu a kafadar cousin din nasa yana murmushi yace “The prince himself” El-Basheer na murmushi yace “It’s been long Captain….” sosai suke shige da Abuturrab sai dai ya fi Abuturrab din haske, don shi ya fi shige da larabawa wanda hakan ke nuna kilan shi din ruwa biyu ne…. El-Basheer na bin gidan da kallo bayan sun shigo yace “Everything seems perfect, sai dai unfortunately ba Aneesah ta fara shigowa gidan ba….” Abuturrab ya shafa sajensa kmr baxai ce komai ba, sae kuma yace “Kwanan nan xata shigo gidan in sha Allah, bikin Ahmad saura few weeks so, bayan bikinsa sai inyi ma su Abba magana….” El-Basheer ya shiga bin parlon da kallo yace “But wait…. Where is…. I mean the wife u married?” Abuturrab ya hade rai yace “Wacce wife din?” El-Basheer yace “Warce muka ji labarin ka aura ma kanka mana…” Abuturrab yace “Pls hakan na bata min rai wllh, Nace maka she isn’t my wife any longer” El-Basheer yace “Yes haka kace, but why not ka sanar ma kowa bbu auren??” Taku suka ji a stairs, Abuturrab ya saci kallon Stairs din da sauri, El-Basheer dai bai juya ba sae kallon Abuturrab yake yana jiran amsan sa Jiddah ta sakko walking slowly ta shigo parlon da ganin kasan a d’an tsorace take, Kallon Abuturrab dake kallonta tayi ganin irin kallon da yake mata ta d’an tsaya ta ki karasowa, El-Basheer ya juya ya kalli inda Abuturrab ke kallo, lkci daya Abuturrab ya mike, ta marairaice tana kallonsa tace “Kai ne kace in daina shan ruwan bandaki, wllh kishi nake ji” Fuska daure yace “Juya ki koma” Juyawa tayi da sauri ta koma sama, Sai a sannan ya koma ya xauna yana kallon El-Basheer da ya bi ta da kallo…..

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE