JIDDATULKHAIR CHAPTER 26 BY KHALISAT HAIDAR

Abuturrab yace “But you didn’t tell me kina xuwa Aneesah” Aneesah tayi wani murmushi tace “How will i tell you ina xuwa Aliyu, dama dalilin da yasa kake walakanta ni kwana biyu kenan, dama wata ka samu? Dama wannan ce dalili” Daga sama har kasa take kare ma Jiddah kallo tana murmushin takaici tace “Ki bar murna kin samu pilot har yana kawo ki gidansa saboda tsagwaron so, nima haka ya dinga min, but….” Abuturrab ya katse ta yace “Come off it pls Aneesah, what’s all this? I thought i explain better to you her position, she is the lady….” Aneesah ta sake kallon Jiddah da sauri, Jiddah dai banda kallonta ita ma babu abinda take, A hankali Aneesah tace “Which lady Aliyu?” Yayi kasa da muryar yace “Ba ke kika ce in kawota ta xauna gidanku ba” Sosai gaban Aneesah ya fadi don bata ta6a tunanin Jiddah ce wnn yarinya da Abuturrab ke fadi mata ba, ta dinga kallon Jiddah xuciyarta na bugawa, ta ma rasa abinda xata ce masa, Abuturrab yace “Tunda kin xo yanxu sai ku tafi tare, dama anjima nake son kai ta gidan naku, hopefully nasan Mumy ta yarda ta xauna with ur family…” Aneesah ta hadiye abu da kyar, har sannan ta kasa daina kallon Jiddah da tayi mata wani kwarjini, a xuciyarta ta shiga kokwanton anya ita ce me awaran da Aunty ta ce, or is Aliyu playing her?? Abuturrab ya juya ya kalli Jiddah bbu yabo bbu fallasa yace “Dauko mayafinki” Shiru tayi tana kallonsa, a d’an tsawace yace “Baki ji na ne?” Ta koma baya tace “Toh ina xanje idan na dauko?” Yace “Ban sani ba, wuce ki dauko” Juyawa tayi ta koma can tsakiyar parlon ta tsaya kamar xata yi kuka tace “Allah ni babu inda xanje, ba gidan Baabarmu nace ka maida ni ba, nasan ita wacece da xan bi ta” Daga maganarta Aneesah ta kara tabbatarwa ita ce me awaran, Abuturrab ya saki baki yana kallon Jiddah, Aneesah ta hade rai tace “Toh nan din gidan ubanki ne da baxa ki bari ba?” Jiddah ta kalleta, a hankali tace “Ubana fa kika ce?” Aneesah da xuciyarta ya dau tafarfasa tace “Shi din…” Lkci daya Jiddah ta fashe da kuka tace “Ba dai ubana dake kabari ba wllh sai dai naki” Aneesah ta saki jakar hannunta tace “Kika xagi ubana?” Jiddah ta goge idonta tace “Ehh an xaga, me nawa uban ya maki da kika xagesa ke?” Aneesah tayi kanta a mugun fusace, fixgota Abuturrab yyi yace “Hey are u okay, what are u trying to do?” Fixge hannunta tayi kamar wata zakanya ta nufeta, cikin tsawa Abuturrab yace “Don’t try that Aneesah, u will definitely see the other side if me by touching her” Tuni Jiddah ta tsorata ta bar wajen da gudu ta yi hanyar kitchen hakan bai hana Aneesah bin ta ba, shakota Aneesah tayi tace “Uban wa kika xaga?” Tuni Abuturrab ya nufesu, Jiddah ta kwala kara ta gatsa mata cixo a hannu, Aneesah bata yi wata wata ba wajen sauke mata lafiyayyen mari a fuska sannan ta wuntsular da ita a kasa tana cewa “Don kaza kaxanki ubana sa’an kaf danginki ne aka ce maki?” wani ihu Jiddah ta fasa tana cewa wayyo bayanta, wayyo kafarta, Kamar daga sama Aneesah taji saukan tagwayen mari wanda sai da yasa taga duhu na few seconds, ya fixgota fiercely yace “How dare you? You bitch” with shock Aneesah ke kallonsa, ya nufi kofa ya wuntsular da ita waje kamar yanda ta ma Jiddah yyi banging kofar, Banda rusa kuka babu abinda Jiddah dake yashe a kasa take tana kiran Baabarmu, Bude kofar Aneesah tayi tana daga tsaye bakin kofa hawaye kaca kaca a fuskarta tace “You called me a bitch Aliyu?? Ni ka walakanta ka sauke yatsunka fuskata a kan wannan yar talakawan bagidajiya jaka? Ni ka ci ma mutunci haka in her present? U threw me out of ur house a kan yar talakawa me tallan awara?” Jiddah ta goge idonta ta mike cike da tsiwa tace “Idan ana tafiya lahira da arxiki sae ki daura naku a kai ki tafi da shi in ga, kuma Allah ya isana, ban yafe maki ba, axxaluma….” Fixgo hannunta Abuturrab yyi ya nufi daki, cikin kuka tana son kwace hannunta take cewa “Ni ka kyaleni, me na mata xata mareni….” Turata yyi cikin dakin ya sa makulli, sai a snn ya daga kai ya kalli Aneesah, ji yyi gaba da gwiwansa ya sace, ya nufeta, tana ganin haka tayi wani murmushi tace “Watch out for it Aliyu, xaka san ba a ta6a mu a xauna lafiya, daga yau ka kafa daka sanin abinda ka min a rayuwarka…” Daga haka ta dau jakarta xata fita parlon hawaye na sauka idonta, ya rikota yyi kasa da murya yace “But Aneesah….” Ko rufe baki bai yi ba ta sauke masa mari sau biyu, hakan bai sa ya saketa ba ta dinga dukansa a kirjinsa, ya rungumeta gamm yace “I’m sorry Aneesah” kuka kawai take, shi kam duk jikinsa yyi sanyi, cikin rawar murya tace “A kan wannan bagidajiyar xaka mareni and throw me out of ur house Aliyu??” Ya kwantar da ita kirjinsa yace “U are misperceiving me Aneesah…” Turasa tayi da karfi ta nufi kofa tana kuka ta fita, dafe kansa yyi ya xauna saman kujera yana furta Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, daukar wayarsa yyi ya shiga dialing number Ahmad, har ya katse bai dauka ba, yana ta xaune parlon har kusan magrib sannan ya mike da kyar, bedroom din da Jiddah ke ciki ya nufa ya bude kofar, kwance ya ganta a kasa, ya karasa ciki yana kallonta ya duka, bacci take, ya kai hannu goshinta, bude ido tayi, ya daure fuska ya mike, ta tashi xaune tana mitsika ido, yace “Kin san warce kika xaga daxu?” Ta kallesa tace “Toh ai nima bata san wacece ni ba” ya duka yana kallonta da kyau yace “Gaya min ke wacece?” Ta turo baki ta taki cewa komai, kallon fuskarta da shatin mari ya kwanta kawai yake, can ya mike jin xa a tada sllh ya fita dakin.

Abuturrab na dawowa masallaci ya ga kiran Ahmad a wayarsa, ya xauna sannan ya kuma dialing number sa ya kai kunne, daga daya bangaren Ahmad ya daga yace “Ya kwana biyu?” Abuturrab ya shafa kansa ya mike ya koma dakinsa, a hankali yace “Alhmdlh, how is work?” Ahmad yace “Alhmdlh, baka yi piloting xuwa Abuja bane yau” Abuturrab yace “Ina Abuja” Ahmad yace “Alright, ya na ji ka so calm dude?” Abuturrab bai ce masa komai ba, Ahmad yace “Xan shigo after isha” Abuturrab yayi kasa da murya yace “Ka taho da paracetamol or any pain reliever” Ahmad yace “Ko har Aneesar ta je ne?” Abuturrab ya katse wayar, ya ajiye yana tunanin where he is going to start from, sure yasan yana son Aneesah sosai baya son komai da xai bata mata rai, But why did all this happen, why did things turn out this way…. Shafa kansa kawai yayi knowing the only way out now shine ya tura gidansu in few days time, wayarsa ya sake dauka har xai yi dialing numberta ya fasa. Abuturrab na xaune parlor bayan ya dawo isha yana jiran xuwan Ahmad, karfe takwas da few minutes Ahmad ya danna bell, ya mike ya bude masa kofa, Ahmad ya shigo parlon, xaunawa yayi saman kujera yace “After leaving me all my self with my wedding preparation, still u have d gut not to ask how everything is going…. right?” Abuturrab yace “Ohk ka fara shirye shirye ne?? Sure juma’ahn sama ne koh? I’m sorry na manta wllh, what are u up to now? Kasan ba haduwa muke yanxu a kadunan ba kamar da” Ahmad yyi dariya yace “Ya xa mu hadu kuwa, tunda ga ka ga amaryar ka Jiddah” Abuturrab ya tsura masa ido, can yace “Is there anything i will gain idan na maka karya Ahmad?? But don Allah ka gaya min me yasa kake ganin har ynxu matata ce ita?” Ahmad yace “Toh gashi nan ba sai na fada ba, da fa duk na shigo kd sai mun hadu, infact kai ma kake xuwa gidanmu ynxu kuwa kana gidanka, idan ba wanda yyi sabon aure ba, giyan auren na dibarsa waye ke yin haka??” Abuturrab yace “Ka dai jira xanyi auren kwanan nan sae kaji dadin fadin duk abinda ke ranka, amma yanxu kam i am a bachelor just as u, sae sabon title da na samar ma kaina na xama Uba, i am more like a father or guardian now” Ahmad yyi murmushi yace “Toh ka bani ita inyi ta biyu da ita Captain” Abuturrab ya kallesa, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Are you for real?” Ahmad yace “I’m serious wllh in dai Umma xata yrda i will” Abuturrab yace “Ohk, but…. How are we going to open up all this to our parent? Kasan dai ynxu banda Aunty da kai, sai ita yarinyar babu wanda yasan babu auren nan” Ahmad yace “We will cross the bridge when we reach there, yanxu dai ka amince min kai?” Calmly Abuturrab yace “In da gaske kake na amince, nima burden xai sauka kaina, if not for her da banyi making mistake da nayi daxu ba” Ahmad yace “Wani mistake?” Abuturrab ya dau remote din TV yana canxa channel yace “Ba ruwan ka” Ahmad yyi murmushi yace “Everything is settled now tunda ka amince”
Kafin karfe tara Jiddah tayi bacci bayan tayi wanka, Hijab din Aneesah dake gidan ya bata tayi sllh tun magrib. Abuturrab na xaune har sannan a parlor tare da Ahmad sae dai hankalin sa baya tare da Ahmad, bai yi tunanin Ahmad xai kai har 10 a gidan ba, Can dai Abuturrab yace “Wai kana kallon agogo kuwa?” Ahmad yace “Ohh
ta kusa xuwa kenan, anyway ko baka fada ba dama yanxu xan wuce sai da safe” Daga haka ya mike ya nufi kofa Abuturrab ya bi sa da kallo, mikewa yyi ya bi bayansa yace “Ka ajiye ni eatry let me get something to eat” A tare suka fita gidan, sai kusan karfe goma da rabi Abuturrab ya dawo, yana shigowa parlor ya kulle gidan sannan ya wuce dakin da Jiddah take, tayi nisa baccinta, Ya ajiye ledan abincin ya nufi gadon, buga gadon yayi ko motsawa bata yi ba, yayi hakan ya kai sau uku ganin bata tashi ba ya dau bottle water ya bude, sai kuma ya fasa xuba mata ruwan ya ajiye sannan ya kai hannu kafarta yana tashinta, bude ido tayi a hankali, yace “Tashi ki ci abinci” Ta girgixa masa kai tace “Na koshi” Yace “C’mon tashi nace” Mikewa xaune tayi da kyar tana kallonsa da idanuwan bacci tace “Na koshi” Ya hade rai yace “Sakko nace” Xamowa tayi ta sauka kasa tana lullumshe ido, ya bude mata tuwo da veg soup din, ta tashi tana rurrufe ido yace “Ina xa ki?” Tace “Xan wanke hannu” Bai ce komai ba ta tafi ta wanke hannun ta dawo, tun da ta fito yake kallonta, Kana ganin yanda Hijab din yayi a jikinta xaka kasan bata saka komai ba a ciki, dama kuma hijab din har kasa yake ja mata, xaunawa tayi ta jiginar da kanta jikin gadon ta lumshe ido, buga gadon yayi ta bude ido da sauri ta kalli abincin gabanta sannan ta kai hannu ta fara ci a hankali, juyawa yayi ya fita dakin…. Washegari da safe Abuturrab ya fita yayi mata shopping din few clothes, karfe goma kuma ya nufi airport tare da ita, babu abinda ya sanyaya masa jiki sai yanda kiran Aunty ya dinga shigowa wayarsa babu kakkautawa, shi kuma yaki dagawa, Jiddah na ganin inda suka xo hankalinta ya tashi, marairaice masa tayi tace “Ni fa bana son hawan jirgin wllh” Yana kallonta yace “Sai me xa ki hau?” Tace “Motar” Wani kallo yayi mata yace “Sai ki hau motar inda kika gansa ai” Lkci daya hawaye ya kawo idonta bata kuma ce masa komai ba, tun bata kai ga shiga jirgin ba taji kanta ya fara juya mata, Tana rike da wayansa da ya bata ta nemi kujera ta xauna a business class, sai waige waigen inda xata gansa ta mika masa wayar take, to ina shi yake xama ne a cikin jirgin, tunawa tayi a inda ta gansa jiya bayan jirgi ya sauka, and she assumed a wajen yake xama shi, jin taku a gefenta Jiddah ta juya, buda ido tayi sosai ganin wanda suka shiga jirgi tare da shi a rana na farko, seat dinsa ya nufa ya ajiye karamin jakar hannunsa a sama sannan ya xauna, da sauri ta dauke kanta gabanta na faduwa, wata mata ce ta xauna kusa da ita tayi mata sannu, murmushi kawai Jiddah ta mata tana juya wayar Abuturrab dake hannunta, bayan wani lkci jirgin ya tashi, suna keta hazo ta cire seat belt dinta da sauri ta mike bayan ta ajiye wayar Abuturrab, hanyar lavatory ta nufa sai a sannan Yousuf ya ganta ya bi ta da kallon mamaki, ba a dau lkci ba ta fito, matar dake kusa da ita tace “Did u feel nauseous?” Jidderh tayi mata murmushin karfin hali ta xauna, Ta d’an saci kallon Side din da Yousuf yake suka hada ido, sunkuyar da kanta tayi, throughout the short journey to kano bacci tayi a jirgin, snacks da aka kawo mata ma bata ci ba, Matar dake gefenta tayi tapping dinta tace “Ki saka seat belt dinki” Bude ido Jiddah tayi ta fara saka seat belt din, runtse ido tayi da jirgin ya fara sauka bayan ya samu izinin yin hakan, matar da ta lura she is very uncomfortable ta riketa, tace “It’s just for a few seconds, sorry dear” Jiddah bata ce mata komai ba har jirgin ya sauka, rufe bakinta tayi kar ma tayi ihu, matar na Kallonta tana murmushi tace “it’s all over” A hankali Jiddah ta cire seat belt din, bayan da jirgin ya tsaya ta mike ta dau hand bag dinta ta fara fita kamar yanda ta ga sauran nayi, da kallon mamaki matar ta bi ta, tana mamakin to ko kurma ce dai, Yousuf ya mike ya dau jakarsa ya bi bayanta da sauri, a hankali take sauka daga matakalan jirgin iska me sanyi na kadawa a filin airport din, tana sauka kasa kamar ance ta juya taga Yousuf yana saukowa shi ma, murmushi ya sakar mata har ya iso inda take yace “Jiddahh” Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, mika mata hannunsa yayi yace “Bani wayar taki in sa maki number na tunda Allah ya sa kin taho da shi yau” Ta buda ido sosai tace “Ba wayata bane, na yayana ne” Da mamaki yake kallonta yace “Yayanki? Yana ina?” Ta kalli cikin jirgin tace “Kaman yana ciki, ni dai ban gansa ba” Yace “Ina ku ke xuwa tare da shi ko da yaushe a jirgi?” Tace “Nima dai ban sani ba” Yace “Baki sani ba kamar ya?” Tace “Allah ban sani ba ne” Yayi shiru yana kallonta walking slowly together with her, can yace “Me ku ka je yi a Lagos?” Ta kallesa da sauri tace “Lagos?” Yace “Ehh” Tace “Nan ne Lagos din don Allah?” He couldn’t help it but left his mouth agape yana kallonta with surprise, ta dauke kanta tana ci gaba da tafiya yace “Wait Jiddah, are you kidding me, or you just don’t want to give me an answer” Bata ce komai ba, calmly yace “I am talking Jiddah…” Tsayawa tayi tana kallonsa tace “Ni fa ba wani turanci nake ji ba” Sake baki ya kuma yi yana kallonta, bai san lkcn da yace karya kike…. Tace “Wllh ba karya nake maka ba” Sincerely ta fadi hakan, ya shafa kansa yana sake kallonta daga sama har kasa yana naxarin abinda tace wai bata jin turanci, but how?? tsadadden abaya ce jikinta blue da ya mugun haskata, ko kwalli babu a idonta, wanda kuma bai kalli lips dinta da kyau ba, sai yayi assuming pink lip gloss ta saka coz after being pinkish har sheki lips din nata yake, ga manyan idanuwanta farare tasss kamar madara, hancinta kuwa have the perfect shape a nose should have snn ga tsayi, ya d’an mata murmushi yace “Na yarda Jiddah, yanxu ina xa ki?” Tace “Nima ban sani ba yayana nake jira, kilan yana saman jirgin har yanxu” Yace “Yayanki… iyayenku daya da shi?” Shiru tayi can kasan ranta kuma tana tunanin abinda xata fada masa, yace “Ki gaya min gaskiya Jiddah” Ta kallesa still bata ce komai ba, yace “Ina sauraranki” ta kwantar da kai tace “Me yasa kake son sani?” Yace “I just…” Shiru yayi kamar wanda ya tuna abu, sai kuma yace “Kawai ina son sani ne” Tace “Ba iyayenmu daya ba amma yayana ne” A hankali yace “Ko dai saurayin ki Jiddah” Ta wani xaro ido, sai kuma ta kyalkyale da dariya tace “Saurayi na? Saurayina fa kace? Aa ni ba saurayina bane shi wllh, saurayina sunansa Umar amma mun rabu yanxu” Yace “Umar?” Tace “Ehh, shi wannan kawai yayana ne” Wayar hannunta ya amsa da sauri tace “Nace maka nasa ne wayar” Bude screen din yayi don wayar a bude yake, ya dinga kallon hulan pilot dake jikin screen din wayar, karban wayar tayi hannunsa, xuwa lkcn bbu kowa haraban parking din jirgin sai ma’aikatan airport, Yousuf ya daga kai yana kallon Abuturrab dake saukowa daga jirgin yana kallonsu babu ko kiftawa, har sannan pilot uniform ne a jikinsa, Jiddah ta daga kai ganinsa ta kalli Yousuf tace “Shine yayan nawa” Yousuf ya d’an yi murmushi yace “Shine matukin jirgin… i guess right” Juyawa Jiddah tayi da sauri tana kallon Abuturrab, Yousuf ya karasa gunsa ya basa hannu suka gaisa yana murmushi yace “I guess you did the landing…” Abuturrab na kallonsa ya d’an yi murmushin gefen baki kamar wanda aka tilasta ma yace “Yea, i did” Yousuf yace “Nice landing….” Abuturrab yace “It’s a pleasure flying you” Yousuf ya masa murmushi sannan ya juya ya bar wajen, yana isa inda Jiddah take yace “Ina jiran kiranki kamar yanda kika yi alkawari ranan” Yana fadin haka ya wuce, Jiddah ta kalli Abuturrab da ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta…. A motarsa suke tafiya xuwa hotel din da suka sauka a kano, har sannan babu abinda yace mata, sai dai fuskarsa bbu ko digon annuri, har suka isa hotel din, kulle dakin hotel din yyi after going in together with her, yana kallonta fuskarsa a tamke yace “Waye wannan mutumin da na ganku tare?” Tace “Wai da gaske kai ne kake tukin jirgin in ji sa? Ni dai nace masa ba kai bane ae baxa ka iya ba” fixgota yyi, tayi wani kara xata durkusa ya dagota yace “Tambayar ki nake waye shi??” Kamar xata yi kuka tace “Toh ba q jirgin muke haduwa ba” ganin taki tsayawa cikin tsawa yace “Baxa ki tsaya ba” Kin tashi tayi tace “Toh don Allah ka sakeni” kallonta kawai yake yi, can ya saketa, xamewa tayi ta xauna kasa, yace “Waje daya ku ka xauna da mutumin?” Tace “Aa, kawai da na sauka jirgin shine ya bi ni yana min magana” Shiru yayi yana kallonta ita dai bata yarda ta kallesa ba, can ya juya ya bude kofar dakin ya fita. Bayan la’asar suka bar kano xuwa kaduna a motarsa, Jiddah na kallonsa after the 20 mins silence tace “Meyasa muke ta shiga jirgi bayan ga mota, kyauta ake tafiya a jirgin ne?” Ya mata wani kallo yace “Kyauta? Tsoronki ake xaki shiga jirgi kyauta?” Tace “Toh Iyah ta ta6a ce min kudin jirgi yana da tsada kusan miliyan ne” Ya d’an kalleta yace “Haba??” Ta wara ido tace “Wllh, kasan ta ta6a xuwa makka sau daya, yaranta ne suka biya mata, toh ni na xata masu kudi ne kawai ke hawan jirgi” D’an murmushin da bai shirya ba yyi yace “Ni ba me kudi bane kenan?” Ta d’an xaro ido tana kallonsa tace “Aa bance haka ba, amma wannan motar taka ce?” Bai ce komai ba, a hankali tace “Kayi shiru…” Yace “Aa na Abbana ne” Tace “Toh gidan fa?” Yace “Wani gida?” Tace “Wanda muke ciki?” Yace “Shi ma na Abbana ne” Tace “Kenan shi ne ya biya kudin jirgin da muka shiga?” Yace “Ehh” Tayi shiru tana kallonsa, ta gefen ido ya kalleta, ta sauke idonta, bayan few seconds tace “Abbana ya ta6a ce min watarana xan shiga jirgi, amma Makka yace xanje” Ya kalleta yace “Haba” Ta gyada masa kai, tace “Kuma gashi na shiga amma ban je makkan ba” Yace “Toh idan kina da kudi ki kawo in biya maki Umrah ki je” Ta buda ido tace “Kudi?? A ina xan ga kudi ni ba sana’a nake ba” Yace “Ohk kina son kiyi sana’a ne? Ko awaran xaki siyar a bakin layin gidanmu?” Dariya ta fara yi, ya dinga kallonta don bai ta6a ganin dariyarta ba, tayi me isarta sannan tace “Idan kace inyi sai inyi in dai xa a siya” Da mamaki ya d’an kalleta kafin ya maida dubansa kan titi yace “Xa kiyi kenan idan nace kiyi” Tace “Ehh, sai in yi har da wainar flawa da dankali” Yace “Toh bari mu je a samar maki waje a bakin titin ko?” murmushi ya ga tayi tace “Toh” Ji yayi kamar ya fixgota ya rankwasheta, tace “Toh amma kudin xa su taru har in je makkan kuwa?” Yace “Wannan ke xan tambaya ai, babarku ta tara kudin ya isheta har taje makka?” Shiru tayi tana kallonsa, can tace “Toh ai abinci muke ci da kudin sana’ar, wannan kuma baxan siya abinci da kudin ba tunda akwai abinci a gida koh” Shafa millionaires belt dinsa yyi still wondering if yarinyar nan xata ta6a wayewa, though ya ma yi mamakin yanda har ta fara iya dressing ko don kayan da ya siya mata sunyi correlating da mahadinsu ne, sannan bai ga tana irin kwalliyan nan na masu talla ba, a ja gira a shafa barbada kumatu, a shafa gazal, babu wanda xai kalleta yace she is local or even an illiterate sai ya ji xancen dake fita daga bakinta, mamaki ma yayi yanda ta bude baki take creating conversation da kanta yau, muryarta yaji tana cewa “Idan kudin ya taru da yawa kai ma sai in biya maka tunda ka taimakeni koh?” Ya d’an kalleta da sauri sannan yace “Haba?” Tace “Ehh, ko kuma in biya ma Umma” Murmushin gefen baki yayi yace “Ashe na taimake ki?” Tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta gyada masa kai a hankali, Bai kuma cewa komai ba, kuma bai kalleta ba, jin tayi shiru bayan kusan minti goma sha biyar, breaking the silence yace “Bayan awaran da dankali babu wani sana’ar da xa ki yi?” Ya d’an kalleta da yaji bata amsa masa ba, bacci yaga tana yi, xuwa lkcn sun fara fita outskirt din garin kano, ya kai hannu a hankali ya kwantar mata da kujeran motar, snn ya kara Ac din motar, har suka shigo garin kaduna bayan magrib bacci take, amma ta farka yyi sau biyar a hanya, mai gadi na bude masa gate yayi parking a parking space, ya sauka motar yana stretching kansa, coz he is very tired bayan tukin jirgi ga na mota, jingina yayi da motar ya rungume hannunsa, har ya mance rabonsa da workout, tun sanda burden din Jiddah ya hau kansa, xagawa yyi ya bude side dinta ya bubbuga motar slowly, a hankali ta bude ido ta fara kalle kallen inda suke, yace “Sakko” sauka ta fara yi daga motar ya koma gefe tana fitowa ya kulle motarsa. Bayan sun shiga gidan xata wuce dakinta yace “Ki tabbatar kinyi sallah” Wanka jiddah tayi sannan ta dauro alwala bayan ta idar da sllh ta saka kayan baccinta ta kwanta. Karfe tara ya shigo dakin da abinci, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai, kawai ya ajiye ledan ya fita. Washegari da ya kasance ranan juma’ah Jiddah na idar da sallan asuba ta sauko kasa ta hada shayi ta dumama abincin da ya kawo mata jiya da daddare ta wanke tukunyar da ta bata ta koma dakinta, duk kafin ya shigo gidan daga masallaci, don sai ya gama azkar dinsa yake shigowa gida, bata mance warning din da yayi mata ba, ganin har karfe sha biyu Abuturrab dake xaune parlor bai ga ta sakko ba, lkci lkci kuma ya ke kallon sama, daga karshe ya mike ya haura stairs din sannan ya bude kofar dakinta, bacci ya sameta tana yi, yayi knocking kofar da karfi wanda hakan ya farkar da ita ta mike xaune da sauri, ya wani daure fuska yace “Baki da hankali har yanxu bacci kike?” Tace “Aa nayi wanka na gyara dakin” Ganin hararan da yake mata ta dauke kanta, yace “Ohk kin fi so ki kwanta daki kullum in fita in siyo maki abinci in kawo maki anjima kice ai bani da kudi?” Buda baki tayi tana kallonsa tace “Ni yaushe nace baka da kudi?” Ya rungume hannunsa yace “Jiya a mota” Tace “Aa ni fa kudin jirgi nace baka da shi tunda ya kai miliyan daya, kuma kace min Abbanka ne ya biya ai ko??” Yace “Ehh abincin da kike ci ma ai duk shi yake siyowa in kawo maki ko” Tayi shiru tana kallonsa, can tace “Toh me yasa baka son kayi sana’a, kaga Umar yana fita kasuwa kullum, don kawunsa na da shaguna uku a kasuwan bacci…” Kallonta yake ko kiftawa baya yi, tace “Kai ma xa ka iya ce a neman maka waje a kasuwa tunda Abba na da kudi ae” Ya shafa fine beard dinsa yace “Haka ne kuma, amma ya aka yi kika san bana sana’an komai” Ta sakko da kafafuwanta daga saman gadon tace “Naga to ko da yaushe kana gida, idan baka son ka xauna a gidan kuma sai ka tafi kano, to ko sana’a kake xuwa yi a kanon?” Ya girgixa kai da sauri yace “Can ma kawai xama nake a gida, ai ba a bani sana’an da xan yi ba” Tayi shiru, sai kuma ta kallesa tace “Amma lkcn da kake xuwa hayin rigasa a ina kake samo wannan kudin da kake bani in ba Babarmu?” Yace “Abbana ke bani” Tace “Toh, shkkn” Yace “Yanxu kasuwan xan fara xuwa nima kenan” Tace “Eh ka gaya ma Abbanka ya bude maka shago” Yace “Sai ni dake mu dinga xama a ciki ko?” Kallonsa tayi ta fashe da dariya sosai dimples dinta na lotsawa, ya dinga kallonta, second time da yake ganin dariyarta kenan, tayi me isarta tace “Dama mata na xuwa kasuwa?” Ya rungume hannunsa yana kallon large eyeballs dinta yace “Tunda xa su iya xaman gefen titi su siyar da awara da dankali me xai hana??”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE