JIDDATULKHAIR CHAPTER 53 BY KHALISAT HAIDAR

Abuturrab ya dauke kansa, Umma tace “A hado maka da abinci ne?” Girgixa kai yayi yace “Aa” Jiddah na ba Huraira sakon Umma ta fito ta wuce dakinsu, Huraira ta fito da ruwan ta ajiye ma Abuturrab, knocking aka yi bakin kofa Huraira ta karasa bakin kofar ganin driver ne ta kalli Umma tace “Umma Musan ya dawo” Umma tace “Ohk to ya jirani” Huraira ta koma ta gaya ma drivern abinda Umma tace, Abuturrab ya dau bottle water ya bude yana kallon Umma yace “Umma fita xa ki yi?” Umma tace “Ehh yanxu kuwa” Tana fadin haka ta mike ta wuce dakinta ta dau hijab da purse dinta, tana fitowa parlon shi dai bin ta kawai yake da kallo, ta xauna saman kujera ta kira Huraira, Huraira na xuwa tace “Kira min Jiddah” kallonta kawai Abuturrab yake, Huraira ta wuce daki sai ga ta sun fito tare da Jiddah, Umma tace “Dauko Hijab dinki ki rakani” Jiddah tace “Toh” sannan ta juya, Abuturrab dai sai kallon small mum din tasa yake, banda danna wayarta babu abinda take, Can ya shafa kansa a hankali yace “Umma ina xa ku?” Tace “Kwana biyu banje na gaida Yaya ba, can xanje yanxu” Yace “Nima can, xan tafi na dai fara xuwa nan in gaisheki ne” Umma tace “Allah sarki, ai ka kyauta” Yace “Toh in ajiye ku can din?” Umma tace “Idan ka ajiye mu wa xai maido mu, gwara mu tafi da driver ko awa nawa xanyi xai jira in gama sannan ya maido mu gida” Abuturrab yace “Ae xan kai har bayan isha a can, duk sanda xa ku dawo sai in dawo da ku sannan in wuce gidana” Umma tace “Toh ai shkkn idan ba takura” Umma ta mike ta wuce kitchen don juye pepper soup din da tayi ma Ummi, Jiddah ta fito daki sanye da hijab din da ta xo da shi, hada ido suka yi da shi, ta juya da sauri ta wuce kitchen, babu 6ata lkci Umma ta fito kitchen Jiddah na biye da ita rike da warmer din pepper soup, Abuturrab ya mike yace “Ina jira a mota Umma” Umma tace “Eh yanxu xa mu fito” Umma ta gama ba Huraira instructions din da xata bata sannan suka fito parlon da Jiddah, driver dake tsaye parking space Umma ta nufa tace “Musa kawai kayi tafiyarka na samu ma wanda xai ajiye ni can gidan” cike da ladabi Musa yace “Toh shkkn Hajiya, Allah ya tsare” Umma tace “Ameen, sai gobe kenan” Daga haka ta nufi gate Jiddah na biye da ita a baya being very careful kar ta 6ata hijab dinta da abinda ke cikin warmer din hannunta, back seat Umma ta bude ta shiga, Jiddah ta shiga bayan ita ma ta kulle motar, Umma na kallonsa tace “Idan ka samu wajen siyar da fruits a hanya” Yace “Ohk” daga haka ya tada motar ya bar layin. Dai dai wajen masu siyar da fruits yayi parking kamar yanda Umma ta umarcesa, Umma ta ciro kudi ta mika masa tace “Apples kawai sai grapes” Ya kalli kudin ya sauka motar yace “Akwai kudi a jikina” daga haka ya kulle motar ya tafi gun masu fruits din, bayan some minutes ya dawo, ya bude back seat yana mika ma Umma ledan amma Jiddah yake kallo, Umma ta kallesa tace “To ita kake ba ledan ko ni Aliyu? idan ita ce sai ka xaga ta can mana” Tana fadin haka ta amshe ledan xata rufo door din motar, shi dai bai ce komai ba ya koma driver seat, Jiddah dai na makale at the far end of d car don bata ma son su hada ido mistakenly ta madubi. A kofar gidansu yayi parking, Umma ta sauka, Jiddah ma ta sauka rike da warmer din ta bi bayan Umma da sauri, Direct bangaren Ummi suka tafi, Jiddah dai na xaune kasa bayan sun gaisa da Ummi da ta fito daga daki, Ummi tace “Toh ki xauna kujera mana Jiddah” Murmushi kawai Jiddah tayi bata ce komai ba, Umma tace “Ko a gida ma kafin ta xauna a kujera sau daya tayi xamanta a carpet ya fi a kirga” Ummi tace “Ikon Allah, to ina su Maimoon?” Umma tace “Suna dawowa boko suka tafi gidan Hajiya Zainab” Ummi tace “Haba, tana garin nan dama?” Umma tace “Aa last week ta shigo” Ummi tace “Allah sarki” Umma tace “Jiddah kuma ai nace maki tana gidan Ramlah ta fara karatu ko?” Ummi tace “Ehh haka kika ce, Allah ya bada ilimi me albarka da amfani” Umma tace “Ameen, Hajiya Hajja fa? Kwana biyu ba a je min ba” Ummi tayi murmushi tace “Shekaranjiya ta tada rigiman a kai ta gombe wajen mai martaba, amma yau kuma wai sai naji suna hanya kilan ma sun kusa, mun yi magana da El-Basheer din da safe” Umma ta tabe baki tace “Toh Allah ya kyauta, meye amfanin tafiya me nisan da ko kwana uku baxa ayi ba” Dariya kawai Ummi tayi, aka bude kofar Abuturrab ya shigo da sallama, xaunawa yayi ya gaida Umminsa, Ummi ta amsa tana kallonsa, Umma tace “Shi ya kawo mu, yaje can gida gaisheni shine yace bari ya ajiye mu tunda nan xa mu xo” Ummi tace “Maa sha Allah, Ina matar taka??” Yace “Tana gida” Ummi tace “Toh yayi kyau, shekaranjiya ma ai ina jin ta xo nan wajen Hafsah, amma ni dai ban ganta ba su Nafisah ke gaya min” Abuturrab dai yyi shiru bai ce komai ba, Umma dai ta ta6e baki tana kallon Tv, Ya kalli Ummi yace “Ummi akwai abinci?” Umma ta wani kallesa tace “Amma da nayi maka magana a can gidan me ka ce min?” Murmushi kawai yayi, Ummi ta kalli Jiddah tace “Akwai abinci kitchen ki dibar masa Jiddah” Sosai gaban Jiddah ya fadi ta kalli Ummi, Umma dai bata ce komai ba, Jiddah ta mike a hankali ta nufi kofa, Abuturrab na kallon Umminsa yace “Aunty na nan?” Ummi tace “Sai kaje ka duba” Bai ce komai ba, sai kuma ya mike yace “Bari in gaisheta in dawo yanxu” Daga haka ya nufi kofa daga Ummi har Umma suka bi sa da kallo, Umma tace “Mu je ciki akwai magana yaya” Ummi ta mike tace “Toh” a tare suka shiga bedroom din Ummi… Abuturrab na fitowa bangaren Ummi kitchen ya nufa direct, Jiddah ta juya da sauri jin an shigo kitchen din, suna hada ido ta juya masa baya, kana ganinta kasan duk a tsorace take ta ma rasa me take yi, sai kuma ta tuna miyan ganyen xata xuba a bowl, tana cikin xubawa taji muryarsa yace “Saboda nace ki daina gaisheni shi yasa idan kika gan ni sai ki min kallon banxa ki wuce right?” Kasa ce masa komai tayi amma banda bugawa babu abinda xuciyarta yake gashi taki juyowa, bude kitchen din aka yi ta juya da sauri, Mai aikin gidan ce ta shigo ganin Abuturrab ta koma xata fita, da sauri Jiddah ta ajiye bowl din miyar hannunta ta fice ta kofar da tagani a kitchen din wanda ke a bude, da mamaki ya bi ta da kallo, har ta xagayo gaban compound din gidan waige waige take ko ya biyota amma bata ga haka ba, mai gadi ya bude gate sai ga mota ya shigo, ko parking din motar ba a yi ba, motar na tsaye tsakar compound din aka bude back seat sae ga Hajja ta sauko da katon jakarta, Jiddah ta karasa gunta don amsan jakarta, Hajja sae kallonta take can tace “Wannan kafafuwa naki haka kamar a Masar, kinsan su ma haka kafafuwansu yake farare tass da yake larabawa ne, to ke kuma ba balarabiya ba sae dai ko sadaka yalla” Jiddah dai tayi murmushi ta amshi jakar Hajja tace “Sannu da dawowa Hajja” Hajja tace “Yauwa wajen d’ana sarkin Bauchi naje, ai da ke nayi niyyar xuwa Usman ya hanani wai inyi ta kaina, banda haka da na kai ki kinga ikon Allah, to ina takalman naki kike yawo haka ke kuwa? Ita mace ae ba a santa da yawo babu takalmi ba, barin ke da taki kafar kamar ta ‘yan Masar” El-Basheer ya sauko daga mota yana kallon Jiddah, Jiddah ta d’an kallesa tace “Ina yini?” Yayi murmushi yace “Lafiya lau Jiddah, how are you doing?” Tace “Alhmdlh” Hajja tace “To ki tsaya ku gaisa a tsanake idan kun gama sai ki taho min da jakata kin ji” Daga haka tayi wucewarta, Jiddah ta d’an kallesa, Murmushi yayi yace “Ya karatu?” Tace “Lafiya lau” yana kallon kafafuwanta yace “Ina takalmanki” Tace “Aa ta kofar kitchen na fito ne” Yace “To muje ciki” Tana gaba yana biye da ita suka wuce parlor din gidan, Abuturrab na xaune parlor Hajja na tsaye sai basa labari take, shi kam ko kallonta baya yi banda danna wayarsa da yake, Jiddah ta shigo parlon tare da El-Basheer, Hajja ta kallesu tace “Har kun gama gaisawa?” Jiddah dai bata ce komai ba tayi hanyar dakin Hajja da jakarta bayan ta saci kallon Abuturrab, Hajja ta bi bayanta murya can kasa tana cewa “Ki daina abu kamar er kauye ‘yar nan, kamata yyi ki buda baki kuyi tadi da shi sosai, ba wai ki ta sunkuyar da kai kina murmushi ba, ubansa fa shine sarkin Bauchi gaba daya, kuma ni na haifi uban, na ya6a da hankalinki ne shi sa nake ta cusa masa ke, amma naga ke kuma kina abu kamar wawa, haba kar kyanki ya tashi a banxa mana er nan” El-Basheer na kallon Abuturrab da ya ki dago kai yace “Na kira ka daxu wayarka a kashe” Abuturrab ya kallesa yace “Ohk kilan na kashe then, ya hanya” El-Basheer yace “Wannan mata ta fiye fitina wllh, i have to drive her all the way from kano, and in sha Allah gobe xan koma Bauchi” Abuturrab ya mike yace “Toh muje can gidana, tafiya xan yi nima” El-Basheer ya d’an buda ido yace “Ae ban gaisa da su Ummi da Aunty ba” Abuturrab yace “Duk basa nan, if u are going mu tafi yanxu don ni tafiya xanyi, gobe idan xaka koma Bauchin sai kaxo kayi masu sallama da safe” El-Basheer ya d’an shafa kansa yace “Ohk, i can even still come back at night in gaisa da su” Abuturrab yace “Eh xai ma fi” Daga haka suka fita parlon, a hanya Abuturrab yayi masu take away din abinci, El-Basheer na kallonsa da mamaki yace “Aneesah bata yi girki bane?” Abuturrab yace “Ehh bata jin dadi” El-Basheer yace “Toh Allah ya sauwake” Abuturrab yace “Ameen” sai da suka kusa gidan Abuturrab ya fara xullumin condition din da xai je ya tarar da gidan nasa with El-Basheer. Amma ga mamakinsa yana bude kofar parlor yaji wani kamshin turaren wuta me dadi ya doki hancinsa, ga sanyin Ac da ya cika parlon, suka shiga ciki tare da El-Basheer, the parlor was more than clean, banda kyalli babu abinda kayan kallon parlon suke, bin ko ina Abuturrab ya dinga yi da kallo yana mamakin anya gidan nasa ne kuwa wannan, El-Basheer ya xauna yana sauke wani numfashi yace “Gidan Amare daban yake, so cool” Daga sama Aneesah ta sauko da atamfa riga da skirt da ya kamata ta kashe dauri, fuskarta kuma tayi light make up, tayi kyau sosai kamar a sace a gudu, da murmushi ta karaso cikin parlon tace “Sannunku da xuwa, bako muka yi captain” El-Basheer yace “Fatan mun same ku lafiya amarya?” Tana ci gaba da murmushi tace “Alhmdlh, u are welcome” karasawa tayi kusa da captain ta xauna gefensa tace “Welcome my captain” Yana gyara xama yace “Yauwa thank you” Murmushi bai gushe a fuskarta ba ta mike ta wuce kitchen, sai gata ta dawo da ruwan gora biyu da drink sai cups, ajiye masu tayi tace “Ga ruwan sanyi” El-Basheer yace “Thank you Aneesah” Ta xauna one sitter tana kallon captain dake ta danna wayarsa, El-Basheer ya dau ruwa ya fara sha, tace “A kawo abinci yanxu?” Sai da captain ya daga kai ya kalleta jin abinda tace, tayi fari da ido tace “Eh, ko sai anjima” El-Basheer yace “Aa kawo min ni dai, Captain sai ya ci take away din da yayi” Ta mike ta dau ledan take away din ta wuce kitchen tana cewa “Shi ma baxai ci ba, ga dai abinci nayi” Captain ya bi ta da kallo, manyan warmers kusan biyar ta kawo parlon ta dire kan carpet, ta koma ta dauko plates, da serving spoon ta ajiye masu tana murmushi tace “Bismillah” daga haka ta wuce sama, El-Basheer ya sauka kasan carpet yana bude warmers din, Abuturrab ma sae kallon warmers din yake, wani lafiyayyen fried rice ne a warmer daya, dayan kuma wainar shinkafa sai tiriri yake, ga hadadden miyar taushe dake ta kamshi, wani warmer kuma peppered chicken ne that looks so enticing, last warmer din pepper soup din kayan ciki shi ma sai kamshi yake, kallon foods din kawai Abuturrab yake, tuni El-Basheer ya fara diban abubuwan da xai diba, Abuturrab ya ci gaba da danna wayarsa, sai kuma ya mike ya wuce kitchen, ko ina fess a kitchen din babu kayan wanke wanke, ya fara dube duben inda xai ga take away din da ta dauke a parlor bai gani ba, hakan ya sa ya bude kofar kitchen yaga a bola ta jefar, ya fi second biyar yana kallon ledan abincin kafin ya gyada kai ya kulle kofar ya fice daga kitchen din, ya dawo parlor ya xauna, El-Basheer yace “Kai baxa ka diba abincin ba?” Ya girgixa kai yace “Na ci abinci a can gida ai” Yace “Ohkk” Abuturrab da El-Basheer suna tare parlon har kusan magrib, ita dai Aneesah na sama, duk da yunwan da Abuturrab ke ji amma ya ki cin abincin, ana kiran magrib suka yi alwala a toilet din downstairs, Abuturrab yyi mamakin ganin toilet din ma fess, ana idar da sallah bayan sun fito masallaci El-Basheer yace ma Abuturrab xai koma can gida don su gaisa da su Ummi tunda gobe da safe xai koma, Abuturrab yace “Toh bari in dauko makullin motar” yana shiga ciki ya dauko makullin motarsa ya fito suka wuce can gidan, El-Basheer ya nufi bangaren Ummi don gaisheta, shi kuma ya tafi dakin Hajja, Hajja na gyara labulayenta Jiddah kuma na durkushe tana sa turaren wuta a garwashin da Mai aiki ta kawo ma Hajja a kasko, Hajja na ganinsa tace “Aliyu wllh bauchi da naje baka ga wata yar yarinya da na maka sha’awa ba, duka duka yarinyar bata wuce Jiddan nan ba, amma abinda yasa ban ce masu komai ba saboda ban san irin tsaftar yarinyar ba, kaga yanxu shi Bashir warce nake sa ran hadashi da ita nasan tsaftarta, to ita wancan gaskiya ban sani ba” Abuturrab dai bai ce mata komai ba, Hajja tace “Duk kwanan nan da kai nake kwana a raina nake tashi, saboda nasan kana cikin jarabawar auren mata kazama, amma in sha Allahu ka sha kurumin ka ina nan ina maka fafatuka, yanda na samar ma Bashir yar kirki me tsafta kai ma haka xan samo maka, Shi kansa Kabiru yyi farin cikin wannan xabin da nayi ma Bashir, uwarsa kuma babu abinda xance da ita sae dai ta ci kanta ni ba ta ita nake ba… Yanxu Usman nake jira ya dawo inji ynda xa a yi, ko shi ne xai xama waliyyin yarinyar to… Bashir kuma yace min shi dai a shirye yake ko gobe ne a daura, amma ae ba gaggawa ake ba ina laifin ma nan da sati uku” Abuturrab yace “A ina kika samar masa matar?” Hajja ta wani kallesa tace “Aa wannan kuma ba ruwan ka ae, wllh Kabiru yace min ya amince indai Bashir din na so, ae karfin xuwa na Bauchin kenan…” Abuturrab ya shafa kansa ya ki cewa komai, can ya kalleta yace “Toh ban ci abinci ba, yunwa nake ji” Hajja tace “Aa ba ma ga yunwa ba a gidan nan, ga dai abinci kaca kaca ka wani ce yunwa, bari wannan yarinyar Nafisah ta shigo ta xubo maka, naga lafiyayyen girki aka yi a gidan, ae Hauwa dama Allah ya hore mata iya sarrafa hatsi” Yace “Sae Nafisa ce xata ban abinci?” Hajja tace “Aa nima sae in je in xubo maka, meye a ciki” yace “To ita warcan baxata iya xuba min ba” Hajja ta kalli Jiddah dake duke da turaren wuta kusa da ita har sannan tace “To ke tashi ki xuba masa” Jiddah ta wani 6ata fuska, Hajja dae sae kallonta take, can ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido, Hajja ta rike ha6a a hankali tace “Sae naga kamar ta fara kiwiya ita ma, to ni dae fa kar ta sa inji kunya a kan abinda nake shirin yi, ko dai tana boye wasu halayyanta ne ban sani ba” Mikewa Abuturrab yyi ya fita daga dakin… Yana shiga kitchen din ya kulle ta juya tana Kallonsa kamar dama tasan xae biyota, ya rungume hannunsa yace “Yanxu ma ki fita ta inda kika fita daxu” Ita dai bata ce komai ba ta ci gaba da dibar masa abincin a hankali, yace “Bude kofar ki fita nace” still taki kallonsa, tsawa yayi mata yace “Baki ji na ne” Ta kallesa kamar xata yi kuka tace “In fita in je ina?” Yace “Inda kika je daxu” Ganin ya nufota ta tafi ta bude kofar ta fita tana kallonsa xuciyarta na bugawa, banda hasken wata babu wani haske a wajen, fitowa taga shi ma yayi bayan ya kashe fitilar kitchen din, bata san lkcn da ta tattare skirt dinta ba da xumar fallawa a guje yayi hanxarin cafkota da sauri, sannan ya kulle kofar kitchen din, iyakar tsorata ta tsorata a lkcn, ta marairaice masa tayi kasa da murya tace “Don girman Allah kayi hakuri ka sakeni… Wllh yanxu Umma xata fito mu wuce gida kar ta fara nemana, tace min yanxu xa mu tafi” Yace “Toh ta nemeki din mana ina ruwana??” Kasa ce masa komai tayi amma scene din ranan a kitchen din gidansa ne ke dawo mata wanda hakan yayi mugun daga mata hankali, duk a tsorace take, ya daure fuska yace “Saboda nace ki daina gaisheni na lura har wani nishadi kike duk sanda kika gani, kuma confidently kike wucewarki…” Tayi narai narai da ido tace “To amma ai kai kace in daina gaisheka, kuma abinda kace min ai shi nake yi” yace “Amma kuma ai murna kike don baki gaisheni?” Ta kasa ce masa komai gabanta na mugun faduwa, sai kuma ta fara kauda fuskarta saboda saukan breathing dinsa da take jiyowa don dab da ita yake, yace “Ohk ni kike dauke ma fuska?” Ta fashe da kuka tace “Ni don girman Allah ka sakeni ana jirana, don Allah fa nace maka….” Tana ganin xai juyo da fuskarta saitin nasa ta rufe fuskar nata a jikinsa hankali tashe tace “Don Allah kayi hakuri bana so wllh” wrapping dinta yyi jikinsa yace “Xan sake ki amma sai kin bani amsar tambayar da xan maki yanxu” Banda bugawa babu abinda xuciyarta ke yi tana jiran jin tambayar tasa, ga kamshinsa me dadi da ya cika hancinta, duk taji ta kasa ci gaba da tsayuwa, xata xame kasa yace “Kee” a hankali tace “Na gaji don Allah ka bar ni in tsugunna” da bango ya hadata ta rufe idonta da sauri, sai kallon fuskarta yake a duhun, taji yace “Duk xaman da muka yi dake a gida daya ki lissafo min abubuwan da na maki na rashin adalci…” A hankali ta bude ido tana kallonsa, yace “Ina sauraronki” Ta girgixa kai tace “Aa babu” ya dafa shoulders dinta yace “Karya kike” Tace “Ba karya nake ba, ban tuna abinda ka min na rashin adalci ba” Yace “To ina son ki tuna sai ki gaya min” Tayi shiru, shi dai kallonta kawai yake, murya can kasa tace “Amma me yasa kake ta6ani bayan kasan ni ba muharramarka bace, nasan kuma ka fini sanin hukuncin….” wani xaro ido tayi jin cold lips dinsa a wuyanta, da duk karfinta ta turasa shi kuma ya rungumeta gaba daya, ai kam neck dinta ya sha kisses iri iri ba a cewa komai tun tana iya turasa har ta hakura ta kasa komai, switch din fitila da aka kunna a kitchen ya sa ya saketa da sauri, without looking at her ya bar wajen, xamewa tayi kasa ta hade kanta da gwiwa amma hawayen ma ta nemesa ta rasa sae sauke numfashi take… Tunda makullin motarsa na jikinsa gate kawai ya nufa ya fice ya shiga motarsa ya wuce gida, ko kallon Aneesah dake xaune parlor duk ta cika turaren wuta bai yi ba ya haura sama yaki xuwa bangarensa ya bude wani daki ya shiga ya kulle kofar da key ya wuce bandaki direct…. Maimoon ta mike xaune ta kunna switch din dakin dake gefenta tana kallon Jiddah cikin muryan bacci tace “What happened Jiddah?” Ganin Jiddah taki bata amsa kuma taki dagowa ta sauka kan gadon ta nufi kofa ta fita xuwa dakin Umma….

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE