KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 3 BY JAMILA UMAR TANKO

manta nace miki na gaji na daina zuwa wajenki, ki ka lallaba ni na dawo a bisa sharadin kin yarda ko a ina ake party za ki bi ni shine yanzu kike duban kwayar idanuwana kike fada min Babanki ya na jiranki a gida? Ma’ana dai ba za ki bi ni ba ko? To shikenan daga yau ba za ki sake gamina ba, kada ki kira ni a waya. Baby kina da kyau, ke kalar shiga taro ce amma ki na kwabsawa da yawa iyayenki sun tauye rayuwarki dan haka sai anjima.”

Ya juya ya shiga zai shiga motarsa ta na tsugunne tana magiya. Idanunta kamar za su fita dan kuka, hawaye su na zuba ratatata. Ta yunkura ta rike kofar motarsa tana bashi hakuri. A fusace ya daga gafa ya cije baki zai mangare ta da tafkeken takalmin gafarsa. Sai tayi tsalle gefe bai same ta ba, ya shiga motarsa ya fisga da garfi gami da qure sautin kid’a kamar zai tashi kunnuwan wanda ke wajen.

Bakura ya durkusa’ a gaban fanfo ya na ajiyar zuciyar dad’i, domin sanda Sajida ta yi kamar za ta shiga motar sai da numfashinsa ya fara cikewa baya dirawa huhunsa saboda tashin hankali. Da Allah Ya sa ba ta bi shi ba ya ji dadi, kuma ya godewa Allah. Ya kunna famfo ya na wanke fuskarsa ya na satar kallon

Sajida wacce ta zo ta wuce ta bayansa ta na sharar hawaye.

_Ta yi wuf ta fada lungun nan ta zurmuga hijabinta ta

fito tsaf a kamalarta, tana tafe tana kwararar da hawaye. A rude take tamkar wacce aka yi mata aiken cewa uwarta ta mutu ko kuma tamkar wacce aka sace d’anta ta yi duban duniya ta rasa shi.

Ta dauko wayarta ta na ta gwada kiran Abdul majid sai ta fara ringing sai ya Katse daga garshe ma ya kashe wayar gaba daya.

Kukan da Sajida ke sharba sai ya qaru, tashin hankalinta ya garu sai taji ta tsaní kowa a duniya babu kuma kyautar da za’ayi mata ta ji dadi idan ba Abdulmajid dinta aka kawo ma taba. Bakura ya tura hula geya ya nad’e hannayen rigarsa kamar wani dan garuwa ya biyota a baya da sauri, ya na isa gare ta sai ya rafka ma ta sallama. Ta ki daga ido ta dube shi sai da gefen ido ta dan waiwaya sannan ta dauke kai ta ci gaba da tafiyarta ta na sharbar kuka.

Bakura ya sake biyo ta ya na yi mata sallama, Sajida taki sauraransa balle ta amsa.Ya ce ” ‘yan mata kukan me kike yi ne?”

Wannan karon a fusace ta dago da jajayen idanuwanta a cike- da hawaye. Cikin tsawa tace “dalla malam ka rabu da ni, ni ba sa’arka ba ce, kowacce kwarya da abokin burminta, haka kuma kwarya ta bi kwarya idan ta bi akushi ba za ta moru ba. Ka je ka samu sa’arka, ballagaza marar aji irinka.”

Sai a yanzu Bakura ya kalli fuskarta tangararai, ya ji

gabansa ya yanke ya fadi ras, kan kace kwabo ya gigice ya fita hayyacinsa, mamaki, d’imuwa, rikirkicewa da d’aurewar kai suka rufto masa. Kallo daya za ka yi masa ka gane haka, babu kalmar da Bakura ya ke fada sai “Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’ una. Tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai. Allah mai iko, Allah mai halittar bayinsa. Yarinya wacece ke? Su waye iyayenki?”Sajida ta yi masa kama da Zuhuriyyarsa. Ikon Allah ta yaya hakan ta faru? Saboda dimuwa sai ya durqushe ya dafe kai yana jujjuyawa. Sajida ta ga alamar tabin hankali a tattara da wannan mutumin sai ta ci gaba da tafiyarta.

Ya miqe a guje,ya sake biyo ta ya na yi mata dan kira.

Ta tsaya cak ta kalle shi ido cikin ido cikin tsiwa da

fitsara ta ce ‘ kai dabba in baka da tunani zan tuna maka, na fada maka niba ajinka ba ce ka rabu da ni.”

Ta juya za ta tafi, a fusace ya fisgi hijabin ya juyo da ita ta fuskanci shi ya na magana cikin fusata. Yace “Na haifi kamar ki ‘yata tana a gida amma kike kallon

idanuwana kike zagina dan baki da kunya. Ga dan iska can mayaudari ya tafi yanzu, ya na zaginki ki na lallaba shi.Sai ni kika raina saboda ni kamili ne na yi shiga ta kamala da manyan kaya.

Ni ne abin wulakanci a wajenki ko? To ni shawara zan baki kiyi hankali da samarin zamani, ki daina-ha’intar iyayenki su na yi miki tarbiyya ki-na-biyewa wani kato ya na rusa musa.”

Tsananin tsanar Bakura ta cusu a zuciyar Sajida sai

hawayen takaici ya kece mata.

Ya ci gaba da cewa “har ki na ce min kwarya ta bi

kwarya idan ta bi akushi ba za ta moru ba, ke ba ajina ba ce don- haka kowacce kwarya da abokiyar burminta. Shin kim san kwayar da ki ke kira kuwa? Kwarya ai kala-kala ce kwaryar dake tunb’ele

a tsakar gida ana rigar tsakuwar shinkafa ko gero da ita, ana bakace, ana zuba tuwon dumame, wacce ake d’orawa gardawan maza a kai su kai gero ko masara surfe da niga kasuwa. Ko kuwa kwarya ta gari wacce aka rataye a ragaya, aka sakale a daki, mata su na kwalliya da ita, ba’a bari a sauko da ita kasa balle a damgeta ta yi datti? Duk wata kwarya ta gari ta na ragaya asirinta a rufe.kwarya marar kyau ce a tsakar gida in anso a kifa, in an so a bude,

idan anga dama a fasa ko kuma a kada ayi kida da ita kowa ya jiyo sautinta ayi rawa. Dan haka ke kwaryar tsakar gida ce waçce take tangaririya a gari. Ke kwaryar kida ce wacce kike barin wani d’a

namiji ba mijinki ba ya jiyo muryarki. Duk wata ‘ya mace ta gari tana qunshe a gidansu ba ta bin maza su, nayi mata wulakanci domin mace daraja ce da ita har tafi lu’ulu’u idan ta kama kanta,

to ita ce nake kwatanta ta da Kwarya ta gari tana ragaya. Ado akeyi da ita ba a wanke-wanké a cikinta.”ba A fusace Sajida ta dube shi duba na tsana don ba ta taba tsanar wani bil-adamama a duniya yadda ta tsani Bakura ba. Hawaye ya sake kwararowa daga idanuwanta. Ta ce yarka da ka ce ka haifa kamar ni ita ce wulakantacciyar kwaryar nan da ka suffanta.”

Bakura ya tsinci kansa yana murmushi maimakon yayi fushi kasancewarsa mutum ne mai yawan fushi, baya son raini daga mutumin daya bawa kwana d’aya ma ba shekara daya ba balle kuma ‘yar cikinsa daya haifa.

Ya ce “idan zan dauki kwaryata in matunta, in adana ta a ragaya, in sagale tak’i zama, in sake sagalewa a sama ta k’i zama to lallai ta zama kwaryar tsakar gida mai garari. ‘Ya ta da kike magana kuwa a tunanina kwarya ta gari ce wacce na sakale ta a ragaya bata fita tsakar gida tayi garari, kamar yadda a tunamin iyayenki sun dauki Kwaryarsu mai kyau sun; sagale a ragaya basu san tana ballewa ba ta fita tayi gararinta ta dawo ta d’ane ragaya tayi luf. Don haka had’uwata dake naga abinda yake faruwa yasa ni dole in koma gida in zauna inyi gadin wannan kwaryar dana sakale don karta sauko ta fice ta yi ta garari a gari.”

Sajida ta qurawa Bakura ido ta na dubansa dubu irin na tsana da takaici sai wani d’aci take ji a ranta na bacin rai, ji take tamkar ta d’aga hannu ta dora masa mari sai dai tana shakkar aikata haka kasancewar taga shima a tsaye yake ya fita fitsara.

Tunda ta ke a rayuwarta bata taba haduwa da mutumin daya cusguna mata irin Bakura.ba

Ta fada cikin kuka da takaici.”Na tsane ka.”

Ta juya ta ci gaba da tafiya. Bakura bai bitaba sai ya dawo jikin motarsa ya jingina yana kallon Sajida. Zuciyarsa cike da tsananin mamaki da son yaga shin su waye mahaifan Sajida, ya aka yi ta yi kama da Zuhuriyyarsa? Maganarsu, kallonsu, harararsu, kukansu, kirar jikinsu,. hannayensasu, kafafuwansu.

Babu yadda za’ayi mutum da mutum ba dangantaka ayi irin wannan kamar sak, dole sai anga ta inda suka bambanta. Ganin Salida da yayi sai ta tuno masa da Zuhuriyyarsa. Ya fashe da kuka

•shi kadai kuma ya lallashi kansa ya goge hawayen ya yi zunbur ya shiga motarsa don kada Sajida ta b’ace masa domin ta fara yin nisan da ya daina hango ta sosai. Sai yake ta bin ta a baya, Idan yayi tafiya kad’an sai ya tsaya har sai da yaga gidan da ta shiga, ba tare da Sajida ta san ya na biye da ita ba.

Ya garasa gofar gidan ya kashe mota ya fito ya karewa

gidan da unguwar kallo ya tabbatar Sajida ‘yar talakawa ce liqis kuma daga dukkan alamu ‘yar malamai ce domin daga ka doso zauren gidan allunan almajirai ne cike a zauren kuma kowacce kusurwar bangon zauren kundun kur’ ani ne a sassakale. Ga almajirai nan reras su na shige da fice a cikin gidan.

Shi dai burinsa yadda zai yi ya ga mahaifan Sajida ba makawa su na da alaga da Zuhuriyyarsa. To amma ya san Zuhuriyya, ya san duk wani d’an uwanta, kakaf dangin Zuhuriyya babu ko daya a Kano gaba daya suna qauyensu Cinkilawa. Amma yaya aka yi Sajida ta yi kama da Zuhuriyya? Tambayar da ya ke yi a ransa kenan. Ya jingina a jikin motarsa kamar wani gunki zancen zuciyarsa har ya fara fitowa fili.

Maganar wani yaro ce ta katse shi ya ce “d’anwake za’a kawo maka ko kunun kanwa?”

Bakura ya yi firgigit. ya dubi yaron ya maimaita

abunda yaron fada “dan wake, kunun kanwa?”

Bakura ya yi minti biyu ya na tunanin menene ma dan wake, yaya ma kunun kanwa yake?

Yaron ya sake cewa “yanzu aka sauke kunun da

zafinsa.”

Hmmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE