K’ADDARA CE CHAPTER 3

 K’ADDARA CE CHAPTER 3

Ahankali yad’aga labulen d’akin daddyne da mummy yagani zaune saman 3 setter sai yaya khairat da Fatima zaune bisa 2 setter,+

Muryarsa tana kyarma yayi sallama,

Dasauri duk suka juyo suka kallosa jin muryar da ba zasu ta6a mantawa da itaba a rayuwarsu,

A firgice mummy tamik’e tsaye tana nunashi da yatsa tace Alhaji kudubu min mafarki nake ko gaske dan Allah kufad’a min fahad dina ne?

Daddy ya yi mutuwar zaune ya kasa motsin kirki kallon fahad kawai yake,

Khairat ce da fatima suka taso dagudu suka nufi wajensa kowa sauri yake yariga d’an uwansa isa.

Rungumesa sukayi su duka biyun suna kuka,

Shima rungume ‘yan uwan nasa yayi yana jin dad’i cikin ransa koda zuciyarsa a tunkushe take da bak’in ciki.

Fatima tace yaya fahad kaine dagaske? Meyasa katafi kabarmu,

Khairat ta amshe tace baka kyauta manaba fahad da har katafi kabarmu ba ka tunanin wane irin hali zamu shiga,

Meyasa ka aikata haka,

Kuka sukeyi sosai, runtse idonsa yayi hawaye suna zubo masa yak’ara matse ‘yan uwan nasa a jikinsa yace,

Kuyi hak’uri wlh ba da son raina hakan tafaruba.

Dai-dai lokacin mummy ta iso inda suke tana kuka tace kumatsa min inji d’umin d’ana,

Janye jikinsu sukayi daga nasa suka bata waje,

Ahankali yabud’e idanuwansa da hawaye suke ta zuba rungumesa mummy tayi tace fahad baka kyauta maniba ashe har zaka iya kai wannan lokacin ba tare da ka nememuba ashe zaka iya fushi da mu haka?

Duk yadda fahad yaso yadaure kar yayi kuka ammah ina ya kasa,

Fashewa yayi da kuka yace mummyna kiyi hak’uri wlh ba da son raina hakan yafaruba dan Allah kuyafe min wlh ba zan k’ara aikata hakan ba,

Bakomai fahad bakayi mana komai ba inma ka yi mana toh wlh mun yafe maka duniya da lahira ammah dan Allah kar kak’ara gudunmu,

Goge hawayen fuskarsa yayi yad’ago mummy daga jikinsa itama yagoge mata hawayen yayi murmushi yace insha Allahu ba zan k’araba mummyna kidaina kuka,

Itama murmushi tayi tace na daina my son.

Kallonsa yamaida a wajen daddy da har yanzu zaune yake saidai ya jingina kansa da kujera ya lumshe idonsa,

Ahankali yarik’o hannun mummy yanufi wajen da daddy yake zaune,

Su khairat suna biye dashi a baya kamar za a k’wace masu shi.

Sakin hannun mummy yayi yamatsa chan kusa da k’afafun daddy yatsugunna hawaye suna zubowa daga idanunsa muryarsa tana rawa yace daddy dan Allah kayafe min abinda yafaru wlh..

STORY CONTINUES BELOW

Bud’e idanuwansa daddy yayi da sukayi jawur ya katse mashi magana yace ya isa haka fahad maganar ta wuce ko a mafarki banson ink’ara tunota,

Nagode ma Allah da gaskiya tabayyana,

Fahad mune yakamata munemi yafiyarka domin mu mukayi maka laifi,

Mun d’aura maka laifin da baka aikataba ba tare da munyi bincikeba.

Fahad yayi murmushi yace bakomai daddy koma minene kuka aikata a gareni daidai ne domin kun isa dani.

Ammah fahad nayi mamaki da kad’auki tsawon wannan lokacin ba tare da ka nememuba duk inda mukasan zamu sameka mun nemeka ammah babu kai babu labarinka,

Hawayen fuskarsa fahad yagoge yace kugafarce ni daddy nima ba a son raina nayi nesa daku ba ammah insha Allahu hakan ba zai k’ara faruwa ba.

Haka suka sha koke-kokensu na murnar dawowarsa,

Ko masallaci daddy yana rik’e dashi sukaje kamar za a k’wace masa shi.

Ma’aikatan gidan duk sunyi muryar dawowarsa,

Abinci mai rai da lafiya mummy tasa aka shirya masa,

Aranar saida akayi ‘yar k’aramar walima a gidan,

Nan yakejin labarin rabuwar daddy da hindatu wajen ‘yan uwan nasa,

Fatima dakanta tashiga tagyara ma yayan nata d’akinsa ko da kasancewar d’akin daman fes yake ana gyarasa.

Sai k’arfe taran dare daddy yasa driver yamaida khairat gidan mijinta ba yadda ta iya dole tatafi tana mai kewar d’an uwan nata.

Abokansa ma sunyi murnar dawowarsa.

**** **** **** ****

A chan 6angaren Amina ko da taga dare ya yi hankalinta yatashi domin tana tsoron dawowar wad’annan ‘yan fashin,

Kwance take a saman gadonta juyi kawai take ta kasa bacci ko kad’an tad’anji motsi sai ta tsorata,

Ga shi ba ta minti talatin sai fuskar guy din ta fad’o mata a rai saidai taja tsaki saboda haushinsa da takeji.

Ahaka har bacci 6arawo yasaceta.

Tun da asuba datayi sallah takoma bacci ba ita ta farkaba sai wajen 8:30am dasauri tafito daga d’akinta tanufi kitchen domin tahad’a masu breakfast kafin ummah tafito tarufeta da masifa,

Sannan tagyara gidan tayi wanke-wanke .

Sai wajen k’arfe goma tagama ayyukanta,

‘Dakin ummah tashiga tagyara mata shi fes kasancewar ta san ummah tana d’akin Abbah.

Fitowa tayi takoma d’akinta tagyara takunna turaren wuta Sannan tafad’a toilet tayo wanka,

Mai da powder kawai tashafa sannan tashirya cikin material riga da skirt pink nd black colour sunyi mata kyau sosai sannan tafeshe jikinta da turare.

Fitowa tayi tanufi d’akin abbanta da sallama tashiga tataddashi yana shirin tafiya kasuwa,

Tsugunnawa tayi har k’asa tagaisheshi kanta yana kallon k’asa saboda kunyar abbah da takeji,

Murmushi yayi yace lfy lou mamana,

Dafatan kema kin tashi lfy,

K’ara sunne kanta tayi tace lafiya lou Abbah

Toh Alhmdllh daman akwai maganar da nakeso muyi in na dawo daga kasuwa ammah bari muyi ta yanzu,

Murmushi tayi tace toh Abbah,

Yauwa ga kud’in wannan bawan Allan da yabada na sadakinki ya..

Bata jira jin abinda abbah zai ida fad’a ba tace,

STORY CONTINUES BELOW

Abbah kawai in angansu amaida masu kud’insu ni wlh ba zan auri d’an fashi ba tafashe da kuka.

Kallonta Abbah yayi yace nima hukuncin da na yanke kenan mamana,

Ko da na yaba da hankalinsa a cikinsu kwata-kwata shi baiyi kama da d’an fashi ba domin yana da tausayi sosai,

Nima ba zanso ad’aura ma d’iyata aure da kud’in sata ba zan aje kud’in.

Kikwantar da hankalinki kidaina kukan haka,

Share hawayenta tayi tace toh Abbah.

Yauwa Allah yayi miki albarka,

Ameen Abbah,

Tashi yayi zai tafi kasuwa rakoshi tayi bakin k’ofar gida tace Allah yakiyaye Abbah sai ka dawo.

Ameen mamana.

Saida taga ya tada mota sannan tadawo gida,

‘Dakin abbah takoma tagyara fes sannan tatafi kitchen tad’auko breakfast d’inta takoma d’akinta tayi.

Da tagama taje tawanke kwanonin da ta 6ata sannan tanufi d’akin ummah da sallama tashiga,

Tsugunnawa tayi k’asa tana gaishe da ummah,

Ummah da take kwance a saman 3 setter tana danna waya ba tare da ta juyo ta kalleta ba ta amsa mata ciki-ciki kamar yadda ta saba,

Ummah yau me za a girka?

Ba tare da ta juyo ta kalleta ba tace amarya har angama amarcin kenan,

Tuwon shinkafa da miyar ku6ewa nakeson ci akwai kifi a cikin fridge ai ko,

Eh akwai,

Ohk, sannan ga wanki na nan na had’a za kiyi min,

Tace Toh ummah, tashi tayi tafita daga d’akin

Tsaki ummah taja tace munafukar banza kullum kaganta sumi-sumi kamar duka kenan.

Kitchen tashiga tad’aura girkin sannan tad’auko wankin ummah tafara,

Ahaka har tagama girkin, sai wajen k’arfe ukku tagama wankin,

‘Dakinta takoma tayi wanka tashirya sannan tad’auko abincinta taci ko da tagama littafin islamiyyarta tad’auko tayi tilawar karatu,

Tana sallar la’asar tayi shirin islamiyya,

Jakar islamiyyar ta tad’auko tanufi d’akin ummah,

Dasallama tashiga tace ummah zan tafi islamiyyah.

Harararta ummah tayi tace kin gama min wanki na?

Eh ummah na gama,

Ta6e baki ummah tayi tace bawani islamiyyar da zakije na san yawon karuwancin da kika saba zakije mudai fatanmu kar akwaso mana cikin shege cikin gida.

‘Dago kai tayi takalli ummah tuni idanuwanta sun cika da k’wallah tace wlh ummah babu inda nike zuwa islamiyyah kawai nake zuwa kiyarda dani.

Ta6e baki ummah tayi tace daman kullum dasunan islamiyyah kike fakewa,

Ni wuce kibani wuri kuma kidawo dawuri tunda yau ba za ayi abincin dareba kiyi min guga,

Goge hawayen fuskarta tayi tace toh ummah sannan tafice tatafi,

A chan gaba da gidansu kad’an tahango k’awarta sumayya a tsaye tana danna waya da alama ita zata kira tafito sutafi islamiyyah domin ba ta shiga gidan saboda tana tsoron masifar ummah da bak’ak’en maganganun da take yada masu.

Daidai lokacin Amina ta iso tayi sallama tace yau ba sai kin kiraniba gani na fito dawuri,

Murmushi sumayya tayi suka gaisa sannan suka kama hanyar islamiyyah.

**** **** **** ****

Bayan wata biyu fahad ya murje ya k’ara kyau ya koma fahad d’insa na ainahi d’an gayu,

Zaune yake d’akinsa yana latsa laptop dinsa Fatima ce tashigo d’akin da sallama.

Amsa mata yayi ba tare da ya juyoba.

Shigowa tayi tanufi inda yake tana murmushi tace yayana nakaina sannu da aiki,

Daina abinda yakeyi yayi yajuyo yakalleta shima yayi murmushi yace yauwa k’anwata takaina,

Yayana kataso muje muyi lunch su mummy suna chan kan dining suna jiranmu,

Murmushi yayi yace toh,

kashe laptop din yayi yatashi suka fito tana mashi shagwa6a yana biye mata har suka isa wajensu mummy,

Wuri suka samu suka zauna suka gaishe da iyayen nasu sannan suka fara cin abinci.

Bayan sun gama zaune suke a parlor suna hira fahad yace daddy dan Allah inaso asamomin admission a india inaso inje inyi masters d’ina a chan,

Kallonsa daddy yayi yace toh insha Allahu za a samo maka nima burina kazama babban likita,

itama Fatima ina neman mata admission ne a university ta nan kaduna domin tacigaba da karatunta,

Murmushi yayi yace toh daddy na gode,

Kallon Fatima yayi da taketa murna yace k’anwata angirma za a shiga university toh wane course zaki yi choosing,

Murmushi tayi tace biochemistry,

Wow gud gurl kin iya za6ar course

Allah yabada sa’a,

Ameen suka ce dukansu,

Tun daga ranar fahad yafara shirye-shiryen tafiya india,

Bayan sati biyu jirginsu yad’aga.

**** **** **** ****

tunda ta tashi yau takejin jikinta ba dad’i daurewa takeyi kawai tana aiki domin ta san ko ta fad’a ma ummah ba ta lafiya ba yarda za tayiba,

duk ta bi ta rame lokaci guda domin ko abinci a ranar ta kasa ci,

Kitchen take tana soya kifin da abbah yadawo dashi daga kasuwa zuciyarta taketa tashi daurewa kawai take,

Amai ne taji yana shirin kufce mata dagudu tafito daga kitchen d’in tanufi chan bakin famfo tafara kwarara amai kamar zata amaye ‘yan cikinta………..

Abbah da yake d’akinsa yajuyota tana ta k’warara amai dasauri yafito yanufi inda take,
Sannu kawai yakeyi mata har tagama aman duk ta galabaita,
Ruwa yad’ebo mata tad’auraye jikinta sannan yataimaka mata takoma d’akinta takwanta,
Kallonta yayi cikin tausayi yace Sannu mamana, me ke damunki?
Yauwa Abbah.
Wlh nima ban san abinda yake damuna ba tun dasafe nakejina kamar banda lafiya ammah kamshin kifin ne yasani amai,
Toh kuma jikinki akwai zazza6i sosai bari inje inkira malam musa mai chemist yaduba ki sannu kinji?
Runtse idonta tayi jin kanta yana sara mata ammah shirin tashi take daga kwancen,
Abbah yace ina kuma zakije mamana?
dakyar tace kifin da nake soyawa kar yak’one abbah shi zanje indubo,
A’a keda bakida lafiya kikwanta kawai bari inyi ma zainab magana sai ta ita ta ida soyawa,
Fitowa yayi daga d’akin yalek’a d’akin ummah tana zaune tana kallon T.V tana jin duk abinda yake faruwa ammah tak’i fitowa,
Kallonta yayi yace zainab ga kifin chan ki ida soyawa Amina ba ta da lafiya bari inje inkira malam musa yadubata,
Kallonshi tayi a wulak’ance tace shine kuma ba za ta iya ida soya kifinba?
Ransa a 6ace yace kar ki ida soyawar kibarshi yak’one ammah Wlh tana ciwo ba za ta je tayi wani aiki ba, ke miye amfaninki a cikin gidan,
Bai jira amsarta ba yaficce daga d’akin yayi tafiyarsa.
Tsaki taja tace yanzu haka munafuncine  ciwon k’aryane shi kuma ga mai d’iya shine duk yabi yarikice,
Tashi tayi tanufi kitchen d”in tana ta fad’a ita kad’ai
Abbah ne yashigo da malam musa nan yadubata yad’ibi jininta da fitsarinta yace zaije yayi awo gobe zai dawo,
Nan sukayi sallama da abbah yatafi,
Abbah dakansa yahad’o mata tea mai kauri tasha yabata magani sannan tayi bacci,
Ummah ko da sau d’aya bata lek’o ta duba ta ba.
Da asuba dakyar tatashi tayi sallah domin har lokacin akwai zazza6i jikinta,
Ko da tagama bacci takoma sai wajen k’arfe goma tafarka, wanka tashiga tayi tashirya sannan tafita tanufi kitchen saboda yunwar da takeji jikinta har kyarma yake,
STORY CONTINUES BELOW
Dubawa tayi ammah babu breakfast d’inta kuma ga alama nan ummah ta had’a domin duk ga wanke-wanke nan an 6ata,
Tana tsoron taje tatambayeta tayi mata wulak’anci.
Ruwan zafi tadafa tahad’a tea tasha sannan tad’an ji dadin jikinta,
Dak’yar tadaure tayi wanke-wanken, sannan a daddafe takoma d’akinta takwanta domin ba za ta iya yin sauran aikiba,
Abbah ne yashigo yadubata yayi mata ya jiki daidai lokacin sukaji sallamar malam musa,
Abbah ne ya amsa masa tare da bashi izinin shigowa bayan sun gaisa da abbah,
Malam musa yakalli abbah yace Alhaji a iya binciken da nayi na gano tana d’auke da ciki tsawon wata biyu,
Zumbur tayi ta tashi zaune tace ciki?,
Abbah yace ciki fa kace malam musa???
Daidai lokacin ummah ta fito daga d’aki za ta shiga kitchen taji ana maganar ciki,
Tana sauri tashigo d’akin tace me naji kunnena yana juyomin wa keda ciki?
Abbah kallonsa yamaida wajen malam musa hankalinsa a tashe yace anya kuwa cikine kodai kak’ara dubata ko kuma inkaita asibiti,
Malam musa yace wlh Alhaji iyakar binciken da nayi kenan ko ina zaku kaita a dubata cikin dai za a ce maku,
Ga wannan takaddar ta magungunan da za ta dinga sha domin tasamu sauk’in laulayi da amai,
Kar6ar takardar abbah yayi jikinsa duk ya mutu nan malam musa yayi masu sallama yafita.
Tunda akace ciki gareta taketa kuka,
Na shiga ukku ni ina nasamo ciki Abbah kodai wasa yakeyi?
Karaf ummah ta amshe cikin fad’a tace ke dallah yi mana shuru munafukar banza duk yawon banzan da kikeyi ba dole kiyi ciki ba,
Duk maganar da nake miki ammah a banza saida kika Kwaso mana abin kunya,
Tana kuka tace Ummah wlh babu inda nake zuwa inba islamiyya ba, wlh ban ta6a yin zina ba, cikin wannan d’an fashin ne, wlh cikinsa ne.
Keh zainab ya isa  haka kar kik’ara ce mata tana yawon banza domin na san d’iyata ba halinta bane kuma cikin tabbas na d’an fashin ne na yarda da maganarta.
Harararshi ummah tayi tace miye abun tada hankali dan ta yo cikin shege daman tabarmar kunya ai da hauka ake nad’eta,
Kuma wlh ba za a haifa mana cikin shege cikin gidaba,
Abbah yace Zainab wlh kin bani mamaki kuma ke sheda ce cikinta ba na shege bane, tunda saida aka d’aura mata aure  k’addara ce kawai,
Toh ba na shege bane naminene cikin d’an fashi ko?
Toh Allah yaraba lafiya bata jira amsar abbah ba tafice daga d’akin.
Kallonsa yamaida wajen Amina da taketa kuka gwanin tausayi yace mamana kukan ya isa haka kikwantar da hankalinki cikinki ai ba na shege bane da ubansa,
‘Dago idanuwanta tayi da duk sun canza kala sun zama ja  tace Abbah na shiga ukku wannan wace kalar k’addara ce dan Allah kakaini asibiti azubar da cikin.
Kul Kar ink’ara ji kince azubar da ciki domin ke shedace tunda kina zuwa islamiyyah  kinsan hakan babu kyau  kisan kai zakiyi, baki tsoron wajen zubar da cikin kimutu? Inkinje kice ma Allah me?
Kikwantar da hankalinki kinji kidaina damuwa kar kija ma kanki wani ciwon, Allah yana sane da halin da kike ciki,
kicigaba da addu’a.
Share hawayen fuskarta tayi tace toh abbah nagode.
Yauwa mamana Allah yayi maki albarka bari inje insamo miki maganin,
Tunda abbah yafita daga d’akin tak’ara fashewa da wani sabon kukan tana shafa cikinta tace wai ni nakeda ciki kuma na d’an fashi wannan wace kalar k’addara ce Allah kakawo min mafita saida tasha kuka mai isarta sannan takoma takwanta,
Duk yadda taso taji tsanar d’an fashin a ranta ammah ta kasa domin kusan kullum sai ta yi tunaninsa tana jinsa cikin ranta sosai,
A da tana tunanin tsanarsa ce tasa take yawan tunaninsa ammah ynz ta yarda ba haka bane.
Abbah ne yadawo hannunsa d’auke daledoji dasallama yashiga d’akin takeaway din abinci da robar damammar fura yad’auko yamik’a mata da magunguna yace tashi kici abincin sai kisha magani,
Kidaina sa damuwa a ranki kinji ko mamana?
idan kina buk’atar wani abu kiyi min magana.
Kar6a tayi tace toh Abbah nagode,
Murmushi yayi yace Allah yayi maki albarka  sannan yafita daga d’akin,
Furar kawai ta iya sha sannan tasha maganin tatashi tayi sallar azahar takoma takwanta nan bacci yayi awon gaba da ita.
A ranar bacci kawai tawuni tana yi Sallah kawai take tashi tayi sai kuma cin abinci.
Washegari tunda tatashi ta ji k’arfin jikinta kitchen tashiga tahad’a masu breakfast sannan tagyara gidan,
Bata jira ummah tafito ba tad’ibi abincinta saboda yunwar da takeji takoma d’aki taci
Bayan ta gama, Wanka tayi tashirya, baccine yasake awon gaba da ita,
chan cikin barcinta tajiyo muryar ummah tana kiranta,
Firgit tayi tatashi tace na’am ummah,
Ummah da take tsaye bakin k’ofar d’aki taharareta tace ubanwa zai yi miki girkin yau da zaki kwanta kisaki le66a kina bacci har k’arfe sha biyun rana?
Ummah kiyi hak’uri wlh baccinne yad’aukeni ynz zan fito inyi,
Munafukar banza kar kiyi tunanin dan kina da ciki zan rangwanta miki wlh ynz kika fara aiki ma tunda kwad’ayi yakaiki har kikayo cikin shege.
Kuma kifito yanzu kizo kid’aura min girki.
Hawayen fuskarta tashare tace toh ummah,
ta tsani ummah takira cikinta da na shege ammah ba yadda ta iya
Kitchen tashiga tad’aura masu girkin ammah saidai ta kulle hancinta saboda bata son jin k’amshin abincin.
Koda tagama dakyar taci d’an kad’an takoma d’aki tayi Sallah sannan tafara aikin bacci.
Bayan wata ukku cikinta har ya d’an fito ya yi mata kyau ta k’ara haske sosai saidai ramar da tad’anyi domin ko ta girka abincin ba ta iya ci ko da taci toh kad’an ne kuma sai ta had’a da yaji,
saidai tasamo yaro yasiyo mata awara ko wainar fulawa kokuma takira wayar abbah yatafo mata da wani abu daga kasuwa,1
Abbah yana jin tausayin d’iyar tasa sosai kullum in zai dawo daga kasuwa ko da batace yasiyo mata wani abu ba toh shi sai ya siyo mata.
Duk yadda taso tacire tunanin d’an fashin a ranta ammah ta kasa a kullum burinta ko da sau d’ayane tasake ganinsa
****     *****      *****   ****
A chan  6angaren fahad karatunshi kawai yake hankalinsa kwance,
Ba ya shiga harkar kowa abokansa biyu kawai a school d’in domin shi daman baida son yawan abokai,
Mata dayawa suna nuna suna sonsa ammah bai kulasu saboda shi a ganinsa har yanzu babu ajin aurensa domin shi ya fi son kamilar mace,
Wani lokacin idan yazauna yana tuno rayuwar da yayi da su ogah saidai yayi murmushi,
Da ya tuno yarinyar da su ogah sukasa yayi ma aika-aika a lokacin sai hankalinsa yatashi duk sai yaji tausayinta ya kamashi saboda ya 6ata mata rayuwa yanzu baisan wane hali take cikiba………….
A chan 6angaren Amina ciki sai girma yake gashi kullum bata da aiki sai tunanin bawan Allan nan tana son cikin sosai saboda yadda takejin ubansa a ranta kullum sonsa k’ara k’aruwa yake, burinta a kullum ko da sau d’ayane tak’ara sanya shi a idanuwanta,+
Ga masifar ummah kullum dad’a k’aruwa take gashi tace ba za su zauna da d’an shegeba, da ta haihu saidai akai yaron gidan marayu.
Ga ayyukan gida kullum cikin yinsu take kwata-kwata ummah ba ta tausaya mata,
Saidai idan abbah yana gida shine zai hana ummah tasa ta aiki ammah daga inda yafita shikenan.
Ahankali cikin nata yake ta k’ara girma dan ma Allah ya taimaketa ba mai laulayi bane sosai kuma Abbah yana kaita awo asibiti,
tana samun kulawa sosai daga 6angaren abbanta ko da yana kasuwa toh baifin 2hrs ba tare da ya kira wayarta ba domin yaji lafiyarta,
Tunda akace tana da ciki toh ko nan da zaure ba ta son lek’awa.
Mak’ociyarsu Gwaggo ladi ita kad’ai tasan da maganar cikin a anguwarsu,
Gwaggo ladi tana tausaya mata sosai itama tana bada gudunmuwarta wajen kula da ita tana aiko mata da abincin da masu ciki sukafi buk’atar suci,
Tun hannatu mahaifiyar Amina tana da rai suke mutunci da gwaggo ladi,
Domin ta maida ta kamar uwarta ba tada abokin shawara sai ita.
Gwaggo ladi ba ta zuwa gidan indai ba dole takama mataba saboda masifar ummah da bak’ak’en maganganunta,
domin ita ummah kwata-kwata bata son ana ra6arsu,
Ta tsani gwaggo ladi saboda mutuncin da taga sunayi da mahaifiyar Amina tun kafin tarasu.
Akwana atashi cikin Amina tun da yashiga wata tara ake sa ran haihuwarta ammah har yanzu cikin wata na goma shuru,
Saidai ciwon ciki da take d’an yi a tsaitsaye.
Yau kasancewar abbah yana gida bai je kasuwaba saida yabud’e ma ummah wuta sosai sannan yasamu takyaleta ba tare da ta yi wani aiki ba, wanke-wanke kawai tayi takoma d’akinta takwanta saboda ciwon da takeji mararta tana yi ahankali-ahankali,
Yau ko abinci ummah hanata tayi, dan ma Allah ya taimaketa gwaggo ladi ta aiko mata da faten wake wanda yaji alayyahu ta ci.
Bayan sallar la’asar kwance take tana bacci firgit tayi tafarka saboda jin ciwon marar ya tsananta,
Duk yadda taso tadaure ammah ta kasa,
Sunan ummah tashiga kira ammah shuru,
Dakyar tamik’a hannunta tajanyo wayarta number din abbah tayi dialing,
Bugu d’aya yad’auka.
Cikin kuka tace abbah kazo cikina zan mutu,
Dasauri Abbah yafito daga d’akinsa yanufi nata hankalinsa a tashe.
Ganinta cikin mawuyacin hali yasa yafita yanufi d’akin ummah har tun tu6e yake.
STORY CONTINUES BELOW
Babu ko sallama yafad’a yace zainab taso kikama min Amina musata mota mukaita asibiti inajin haihuwarce tazo,
Kallonsa ummah tayi a wulak’ance tace gaskiya Alhaji ba zan iyaba nima nan da ka ganni banda lafiya,
Haba zainab yanzu ko bakida lafiya ba zaki daureba mukaita asibiti?
Gaskiya Alhaji kanason takura min nifa bani nayi mata cikin nan ba, ko shi wanda yayi cikin ko k’eyarsa ba a gani.
Kallon mamaki yabita dashi yace ya yi maki kyau zainab duk abinda kikayi daidaine ammah wlh kiji tsoron Allah,
Baijira amsartaba yafice daga d’akin cikin fushi.
Tsaki ummah tayi tace aikin banza.
Dataimakon abbah tasamu tatashi takawa take dakyar ahankali abbah yana rik’e da ita kuka takeyi sosai ahaka yasakata a mota sannan yakoma d’akinsa yakwaso kayan haihuwar da yake tarawa.
Private hospital yakaita ba asha wahala ba wajen kar6arsu.
Tunda aka shiga da ita abbah tsaye yake ya kasa zama yanata saffa da marwa hankalinsa a tashe tausayin d’iyar tasa yakeji,
Addu’a yake mata Allah yasafketa lafiya.
Har wajen sallar magrib shuru babu haihuwa ahaka dai yahak’ura yatafi masallacin da ke cikin asibitin.
Amina ta jigata sosai duk ta fita hayyacinta likitoci suna ta bakin k’ok’arinsu ammah d’a ya k’i fitowa.
Yana dawowa daga masallaci daidai lokacin doctor yafito daga d’akin yana zufa dasauri abbah yatareshi yana tambayarsa.
Kallonsa doctor yayi yace har yanzu shuru muna dai bakin k’okarinmu muga ta haihu dakanta batare da anmata cs ba.
Hankalin abbah a tashe yace to dr Allah yasafketa lafiya.
Abbah gida yakoma duk yadda yaso ummah tabishi suzo asibitin domin tazauna da ita k’iyawa tayi ran abbah ya 6aci sosai kan dole yakyaleta.
Gidan gwaggo ladi yaje ya aika yaro yayi mashi sallama da ita,
Ba a d’au wani lokaci sosai ba sai gata ta fito nan suka gaisa da abbah cikin girmamawa.
Abbah yace gwaggo Amina ce a asibiti tun d’azu nakaita ammah haihuwa shuru shine nakeso dan Allah kizo muje kizauna da ita idan babu matsala.
Batayi mamakin jin hakan daga gareshi ba domin tasan ummah ko giyar wake tasha toh ba zata je ba.
Kallonsa tayi tace haba Alhaji ai Amina jika ce a wajena idan ban mataba toh wa zanyi mawa na yi zaman lafiya da uwarta idan ban kula da ‘yarta ba ai ban kyautaba amana ma batace hakaba.
Cikin gida takoma tashirya sannan takullo gidan nata kasancewar mijinta ya rasu ita kad’ai ce a gidan sai kuma idan ‘yan jikokinta sunzo.
Ahanya abbah yatsaya a wani resturent yasai masu abinci sannan suka wuce asibitin.
Har lokacin dai bata haihu ba,
Likitane yakira abbah office d’insa.
Jikin abbah duk ya yi sanyi yashiga office d’in.
Waje likitan yanuna mashi yazauna sannan yafara mashi bayani,
Agaskiya Alhaji muna bakin k’ok’arinmu muga ta haihu ammah ta kasa ammah muna tunanin insha Allahu daga nan zuwa cikin dare za ta iya haihuwa kucigaba dayi mata addu’a ammah idan kuma har takai safe toh gaskiya saidai muyi mata aiki afito da abinda yake cikin nata saboda zata jigata dayawa zatakai limit d’in da ba zata iya nishin kirki ba.
Abbah jin d’iyarsa tana shan wuya yaji duk tausayinta ya k’ara kamashi musamman idan yatuno mahaifiyarta wahalar da tasha wajen haihuwa har tarasu ita da abinda ke cikin nata.
Jikinsa duk ya yi sanyi yace toh Dr mungode sosai Allah yasafketa lafiya.
Haka yazo yayi ma gwaggo ladi bayani sukayi ta zama kowa jikinsa ya yi sanyi
Wajen goman dare dakyar aka barsu suka shiga d’akin kwance take tana bacci ammah da ka ganta kasan baccin ba dan dad’i take yinsaba na wuyane ga drip ansanya mata.
Sai wajen sha d’ayan dare abbah yakoma gida ummah tuni har ta yi bacci ko inda take bai kallaba ammah baiyi baccin kirki ba addu’a kawai yakeyi ma d’iyar tasa burinsa tahaihu kafin safe.
Sai wajen sha biyun dare tafarka nan nurses d’in sukasa gwaggo ladi tahad’a mata tea tasha sannan takoma bacci.
Cikin dare firgit tayi tafarka jin ciwon ya koma mata sabo dasauri gwaggo ladi taje takira likita nan sukayi ta bakin k’okarinsu ammah shuru babu haihuwar allurar bacci aka k’ara yi mata.
tun k’arfe shidda abbah yabaro gida ko breakfast baiyi ba restaurant yabiya yasiyo masu sannan yawuce asibitin.
Duk wanda yaga Amina a wannan lokacin sai ya tausaya mata domin ta jigata sosai.
Wajen k’arfe tara aka shiga da ita theatre room lokacin batasan inda kanta yakeba.
Masallaci abbah yakoma yad’auro Alwallah nafila yayi yana rok’on Allah yasa ayi a sa’a.
Sai wajen k’arfe goma da rabi sannan likitocin suka fito,
Dasauri abbah yanufi wajensu domin jin halin da d’iyar tasa take ciki….

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE