JIDDATULKHAIR CHAPTER 50 BY KHALISAT HAIDAR
Har Jiddah ta isa bakin titi waigen layin take xuciyarta na bugawa, tana ta tsaye har ta samu adaidaita ta hau ta gaya masa inda xai kai ta, dai dai kofar gidan Umma mai adaidaita sahun yayi parking ta sauka ta ciro kudin da Umma ta bata jiya a jaka ta mika masa, ya bata canji sannan ta shiga cikin gidan… Babu kowa parlon don su Maimoon sun tafi Islamiyya, ta karasa kitchen don gaida Huraira dake aiki a ciki, Huraira tace “Dama Umma tace sai yau xaki dawo da aka ji shiru har dare jiya” Jiddah ta d’an yi murmushi kawai tace “Umma bata tashi ba?” Huraira tace “Bata tashi ba ko” Juyawa Jiddah tayi ta wuce dakinsu, sai da ta fara shiga bandaki ta wanke baki tayi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga bayan ta gama shafe shafenta sannan ta kwanta, da ta runtse ido abinda Abuturrab yayi mata kawai take gani, tana ganin hakan kuma sai gabanta ya fadi, ita har yanxu ganin lamarin take kamar a mafarki, da yake bata wani samu baccin kirki daren jiya ba nan da nan bacci me nauyi ya dauketa. Karfe sha daya saura Umma ta fito daga dakinta ta dalilin kiranta da Huraira taje tayi wai tayi bakuwa, Tsaye taga Hajja a parlon sai hura hanci take, Umma ta karaso tana kallonta tace “Lafiya Hajja?? sannun da xuwa” Hajja ta dakatar da ita tayi mici mici da ido tace “Jiddah ta dawo??” Umma ta kalli Huraira dake bayan kujera a tsaye, Huraira tace “Ehh ta dawo tun daxu amma tana daki tana bacci” Umma ta kalli Hajja, Hajja ta rushe da kuka ta nemi kujera ta xauna tace “Toh a gaskiya Allah ya isa, wannan daga min hankali da tayi taje don kanta, idan kuma ke kika koya mata hakan kema kije don kanki… Kuma ni ban san haka take ba da ban fara xura jiki ina kulata tun farko ba, ashe su Maimu da Aisha kananun yan iska ne a inda wannan yarinya jiddah take ban sani ba?? Amma ba komai nasan duk karatunki ne ta dauka ba wani abu ba” tana fadin haka ta fyace hanci, Umma da ranta ya gama baci tace “Kawai sai in xaunar da ita don rashin aikin yi ince ta baro gidan da ku ka je da sassafe ko Hajja??” A fusace Hajja tace “Oho… Xaki aika wllh, waye bai sanki da halinki ba? dama kuma da ya kika bari ta bini, bai sai da na hadaki Allah… annabi ba?? ni dai ai na gode Allah da ta dawo gida lafiya abu bai sameta a hanya ba balle hukuma su garkameni ko jikana, wai kawai ina farkawa daga bacci barawon da ya sace ni da asuba sai naga daki wayam babu mata babu dalilinta, ban kawo komai a rai ba ina ta jan carbi har kusan karfe tara, nace kai bari dai in sauka in duba ko kumallo take nema mana a kitchen, ina sauka naga gidan wayam babu ita babu isilinta, na duba inda takalmanmu suke naga ai babu nata sai nawo kwallin kwal kamar maye, da gudu na koma sama na taso wancan mutumi Aliyu shi ma dai ya fito muka yi ta bulayin neman yarinya a cikin gidan, banda kuka da rokon Allah ya taimakeni babu abinda nake a lkcn, daga karshe ya bada shawaran mu taho nan kilan ta dawo, shine fa na taho ko wanka banyi ba yanxu haka, abinda ban ta6a yi ba a Masar, gudun fitinarki ma gashi can yaki shigowa yana can xaune cikin mota, to yana da gaskiya mana tunda bai san ko yarinyar ta dawo ko bata dawo ba, daga ni har shi sai ki iya sa a garkame mu kadan da aikin ki” Umma ta kalli Huraira tace “Kira min Jiddah” Huraira ta tafi daki, a durkushe taga Jiddah ta daura kanta saman gado idonta lumshe, baccin ma gaba daya ba me dadi tayi ba banda mafarkan Abuturrab babu abinda take, ga ciwon ciki da ya matsa mata, Huraira tace “Lafiya Jiddah” Da sauri ta bude idonta sai kuma ta dago kanta daga saman gadon ta nuna mata cikinta alamar yana mata ciwo, Huraira tace “Subhanallah sannu kinji, xaki iya fitowa kuwa, Umma na kiranki” Jiddah ta daure ta mike ta dau hularta ta saka sannan ta fito parlor, wani kallo Hajja ta dinga mata daga sama har kasa, Jiddah ta kasa kallonta ta karaso parlon ta durkusa, a hankali tace “Ina kwana Umma” Umma tace “Lafiya lau, why did u leave without telling anyone?” Jiddah ta girgixa mata kai kawai bata ce komai ba, Umma tace “Ki bude baki kiyi min magana” a hankali tace “Umma cikina ke min ciwo” Hajja tace “Kaji sharri?? Dama ba gari muke jira ya waye a kai ki asibiti ba? in ni kina tunanin tsohuwar banxa ce don me baki sanar ma me gidan cewar xaki koma gidanku ba xaki tafi ki bar xuciyoyin mu a gantale da fargaba??” Umma tace “To ayi hakuri Hajja, Allah ya huci xuciyarki” Hajja tace “Aa bbu ruwana wllh, sai kinga tijaran da nayi ma matar gidan a kanta jiya, shine ni xata watsa min kasa a ido?” Umma da mitan ya fara isarta tace “Toh ke yanxu ya kike son ayi Hajja? Komawa gidan xa kiyi tare da ita yanxu?” Jiddah da taji gabanta yayi wani irin faduwa ta fashe da kuka ba tare da ta shirya ba tace “Wllh cikina ciwo yake min Umma” Hajja ta rike ha6a tana kallon Umma tace “In koma ina da ita? Matar da ta kashe mana baccin jiya duk a xaxxaune muka kwana a gidan kamar almajirai, aa tunda ta dawo gida lafiya Alhmdlhi, nima xuwa xanyi ya ajiyeni a gida ashe matar gidan yaji tayi daga jin mun xo, to ni ina na sani, sai yau da safe yake gaya min” Umma dai tace “To Allah ya kyauta, kiyi hakuri Hajja” Hajja ta juya ta nufi kofa tace “D’an ba kara, tunda dai ta dawo xan turo Aliyun ya shigo ya gaisheki mu san inda dare ya mana” Mikewa Jiddah tayi ta wuce daki kamar warce aka tsikara jin xancen Hajja na karshe, Umma ta bi ta da kallo, Hajja na fita kofar gida tana kallon Abuturrab dake xaune cikin motarsa tace “So tayi ta tona mana asiri Allah bai yi ba, gata can munafukar tana ciki, ka shiga kawai ka gaida uwarka muyi ta kanmu, mu dai ba ta dawo gidan lfya ba Alhmdlh” Abuturrab yace “Ke kin ganta a ciki?” Hajja tace “To da fa? Wai sai ta fashe da kukan munafurci daga Uwar tace mu koma tare, bata san nima ta sire min ba baxan sake xuwa da ita ko ina ba, har abada kuwa, jiya kaga abinda dai ta dinga mana cikin dare kamar me cikin wata tara” Abuturrab ya shafa kansa yace “To shigo mu tafi” Hajja tace “Aa rufa min asiri so kake Ramlah tayi dani idan mun tafi tace na hanaka shiga ka gaisheta?? Kaje ko minti daya ne ka gaisheta ka fito kawai” Bude motar Abuturrab yyi ya sauka, Hajja tace “Kayi maxa ina jiranka” Umma na xaune parlon tana ma Jiddah dake xaune kasa kusa da ita magana a kan me yasa xata bar gidan da sassafe, ita dai Jiddah bata ce komai, Abuturrab yyi sallama bakin kofa, sosai gabanta ya fadi tayi kasa da kanta kamar me neman allura a kasan, Shi ma tun da ya kalli inda take sau daya bai sake kallo ba, ya dai karaso parlon ya xauna saman kujera yace “Ina kwana Umma” Umma tace “Lafiya lau, an tashi lafiya” Yace “Alhmdlh, ya gida” Tace “Lafiya lau” Kamar yanda Jiddah taki dago kanta shi ma haka ya ki kallon inda take, Bayan few seconds yace “Hajja na jira na Umma” Umma tace “Toh Allah ya tsare” mikewa yayi yace mata sai anjima sannan ya nufi kofa, Jiddah dai taki dagowa ko da wasa, Umma sai kallonta take kamar dai tana son gano wani abu, bayan fitar Abuturrab tace “Me ya sameki jiya da daddare a can gidan?” A hankali Jiddah tace “Ciwon ciki nake yi?” Umma tace “Ikon Allah, amma da sauki yanxu?” Tace “Idan yayi min sauki sai ya fara kuma” Umma tace “Toh Allah ya sauwake bari anjima Ahmad ya xo sai ya baki magani ko kuma aje asibiti” Jiddah dai bata ce komai ba, Umma tace “Kin karya?” Girgixa mata kai tayi, Umma tace “To tafi ki karya” Mikewa tayi a hankali ta nufi kitchen Umma ta bi ta da kallo ganin duk tayi wani irin sanyi. Hajja na shigowa parlon Abba ganin Aunty da Ummi sai Aneesah a parlon ta dinga bin su da kallo tace “Wacece wannan kuma?” Lkci daya Aunty ta murtuke fuska, Ummi tace “Sannu da xuwa Hajja” Hajja tace “Yauwa me ke faruwa a nan din?” Abba dake xaune shi ma parlon yace “Sannu da xuwa” Hajja tace “Ba batun sannu da xuwa ba, xaman me ake a nan?” Dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon da sallama, tun karfe tara Abba ya kirasa yana nemansa a gida, suna mota kuma yake sanar ma Hajja cewar Abba yace yaje, Kallo daya yayi ma Aneesah da ta sha lullubi da babban gyale wanda da alama Aunty ce ta 6ata, ya dauke kai ya xauna saman carpet yana kallon Abbansa yace “Ina kwana Abba?” Abba yace “Lafiya lau” Kallon Ummi yayi ya gaisheta, snn ya gaida Aunty da tayi masa banxa, Hajja dai na tsaye kansu kamar soja, Abba yace “Ga kujera Hajja” Hajja tace “Aa bar ni in tsaya abuna, mu da muka sa6a tsayuwa a Masar” Aunty na kallon Abba tace “Alhaji i think we can leave the sitting for now, may be in the evening” Abuturrab ya kalleta yace “Yau xan koma aiki in sha Allah” Wani shegen kallo Aunty tayi masa tana kallon Aneesah tace “Tashi mu je” Hajja tace “Ta tashi aje Ina? Ina ce k’aran jikana ta kawo ko? to wllh sai kun ga walakanci da tarban tsiyar da matar nan tayi mana ni da Jiddah, ni dai har hawaye sai da nayi a boye don tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin anyi haka ba a Masar, sannan gida dai in baku labari da muka shiga duk wari, wllh ta rubar masa gida, kitchen kuma dai ya fara wasu irin tsutsa, bandakin gidan duk sunyi gantsa kuka, to banda lalacewar yaran kasar nan daga nayi mata gyara sai ta kawo karata da na jikana har a wani xauna xa ayi meeting a kanmu?? Ehh lallai yau nake ganin lalacewa a Najeriya” Abba dai yyi shiru bai ce komai ba, haka Ummi da kanta ke kasa, Aunty sai tafarfasa xuciyarta yake tana kallon Hajja, Hajja ta ta6e baki tana gyara yafin gyalenta tace “Hatta abincin da xa mu ci sai da yaron nan ya fita ya samo mana, to ina girki xai yiwu a wnn axabbabben kitchen din duk wari, salon ma mu ci mu tsuge da xawo idan an girka, wllh da ido daya nayi bacci a gidan sbda datti da kazanta, to bari kuji ita yar rakiyar tawa ma da ciwon ciki ta kwana a gidan tsabar kazantar gidan kuma ni nasan hakan na da nasaba da ruwan da muka sha na gidan, yanxu haka tana can baiwar Allahn tana jinya gun uwar rikonta ni dai duk ni na ja mata bani da bakin magana, to idan ba rashin kunya ba shine har xata kwaso kafafuwarta kamar kara tace ta xo kawo kararmu, bayan duk hakurin da jikana ke yi da ita?? Lallai ma, ai ni da Masar har abada jikana na wannan halin, in sha Allahu sai na samar masa mata me tsafta irinsa warce xata dinga gyara masa gida” Abba na kallon Aunty da turanci yace “Su tashi su tafi kawai da Aneesah” Kamar jira take ta mike ta daga Aneesah suka fice daga parlon tana huci. Hajja ta kalli Abba ta ta6e baki sannan ta kalli Abuturrab da ya sunkuyar da kansa tace “Tashi mu je o, Allah ubangiji ya kawo maka karshen jarabawar nan da kake ciki” Daga haka ta nufi kofa abunta…. Bayan azahar Ahmad ya shigo gidan Umma, bayan sun gaisa da Umma yace “Su Maimoon sun tafi Islamiyya ne?” Umma tace “Ehh sun tafi Jiddah dai ce bata je ba, bata jin dadi” Yace “What’s wrong with her?” Umma tace “Wai ciwon ciki take, dama jira nake ka xo” Yace “Wani irin ciwon ciki tace?” Umma tace “ka kai ta asibiti kawai, ai nima ba sani xanyi ba” Yace “To Allah ya sauwake” Umma tace “Ameen” yace “Tana daki ne?” Umma tace “Ehh bari Huraira ta kirata idan ba bacci take ba” Umma na fadin haka ta kirawo Huraira, Huraira ta tafi dakinsu Maimoon, kwance ta tadda Jiddah saman gado tayi shiru, Huraira tace “Ya jikin Jiddah?” Jiddah ta mike xaune tayi murmushi tace “Naji sauki” Huraira tace “Toh Allah ya kara lafiya, Umma na kiranki’ Jiddah tace “Toh” Sannan ta sauka saman gadon, tun da safe bata sake jin ciwon cikin ba, amma gaba daya jikinta a sanyaye yake, hakan ne da Umma ta gani yasa tace ta xauna gida kawai ta xata duk ciwon cikin ne, Jiddah na fitowa parlor ta xauna kasa ta gaida Ahmad dake kallonta ya amsa da murmushi fuskarsa yace “Ya jikin?” Tace “Naji sauki” Umma tace “Cikin ya maki sauki?” Jiddah ta gyada mata kai tace “Ehh ya daina yanxu Umma” Umma tace “To sannu, Allah ya sauwake” Ta sunkuyar da kanta tace “Ameen” Ahmad yace “Why not ta dakatar da amfani da drugs da aka rubuta maku a hospital for the meantime Umma?” Umma tace “Kana tunanin shi ke sa mata ciwon?” Yace “Ta dai dau break na wani d’an lkci a gani” Umma tace “Toh shkkn” Yace “Xan siyo mata pain reliever yanxu” Umma dai sai kallon Jiddah take ganin yanayinta, Ahmad yace “Umma gobe kika ce xa a kai ta makarantar ko?” Umma ta kallesa tace “Ehh” Yace “Toh idan xan koma gida sai mu tafi tare da ita, idan ya so gobe da safe sai mu je makarantar” Umma tace “Daga nan din baxa ka iya xuwa ka dauketa ba?” Yace “Toh shkkn Allah ya kai mu” Umma ta kalli Jiddah tace “Tashi ki je ki ci abinci” Ba musu Jiddah ta mike ta wuce kitchen. Sai kusan la’asar Ahmad ya shirya xai koma gida, bayan yayi ma Umma sallama tace “Shkkn kawai ta dau kayanta kala daya ko biyu ku tafi can gidan din” Yace “Ohk toh” Umma ta tafi da kanta daki wajen Jiddah ta sanar mata xa su tafi gidan Ahmad tare, ta dau kayanta kala biyu, Jiddah bata mata musu ba tayi yanda Umma tace sannan ta fito parlor rike da jakarta. Huraira dake tunanin har sannan Jiddah bata jin dadi ne ta amsar mata jakar ta kai motar Ahmad, Ahmad yyi sallama da Umma, jiddah ma tayi mata sallama, Umma tace “A gaida Ramlah” daga nan suka fita gidan, Suna shiga motar Ahmad yaga missed calls din Abuturrab har uku a wayarsa da ya bari a cikin mota, Sai da ya tada motar yyi reverse sannan yayi dialing number Abuturrab din, yana dagawa Ahmad ya kai kunne yace “Ya aka yi?” Dariya Ahmad yyi yace “Ni fa wllh kana bani mamaki Captain, ga dai matarka ka bi ka takurani in maka prescription drug? Are u even okay?” Jiddah dake xaune gefensa cikin motar taji gabanta ya fadi jin sunan da ya ambato, Ahmad yace “Toh ka taho gida ka amsa, ina driving yanxu…” Daga haka ya katse wayar yana maida hankalinsa kan titi, sai da suka yi nisa yace “Kin ma san gidana kuwa Jiddah?” Ta kirkiri murmushi tace “Um na sani, mun je sau uku” Yace “Would u like to stay in my house ki dinga xuwa makaranta daga can?” Jiddah ta d’an buda ido ta kallesa, yace “Yea, sai ki xauna ke da Ramlah koh??”