K’ADDARA CE CHAPTER 6 BY MAMAN NUSAIBA
Iman na shiga ciki kafin ta k’arasa ta tsaya a bakin k’ofar Gidan ta fashe da kuka, Cikin kuka ta soma magana kamar haka: Kayi hak’uri Abdul Malik bazan iya Auren mai kud’i ba, gashi ka dasa min Soyayyar ka a raina , ni kuma bani da ra’ayin auren irin ku. Saina taci kuka mai isar ta tukun ta shiga ciki, babu wanda tawa magana ta shige d’aki. Sultana ce ta bita ciki ganin yadda hawaye ya jik’a mata fuska…
A Zau ne ta sameta tana kallon gefe d’aya , zama Tayi a kusan ta Ta ce.” Iman banji dad’in Abun da kika fad’awa Abdul ba gaskiya! Kina tunanin Abdul Malik zai cutar dakene? Ko kina tunanin zai ke wulak’anta kine? Da ace zaiyi haka da bazai ce yana son Y’ar Talakawa ba, sai kuma gashi Yace” yana sonki da aure, Iman wai wannan wani irin ra’ayi ne gareki? Ko kanki ya soma kuncewa ne?
Kallon ta Iman Tayi Ta ce.” Ki fad’i duk Abun dake ranki, amma ni bazan auri mai kud’i ba, kema kinsan tin muna Yara nake da wannan ra’ayin, ke kanki kisan masu kud’i in suka auri D’iyan Talakawa sai suke wulak’anta su, ni kuma kinsan bana daukar reni….
Sultana Ta ce.” To shikenan ai amma baki yiwa masu kud’i adalci ba Iman, tinda har kika musu kud’in goro, ai ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai na gari a cikin su, dan Allah ki daure ki amshi Soyayyar shi! Idan kika mishi haka kin zama marar adalci, kuma kinga Abdul Malik da gaskiya yake sonki ba da wata manufa ba! Amma kiyi tunani akan magana ta ni zan koma Gida, Abincin mu ma shiya siyawa Y’an tsaron shagon Daddyn shi…..
Ita dai Iman shuru Tayi bata k’ala ba, sai bin Sultana da ido take ganin tana had’e rai, tana ganin fitar ta ta koma gado ta kwanta , sosai take jin zuciyar ta na mata wani irin rad’adi da zafi, taya zata iya rabuwa da Abdul Malik a lokaci d’aya? Alhalin zuciyar ta Ta dad’e ta kamuwa da k’aunar shi. Haka tayi ta tunani ban katai har bacci Yayi gaba da ita….
**************************
B’an garan su Sultan, tinda suka bar Kasuwar ran Imam a matuk’ar b’ace har suka nufi Masaukin su, _Royal Hotel_ nan naga sun nufa ,sun packing ko motar Sultan bai kashe ba Imam ya futo fuuu…..
Shi dai Sultan da kallo ya bishi san nan Yayi dariya, fitowa Yayi ya nufi ciki, da mai lamba 25 suka shiga, a kan gado Imam ya zauna sai cin magani yake yana huci kamar wani kumurcin maciji.. Sultan Ya ce.” Haba Imam wai duk saboda da wannan Yarinyar ne kake wannan hawan kamar an fulawar yin banke? To kayi hak’uri! Bakaga Yarinyar ma bata da lafiya, kai da gani wannan mai irin sunan naka Aljannu gareta…
Kamar Imam bazai yi magana sai cen yaja numfashi tukun ya motsa d’an k’aramin bakin shi Ya ce.” Haba Sultan taya zakace wai karna damu! Ka duba fa wannan k’azamar Y’ar Talakawa kucaka marar tarbiya mai gantali da Kasuwa, ta had’a jikin ta da nawa taya zaka ce ba wani abu bane? Kaima kasan ai wannan renin hankali ne. Imam ya k’arashe maganar yana cire rigar shi……
Sultan baiyi mamakin jin haka daga Abokin nashi ba, saboda ya riga daya san yadda Imam ya tsani Talaka baya son had’a guri da Talaka, zaiyi magana yaga Imam ya shige toilet yana kwarara amai. Zama Yayi ya dafe kanshi Ya ce.” Ya Allah! Ina rok’on ka da Sunayen ka tsarkaka Allah ka shirya min Abokina, Allah ka jarabceshi da son Y’ar Talakawa ita kuma Tace” duk Duniya va wanda ta tsana kamar shi, dauke hannun shi Yayi yana fad’in. Wallahi Imam sai kaga yadda rayuwa zatayi dakai! Ni bansan wani irin bak’ar zuciya ne dakai ba! Wai kake cewa baka son Talaka ko? To Insha Allah Y’ar Talakawa ce Matar ka, kuma itama sai yi kamar kayi hauka akan son ta tukun ta aure ka, banza kawai shashasha, Wallahi da ana cenja zuciyar Mutum ba tare da sanin mai zuciyar ba dana canja taka! Zakaga yadda ake wulak’anta Talaka, saika nemi taimakon Talaka a rayuwar ka.. Sultan iya matuk’ar b’acin rai yau Imam ya k’ure shi, saboda yadda yake fad’awa Imam bak’ar magana……
Fitowa Imam Yayi yana wani done hanci sai shinshina jikin shi yake yana yin kamar zaiyi amai , Ya ce.” Oho dai koma meye kai kasan har abada bazan taba neman taimakon talaka ba, kuma ko a mafarki bazan taba had’a gurin zama da Y’ar Talakawa ba bare har na zauna inuwa d’aya da ita a matsayin Matar aure na ta Sunna, kai meye had’in ka da wannan banzayen Yaran da har kake fad’a min magana a kansu?
Sultan Ya ce.” Y’an Uwana ne tinda suma mutane ne kuma Musulmai , k’ila ma sun fika matsayi da daraja a wajan Ubangiji, Wallahi Imam kabi Duniya a hankali! Nifa gaskiya nake fad’a maka , duk Abun da kaga ina maka son ina k’aunar kane tsakani da Allah, sai fa Masoyin ka yake fad’a maka gaskiya duk d’acinta! Ka sani ita fa rayuwar ba wata mai tsayi bace, Imam ka zauna da kowa lafiya saboda baka san nan gaba waye zai taimake kaba! Yanzu su Yaran da kake fad’a musu bak’ar magana kana tunani wata rana bazasu taimake kaba? To ka canja halin ka tin kafin Duniya da Mutanen cikin ta su canja maka! Idan kaga dama ka dauka,idan baka ga dama ba karka dauka ruwanka ne. Sultan na gama maganar shi ya janyo wayar shi ya danna kira……
Imam kuwa ko a jikin shi babu wata magana data shigeshi saima mita daya soma yana fad’in. Ba dama Mutum yayi abu sai an mishi sa ido to ni bazan iya irin wannan banzan halin naka ba, kai kowa ma ka gani saika ce zaka kula shi , kuam Allah ya kiyaye ma wannan marassa tarbiyar Yaran su taimakeni, ko mafarki nayi sun taimake ne inna tashi sai nayi Addu’ar neman tsari dasu…..
Sultan na jin shi amma ya maida shi gefe yaci gaba da maganar da yake a waya, Ya ce.” Y’an Mata ya jikin naki? Kiyi Hak’uri kinga banzo na duba kiba Wallahi mun zo K’asar Kwatano ne bama Gida, amma inna koma zanzo yaga ya jikin naki yake….
Daga cikin wayar Yarinyar ta soma magana ,dayake ya bud’e volume d’in ne duk dan ya cusawa Imam haushi, Ta ce.” Uncle yau she zaka dawo? Inaso na ganka kuma Mama ta nuk’o gari zata maka tuwon gero da miyan kuka, to da baka zoba sai ta shanya ya bushe Tace” wai sai kazo sai ta maka, Uncle ka siyo min Teddy mai kyau inaso kaji!
Y’ar dariya Yayi Ya ce” to shikenan zan kuwa siyo miki, kice wa Mama na kusa zuwa Gida tayimin tuwon dama na jima banci tuwo ba.. To Yarinyar Tace” mishi tukun sukayi Sallama….
Done hanci Imam Yayi Ya ce.” Wai kai har Yanzu kana tare da wannan Y’ar Yarinyar? Har da wani a maka tuwon gero da miyan kuka, wai Allah kamar nayi amai nakeji, ai ko ciwon mutuwa nake bazan ci tuwon gero ba…..
Sultan Ya ce.” To ina ruwan ka? Ni da nakeso ai zanci d’an renin hankali, kaje kayi duk Abun da kaga dama.. Yana fad’in haka ya kwanta ya juya mishi baya. Shima Imam kaya ya saka marar nauyi ya kwanta a gefe d’aya yana cin alwashin duk ranar daya gamu da Iman ko Sultana saiya musu rashin mutumci, tinda a kansu ne har Sultan yake mishi muguwar Addu’a, saiya wulak’anta su fiye da yadda basa tunani tinda su basu da tarbiya. Haka dai yake karatun jaki har bacci Yayi gaba dashi………
**************************
Hanan ce ta fito jiki a sanyaye ta saka hijabin ta, komai a sanyaye take inta tuna wai ita ce zatayi auren cin amana? Hakan na sakata damuwa, su Saudat ta raka school tukun ta nufi Gidan Maman Islam. Da Sallama ta shiga tana kallon ko ina kamar wata B’akuwa a Gidan.
Ilham ce ta fito tana saka mayafi kafad’ar ta dauke da Y’ar k’aramar jakar ta, cikin fara’a Ta ce .”A q Hanan kece dama jiran ki nake yi sai gaki kinzo….
Cike da fargaba Hanan ta dafe kirji Ta ce.” Ni kuma Anty! Allah yasa ba wani abu nayi ba…
Ilham dariya Tayi ganin yadda ta tsorata Ta ce”. Babu Abun da kikayi Hanan girki zaki mana duka daku zanje Unguwa ne, kafin na dawo k’ila kin gama ko kin kusa…
Hanan Ta ce.” To Anty amma in kika jima zan tafi Gida.
Ilham Ta ce” to bazan jima ba na tafi saina dawo. Tana fad’in bata ko tsaya jin Abun da Hanan zata fad’a ba ta wuce …..
Ajiyar zuciya Hanan ta sauke tukun ta shiga kitchen d’in, Abinci mai sauk’i Ta dafa, komai a gaggauce take yi saboda bata so Yaya Faris yazo ya sameta a Gidan, tana gamawa ta jere kulolin Abincin a kan dirning…
Duk Abun da take Yana zaune yana kallon ta shi dariya ma ta bashi ganin yadda take sauri, baiyi magana saboda yanaso ya more da kallon ta…
Hanan ta fito falon, dan kwalin ta ta cire tana zama a kan kujera Ta ce.” Wash Allah gaskiya na gaj… Ai bata k’arasa maganar ba tayi ido hud’u da Faris har tana gogar kafad’ar shi. Da sauri ta yunkura zata mike Yayi saurin janyota ta fad’o jikin shi ya rufe mata baki…….
Zaro ido Tayi jin ta a jikin shi, sosai taji yadda zuciyar shi take bugawa da sauri da sauri, jin ya k’ara rumgume ta sai Abun ya tsorata matuk’a gaban ta na dukan uku- uku jin yadda ya matse ta kamar zai maida ta cikin shi…….
_Wannan Littafin na kud’i ne ki biya naki kud’in Sister domin ayi tafiyar nan dake_
_Nomal N 300 ne_
_Vip N500 ne_
TAKU HAR KULLIN MAMAN NUSAIBA CE ✍🏻 ALK’ALAMI YAFI TAKOBI 🗡️📿