KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 11 BY JAMILA UMAR TANKO
Furera ta zabura ta ce, “Wallahi ni na dauka bakuwar
Sajida ce ko ‘yar makarantarsu ce ta ga kwana biyu ba ta zuwa ta to ta gani ko lafiya. Ta shigo ta yi sallama na ba ta tabarma ta zauna muka gaisa, ai ban san daga kofar gida ka ce ta shigo ba.”
Malam ya fusata ya daka tsawa, “rufe min baki, bakya
kula ni, ni kaina idan kina gaban kunun nan baki da lokacin kowa ta sayar da kununki kike yi kawai. To wallahi zan-hana sana’ar nan.”
• Ya juya ya dubi Yahuza ya yi masa tsawa ya ce, “Me ye kai kuma ka zo ka saka ta a gaba? Tashi ka dauko mata ruwa ta sha.”Furera ta tambaya;
“Malam yar gidan waye wannan din.”
Malam ya ce,Tsagwaron zumunci da girmamawa ce
tsakanina da mahaifinta, shi ne mai zuwa daukar karatun nan wanda nake cewa a dinga zubo min abicin mutane biyu ni da shi.
To ‘yarsa ce ya kawo ta ta gaishe mu.”
Furera na budar baki sai ta ce, “Wai wa yaga dorin dosano ‘yar gidan mai daukar karatu a kofar gida. To mu da ba kofar gida muke lekawa ba yaya za a yi mu san mahaifinta, balle mu san ‘yarsa? ka ga dole sai ka shigo ka yi mana bayani.”.
Zahra ta dago da sauri ta dubi Furera da alama
kalaman Furera bai yi mata dadi ba. Malam ma bai ji dadin maganar ba, sai ya ji kunya ta lullube shi. Yahuza ya kawo wani dakalallen ruwa a cikin wani ragargajejjen kwano mai lamba da tsatsa. Sajida na tsaye ta na kallon Zahra kasa-kasa, Allah-Allah take Malam ya fita ta kara hawa turmi ta leka katanga kawarta ta miko mata aron waya ta kira rabin ranta Abdulmaid.Malam ya harari Sajida ya ce, “Ki dauki ruwan ki ja ta dakinki ku gaisa mana ki dawo ki zuba mata kunu.”
Furera ta zabura ta dube shi ta ce, “Kunun nawa zan
zuba?Ai ka san na siyarwa ne.”
Zahra ta yi sauri ta ce, “Ah! Alhamdulillah, à bar shi
“na koshi.”
Malam ya ji wani mummunan bacin rai, ya kudira a
•ransa idan Zahra ta tafi sai ya tozarta su kamar yadda su ka tozarta shi gaban baquwarsa. Bai ce-komai ba sai ya kada kai ya fice.
•Ya na fita Sajida ta dubi Zahra ta ce, “Ke-dan Allah ki na da waya?”Zahra ta tambaya “Wacce irin waya?”
Sajida ta ce, “Ashe fa ‘yar gayu ce ba ki san waya ba, ina nufin hanset.”Zahra ta ce, “Yes, ina da hand set.”
Sajida ta yi fari da ido ta ce, “Akwai kudi kuwa a wayar? Zahra ta ce, “Akwai dubu shida a ciki.”
Sajida ta yi ihu ta fada cike da mamaki mai yawa ta ce,
“Dubu shida? Lallai wannan ‘yar gidan masu maiko ce. Saurayinki ne ya hada miki wayar ya ke sako miki kati haka da yawa?”Zahra ta bude baki tana kallon Sajida cike da mamaki;yayin da kalmar saurayi take yi mata reto a kwakwalwa.Furera ta tsaya tsai daga zuba kunun da take yi. Ta ce Wayar ce dubu shida ko kudin cikin wayar?
Sajida ta ce, “‘Umma! kudin cikin wayar ne dubu shida, wayar kuma ai sai dubu hamsin.”
Furcra ta gyada kai ta fada a hankali, “Cafdijam dan garawa mai karfi-karfi za a ce in zuba ma ta kunu kyauta.”Sajida ta ce “To kawata dan ba aron wayar ta ki inci ko dubu daya ne.” Zahra ta bude jaka ta dauko wayarta tsaleliya kirar N85 ta miga mata. Sajida ta latsa wasu lambobi kan a jima network ya hada ta da abin kaunarta Abdulmajid.
Ta fada cikin lallausar murya.Hello darling
Abdulmajid, Sajimajid ce, kar ka damu ba flashing nake ba wallahi wayar wata girl ce ‘yar gidan masu naira. Ka san nawa ne a cikin wayar?
Naira dubu shida, ka ga za mu iya kaiwa tsakar dare muna magana.”
Furera ta dubi Sajida ta ce, “Shegiyar yarinya. marar
jin magana, ai sai ki shiga daki ki yi wayar kafin Malam ya shigo ya hada mu duka ya zage.”
Sajida ta ce, “Umma ba abin da nake fada muku kenan
ba, ga Zahra nan ita iyayenta sun yarda ta kula samari, na tabbata saurayinta ne ya hada mata wayar nan, yake zuba mata kudi.”.
Furera ta ce, “A to ‘ya’yan masu hali ma kenan balle mu yan Allah Ya baku ku ba mu. Laifin mahaifinki ne da ya hana.”Abdulmajid da yake kan layi har yanzu yana jin abin da Sajida da mahaifiyarta su ke fada..
Ya yi murmushi ya ce, “‘Ki ce kina magana a wayar big
giri, wanne irin model ce.” Sajid ta ce, “N85 ce.”
Ya ce, “Lallai babbar harka take yi. Ya ya sunanta ko
Allah zai sa wani lokaci in kira layin kuna tare ta ba ni ke mu yi magana?”
Sajida ta ce, “Ina jin Zahra sunanta, but l’am not Sure,
•kar ka damu ta zo ne za ta tafi ba lallai ne mu sake haduwa ba, mu yi maganarmu kawai.”
Sajida ta dubi Zahra, ta juya ta dubi mahaifiyarta sai*
ta ga gaba daya sun zura mata ido su na kallonta su na sauraronta. Sai ta ji kunya ta tashi ta shiga daki ta cigaba da yaryada masa zakakan kalamai na so da Kauna.
Malam ya turo Yahuza fiye da sau biyar kiran Zahra ta fito za su tafi, babanta ya gaji da jira. Ba Zahra, Da dalilinta, domin har yanzu Sajida ba ta gama da wayar ba. Ita kuma nauyi da kunya ya hana ta je cikin daki ta sami Sajida ta karbi wayarta.
Sai da Malam ya shigo da kansa ya sami Zahra a zaune a inda ya. barta ya dube ta ya yi dariya.
Ya ce, “Zahra hira ta yi dadi ko? Abbanki ya ce ki zo ku tafi, nayi-nayi ma ya barki ki kwana ya ce gobe da safe akwai makarantar boko:” ta sunkuyar da kai kasa tace, “Baba yanzu zan fito Sajida nake jira tana daki tana…”
- Furera ta katse ta ta yi sauri ta mike tsaye ta ga asiri zai tonu. Ta ce “Sajida take jira ta fito ta raka ta, ka san har sun zama kawaye, wato dai yau rakiyar kura za a yi idan ta raka ta ita ma sai kaga ta rako ta. Bari in kira Sajidar a daki ina ga kuka ma take yi na rabuwa da zahra in ce ta zo ta rakata.”Malam ya ce,Kai rakiyar meye za a yi tayi mu tafi kawai.”
-Zahra ta mike ta bi Malam a baya suka nufi qofar waje.Har sun kai zaure sai ta ji Umma Furera ta jawo hannunta ta cikin hijabi ta sunna mata wayar a hannunta, gami da yi mata rada a kunne. Ta ce, “Yarinya kar ki fadawa Malam ko mahaifinki sai ya
• yi fada.”Zahra ta gyada kai ta duga ta ce, “Na gode.”
Malam ya waiwayo a fusace ya ce da Furera. “Me ye
kuma kike yi ma ta rada?”Umma Furera ta yi sauri tace, “Lah! Ba komai kudin mota na ba ta.” Sai ta tuna da mota suka zo sai ta ce, “Au! Kudin da za ta sayi ‘yar alewa ta kaiwa Kannenta.”
Malam ya yi murmushin jin dadi ya ce, “Madalla Allah ya saka da alkhairi, to ki koma ciki rakiyarta isa.”
Mamaki marar musaltuwa ya rufe zuciyar Zahra da ta
ga babba tana karya. Furera ta dade a zaure tana leken Zahra da mahaifinta har suka shiga mota suka tafi.Zahra ta na zama a cikin mota ta dubi mahaifinta.
Ta ce “Abba ka yi hakuri na dade.”
Ya girgiza kai ya ci gaba da tuki. Ya ce, “Ba damuwa.
Ina fatan kinji dadin ziyarar da kika kai?”
Ta ce “Eh, to gani nan dai, na yi farin ciki ban yi farin
ciki ba.”Bakura ya waigo da sauri ya dubi Zahra yayin da ya ji zuciyarsa na bugawa, don fargaba.
Ya tambaya ya ce, “Me yasa kika fadi haka Mamana?”
Ta yi dan murmushi ta ce “Abba Sajida da Umma
Zuhuriyya ta yi kama ko Mamarta Furera?” *
Bakura ya yi shiru na dan wani lokaci sannan ya ce
“Sajida da mahaifiyarta Furera su na kama ne?”
Zahra ta girgiza kai
Ta ce “Ba sa kama kwata-kwata. Mamar Sajida fara ce sol, amma duk fuskarta tsage-tsage irin na Fulani kuma ita mai kiba ce sosai. Hancinsu ba iri daya ba, bakinsu, idonsu, kafarsu, qirar jikinsu, duk daban-daban ko kadan ba su yi kama ba. Sajida tana da kyau sosai ta fi mahaifanta da wannan qanin nata Yahuza kyau.”
Hmmm