KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 10 BY JAMILA UMAR TANKO

Nan da nan ta hau kisisina ta na fitar da kalaman bada

hakuri da kwantar da hankali.

Ta ce “kama ce kawai, kuma daman a duniyà ba’a rasa irin wannan kamar.”

Bakura ya mike tsaye, kallon ya fita a ransa hakika ya

fara shiga yanayin daya saba shiga idan tunanin Zuhuriyya ya juyo masa. Babu wata kalma, babu wani-mahalukin da zai iya hana shi zubar da hawaye da dogon tunani. Sai yayi ta addu’a da zikiri sannan abun yake fada masa. Don haka Samira ta dade da sanin haka, amma bata barinsa haka tana kokarin zama da shi ta bashi baki, ta nuna masa ta fishi damuwa akan haka. Ya mike ya nufi dakinsa cikin sauri ta kashe kallon ta bishi, su ka raba dare tana fada masa maganganun kwantar da hankali, shi dai yayi shiru yana sauraranta bai ce da ita uffan ba.

Da ya gaji da kwanciyar sai ya tashi yayi alwala ya dinga salloli ya na addu’a har asuba.

Kwanci tashi Bakura ya shafe watanni hudu yana zuwa daukar karatu wajen malam Yakubu, a sati sau uku bai taba fashi ba. Haka sabon_zumunci da shakuwa ya dasu a zuciyoyinsu. Abu kamar wasa har abun ya fara bawa Bakura kunya domin kusan duk haduwar da zasu yi da Malam Yakubu sai ya dauko wani abu ya bashi, kuma ya tilasta masa dole sai ya karba. Ga uwa uba hidimar abinci da yake sawa a dafa masa duk sanda- suka gama karatu ya kuma tilasta masa sai ya. ci, amma har rana irin ta yau Bakura bai taba ido hudu da Sajida ba balle mahaifiyarta sai dai yakan jiyo muryarsu sama-sama daga cikin gida. Wata rana, ranar Litinin da yamma Bakura ne ke tafe cikin jibgegiyar motarsa Jeep Murano. Gefansa kuma babbar ‘yarsa ce Zahra, sanye take da qaton hijabi. Babu abin dà za ka iya gani a jikinta daga fuskarta, sai tafukan hannayenta. Daga dukkan alamu daga makarantar Islamiyya take, domin ga jakarta a rataye a kafadarta cike da Kur’anai Ta juya ta dubi mahaifinta wanda ke kallon gabansa

  • yana tuki da alama ya na cikin matsanancin tunanin da ya saba yi a kwanakin nan. Ta mika hannu ta kunna C.D da ke jikin motar.
  • Kan ka ce kwabo wakar Sani Aliyu Dan Dawo wacce ya yi wa gwamnan Sokoto ta fara tashi, yayin da speakers din da ke kusurwoyin motar suka fara fitar da sautin ganguna.
  • Bakura ya juya ya dubi Zahra, sai ta yi murmushi, ya sa hannu ya kashe radiyon ya juya kansa ya ci gaba da kallon. gabansa ba tare da ya ce mata komai ba:
  • Ta yi shiru na wani dan lokaci mai tsawo. Can ta murda
  • makulli ta bude gaban motar inda gaba daya disc din C.D kala-kala a layi ta zabo wani, shi kuma na karatun Kur’ani ne wanda Sudes limamin masallacin Makkah ya yi. Ta cire wancan na ciki ta. saka wani. Cikin ‘yan sakonni qira ‘a mai dadi ta fara tashi. Bakura …ya juya ya dubi Zahra sai ta yi murmushi a karo na” biyu, ya sa hannu ya kashe. Sai mamaki ya rufe Zahra kamar za ta yi magana sai ta fasa don ba ta ga fuskar yin magana ba. Ta sake bude wajen ajiyar za ta dauko wani C.D na-wakar Shata sai Bakura ya ture hannunta gefe ya mayar da wajen ya rufe.
  • Ya ce, “Wai yaya haka ne Mamana. Kin cika kiriniya kamar wata karamar yarinya, ko ke ce Usman dan auta?”
  • Ta yi dariya ta gyara zama ta zare farin gilashin da ke
  • fuskarta. Ta ce “Abba, kwana biyu kamar kana cikin damuwa, Umma ta ce wai ka ga wata mai kama da Zuhuriyya?”  Yayi shiru yana dubanta yayin da amsa ta qaurace masa Can jimawa Zahra ta sake cewa. “Abba, ni kuwa zan so in ga mai kama da Zuhuriyyarka ko ba komai zan dinga tuna: kamanninta a rayuwata.”
  • Wannan karon ma da sauri ya waiwayo ya dube ta ba tare da ya ce mata komai ba, sai ta ga ya juya kan mota sun canza titi sun baude daga hanyar gida su na ta tafiya ba tare da wani daga cikinsu ya sake magana ba.
  • Zahra ta yi shiru tana tunani a ranta. “Shin me yasa
  • Abba ya juya da kan mota, ina za mu je ne?”
  • Musamman da ta ga an wuce Lamido Cresent an shiga
  • Badawa Layout. Su ka wuce sai ta ga su na ketawa cikin gidajen gargajiya. Zahra ta gyara zama ta dubi unguwar sosai ta juya ta dubi mahaifinta.
  • Ta ce “Abba, ya sunan nan unguwar?”
  • Ya dube ta ya kawar da kai gefe kamar ba zai bata amsa ba, dan daga dukkan alamu baya son yin magana. Can ya bude baki da kyar.
  • Ya ce, “Sunan nan unguwar Kawon Alhaji Sani.” Zahra ta gyada kai sannan ta maimaita sunan unguwar.Ta ga yana sake danna kan motar cikin lunguna, ga kwata -ga gidajen kasa. Sai Zahra ta ji hankalinta ya fara tashi a. tunaninta wani kauye ne suka shigo ba cikin. Kano ba.Tsoro ya hana ta sake yi masa wata tambayar. Daidai wani kofar gida ta ga ya ja burki ya tsaya. Zahra ta dubi kofar gidan da suka tsaya ta daga-daga babu ko fenti ga almajirai nan tsibiri-tsibiri a gofar gidan su na ta karatu. Ta juya ta dubi mahaifinta cike da mamaki take
  • tambayarsa. “Abba, ina ne nan?”
  • Ya yi dan murmushi ya ce, “Na kawo ki gidan, mai
  • kâma da Zuhuriyya. Ba kin ce ki na so ki ganta ba, ko kin fasa mu juya?”
  • Ta yi dariya ta ce, “A’a mu shiga mu ganta.”
  • Ya yi dariya ya ce, “Ki shiga-dai ni ina kofar gida, ya ya zan shiga gidan matan aure? Ki shiga tana ciki Sunanta Sajida.”
  • Zahra ta tambaya, ‘Sajida sunanta? What a nice name? I like the name Sajida.”
  • Su ka bude kofar mota suka fito gaba daya. Malam Yakubu cike da mamaki mai hade da farin ciki ya mike ya tari Bakura ya na; fadin, “Lale marhaban, yau muna da manyan baki sannunku da zuwa, Kai da ‘yar jikar tamu ce?”
  • Bakura ya duga ya gaishe da Malam. Nan da nan Zahra
  • ta zube har kasa ta kwashi gaisuwa.
  • Bakura ya nuna Zahra ya ce, “Malam ga Zahra ‘yata
  • ta fari na dauko ta daga Islamiyya na ce bari in bio da ita ta gaishe ku saboda wata rana, kar a hadu a hanya ba a san juna ba.”
  • Malam Yakubu ya fada cikin jin dadi, “Lallai naga
  • -Zahra ai daga gani babu tambaya naga kamarta da kai sak, Zahra kai ta biyo kama daina wahalar da kanka wajen gabatar da ita duk inda ku ka shiga kallo daya za’asan ‘yarka ce,na dade banga irin dan da yayi kama da uba ba haka. kuma ka kyauta daka kawo min Zahra, amma fa na ji dadi. Allah ya yi muku albarka, Allah ya gara zumunci. Zahra shiga cikin gida gani nan zan shigowa zan y musu bayani. Alh. Bakura bari in dauko maka tabarma® shimfida maka a kofar gidan makwabtanmu saboda kofar gidan namu yau a cike yake da yan makaranta. Bakura ya yi dariya ya ce, “A’a babu komai Malam, zan
  • koma cikin mota in jira har ta fito saboda ba dadewa za ta yi ba, za mù wuce Magriba ta kusa.”Malam Yakubu ya ce, “To bari in shiga cikin gidan in gabatar da ita a wajen Sajida da mahaifiyarta, don ba su sanku ba, ita:ba ta san su ba.”
  • Bakura ya ce, “Haka ne, lallai ba ta san yadda za ta gabatar da kanta ba, don nima ban yi mata bayani ba.”
  • Malam na shiga cikin gidansa ya iske Zahra a Zaune
  • kan tabarma, mahaifiyar Sajida kuwa Furera na Zaune akan kujera a gaban murhu tana hidimar siyar da kunun kanwarta da dan wake.
  • Yahuza kuwa ya zo ya saka Zahra a gaba a ya faki idonsu ya ce mata. “Bakuwa za ki ba ni naira hamsin idan za ki tafi?”
  • Sajida kuwa ta dauko turmi ta hau tana hira da
  • makwabta. Wayar da aka hana ta yi shine take lekawa makwabta ta katanga kawarta Hajiyayye tana ba ta aron waya tana kiran Abdulmajid. Don haka tana jin muryar mahaifinta ta yi sauri ta wurga musu wayarsu ta daka tsalle ta diro.
  • Malam ya daka mata tsawa ya ce, “‘Sajida ban hana ki hirar nan da kawayenki ta katanga ba? Idan hirar suke so da ke su. zagayo mana dan dai ke ba zan bari ki leka kofar gida ba, balle ki shiga makwabta mutaniyar banza. Ga bakuwa nan kin yi ko kula : ta- ba ki yi ba, baki iya sannu da zuwa ba, balle ga ruwa. Kunqi. shimfida mata tabarma kowa ya juya yana harkokinsa, ko ruwa ba ku iya kawowa bakuwa ba. Yanzu Furera da girmanki a matsayinki na uwa sai an fada miki, sannan za ki kula bakuwa dan baki san ta ba.”

Hmmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE