JIDDATULKHAIR CHAPTER 3 BY KHALISAT HAIDAR

JIDDATULKHAIR CHAPTER 3 BY KHALISAT HAIDAR

 

 

 

Karfe taran dare Jiddah ta fito tsakar gida ta xauna kan tabarman dake bakin kofar dakinsu, muryar Hansai ne ya kaurade d’an tsakar gidan tana ma mai gidanta isuhu masifan ita ta gaji da ciyar da shi, shi dai yana xaune baya cewa komai hakan yasa tayi ta daga murya wanda da kyar ba a jin ta a kofar gida, a hankali Jiddah ta mike ta sa takalminta ta fita gidan, wani karamin gida can karshen layinsu ta tafi, tana waige waige ta shiga zauren gidan sannan ta karasa ciki, Wata yar dattijuwa ce tsakar gidan xaune tana ma yara uku dake kwance kan tabarma fifita, Datijuwar tace “An gama tuyar kenan…” Jiddah ta kwance ha6ar xaninta ta ciro dubu biyu tace “Aa yau ai bamu yi ba Baabarmu taje gidan gaisuwa, Iyah ki ajiye min wannan Usman ne ya bani daxu mun hadu bakin titi naje auno waken suya, ki dau dari biyar, sai ki ajiye min dari biyar sai ki sa dubu dayan a asusun da nayi ma Abbana” Iyah tace “Kai Allah dai yyi ma yaron nan albarka, kwana biyu ma bai shigo ya gaisheni ba, ni da a shirye yake ai da ya fito kawai ko Allah xai yanke maki wnn shegen wahalan, kai ko da akwati daya yayi maki indai xai rabaki da Hansai yafi maki wllh, ba yace min a can cikin gari yake da iyayensa ba, nan kuma wajen kanwar babarsa yake xuwa?” Jiddah ta gyada mata kai ta mike ta nufi kofa tace “Sai da safe Iyah kar baabarmu ta nemeni” Tana fadin haka ta fita da sauri kafin a lura bbu ita a can gida, Iyah ta girgixa kai tace “Allah sarki, tsakaninsa da Allah yake sonta wllh, tsorona daya makirar bakar matar can kada ta shiga ta fita ta raba su, tunda ga bibalo babu mashinshini har yanxu sai yawon unguwa unguwa take a hayi, kuma duk sa’annin juna ne, to dai bbu ruwana tunda babu dangin iya balle na baba”

Ahmad ya gama sa cover shoe dinsa yana kallon Abuturrab dake kwance kan 3 seater hannunsa rike da remote yace “Ya naga kamar duk ka damu in tafi ne Captain?” Abuturrab ya kike xaune yace “Ohh toh ka yi xamanka mana ina ruwana, dama don kace kana night duty ne yasa nake ta reminding dinka, naga it’s almost 6, an kusa kiran magrib” Ahmad ya ta6e baki ya mike yace “Yaushe xa ku wuce kanon ne?” Abuturrab yace “Am off for someday kawai i just decided to be in Abuja for a while, may be on friday xan bi train in sha Allah” Ahmad yace “Ohh that’s great nima friday nake son xuwa kadunan, rabona da kaduna ai an kwana biyu” Daga haka ya nufi kofa ya fita, yana fita gidan ko minti goma ba ayi ba Aneesah ta shigo, Abuturrab na kallonta yace “Sorry i kept u waiting kinsan Ahmad….” Ta karaso parlon tace “Yeah i understand…” Xaunawa tayi ta ajiye jakarta, ya dawo kusa da ita yace “Kwana uku xan yi a Abuja….” Ta wara ido tace “Har uku?” yace “Yea, ko baxa ki tayani xama ba?” Ta juya ido tace “Aa kaga Dad dinmu yana gari, sai dai in dinga xuwa Ina tafiya…” Ya jingina da kujera yace “No need inyi kwana uku kenan, gobe inyi tafiyata kaduna dama sbda ke na sauka Abuja” Ta marairaice masa tace “Haba dear, to kar ka damu i will try and be with u” Mikewa tayi tace “Me xan girka maka nasan har yanxu baka ci abinci ba” Yace “Just a cup of tea now, mun sha fruits tare da Ahmad” bude kofar aka yi duk suka juya lkci daya, Ahmad ne ya shigo parlon, kallo daya yyi masu ya nufi gun da ya mance wayarsa ya dauka, yana kallon Abuturrab yace “Shi yasa ka damu in tafi kenan” Aneesah dai daure fuska tayi, kamar baxata ce komai ba sai da ya nufi kofa tace “Ina yini?” Banxa yyi mata ya fita ya kulle kofar, Abuturrab ya shafa kansa, a hankali tace “But am afraid Captain…” Yace “You are afraid of what?” Komawa tayi ta xauna da damuwa tace “I think this is the 5th time da Ahmad ke ganina a gidanka, ina tsoron kada ya sa iyayenku su ki amincewa da aurenmu” Abuturrab yace “Ni xan xauna da ke ko wani, don kina xuwa gidana does that mean anything?” Ta girgixa kai bata dai ce komai ba, ya mike ya isa kusa da ita ya kamo hannunta yace “Cheer up dear, beside Ahmad will never do that, i know who he is” kallonsa tayi da manyan idanuwanta ya sakar mata lallausan murmushi ya kai hannu dogon hancinta yace “Basu san samun me tsafta irin ki yanxu sai mutum ya dage ba?” Murmushi kawai tayi yyi pecking cheeks dinta yace “Babu wanda xai raba mu in sha Allah” hanyar kitchen ta nufa ya bi ta da kallo. Suna fitowa train station suka nufi motar dake tsaye yana jiransu, Ahmad ya bude back seat yana kallon saurayin dake xaune driver seat yace “Sorry for keeping u waiting salem, mun hadu da wani abokinmu ne muka tsaya gaisawa” Salem na murmushi yace “Ina yini ya Ahmad” Ahmad yace “Lafiya lau, ya su Aunty” Salem yace “Lafiya kalau” Abuturrab ya xaga ya shiga front seat bayan ya gama wayar da yake yana kallon stepbrother din nasa yace “How are you” Salem yace “Fine, how was the journey?” Abuturrab yace “Cool” Driving din motar salem yyi suka fara tafiya, tunda suka hau saman titin hayi idon Abuturrab ke gefen hanya, Ta madubi ya kalli Ahmad dake danna wayarsa, da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Yau baxa ka siyi awara ba kenan” Sai a sannan Ahmad ya dago kai ya kalli inda suke, ganin sun kusa wajen da yake siyan awaran yace “I had no intention but let me get it for Umma and my siblings” Abuturrab ya ta6e baki bai ce komai ba, Ahmad na kallon Salem yace “Kana wuce layin nan ka tsaya a layin gaba” Salem yyi parking dai dai inda Ahmad yace, Ido hudu Jiddah tayi da Abuturrab da sauri ta sunkuyar da kanta tana gyara hijab din jikinta, Ahmad ya bude motar ya sauka yana kallonta smiling broadly ya rungume hannunsa yace “Sannu me awara” Bata yarda ta kallesa ba tace “Ina yini” yace “Lafiya lau ya kasuwa?” Tace “Na nawa xa a sa maka?” Yace “Ki sa na dari biyar ko?” Satan kallon Abuturrab tayi suka sake hada ido ya dauke nasa idon yana kallon gefen hanya, ta gama sa awaran ta mike ta mika ma Ahmad, ya amsa yana kallonta, sae kuma ya juya ya kalli Abuturrab yace “Bani 1k wajenka I’m not with cash” Abuturrab bai ce komai ba, ita dai tana tsaye, can ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika ma Ahmad, Ahmad ya amso ya mika mata ta amsa ta koma ta durkusa xata dauko canji yace “Aa ki bari idan na xo sake siya, shkkn ba sai na sake bada kudi ba koh?” shiru tayi, lkci daya ta mike tace “Toh ai akwai canjinka dari biyar a wajena da ka siya ranan nan, ka tuna?” tana fadin haka ta mika masa dubu dayan, yace “Aa ni na manta…” Daga haka ya shiga mota yace ma Salem su tafi, da ido ta bi motar sannan ta koma ta xauna gun kaskon awaranta. Hansai ta rike ha6a tace “Yau naga ikon Allah, baxa ki fito ana jiranki ba Jiddah???” Sai kuma tana murmushi ta kalli Iliya dake xaune kan tabarma tace “Da yake bata yi la’asar ba kilan sllh ta fara, bari in shiga ciki dai” daga haka ta mike daga kan kujeran tsugunno da take ta shiga dakin, can taga Jiddah xaune kusa da ghana must go din kayansu tana kuka a hankali, Bude baki Hansai tayi tana kallonta, can ta karasa a mugun fusace ta fincikota ta bugata da bango murya can kasa tace “Don ubanki kina ji na kika kyaleni bawan Allah ya xo tun daxu yana jiranki? Saukansa fa kenan daga legas yace kuma anjima da daddare xa su bi tirelan kaya su koma” Cikin rawan murya hawaye na sauka idonta tace “Wllh Baabarmu bana sonsa, shaye shaye fa yake….” Bata rufe baki ba Hansai ta buge mata bakin da karfi ta rankwasheta ta hankadata bakin kofa tace “Fita kar in sumar da ke, yar bakin ciki kawai muguwa” Goge hawayenta tayi ta fita da sauri tana hadiye kukan dake son subce mata, Can nesa da tabarman ta xauna ta hade rai taki cewa komai, Iliya na murmushi da jajayen idonsa yace “Hauwa kuluwa kwandon kilishi…” Sosai ta kara hade rai, yace “To d’an kalleni mana farin cikin xuciyataa” wani harara ta xabga masa, yayi wani murmushin da lebensa da ya dafe saboda shaye shaye ga idanuwansa kamar garwashi, yace “Mun sauke wani kayan ne yau, amma mun yi lodi xa mu koma xuwa nan da bayan magariba” Ita dai ko kallonsa bata sake yi ba, ya ciro rafan ‘yan ashirin ashirin guda biyu sababbi ya ajiye kusa da ita yace “Hansai tace Babanki ya bukaci in turo magabatana, to in sha Allahu ranan laraba xamu yo lodi daga lagos, ina dawowa kuma xan turo tsohona da yayansa, a nan take ma xa a bada sadaki a saka mana rana, don ni a shirye nake” Wasu hawaye suka kawo idon jiddah, ya mike yace “Kice ma Hansai na tafi sai Allah yayi mana dawowa” daga haka ya fita ta bi sa da kallo da dafaffen farin shaddan jikinsa, yana fita Hansai dake la6e tana sauraron duk abinda yace ta fito, dauke kudin tayi tace “Allah yayi masa albarka, ai iliya ba dai xuciya ba, ga masara can ya kawo mana rabin buhu, da wake xai yi kwano biyar wllh, Allah yayi masa albarka” tana gama fadin haka ta dau gyale ta fita gidan….. Jiddah ta hade kai tana kuka sosai, mikewa tayi ita ma ta fita gidan, ta shiga gidan iyah, Iyah ta dinga salati tana kallonta ganin yanda take kuka, duk lallashin duniyan nan tayi mata amma taki sauraronta balle tayi shiru, Iyah tace “Atoh bari in je in ci gaba da tankade gari na kawai” daga haka ta mike ta koma gun da take tankadenta ta xauna ta ci gaba, Da kyar Jiddah ta dago kanta bayan wani lkci tana share sauran hawayen idonta cikin rawar murya ta shiga gaya ma Iyah abinda ya faru, Iyah ta ajiye matankadin hannunta tace “To ubanki ya xama sususu shashasha kenan, banda haka meye mutum xai maida kansa kamar gunki, ko min wani irin asiri tayi masa ai bai ci ya xama kamar gunki haka ba, mutum kawai bai da amfani Allah na tuba, Hansai dai wllh baxata gama da duniya lafiya ba, me yasa bata ba ma Bibalo iliyasun ba, waye bai san iliya ba a garin nan, kawai don axxaluma ce ita ta dage sai ta hadaki da d’an gwangwan d’an shaye shaye? Ranan babu inda labari bai kai ba kan cewar Iliya ya mari mahaifinsa, ba ga uwarsa can a kana radd ba tana 6ara, kanninsa mata kuwa duk karuwanci suke kowa yasani ba wani boyayyen abu bane, ohh na shiga uku ni iyantama, kaiii Hansai da kyar taga annabin rahama, da tasan abun arxiki ne iliya wllh baxa ta so ki da shi ba sai dai Bibalo amma da yake tasan waye shi sai cusa maki shi take alallai adole….” Jiddah dai kuka kawai take, Iyah tace “To dai ba ruwana nawa ido tunda ‘ya yana sun hanani shiga maganan da bai shafeni ba, barin ma na gidan Hansai matar da bata gaji mutunci ba” tana fadin haka ta tafi ta ci gaba da abinda take, a hankali Jiddah ta mike tana share idonta ta fita gidan kada Hansai ta koma taga bata nan.

Abuturrab na xaune parlon Umma tare da Ahmad suna cin abinci a tare, Umma dake xaune tana kallo tace “Toh ba dole ku yi shiru ba dama” murmushi kawai Abuturrab yyi, Ahmad yace “Ni xan kawo maki ita ai ta gaisheki Umma….” Umma ta katse sa tace “Ka kawo min wa?” Bai kuma cewa komai, Abuturrab yace “Warce xai aura wai Umma” Umma tace “Akwai wata da xai aura bayan Ramlah ban sani ba?” A tare suka kalleta, Ahmad dai ya ci gaba da cin abincin gabansa bai ce komai ba, Umma tace “Ban da dai ku yaran yanxu abinda ku ke hange daban gida bai koshi ba ai ba a kai waje ba, is there anything wrong with Ramlah da baxaka iya aure ba?” Still Ahmad bai ce komai ba, Umma tace “Ni baxan yi abinda xai cutar da kai ba, meye da Ramlan da baka sonta ka gaya min” Jin bashi da abun ce mata ta mike ta fita daga parlon, Abuturrab dai sai kallon Ahmad yake, bayan few seconds Ahmad ya dago ya kallesa, d’an murmushi kawai yyi ya ci gaba da cin abincinsa, calmly Abuturrab yace “I dont want to believe kayi ma Umma shiru ne saboda Ramlah kanwata ce” Ahmad ya d’an kallesa sai dai he was mute, Abuturrab ya girgixa kai yace “Don’t be quiet because of me, coz if i were in ur shoes i wont keep quiet, baka son Ramlah ga warce kake so to meye na yin shiru? Abinda ake tunanin shi xai karfafa xumunci shi ke 6ata shi, meet Umma…. Pour out ur mind to her, tell her who u intend marrying” Murmushi kawai Ahmad yyi ya maida dubansa kan TV, mikewa Abuturrab yyi yace “Xan amsan ma Ummi drugs a pharmacy so i will be on my way now” Ahmad yace “Alright, anjima da daddare xan shigo in sha Allah” Abuturrab yace “Ok then” daga haka ya fita parlon, amma sai da ya fara shiga main parlor yyi ma kanwar Mahaifiyarsa sallama sannan ya fita gidan. Abuturrab na bedroom dinsa bayan magrib Ahmad ya shigo, Ramlah ce biye a bayansa hannunta rike da cup din shayi da xata kai ma yayanta kamar yanda ya sa ta, Ahmad ya xauna gefen gado, Abuturrab na kallon Ramlah bayan ta ajiye shayin yace “Aunty ta dawo?” Ta girgixa kai tace “Aa bata dawo ba” Yace “Ohk” Ta kalli Ahmad dake danna wayarsa tace “Ya Ahmad su Umma fa?” Ya kalleta yace “She is fine, ya school?” tace “Lafiya lau, ya su Siyama” Yace “Alhmdlh” tace “Kai ma in hado maka shayin?” Yace “Aa sai kace nine Abuturrab” Dariya tayi, Abuturrab dai bai ce masu komai ba, ta nufi kofa, bayan ta fita Abuturrab yace “Mun yi waya da El-Basheer daxu yana gaisheka” Ahmad yace “Oh Yarima, kwana biyu bamu yi magana da shi ba ma” Abuturrab yace “Xai shigo Kadunan amma may be kana Abuja lkcn” Ahmad yace “Allah sarki, Allah ya kawosa lfya” Abuturrab yace “Did u talk to Umma?” Ahmad yace “About what?” Abuturrab yace “Ohh har ka manta” Ahmad yyi murmushi yace “No i dont need to, tunda ga abinda Umma take so, in sha Allah hakan xa ayi” Abuturrab ya mike a fusace yace “What nonsense, why will u say so bayan kai ba son hakan kake ba” Ahmad yace “Tunda Umma tana so nima dole in so” Abuturrab yyi masa kallo yace “Why just speak like an illiterate now?” Ahmad yace “Wait Captain, is there anything wrong with Umma’s choice?” Abuturrab yace “Yes tunda ba son choice din kake ba” Dariya Ahmad yyi yace “Mun ta6a magana da kai nace bana son Ramlah? Asali ma duk cikin cousins dina babu wanda muke shiri da irin Ramlah, Ramlah was kinda brought up in our home since she was 2, tunda takwaran Umma ce kuma rainonta ce ita shi yasa take son ta hadamu, fine if Ramlah is okay with that ni bani da damuwa” Tsaki Abuturrab yyi ya koma ya xauna, Can yace “Ita kuma Maryam din dama yaudaranta kake kenan?” Ahmad yace “Idan wani xai min wnn kallon banda kai Abuturrab, it’s just that my Umma’s choice is my choice” Abuturrab ya jawo wayarsa dake ring ganin Aneesah ke kiransa ya katse ya shiga kiranta, Ahmad ya mike yace “Bari in gaida Ummi” daga haka ya fita dakin….

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE