KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 13 BY JAMILA UMAR TANKO

waya in kada ta sake baki. Ahirr dinta kar in ji kar in gani. Ko Abdulmajid din ne ya bugo ya ce a bakita ce

mahaifinki ya hana ku yi magana. Ke in ki na da zuciya ma har za ki tsaya kina shan duka akan dan iskan nan Abdulmajid, yaron da ya ke shigowa har zaure ya na zagin mu ya na kiranmu mutsiyata. Idan da gaske yake son naki ba lalata yake nema ba, ai ko boye zai ringa ambulo miki kudi, amma ni dai ko sisinsa ban taba ci ba sai alewa cakulet mai zagi da askirim babu abin da su ke gara min illa su sagar min da hakora. Ni ba atamfa ko leshi yake aiko min ba. Idan ya yi tafiya ne yake ciko leda da riga da skirt da wanduna ya ce ga nawa ga naki. Dan iskanci ya dube ni ya aiko min da jeans da T-shirt. Har da suyo tafka-tafka wanduna wato daidai jikina in tsuke in fita gofar gida cikin almajirai mu yi wakar Micheal Jackson kenan, ko mu yi rawar nanaye.”

Sajida ta fusata ta mige da sauri ta na buga gafa, ta

shiga cikin daki ta na cewa “To wallahi tunda takura min za’a yi, cikin dare zan hada kayana a neme ni a rasa tunda abin haka ne.”

Umma Furera ma ta na ta babbamin fadanta a gindin

murhu inda ta kunna itace ta dora ruwan zafi cikin katuwar tukunya don gasawa Sajida jikinta don duk ya farfashe.

Bayan Umma Furera ta gamawa Sajida gashin baya da

tsumma da ruwan dumi, ta umarci Sajida ta daure ta shiga bandaki ta yi wanka da zazzafan ruwa, saboda ciwon jiki. Bayan Sajida fito daga wanka suka dasa kujerar zama su na jiran shigowar Yahuza, domin su dauki fansa akan masifar da ya jawo mu su a sanadiyyar gulma, munafunci da tsegumi dukka ya iya.

Shiru-shiru Yahuza bai shigo gidan ba, dare ya fara nutsawa, goma tayi har Malam ya shigo ya shiga daki ya kwanta babu Yahuza, babu dalilinsa. Daga nan su ka gasgata zargin da suke yi wa Yahuza cewar shi ya aikata, don haka ya qi dawowa. Ba su damu su dauki gyalensu su fita nemansa ba, haka ba su damu su fadawa Malam cewar har yanzu Yahuza bai shigo gida ba. Daman ya saba idan ya ga dama ya kwana a gofar gida cikin almajirai.

Idan ya so ya kwana da almajiran zaure, haka idan ya so ya shigo cikin dakinsa ya kwana. Daman ba rufe gida ake yi ba gofar daki ake sakayawa. Don haka Yahuza bai dawo ba su ka gaji da jira sai suka yankewa Kans shawara su tafi su kwanta.Allah ya kai su gobe ai dole zai shigo da safe daukar kayan makaranta a dakinsa, to anan sai su yi caraf su damke shi: Umma Furera ta shiga dakinta, Sajida ma ta shiga nata akurkin. Kowa ya jawo bushashshen katakon da aka lagabawa da suna gofa ya rufe. Sabanin Umma Furera Wacce tama shiga daki minti biyar ya yi yawa ta fara jin jiniyar munsharinta na tashi, amma Saida five da awa biyar bacci ya yi wa idanuwanta yajin aiki. Juyi take akan ‘yar katifarta yaloluwa irin ta ‘yan makaranta, ta kasa bacci saboda tsananin takaici da tashin hankali. Sai a lokacin ne ma ta yi kukan dukan da aka yi mata, don dazu azaba ta hana ta kuka. Sheshshega take tana ajiyar zuciya, fadi take bayyane.

“Wayyo Majid dina.”

Kaico! Soyayya gamon jini, ko shi Abdulmaji din da ake yi dominsa a wanne hali yake a daidai wannan lokaci? Oh00000o!!! Asubah ta gari SajiMajid.

*********

Washe gari da sassafe Sajida ta fito tsakar gida tana mika game da doguwar hamma, ta cije baki ta masa gabobin hannayenta ta danna doron bayanta, saboda ciwon da suke yi mata a sanadiyyar bugun da ta sha.jiya. Umma Furera kuwa tunda

Asuba kiran fari ta hau hidimar dora ruwan koko da wainar geron da take yi da safe ta siyarwa, dan haka tana gindi murhu a tsakar gida.

Malam kuwa tun kafin kiran fari na asuba ya yi alwala

ya fice, sai kuma da hantsi zai shigo gida.

Yahuza ne ya shigo cikin gida cike da fara’a da farin

ciki. Wata karamar bagar leda ce a hannunsa. Ya dubi

mahaifiyarsa ya juya ya dubi Sajida bai kula da kibiyoyin harare-.hararen da suke harbo masa ba.

Yayi dariya ya ce, “Kun san meye a cikin ledar nan

kuwa? Soyayyan dankalin turawa ne da kwai, na bi almajirai bara cikin Badawa layout gidan da Abashe yake aiki aka ba mu sadaka.

Ashe almajiran nan dadi suke ci. Nima daga yau idan zasu je sai na bi su. Wallahi attajirai nan wayo suke yi mana dadi suke ci. Idan Baba baya nan almajiran nan zan dinga bi bara. Haka jiya

shinkafa da kaji muka ci a kofar gida. Muzambilu ne ya samo mana.”Umma Furera ta daka masa tsawa, ta ce “rufe min baki munafuki, kai za ka yi laifi a rufa maka asiri, amma kai ka kwashi maganar da ba a saka a ciki ba ka je ka yi gulma. Yau sai na fasa maka baki. Bari Malam ya shigo, sai na fada masa ashe har yanzu ka na zuwa bara.”

Sajida ta fisgo ledar dankalin da ke hannunsa ta

zazzage a cikin bokitin sharar da ke kusa da ita, tasa tsinke ta daddanna ta cakuda da bolar. Yahuza ya ji tamkar ‘ya’yan hanjin cikinsa ta yi wa haka. Don a

halin yanzu ya fi son dankalin nan akan rayuwarsa. Ya

kwalla wani ihu kai ka ce ransa ake kokarin fitar masa.

Ihu yake ya na kiran “Wayyo dankalina, na shiga uku na lalace. Wallahi sai na fadawa Baba.” Sajida ta ce, “Ka fadawa Baba ka tonawa kanka asiri, daman ai ya hana ka zuwa bara.”

Sajida ta jawo shi ta durkusar a gabanta, sannan ta

kwaye masa riga ta bayansa, sai ga doron bayansa muraran ta dauke takalmin danko ta yi ta lafta -masa, ya na ihu ya na. tambayar abin da ya yi mata. Kamar yadda: lokacin da Malam ya dinga nadarta ba ji ba gani, har sai da ya gaji haka ita ma ta lode shi har Sai da ta gaji da kanta, ta sake shi. Bayan da ta tabbatar bayansa ya dau shaida kamar yadda na ta ya dauka, wannan tabon in ba sa’a ta ci ba har mutuwarta ba zai bace ba kuwa.

Umma Furera na can ta na saka gayan koko fadi take,

“Bar shi haka, ai ya daku.”

-Yahuza ya laftu a gasa ya na narkar kuka gami da

gungunin da ba a fahimtar abin da yake cewa ba. Amma idan kunnuwansu ba su yi kuskure ji ba sun jiyo musu yana cewa,

“Haka kawai dan cin zali ki yi ta dukana babu abin da na yi miki.”

Umma Furera ta fada cikin daga murya ta ce, “Ka san

abin da ka yi mana. Idan ba ka san abin da ka yi ba yaya za a yi daga fara dukan Sajida za kä arce waje baka sake shigowa ba sai yau.

Sajida ta zo ta murde masa kunne ta ce, “To bari in

karanto maka abin da muke nufi. An yi walkiya mun ganka munafuki asha kai ne ka ke zagayewa ka ke fadawa Baba maganar Abdul majid. Ka dade ka na hada min tuggu, kasa na bata da mutane da yawa, wadanda kake cewa sune suke fadawa Baba in an ganni da Abdul majid. Musamman na rannan da na fita karbo littafi a gidan su Asiya na hadu da Abdulmajid ina dawowa gida Baba ya shigo ya yi min duka har ka ke ce min wani mutum ne ya zo a motà qofar gida shine ya fadawa Baba har da cewa za ka nuna min mutumin.Ashe babu wani mutum kai ne munafukina. Idan rannan ka ce wani mutum ne ya ganni a waje ya zo ya fada, a cikin gidan nan da nakè hawa katanga ina karbar aron waya ina kiran Abdulmajid waye ya shigo ya ganni, shi ma munafukin mai motar ne ya zo ya fada?”

Umma Furera katseta, “Ke kike biye masa ma, kike

maganar wani mai mota, wanne mai mota ne ya zo ya fada? Wanne babban mutum ne mai mota wanda ba shi da ailkin yi har zai zo ya ce ya ganki da Abdulmajid? Yaushe wani mai mota ya sanki har ya san gidanku, har ya san a gidanku an raba ki da Abdulmajid kin ki

‘Yan unguwar nan ne kawai suka sanki, suka san Malam ya raba ki da Abdulmajid su ne suka sha kawo gulma, kuma babu wani mai mota a cikinsu. In har da gaske ne ka fadi sunan mai motar mana, ai kai ne don gari babu wanda baka san shi a cikin unguwar Kawon nan ba, har unguwar Giginyu shiga ka ke ka nemo labari.”

Sajida ta ce, “Ga gaskiya ma ta fito abu a cikin gida

akan katanga har Malam ya sani na san da Iyayye ba za ta fada ba ta ce ita take ba ni aron waya in yi, idan ta fada ma ta tonawa kanta asiri, don sai Malam ya shiga har gida ya zane ta. Babanta ma idan ya ji sai ya kwace wayar. Waye zai fada in ba kai ba”

Yahuza ya zabura ya miqe tsaye cikin kuka yana cewa,

“Wallahi ban taba fadawa Baba ki na aron waya ta katanga ki na yi wa Abdulmajid waya ba. Saboda na san irin dukan da yake yi miki. Ni kuma tunda ku ka ce ni na fada masa, Baban ya zo nan gani, ga shi, ga ku a tambaye shi idan na fada masa wata magana.

Yaushe ma muke zama da Baba mu yi hira shi da yake da baqi ko da yaushe kora ta yake ko na zauna a cikinsu.”

Hmmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE