JIDDATULKHAIR CHAPTER 34 BY KHALISAT HAIDAR

Ranan asabar kamar yanda Ummi ta sanar ma Umma aka kai kudin auren Aneesah, on that same day kuma aka saka ranan bikin wata biyu, Umma na xaune parlor da yamma Hajja ta shigo parlon ta rike ha6a tace “Ramlah kinji wai an sa bikin Aliyu nan da wata biyu, yanxu Usman ya kirani yake sanar min, sun kai komai saura sadaki” Umma tace “Toh Allah ya sanya alkhairi” Hajja tace “Atoh dai, mu iyakar abinda xa mu ce kenan, yaron da baya mutunta iyayensa….” Daga haka ta juya ta koma ciki, ita dai Umma bata ce komai ba. Abuturrab na xaune shi kadai a parlorn gidansa dake Abuja idonsa na kan screen din wayarsa da yake dannawa…. knocking din kofar parlon aka yi ya kalli hanyar kofar, amma bai yi wani yunkurin tashi ya bude ba, aka sake knocking duk a tunaninsa Aneesah ce, wayar hannunsa ya fara vibrate ya ga Ahmad, yyi ta kallon wayar kafin ya daga ya kai kunne, Ahmad yace “Are visitors not welcome any longer?” Abuturrab yace “Nace maka ina nan ne?” Ahmad yace “Su kuma takalman da ka bari bakin kofa fa?” Abuturrab bai ce komai ba ya katse wayar, bayan few seconds ya mike ya nufi kofar ya bude ya dawo cikin parlon, kallonsa kawai Ahmad yake don rabon da ya gansa an yi sati uku yanxu, ya kirasa severally baya responding, har ma ya daina kiransa, Ahmad ya karasa ya dau drugs da ya gani kan center table yana jujjuya su, lkci daya ya ajiyesu yace “Bai kamata ka dinga shan irin wa ennan magungunan saboda yanayin aikin ka, and why are u having sleepless night?” Abuturrab ya kallesa yace “Haka nace maka?” Ahmad yace “Aa haka dai drugs din yace min…” Abuturrab yace “Then you are mistaken, ka kara gaba can da karyar likitancin ka…” Murmushi Ahmad yyi yace “Toh Shikenan, amma da an canxa maka prescription din drugs din” Abuturrab yace “Wannan kuma likitan da ya fi ka yayi prescription din” Ahmad yace “Ohk then, kwana da yawa, i called severally baka responding ko nayi wani laifi ne” Abuturrab ya ki kallonsa, Ahmad yace “Shine dai yau sanin schedules dinka nace bari in karaso gidanka na nan inji laifin da nayi” Abuturrab yace “I just decided to live my life without hypocrite” Ahmad ya buda ido sosai yace “Hypocrite? Su waye hypocrite din?” Abuturrab yace “Decision dina kenan” Ahmad yace “Kai ne babban hypocrite ai tunda har kana tunanin anyi wronging dinka amma ka kasa bude baki kayi magana ka dau gaba da mutane, balle ni dai nasan i did nothing to you” Abuturrab ya jefa masa wani kallo yace “You did nothing to me?” Ahmad yace “Of course, ba abinda na maka” Abuturrab yace “That’s ur cup of tea… To yanxu bayan munafurcin da ku ka je ku ka hada har aka sa na saki wancan yarinyar ko da akwai wani abu da ya ragu a rayuwata tun bayan wannan lkcn, akwai wani abu da nayi loosing?” Ahmad yace “Eh mana gashi har bacci kayi loosing, sbda duk wanda ke isasshen bacci babu abinda xai hadasa da wa en nan kwayoyin dake gabanka….” Kallonsa kawai Abuturrab ke yi babu ko kiftawa, Ahmad ya daga shoulder yace “And da bai dameka ba ko baka yi loosing komai ba babu abinda xai sa ka dinga isolating kanka daga cikin al’umma, but that’s not my problem now, my major problem is that daga yanda na ganka nasan you are down for now may be they took u unexpected, don haka take a break from work, kada wataran muje mu ji labarin da ba shi kenan ba, shi Pilot banda nutsuwa da kwanciyar hankali ba a bukatar komai daga garesa, amma yanxu yanda kake a birkicen nan bai kamata ka dinga daga al’umma xuwa sararin samaniya ba, toh bayan wannan kuma ina son ka cire duk xargi a ranka, ka bar ganin ko da hadin bakina aka saka ka saki Jiddah, i know nothing about it… Kawai dai coincidentally nayi maka magana da kwana biyu sae kuma abinda ya faru ya faru, da ina da niyyar sanar ma kowa tun farkon auren xan sanar ae ba sai da aka dau lkci ba” Abuturrab yace “To ko kai ka fada ko ba kai ka fada ba ance maka abun damuna yyi ne? Banda ma wani burden da aka sauke min meye nayi loosing a lamarin nan, sae ma peace of mind da freedom da na samu, plss close this chapter, ba shi da wani amfani a gareni” Ahmad yace “Ok then, i heard su Abba sun xo gidansu Aneesah yau” Abuturrab yace “You heard right!!” Ahmad yace “Toh Allah ya sanya alkhairi” Abuturrab bai tankasa ba ya mike ya shiga kitchen, Ahmad ya bi sa da kallo yana murmushi, Hmm is Abuturrab really sure he looses nothing living without Jiddah?” Har karfe sha biyu Ahmad na gidan kasancewar bashi da night duty, ya tashi ya shiga bedroom yyi kwanciyarsa ya bar Abuturrab yana operating laptop. Karfe uku da yan mintuna Ahmad ya fito parlor ganin Abuturrab bai shigo ba, bai gansa a parlon ba har sannan kuma wutan parlon na kunne ga laptop dinsa ka a kunne, kitchen ya karasa nan ma bai gansa ba, ya fito ya duba sauran dakunan duk baya ciki, ganin kofar parlon da ba ayi jamming ba ya karasa ya bude kofar, xaune ya gansa balcony with his phone, da mamaki Ahmad yace “What are you doing here by this time?” Abuturrab yace “Zafi nake ji” Da mamaki Ahmad yace “Xafi kuma ga Ac ga fanka? Are you okay?” Abuturrab yace “To iskan waje nake so ba na Ac ba” Ahmad ya fi minti biyu tsaye yana kallonsa, Abuturrab bai kuma kallon inda yake ba, Ahmad yace “Ka sha drugs din naka?” Abuturrab yace “Ae ba kai ka min prescribing ba balle ka tambayeni” Ahmad bai kuma ce masa komai ba don sae a sannan ya tuna cewar ya sha wajen karfe sha daya, juyawa yyi ya koma parlon ya xauna yana mamakin is Abuturrab okay?? Har kiran sallan farko Abuturrab na xaune balcony, Ahmad ya gaji da xama ya koma daki ya kwanta. Da asuba Ahmad ya fito da alwala parlon, dai dai sanda Abuturrab ma ya fito daga bathroom din parlon, shi dai Ahmad kallonsa kawai yake har ya fita don bai ga alamar ya kwanta ba, Abuturrab ya bi bayansa xuwa masallaci… Bayan an idar sun fito mosque din Ahmad na kallonsa yace “Karfe nawa xaka yi piloting yau?” Abuturrab yace “Karfe daya…” Ahmad yace “Okay…” Gidan ya shiga ya dau makullin motarsa ya fito ya ga Abuturrab xaune balcony yace “Xan dawo before 7” Da ido Abuturrab ya bi sa har ya wuce. Kamar yanda ya fada karfe bakwai ya dawo gidan, xaune ya tadda Abuturrab a parlor ya jinginar da kansa jikin kujera, Ahmad ya xauna ya ajiye ledan hannunsa yace “Good morning” Abuturrab yace “Afternoon duty ka koma yanxu” Ahmad na bude ledan da ya ajiye yace “I think u are suffering from lack of sleep” Abuturrab ya dinga kallonsa yace “Wa ye xaka yi ma allura? Ni nace maka bani da lafiya ne??” Ahmad ya kallesa yace “Aa baka ce min ba, but this will help” Abuturrab ya gyara xama yace “You are wasting ur time, gwara ma kar kayi wasting alluranka, idan kuma ka hada sae ka nemi wanda xaka yi ma” Ahmad bai tanka sa ba ya gama hada ruwan alluran, sannan yace “Kaga kar ka 6ata min lkci ka 6ata ma kanka lokaci Captain, how will a normal human being stay all through the night without sleeping, sannan anjima yaje ya daga jirgi with over 300 passengers or less??” Abuturrab yace “Wai kai nace maka banyi bacci bane, shkkn kuma mutum daga farkon dare har karshe sae yayi ta bacci?” Ahmad yace “Duk kwararren likita ya ganka yasan baka bacci bawan Allah, don haka idan xaka daina gardama ka daina….” Abuturrab yace “Ashe kai kwararren likita ne” Mikewa Ahmad yyi yace “You ur self will feel relieved after the injection….” It took anoda 15mins to convince Abuturrab sannan ya yarda Ahmad yyi masa alluran, in just less than 20mins ya kwanta nan kan doguwar kujera, Ahmad dake watching dinsa yace “Da dai ka tashi ka shiga ciki baccin xae fi maka ma’ana” Tashi Abuturrab yyi ya wuce bedroom dinsa, yyi rub da ciki saman gado…. Sae wajen takwas da minti goma Ahmad ya bar gidan bayan ya ga Abuturrab yayi bacci. Sha biyu da rabi na rana Ahmad ya dawo gidan ya tadda Abuturrab yana bacci har sannan, ya ajiye masa ledan takeaway din abincin da ya kawo masa, ya karasa yana kallonsa da kyau, lkci daya Abuturrab ya bude ido, ya dafe forehead dinsa yace “What’s the time, our flight is…” Da sauri ya mike xaune yace “Karfe nawa?” Ahmad ya rungume hannu yace “This is after 12” Abuturrab ya xaro ido yace “What????” Tashi yyi daga kan gadon yaji wani jiri ya debesa ya koma, Ahmad yace “Look, don’t deceive ur self nd ur Airline Captain, ka tura masu text yanxu cewar baka da lafiya” Abuturrab yace “Ni nace maka bani da….” Rike cikinsa yyi da sauri, yace “I feel like throwing up” Ahmad ya karasa ya bude masa bandakin, da kyar Abuturrab ya tashi ya shiga bathroom din. Karfe shidda suka iso train station na rigasa, Salem na cikin mota yana jiransu, Ahmad ya bude front seat ya shiga, Abuturrab ya xauna bayan motar ya jinginar da kansa da seat, Salem na kallonsa ta madubi yace “How are you feeling now?” Abuturrab yace “Alhmdlh” Salem ya gaisa da Ahmad sannan ya tada motar suka bar station din. Da magrib Aunty na tsaye kan Abuturrab dake kwance saman gadonsa with drip, tace “Ko wannan aikin naka ai ya isa yyi weighing dinka down, aiki babu hutu kullum mutum na sararin samaniya” Shi dai bai ce mata komai ba, tace “Toh Allah ya sauwake” daga haka ta juya ta nufi kofa ta fita, Aisha ce ta shigo dakin da cup din shayi ta ajiye masa tace “Ya jikin yaya?” Yace “Ummi fa?” Tace “Tana can daki” bai kuma cewa komai ba ta ajiye shayin ta fita. Umma ce xaune parlor tana kallon Ahmad da bai jima da shigowa gidsn ba, tace “Toh ya jikin nasa yanxu?” Ahmad yace “A’a da sauki nayi masa allurori kuma na sa masa drip” Umma tace “Ikon Allah, kuma yaya bata gaya min ba wllh, bari in kirata” Wayarta ta dauka ta shiga kiran yayarta, Bude kofar parlon aka yi Jiddah ta shigo da sallama rike da qur’ani da takardunta, Ahmad ya amsa, ta karasa parlon ta duka kasan carpet a hankali tace “Ina yini?” Yace “Lafiya lau Jiddah, har kun gama karatun?” Tace “Eh, ya Aunty Ramlah?” Yace “Tana can gida ai, baku je bane?” Tayi murmushi tace “Aa bamu je ba” Umma tayi ma Ummi sallama bayan ta daga wayar, suka gaisa sannan tace “Yaya ashe Aliyu bai ji dadi ba” Ummi tace “Ehh haka aka ce min” Umma ta kalli Ahmad tace “Wai dama ba can gida yake ba?” Ahmad yace “Can yake” Umma tace “Toh baki shiga kin dubasa bane Yaya?” Ummi tace “Aa masu dubasa dai nayi, ni yace min bashi da lafiya ne?” Umma tace “Aa yaya ai rashin lafiya daban ne, da kin shiga kin dubasa ai, nima ynxu Ahmad ke gaya min shi ya taho da shi daga Abuja ma” Ummi tace “Allah ya kara mana lafiya gaba daya” Umma ta d’an yi shiru sae kuma tace “Toh Ameen” sallama suka yi ta ajiye wayar, Umma ta kalli agogo dake nuna biyar da rabi sannan ta kalli Jiddah tace “Malamar ta tafi ne?” Jiddah tace “Ehh ta tafi” Wayar Umma ya fara ring ganin Ummi ke kiranta ta dau wayar ta mike ta wuce cikin daki, Ahmad na kallon Jiddah yace “Hope baki bukatar wani abu yanxu?” Ta girgixa kai tace “Aa ba komai” Yace “To ya karatun?” Tace “Alhmdlh” Yace “Kina dai ganewa sosai ae” Murmushi kawai tayi tace “Ina ganewa” yace “Toh ki dinga maida hankali sosai pls kin ji?” Ta gyada masa kai, a hankali tace “Ina son in tambayeka wani abu” yana kallonta attentively yace “Toh ina jin ki Jiddah” Ta sunkuyar da kanta tace “Don Allah xaka iya kai ni can gidanmu in ga Baabarmu?” Sake baki yayi yana kallonta, can yace “Me xa kiyi ma baabar taku?” Cikin sanyin murya tace “Ina son xuwa in gaisheta” Ahmad ya girgixa kai yace “ko xaki je ba yanxu ba tukun Jiddah….” Tayi kasa da murya tace “To akwai wata Iyah a layinmu, tana min kirki sosai, baxan iya xuwa gaisheta ba ita?” Da mamaki Ahmad ke kallonta, can dai yace “A layin baabar taku?” Ta sunkuyar da kanta, Murmushi kawai yayi ya rasa abinda xai ce mata… Umma ce ta shigo parlon, tana kallon Ahmad tace “Idan anyi magrib sai ka kai ni can gidan in duba Aliyun” Ahmad yace “Toh Allah ya kai mu” kitchen ta wuce, Jiddah na kallonsa tace “Bashi da lafiya ne?” Ahmad yace “Ehh amma da sauki” Tana kallonsa tace “Nima xan iya bin ku in gaishesa da jiki?” Ahmad yace “Sai yanda Umma tace” Bata kuma cewa komai ba, bayan few seconds ta kallesa taga kallonta yake, murmushi ya sakar mata, ta sunkuyar da kanta tana murmushin ita ma sannan ta mike tace “Xan kai kayan karatuna daki” Yace “Toh Jiddah” Tana fadin haka ta yi hanyar dakinsu. Da magrib kamar yanda Umma tace ta shirya don xuwa duba Abuturrab tare da Ahmad, Jiddah ta rasa ta yanda xata ce mata ita ma tana son xuwa ta dubasa, ganin Ahmad ya fita kafin Umma ya fito ta bi sa da sauri ta riskesa a waje tace “Yaya don Allah xaka tayani gaya ma Umma, ni ina jin tsoro” Ya wara ido yace “Aa nima ba ruwana sai dai ki gaya mata da kanki” Jikinta yayi sanyi, a hankali tace “Toh” sannan ta juya ta koma cikin gidan, Umma ta fito parlor da hijab da jakarta tana kallonsu Maimoon dake parlon tace “Kar dai ku bar ruwa ya cika yyi ta xubewa….” Maimoon tace “Umma ni ma xata da mu xa ku je mu duba yayan muma?” Umma tace “Ba cewa kika yi kina da Hadda ba” Maimoon tace “Toh shkkn sai kun dawo” Safiyya dai na xaune tana danna wayarta, Umma ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo, a hankali tace “Umma sai kun dawo” Umma tace “Yauwa, kema kiyi karatun ki duk da dai ba kallo kike ba na sani” Jiddah bata ce komai ba har Umma ta fita parlon… Umma na shiga mota Ahmad ya kalleta yace “Umma na xata da su xa mu je can gidan su duba Aliyun, daxu Mumy ta tambayeni nace xan taho da su….” Umma tace “Toh ai ni baka gaya min ba, kuma sai a bar Huraira ita kadai a gidan?” Ahmad yace “Toh shkkn” Xai tada motar Umma tace “Bari su fito din dai” Wayar Safiyya Umma fa kira, tana dagawa tace “Safiyya wai yayanku ku fito mu tafi tare” Tana fadin haka ta katse wayar, Tun da suka fito outside gate din Ahmad ke kallon Jiddah sai dai ba ga expression da yake expecting gani a fuskarta ba, ita da Maimoon suka shiga bayan motar sannna Ahmad ya kunna motar suka bar layin…. A kofa gida yayi parking, Safiyya ta sauka sannan jiddah ma ta sauka, su Umma ma suka sauka duk suka shiga gidan, Ummi ce xaune parlor tare da Hajja, Hajja na cewa “Tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irin haka ba wllh sai a kanki…” Sai kuma tayi shiru tana amsa sallaman Umma, Umma tace “Sannu Hajja” Hajja tace “Yauwa sannu, sai kika ji Aliyu ba lafiya ko?” Umma tace “Eh wllh” Hajja tace “Toh mu ma haka muka ji, ashe wannan yaro Ahmad ne ya tafi ya dauko sa a Habuja rai a hannun Allah, ni dai dama nace wannan halin da ya tsiro ma kansa ba halinsa bane, ashe bashi da lafiya ne bawan Allah” Umma tace “Allah dai ya basa lafiya, yana dakinsa ne?” Hajja tace “Ehh yana can an kara masa ruwa, kai har makota babu wanda bai shigo dubasa ba amma uwarsa ta ki shiga ban san dalili ba” Umma dai bata ce komai ba ta yi hanyar dakin Abuturrab, yana xaune hannunsa rike da bowl din farfesun hanta, Aunty ma na xaune dakin tana cewa “Idan ka ci wllh xaka ji dadin bakinka, sannan kar kaji komai ni da kaina na maka sai da na tsaftace shi” Aunty tace “Aa sannu da xuwa Hajiya Ramlah” Umma tace “Yauwa sannu ya mai jiki?” Aunty tace “Aa yaji sauki wllh, ai da ma baku wahalar da kanku kun fito ba, jiki ai da sauki sosai” Umma na kallonta tace “Xuwa duba d’an nawa ne wahal da kai?” Aunty tace “Aa wai naga dare yayi ne ai…” Umma tace “To ba wahal da kai bane, d’a na ne halaq malaq” Aunty dai bata ce komai ba, Umma na kallonsa tace “How are you feeling now” Ya sunkuyar da kansa yace “Alhmdlh da sauki” Aunty tace “Nace maki ai da sauki” Umma ta kalleta tace “Naga shi ma yana da baki ai Hafsah” Aunty ta mike tace “Bari a kawo maka shayin Aliyu” daga haka ta fita, Maimoon da Safiyya ne suka shigo dakin da sallama, Umma da ta nemi waje ta xauna ta kallesu tace “Ina Jiddar?” Sai a sannan Abuturrab ya daga kai suka yi ido hudu da Jiddah da ta shigo dakin a lkcn, Maimoon da Safiyya suka xauna kasan carpet din dakin suna kallonsa suka yi masa ya jiki, yace “Alhmdlh” kusa da Umma Jiddah ta xauna a kasa tana kallonsa a hankali tace “Ya jiki?”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE