KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 2 BY JAMILA UMAR TANKO
leda, sai ga mace cikin matsatstsun kaya ta bayyana. Babu jimawa ta fito sanye da riga da wando da wata ‘yar jaka da takalmi mai tsini, wani dan yalolon gyale ne ta yafa akanta ana hango gashin kanta gara ma ace babu gyalen.
Ya ji gabansa ya yanke ya fadi daga nan ya bar jin
sanyin zagin da tayi masa tunda ya tabbatar ba mutuniyar kirki ba ce, za ta yi abin da ya-fi haka ma. Ya yi sauri ya d’aga gilasan motar dan kada ta gane shi. Tagumi ya yi kawai yana kallonta nan da nan ya fita daga cikin hayyacinsa ganin halin da yarinyar nan ta shiga, yayi matukar tayar masa da hankali.
Yarinyar ta dubi motar Bakura duba sosai don ta gani
ko akwai mutum a ciki yana kallonta ko kuwa parking kawai akayi ba kowa. Amma ta kasa gane inuwar mutum kasancewar ba farin gilashi ba ne ya na da dan duhu, na ciki na ganin na waje, na waje baya ganin na ciki. Sai hankalinta ya kwanta ta wuce ta na rangwada ta nufi wajen wata farar mota kirar AUDI A4 dake can gefe guda a ajiye.
Babu alama mutum a ciki kasancewar gilashin motar bakikirin ne.Ta tsaya a jikin motar a daidai wundon direba ta na kwankwasawa, fiye da mintuna biyar ba’a bude ba, sai daga baya aka bude kofar motar. Sai ga wani dogon saurayi .wankan tarwada mai dogon hanci gami da dara-daran idanuwa, ya bayyana, ya fito ya tsaya a gabanta.
Hakika saurayin ya hadu yana da kyau wanda duk wata mace za ta so shi a matsayin saurayinta, sai dai kyawun d’an miciji ne idan ka zauna da shi za ka san bashi da tarbiyya gara ma ka zauna da kumurcin miciji akan ka zauna da mai irin halayensa. Sanye yake da bakin wardo jeans da farar riga
matsatstsiya ‘yar karama mai dan garamin hannu, fuskarsa cike
da wani kwabcecen gilas baqi qirin.
.Takalmin gafarsa kuwa wani dangaretan kambas ne
tattaura mai laumin fari da bagi irin na samarin zamani, wanda
idan aka jefe ka da shi ko aka taka ka da shi ka tabbatar gadon
asibiti zai yi bakuncinka. Yatsun hannayensa dukka goma zobbuna ne rangada rangada. Askin kansa kuwa kai kace shataletalan titi irin (round about) da rassan titina guda hudu gabas da yamma kudu
da arewa, wanda duk ta inda aka bullo za’a hadu a tsakiya. Bakura ya na zaune a cikin motarsa ta mudubin saman gilashin gaba yana hango bayansa yana dubansu cike da takaici ya rasa dalilian da ya sa zuciyar ta ke bugawa dan fargaba da b’acin rai.
KAI KA FI CANCANTA
Gabansa sai faduwa yake yi tamkar, ‘yarsa ce ta fad’a
hannun tantirin niga irin wannan. Sai dai kash sun yi masa nisa ba zai iya jiyo abinda suke cewa ba. Ya yi zuruf ya fito daga cikin
motar ya rufe, sai ya yi tamkar sabgar gabansa yake vi kamar bai
san abinda suke yi ba, ya na tafiya ya na wayencewa kamar bai sanda su ba amma wajensu ya tunkara. Bai yi wahalar qarasawa inda
suke ba ya fara jiyo abinda suke fada tar a kunnuwansa. Sai kuwa ya ci sa’a akwai wani karamin masallaci da famfo a wajen. Ya
garasa wajen famfon ya bude ya dinga kurbar ruwa yana wanke fuskarsa, ya kasa kunnuwansa sai ya ji yana jiyo komai ba tare da sun gane su yake saurara ba. Sunan daya ta ambata shi ne Abdul
majid shi kuma ya ambaci sunanta Sajida.
Abdulmajid ya ce da Sajida ‘ni ba bawanki ba ne, kuma
ba direbanki ba ne da zan yi miki waya fiye da awa daya sai yanzu ki ka fito. Daga an yi magana sai ki ce Baba da Umma ne suka hana ni fitewa. Ai babbar matsalar iyaye ‘yan gargajiya kenan komai sai ace addini kuma addinin na su duk kame-kame ne, sun hana yaransu shakatawa a banza. Wallahi ba dan Allah Ya jarrabe” ni da sonki ba da tuni na rabu da ke, tun sanda tsohonki ya hana ni zuwa kofar gidanku, har yanzu ina jin zafi da quna irin wulakancin da tsohon nan ya shuka min a gaban mutane har yanzu bai bar zuciyata ba. Ke ana son–a-wayar dake a kwatar miki
‘yancinki amma kin k’i yarda, kin zauna ki na bin dokar ‘yan gidanku gidadawa. Wai ku ustazai, malamai kuma almajirai.”
Babu abinda Sajida take yi sai karkarwar jiki, babu
furucin da yake fita daga bakinta sai ” Abdul majid kayi hakuri, dan Allah dan Annabi ka yi hakuri.”
Abdul majid ya yi mata wani kallo na wulakanci ya zare
bakin glashin dake fuskarsa ya tabe baki.
Ya ce “ki na nufin da wadannan kayan na jikinki za ki bi ni party? Ki na nufin da dogon wando da gale zan shiga dake wajen hadadden party da hadaddun abokaina? Ke bakauyiya ce har yanzu kin kasa wayewa.” Sajida ta dubi jikinta sama da kasa ta rasa illar dake tattare da ita. Wandon jeans ne hadadde kuma matsatstse shine ma ya siyo mata daga America, haka itama rigar a matse take.
Tunanin da take yi ya katse ya ce “dole in kai ki.wani
kanti in siya miki kaya, mini skirt za’a saka iya cinya da zurmukeken takalmi mai tsini irin mai zif din nan har gwaiwa da riga shimi iya kirji wacce ba ta rufe cibiya ba, kuma babu ke ba zancen dankwali, kin ci sa’a ma ki na da gashi ba sai an gara miki ba.”
Sajida ta zabura ta dubi Abdul Majid cike da fargaba
ta ce “riga iya kirji?” Ya daka mata tsawa ya ce “to meye, ki na nufin ba za ki iya sawa bane?”
” musu. Tsoransa take, sonsa ta ke don haka ba ta iya yi masa musu ba Ta ce “zan saka mana.” Ta dubi agogon dake daure a hannunta daga dukkan alamu ta gagu ta koma gida don kada a
• nemeta. Wanna karon-ma tsawa ya daka mata mai firgitar da wanda ke kusa da su, ba ma wacce aka yiwa ba. Nan da nan jikinta ya hau karkarwa.
Ya ce “duba agogon me kike yi, ko yau ma an baki lokacin da za ki koma gida ne?”
Sajida ta na karkarwa
ta ce “a’a ba duba agogo nake yi ba, yi hakuri.”
Ya ce “to zagaya ki shiga mota mu tafi.”
Sand’a ta ke kamar wacce kwai ya fashe ma ta a ciki,
saboda ba ta son shiga motar amma tsoransa take ta kasa ce masa ba za ta je ba.
Bakura ya dago da sauri zuciyarsa tamkar ta fashe, tashin hankali ya rufto masa lallai kuwa zai shiga wani mummunan hali idan har ya bari yaron nan ya fita da yarinyar nan ya je ya ba’ta mata rayuwa ba tare da samin iyayenta ba.
Tabbas – abin zai dad’e bai fita daga cikin zuciyarsa ba zai ga kamar ya ci amanar musulumci da iyayenta da ita kanta.
“Tabbas yaron nan ya na niyyar ruguza tarbiyyar da
iyayenta yaringar nan su ka dade su na gina mata.” Ya fada a ransa.
Sai ya ji wani hawaye mai zafi ya surnanu masa, yaransa ne kawai suka fad’o masa a rai, gaba d’aya ya ji ya shiga zargi anya kuwa shima ba ci gaban mai haqar rijiya ya ke yi ba kuwa, kullum haga ya ke amma ya na qara yin qasa. Anya kuwa ba tufka ya ke yi wani ya na warware masa a waje ba kuwa? Ya tuna
hadisin da Manzon Annabi (S.A.W) ya koyar damu ce wa “idan ka ga ana aikata barna to ka hana da hannunka, idan ba za ka iya ba to ka gyara da bakinka, idan ba halin haka to ka abin a zuciyarka wannan shine mafi raunin imani.”
- Nan da nan ya ji a ransa zai iya zuwa ya hana da baki tunda bashi da ikon gyarawa da hannu. Ya zabura zai je wajensu kenan don ya ba ta shawara da baki ya ce kada ta bi shi. Sai ya ji
- Abdul Majid ya ce da ita “da fatan kin fad’a a gida cewar kwanaki biyu za ki yi ko?”
Gabanta ya fadi ‘rass’ ta dafe kirji ta tambaya cikin firgici “kwana biyu?”
Ya yi mata tsawa ya ce “toh meye abin fargabar, ban isa da ke ba ne? A Abuja Nicon Hotel za’a yi casun kuma sai garfe d’aya na dare za’a fara dan haka daga nan ma Abuja za mu wuce.
Sajida ta zagayo da sauri in da yake ta tsugunna a
- gabansa ta fashe da kuka ta ce “Abdul majid ka taimake ni, ka rufa min asiri kada ka yi fushi da ni. Da ka san ta yadda aka yi na fito yanzu ma da sai ka tausaya min. Sai da na yi dubara da magya Babana ya bari na fito da zummar zan je gidan su Asiya kawata in karbi qur’ani. Mintina talatin ya ba ni kasancewar gidan babu nisa ya na gida ya na jirana. My dear, idan na bi ka Abuja har kwana biyu kashe nine kawai ba za’ ayi a gidanmu ba, ka rufa min asiri.
Ina sonka Abdul Majid fiye da yadda na ke son rayuwata.” - Abdul Majid ya dakatar da ita da hannnun ya katse ta.
Ya ce “ba na bukatar bada hakurinki, ai na fad’a miki a baya hakurin da na yi ya isa nan gaba ba zan sake ba. Kin manta alkawarin da kika daukar min har na yarda na sake dawowa muka shirya? Ban taba gayyatarki fita kin yarda kin bi ni ba, sai kin kawo min ba’adi da qa’bali, rawawul Baba rawawul Umma. Kar ki
Hmmmm