K’ADDARA CE CHAPTER 3 BY MAMAN NUSAIBA
K’ADDARA CE CHAPTER 3 BY MAMAN NUSAIBA
Hanan na zuwa shagon data saba siyan magani ta bada dubu shabiyar Ta ce”ya bata maganin da ta saba siya.. Shi kuma mai shagon sai Kallon Hanan yake yana lashe baki kamar wani maye, Ya ce” a a Hanan kece yau a shagon namu? sannu da zuwa…. Hanan murmishin yak’e Tayi Ta ce” eh ranka ya dad’e nice magani nazo siyawa Baba na ….
Sake washe baki Ya yi Ya ce” to Masha Allah ya jikin Baban? to Allah ya bashi lafiya. Ameen Hanan Ta ce” bata sake cewa komai ba , saboda ta tsani mutumin bata ganin mutumcin shi a idon ta, dan ma ita bata da fad’a da ko gaisuwa baza ta sake had’a su ba… Maganin aka mik’o mata katan biyar ne duk katan d’aya guda Ashirin ne a ciki , Amsa Tayi ta mishi godiya ta juya zata tafi…
Mai shagon Ya ce” bari na taka miki mana Hanan! Harara Ta aika mishi Ta ce” ka barshi na gode kasuwa zan k’arasa ne ba Gida zani ba… Haka Ya yi ta mata magiya akan ta bari ya raka ta, amma Ta ce” da shi ya barta kasuwa zata je siyayya, amma daya ke makwawaci ne sai da ya biyo ta har Kasuwar…
Suna shiga cikin Kasuwar Hanan ta sayi Shinkafa kwano biyu da taliya Y’ar leda guda goma, da sauran kayan miya sosai tayi sayayya da wannan dubun shabiyar, sai da ya rage mata saura dubu uku tukun ta bar siyayya, d’an dako ya daukar mata ya saka mata a Nepep, ta biyashi Hakk’in sa ya mata godiya ya tafi….
Kallon shi Ta yi Ta ce” wai Abdul Majeed lafiya kake bina? nace maka ka kyale ni ko ni ba Y’ar iska bace ka fita sabga ta na fad’a maka! Murmishi Ya yi Ya ce” dama Hak’uri ne nazo na bak’i akan Abubuwan da nasha miki a baya kiyi Hak’uri dan Allah ! Hanan ni yanzu sonki nake da aure…. kallon baka da hankali Hanan ta mishi ta shiga cikin motar Ta ce” direban yaja su tafi…. Abdul Majeed na fad’in, Hanan ki tsaya dan Allah !Muyi magana ta fahimta, amma ta ki sauraron shi suka bad’e shi da k’ura suka tafiyar su……
A hanya Hanan kuka take tana tuna rashin mutumcin da Abdul Majeed ke mata a baya, amma Yan zu shine zaizo Ya ce” wai yana sonta, lalle maza basu da kunya, an fada mishi rashin gata hauka ne, dan yaga bata da kowa sai ya dauka ita lalatacciya ce.. sake share hawaye Tayi Ta ce” saina nuna maka cewa tarbiya tafi kud’i daud’ar Duniya, D’an Iska kawai marar mutumci, Allah ya isa ban yafe maka ba da cin zarafi na da kake yi, shine Yan zu idon ka da kunya kazo kace kana sona, Insha Allah yadda kaso wulak’anta ni sai Allah ya wulak’anta ka, Allah ya kare ni daga sharri Samari irin ka masu zuciya a bushe……
Direban Nepep Ya ce” Hajiya kiyi Hak’uri kinsan Mutane haka suke, idan kai Talaka ne to kaine D’an Iska lallatacce, baka da gata indai kai Talaka ne ,ki k’ara Hak’uri wata rana sai labari….. Hanan Ta ce” nagode Malam Allah yasaka maka da alkhairi. Ameen Ya ce” tukun ya tsaya ta sauka saboda sunzo Gidan su Hanan.. kud’in ta tambaye shi nawa ne? sai Ya ce” ba komai ki barshi kawai.. Godiya sosai Hanan ta mishi tukun ta shiga Gida…
Da Sallama Ta shiga tin kafin ta k’arasa ma K’annuwan ta suka yo kanta da gudun su, suna murnar ganin ta…, Saudst Ta ce” Anty Tin d’azun muka zo Baba Ya ce” kin tafi ki siyo mana Abinci, gashi cen ma Baban Ya ce” kuma K’afar shi ta soma mishi ciwo….
Da sauri ta k’araso wajan Baba Ta ce” Baba sannu Allah ya baka lafiya ga maganin tashi kasha, Sadaut maza kije ki kawo min ruwa Naba Baba magani… Saudat da sauri Tayi wajan wata roba babba wadda suke zuba ruwa a cikin ta, ta dauko ta kawowa Hanan.. Amsa Hanan Tayi ta b’alli maganin guda biyu ta sakawa Baba a baki, Ta ce” ga ruwan Baba kasha maganin Anjima zaka ji k’afar ta dena ciwo. Baba ya amshi ruwan yasha maganin tukun ya koma ya kwanta akan tabarmar shi…
Kallon Hanan Yayi tana share hawaye Ya ce” Allah ya miki albarka, Hanan yadda kike d’awainiya dani Allah yasa kema wata rana Yaran ki su miki fiye da yadda kike min, bani da D’a Namiji Babba amma ke kinfi Namiji goma a gurina, Allah ya muku albarka dake da Y’an Uwan ki, kije ki dafa musu Abincin, ga Mahfuz cen ma Yayi ta kukan yunwa ya gaji Bacci ya dauke shi…..
Hanan Ta ce” Ameen Baba Allah yabaka lafiya , bari naje na daura musu Abincin. tashi Tayi ta shiga dakin su ta fito da tukunya ta daura ta soma had’a girki.. Taliya tayi sauri ta dafa ganin Saudat Tayi lakwas sai lumshe ido take alamar dai yunwa take ji sosai..
Tana gamawa Ta zuba wa Saudat ta koma Gidin Bishiyar da Baba yake ta shinfid’a wata tabarmar babba, Mahfuz ta tasa ta wanke mishi fuskar shi da hannun shi. Ta ce” Auta muje kaci Abinci kaji , maza bude idon gashi cen na dafa. Mahfuz Ya yi sauri ya k’araso kan ta barmar, zama Ya yi suka soma cin abincin..
Baba ta zubo wa Ita kuma ta koma Kauye tana kallon su hawaye na bin kuncin ta, ganin yadda su Saudat ke ta cin abincin kamar sunyi wata basuci komai ba, dama da safe garin kwaki ne ta jik’a musu sukaci, shine a cikin su har suka dawo daga Makaranta. Sai da taga dukkan su kowa ya k’oshi har Baba tukun ta dauk’e kwanukan, sauran da tayi saura ita taci badan ta koshi ba haka ta Hak’ura, ta san in tace Gidan Maman Islam zata ci Abinci har ta kawo wani Gida.. Da haka ta dawo kan wankin ta taci gaba da yi , su kuma su Saudat suka kama wasan su…..
Hanan ma gama wankin ta, cikin sauri take komai ganin La’asar ta kusa, sai da ta linke kayan da suka bushe ta zuba su a wata leda mai d’an girma ta aje a gefe. Kallon Saudat Tayi Ta ce” Saudat ku Zau na naje Gidan Maman Islam na dawo, karki tafi ko ina ga Baba nan idan An jima ki dauki maganin shi guda biyu ki bashi yasha, kina jina Saudat!
Saudat kamar za Tayi kuka Ta ce” Anty zan biki Gidan su Islam d’in sai muyi wasa da ita, kin ga ita tana son mu nida Mahfuz, idan muka je school har Abinci take kawo mana muci tare, yau kuma hadda Indomie ta bamu a school d’in. Saudat ta k’arasa maganar cikin jin dad’i…..
Hanan Ta ce” a a bazan je dake ba ki Zau na a Gida, indai Islam ce Zan turo muku ita sai kuyi wasan, kinga sai ki taya Mahfuz wanka anjima ku tafi Islamaya kinji Y’ar kirki! Saudat tsalle Tayi na jin dad’i jin ance mata Y’ar kirki. Ta ce” to shikenan kice tazo da wuri muyi wasa… Hanan Ta ce” to zan fad’a mata Insha Allah. Kayan wankin ta dauka ta kalli Baba Ta ce” Baba saina dawo , idan banzo da wuri ba zan siyo mana Abinci a hanya…
Baba Ya ce” to Hanan Allah ya kareki Allah ya kiyaye hanya a dawo Lafiya.. Ameen Ta ce” tana wucewa waje.. Gidan Maman Islam ba nisa da Gidan su Hanan, bata fi minti goma ba taje Gidan..
Da Sallama ta shiga cikin Gidan, Mai Gadin ne ya amsa mata Sallamar fuskar shi dauke da Murmishi ganin Hanan ce. Ya ce” a a Hanan kice da Kusan La’asar D’in nan? Murmishi Hanan Tayi Ta ce” eh Baba nice barka da yini ya aikin? Ya ce”lafiya lau yasu Mahfuz? Suna gida lafiya, tukun ta nufi k’ofar da zata sada ta da falon Gidan…
Da Sallama ta kutsa kai cikin falon, Maman Islam na Zau ne tana zaman jiran ta sai taji Sallamar ta. D’ago da kanta Tayi fuskar ta dauke da Murmishi Ta ce” Amin wa’alaikum salam Hanan sannu da zuwa Tun d’azu nake zaman jiran zuwan ki, da har zan tura Islam Ta gano min ko lafiya sai gaki ma Zauna mana ga kujera!
Murmishi Hanan Tayi Ta ce” Wallahi Anty na tsaya wanke kayan ku ne, shiyasa kikaji ban zo da wuri ba, ai ba sai na Zau na ba muje kitchen d’in a soma girkin.. Anty Islam Ta kawo kud’i har da k’arin dubu goma , Nagode sosai Allah yasaka miki da alkhairi, kina da kirki sosai bazan tab’a manta alkhairi a garemu ba a duk inda na tsinci kaina, koda K’ADDARA CE ta raba mu bazan manta dake ba, nagode sosai.. Hanan na magana tana kuka…
Maman Islam d’ago da Hanan Tayi daga durk’ushen da tayi a gaban ta , Ta ce” haba Hanan meye na godiya ai kin zama Y’ar Uwa ta, karki damu ki dena gode min dan na taimaka muku, ni Y’ar Uwa ce a gare ki kinji! Tashi muje a soma girkin.. Tashi Hanan Tayi suka tafi kitchen, babu b’ata lokaci suka soma girki kala-kala..
Bayan sun gama ne Bak’in Mijin Maman Islam suka zosu, dama tuni sun shirya musu Abincin, Baban Islam Yayiwa Bak’in shi jagora zuwa dirning, Nan suka soma cin abincin kowa sai santi yake zuba wa… Bayan sun gama ne su Hanan suka gyara wajan, Hanan ta wanke kayan tas ta gyara kitchen d’in, tana gama wa ta fito zata tafi gida…
Maman Islam Ta ce” Hanan har Gida ne zaki tafi? Sun kuyar da kanta Hanan tayi saboda bata son tsaya wa idan Baban Islam yana nan duk kunya ke kama ta. Ta ce” eh Anty zan tafi idan naje sai na turo miki da Islam d’in…
Tashi Maman Islam Tayi ta sauko Abincin cike da kula Babba da kud’i dubu biyar ta mik’awa Hanan. Hanan Ta ce” haba Anty ki bar kud’in nan dan Allah! Abincin ma Yayi ba sai kin bani kud’i ba…Daure fuska Maman Islam Tayi Ta ce” bana son haka Hanan amshi nace! ke kullin sai mun ringa jayayya dake, kama amshi inba so kike ranki ya b’aci ba! Maman Islam Ta yi magana cikin tsawa² ,saboda tasan inba haka tayi wa Hanan ba baza ta amsa ba……
Hanan ganin ba wasa a fuskar Antyn nata sai ta amsa ta mata godiya tukun sukayi Sallama ta tafi Gida.. Tana zuwa gida ta tura Islam Gida, Abincin ta zuba musu sukaci Ita ma taci, sauran ta aje musu anjima da dare sai su k’ara……
*****************************
Iman ce ta fito da kayan Tallar ta, ta nufo Gidan su Sultana, Mama na mata fatan siyar wa da wuri ,tana amsawa da Ameen har ta baro Gidan..
A bakin k’ofar Gidan su Sultana suka had’u da Sultana, itama ta fito da kayan Tallar ta, ba bata lokaci sukayo bakin hanya… Wanda ya dauke su Jiya shine ya tsaya. Kallon su Ya yi a a an fito ba? sannunku, Ina zan kaiku ku?
Sultana ce Tayi saurin fad’in *MARSHÈ DANTOKPA* Cen Kasuwar zaka kai mu.. Ya ce to kuzo muje. Sai da Iman Ta aika mishi harara tukun Ta shiga . Dariya Yayi Ya ce” Hajiya Iman bako gaisuwa ma , irin wannan shan kunu haka! Sake aika mishi harara Tayi Ta ce” baza a gaishe ka d’in ba, ko dole ne sai na gaishe ka Iyeee? Kai kafita ido na ,hadda wani cemin hajiya ko wa ya kaini Makkah d’in da kake cemin Hajiya, wato saboda neman guri ko? to bana son wannan Iyayin naka.. .
Sultana Ta ce” kai rabu da ita wannan rik’on Mahaukaci sai Sarki ce, ka dena tab’a ta tana cika min kunne da fad’a, Sarkin fad’a ai wanda zai aure ki ya shiga uku da wannan masifar taki, sakarya kawai, duk kin cika min kunne da ihun ki…
Kuka Iman Ta saka jin Abin da Sultana Ta fad’a mata, har suka je Kasuwa bata dena kukan ba, sai da suka sauka ta goge hawayen Ta, tukun suka sauke kayan su na Abincin, zama sukayi amma Hajiya Iman Ta cika tayi fam, tana hura hanci sama sai aikawa Sultana harara take…. Ita kuwa dariya take ciki-ciki ganin yadda Mutuniyar ta,ta ke aiko mata da sak’on harara. Ta ce” Masifaffiya inba haka na miki ba da sai kin yiwa bawan Allah rashin kunya, idan aka jima mun shirya ai…. ..
*WACECE IMAN*
*WACECE SULTANA*
*WACECE HANAN*
*Wacece Iman?*
Malam Jibril Shine asalin sunan Mahaifin Iman, d’an asalin cikin garin Kwatano ne, anan Yayi karatun shi ya gama. Su biyu ne a wajan Iyayen su, daga shi sai k’anwar sa mai suna Laraba..
Bayan kammala karatun shi ya kama kasuwanci, sosai Allah ya bud’e mishi k’ofar samu, ya soma kasuwanci da shekara daya Allah ya had’a shi da wata Budurwa Y’ar nan layin su, mai sunan Mariya.. Tinda ya daura idon shi akan ta Allah ya jarabce shi da Kaunar Mariya, baiyi k’asa da gwiwa ba ya garzaya zuwa Gidan su dan ya fad’i sak’on dake cikin zuciyar shi.. Bayan ta fito ne suka gaisa da ita, da farko k’asa cewa komai Ya yi sai da yaga dai shurun ba anfani zai mishi ba ya soma magana kamar haka:
Am Mariya dama nazo ne na fad’a miki sak’on dake cikin zuciya ta, a gaskiya tinda na ganki ranar da kika je Gidan mu wajan k’anwata naji na kamu da kaunar ki sosai, shine nace bazan bari wani ya rigani ba gyara nazo na fad’i sirrin nake raina, kar nayiwa kaina, Ina fatan zan samu k’arrubu wa a cikin zuciyar ki, kuma ni bada wasa nazo ba auren ki nake son yi, Allah yasa dai wani bai rigani sace zuciyar kiba… Jibril Ya yi maganar cike da rauni dan ba k’aramin so yake yiwa Mariya ba……
Wani mugun dad’i Mariya taji ganin Jibril Ya ce” Yana son ta da aure, amma saboda Jan aji irin na Mata sai ta sunkuyar da kanta Ta ce” naji dad’i sosai da wannan Babbar kyautar, amma ka bani nan da kwana uku ko hud’u zanyi tunani sai na baka amsa, idan kuma ban fad’a maka ba to zakaji komai daga bakin Laraba…..
Kamar Jibril zai mata kuka, Yayi fuskar Tausayi Ya ce” to Allah yasa ayi tunani mai kyau please Mariya kar kice baki sona, Wallahi ina mugun kaunar ki kinji! Murmishi Tayi Ta ce” to karka damu ,Yan zu zan shiga ciki sai an jima … Sallama sukayi ta shige Gida ta bar shi anan. Haka dai ya tafi jiki a sanyaye yana Addu’ar Allah yasa ta amince da Soyayyar shi.
A kwana a tashi ba wuya a wajan Allah Mariya ta amince da Soyayyar Jibril, hakan ba k’aramin farin ciki ya saka Iyayen basu ba ,babu bata lokaci aka saka ranar bikin sati biyu kacal, masu zuwa.. Lokacin biki nayi aka sha shagali, aka kai Amarya Gidan ta. Sosai Mariya take ganin Soyayya da kulawa a wajan Mijin nata, Sai da sukayi shekara biyar da aure tukun Allah yabasu haihuwa, sosai suka shiga farin ciki marar musultuwa..
Lokacin Haihuwa Ya yi Mariya ta haifi Y’ar ta Mace kyakyawa mai kama da Uban ta, ranar suna Yarinyar taci sunan Iman, haka Iman Ta ringa samun kulawa tako wani b’an gare, duk inda Jibril
zaije wajan kasuwanci shi tare yake tafiya da Matar shi da Y’ar shi.. Wata rana wadda ahalin Jibril baza su tab’a mantawa da wannan bak’ar ranar ba. Jibril Ya shirya shida Abokin shi zasu tafi Kasuwancin da suka saba, kamar yana duba lokacin daya shirya sai ya fita zai tafi sai ya dawo ya kuma kallon Mariya.. Ya ce” Mariya ga amanar Iman nan nabar miki DUK TSANANI kar ki bari ta wulak’anta, ki kula min da ita kada ki bari zamani ya rud’e ta,ki bata tarbiya mai kyau..
Idan ya fad’i haka sai Mariya ta saka kuka ganin yana mata magana kamar mai barin Wasiyya inzai mutu. A haka dai suka tafi yana waiwayen ta , suka shiga mota suka bar Gidan.. Bayan kwana biyu da tafiyar su aka kira Mariya a waya, ganin bata san number ba sai taki dauka, sake kira akayi tukun ta dauka cike da far gaba Ta kara wayar a kunan ta, dama tin safe gaban ta ke fad’uwa ta rasa mai yake mata dad’i, sai gashi an kira ta da sabuwar number…
Cike da tsoro Tace” Assalam alaikum..
Wata murya taji marar dad’in ji ana fad’in, ke Y’ar renin hankali ga Mijin ki nan zai miki magana.. Mariya a furgice ta mik’e tana son jin muryar mijin nata.. Daga cen b’an garan Jibril Yayi magana cikin galabaita Ya ce” Hello Mariya dan Allah ku basu duk Abin da suke so,kin ganmu Tin ranar da muka tafo zamu shiga Ibadan suka tare mu ,sun kawo mu wani daji mai Abin tsoro, dan Allah a basu ko nawa suke buk’ata dan su sake mu…Kwace wayar akayi, aka cewa Mariya. Ke idan baku kawo naira million ashirin ba baza mu sake su ba, ko wanne million ashirin-ashirin zaku kawo, maza ku kawo million arba’in su biyu, inba haka ba zamu kashe su mu bawa kura naman su ta cinye. Yana fad’in haka ya kashe kiran…
Kuka Mariya ta fasa ta kama hanun Iman Ta nufi Gidan surukan ta, tana zuwa ta fad’a musu Abin da wanda suka sace su Jibril suka fad’i, ranar sun shiga tashin hankali, marar musultuwa, haka aka had’a kud’in da Jibril Ya bari a cikin account bank d’in shi,amma duka million shida ne,duk ya dauke kud’in ya tafi dasu kasuwancin shi.. Sosai suka k’ara shiga tashin hankali…
sake kira sukayi nan Baban Jibril Ya fad’a musu basu cika ba kud’in million shida ne, suyi Hak’uri su karb’a.. Y’an garkuwar suka ce to a kawo musu million shidan d’in zasu sakesu. Cike da farin Baban Jibril Ya had’a kud’in ya tafi inda suka ce ya kai kud’in.. Yana kai wa Ya ce” gashi ya kawo amma baiga Jibril ba? sai suka ce ya aje kud’in ya koma Gida su zasu kawo Jibril har bakin gari sai ya k’arasa da kanshi… Haka Baban Jibril Ya koma Gida suna kallon hanya suka yau she Jibril zai zo Gida, Shuru shuru Jibril bai zo ba har akayi kwana biyu, nan suka kara shiga wani tashin hankalin,Har yau ba’a san a ina Baban Iman yake ba,ya mutu ko yana raye ba wanda ya sani har yau…
Maman Iman Ta shiga cikin tsananin damuwa koda yau she kuka take, ga shi basu da komai duk kud’in daya rage a hannun ta ya k’are, ganin tana da dubu goma a hannun ta sai ta fara daura wa Iman tallar WAGASHI tin tana Y’ar shekara 10 take tallar WAGASHI har izuwa yau, kuma Alhamdulillah suna samun na rufin asiri…
*Wannan shine asalin Iman*
**************************
*Wacece Sultana*
Malam Ilyas shine asalin sunan Mahaifin Sultana, shi kadai Iyayen shi suka haifa, daga kanshi basu sake samun haihuwa ba,ta tsaya.. Ya taso cikin gata da kulawan Iyayen shi, sun bashi tarbiya ta gari, tin a school ya had’u da Hassana, Allah ya daura mishi son ta,Tin yana b’oye wa har ya gaji yazo ya fad’a mata, ta kuwa Amince… Bayan sun gama karatu ne manya suka shigo maganar , Babu bata lokaci suka saka ranar bikin Tinda Ilyas ya samu aiki, ita kuma Hassana idan ta gama exams za’a yi bikin su sai taci gaba da karatu a Gidan ta..
Haka kuwa aka yi tana gama exams aka musu aure ansha biki Iyayen Ilyas sun yi rawar gani a bikin d’an nasu,kayan d’aki ma su suka yiwa Hassana, hakan ba k’aramin farin ciki ya saka Iyayen Hassana ba, saboda su Talakawa ne basu da komai… Bayan auren su da shekara d’aya Hassana ta samu ciki, zo kuga murna a wajan Ilyas da Iyayen sa, kamar ya maida Hassana ciki yake ji .., Haka suka reni cikin cike da so ta kauna, kai yakai wata takwas …
Wani biki ya tashi a dangin Baban Ilyas suka shirya su hud’u suka tafi Garin Jos, acen duk familyn su suke Dangin Baban Ilyas har da Maman shi,aiki ne ya kawo Baban shi garin Kwatano.. A hanya sun kusa zuwa Garin Jos sukayi accident, Babu wanda Yayi rai sai Hassana ita ma sai da ta samu karaya biyu a k’afa da hannu.. Tana dawowa Hayyacin ta aka bata labarin ai Mijin ta da Surukan ta sun mutu, ai ko ta suma sai da tayi sati a sume tukun ta farfad’o.. Koda yau she kaga Hassana cikin kuka take, Dangin Ilyas suka zo suka amshe kud’in da ya bari suka hana Hasana gadon ta da na Abin da yake cikin ta, rayuwa ta dawo mata mai cike da talauci wahala ga ciki gashi Iyayen ta basu da shi, haka dai har ta haifi Y’ar ta Mace kyakyawa mai kama da ita, ranar sai da ta raba dare tana kuka, inta kalli Jaririyar sai ta tuna burin da Ilyas yaci a kan Babyn cikin ta, Yan zu gashi ta haihu baya Duniyar, wannan cike saka ta kuka…..
Ranar suna Yarinyar taci sunan Sultana, Hassana Ta ce” Ilyas Yace yana son sunan Dan haka ta saka wa Jaririyar ta.. Haka ta reni Y’ar ta kullin sai Tayi aiki a Gidan masu kud’i take samu ta kula da Jaririyar ta…..
sosai take shan wahala da haka dai har Sultana Ta isa zuwa Makaranta, haka ta kai ta Makaranta ta saka ta a Boko da Islamiyya..
A nan ne suka had’u da Iman jinin su yazo d’aya she suke komai tare in suka je school, sosai shak’uwa ta shiga tsakanin Iman da Sultana, idan d’aya bashi da labari to d’ayan bazai je ko ina yana tare ta d’an Uwan shi.. Ta dalilin k’awancen Iman da Sultana Iyayen su suka san juna, suma suka daura k’awancen su. Maman Iman ce ta taimakawa Maman Sultana da Jari na kud’i da take Sana’a , ta bata dubu goma ita ma ta soma sana’ar , tana daura wa Sultana, kullin a tare suke zuwa talla school Islamiyya, koda yau she suna tare in kaga sun rabu to bacci ne…….
*Wannan shine asalin Sultana da kuma k’awancen su da Iman*
_________________________
*Wacece Hanan?*
wannan amsar sai ku biyo Mom Nusy domin jin wacece Hanan?
Masu buk’atar littafin nan zaku Iya tuntub’a ta ta WhatsApp number nan +966599791573
Zaki iya biyan kud’in ki ta wannan hanyar 0002482217 jaiz bank
Mu’utasim Ibrahim
idan kuma katin waya ne zaki iya tura wa ta wannan number 08149194919
sai ki turo da biyar ki ta wannan number +966599791573
Taku har kullin *MAMAN NUSAIBA CE*
Wannan amsar duk sai kun niyo Mom Nusy..
Masu buk’atar littafin nan zaku Iya tuntub’a ta ta WhatsApp number nan + 966599791573
Zaki iya biyan kud’in ki ta wannan hanyar
000 2482217 jaiz bank
Mu’utasim Ibrahim
idan kuma katin waya ne zaki iya tura wa ta wannan number 08149194919
sai ki turo shidar ki ta wannan number +966599791573