KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 5 BY JAMILA UMAR TANKO

aiwatar da ta ta sallar, bayan ta idar ta yi shafa’i da wutiri da laziminta sannan ta miqe ta karasa wajen kayan kwalliya ta sake caba ado. Aka sake saka hoda, jagira, jan baki, ta sake yin daurin dankwali ta feshe jiki da turararruka designers sannan ta fito.

Ta na fitowa ta nufi dakin Zahra, ta iske Zahra ma ta

idar da sallah. Cikin ladabi Zahra ta dubi mahaifiyarta tayi murmushi;

Ta ce “Mama sannu da gida. Kinyi kyau.”

Samira tayi murmushi ta ce “Zahra sannu- da karatu, ki fito mu ci abinci, Abbanki ya dawo ki yi masa sannu da zuwa don ya tambayeki kafin ya tafi masallaci.”

– Zahra ta amsa da “to Mama.”

Su ka d’unguma suka fito, Zahra sane doguwar riga

baga (abaya) kanta a lullude da garamin hijab baki mai hula iyaka kirji. A babban falon gidan suka ci karo da Bakura tare da yaransa Abubakar, Umar da Usman sun dawo daga masallaci.

Samira ta ce “yauwa sai mu wuce kan dining table muci abinci ko Abban Zahra? Yau da kaina na shiga kicin na dafa maka burabusko irin na ku na barebari.”

Ta ga ya yi turus bai juya ya kalli dining table din ba

ma balle ya bude ya ga abinda aka dafa masa balle ya burge shi.

Zahra ta ce “Abba sannu da zuwa, shugabar

makarantarmu ta ce in gaisheka.

Sai su ka ga ya tsuke fuska ya kada kai zai nufi dakinsa, har ya kai kofar fita sai ya juyo ya dubi Zahra.

‘Ya ce ” Zahra ki kula da rayuwa, ki tabbatar kin saka tsoran Allah a cikin zuciyarki a duk inda kike. Ba ruwanki da lalatattun qawaye da samari bata gari. Na sakale Kwaryata ta gari a ragaya ba na fatan kwaryar nan ta tsinke ta fado daga ragaya ta dinga garari a tsakar gida.” Yajuya ya tafi abinsa ya tafi.

Cafdijam!!! Wannan Hausa ta yiwa Uwar Zahra tsauri

balle ita Zahrar kanta. Daman idan aka dunkule Hausa, ko karin magana ZAhra bata ganewa, ta fi gane yaren kanuri sai kuma

turanci. Tabbas tana jin Hausa amma ta ina za ta fahimci wannan maganar Samira bahaushiya ce gaba da baya-amma yaya aka yi wannan Babarbaren ya yi mata Hausa cikin Hausa ba ta fahimce shi ba? Dadin dadawa ba su san kan maganar da ya ke yi ba balle su gano bakin maganar.

Hanakalin Zahra ya tashi, ta kalli mahaifiyarta ta dafe

kirji. Ta ce “Mama me na yiwa Abba, wacce kwarya ya ke magana?” Samira ta fita da sauri ta bi shi dakinsa, ta iske zai shiga wanka, ta dube shi.

Ta ce “Sweety Zahra ta damu ta na tambavar ko wanni laifi ta yi maka.” Ya girgiza kai ya ce “ba laifin komai ta yi min ba dama ba lallai ne ku gane abinda na ke nufi ba yanzu sai a nan gaba.”

Ya juya zai shiga bandaki Samira ta kara dakatar da shi. Ta ce “sai kayi wanka za ka fito mu ci abinci ko na kawo maka naka kan daning table din nan dakinka?”

Ya girgiza kai yace “ba zan ci ba na koshi.”

Hankalin Samira ya tashi ta fara magana kamar mai

shirin fashewa da kukan kissa da nuna damuwa.

Ta ce “haba Yayana, maigidana, abin kaunata. Ya zan

dage inyi maka abincin daka fi so a rayuwarka wato burabuskon gero, kuma ka ce ba za ka ci ba. Mu yaya za’ ayi mu iya ci…?”

Kafin ta rufe bakinta ya dakatar da ita ya ce “ki je ke da yaranki ku ci, ni na goshi. zan yi wanka in kwanta idan kin shigo kada ki kunna min fitila, kada ki tashe ni ba zanyi hira ba yau. Kada ki kikuskure abinda na fada miki wannan doka ce.”

“Samira ta juya sadan-sadan ta fice daga dakin ba tare da tà sake cewa komai ba kuma bata san me hakan yake nufi ba.

Sai ta ji ya yi magana ya ce “ka da ku damu ke da

yaranki babu wanda ya yi min wani laifi a cikinku.”

Ta juyo da murna ta dube shi-ta ce “kawai yanayi ne ya canja?”

Ya ce “yanayi ne kawai, yau na ga mai- kama da

Zuhuriyya sak kamar an tsaga kara shine hankalina ya tashi.” Mai kama da Zuhuriyya fa ka ce? A ina? Bakura kasan abinda kake fada kuwa?” Samira ta tambaya cike da mamaki. Ya daga mata hannu ya dakatar da ita. Ya ce “tambayoyin sun’ isa haka. Sai da safe.”

Samira ta fito zuciyarta cike da mamaki da kokonton

anya Kuwa Bakura ba shi da wata aljana a jikinsa? Ko dai aljanun ne su ka tashi yau?”

Samira mace ce dirarriya mai tsawo da ‘yar giba. Fara

ce sosai, sai dai ba ta da dogon hanci, bakinta madaidaici ta na da dara-daran idanuwa farare qal masu kyau. Ba ta da gashi mai tsawo amma kuma ba gwaguyyaye ba ne. Mace ce mai tsafta gami da taushin murya, mai tsananin haquri domin idan ba ita ba ba mai iya zama da Bakura. Ta iya lallashi ta iya, tausar ran mijinta, ta na da tausayi da kyautatawa masu aikinta. Ta na da son wasa da

•dariya da yaranta har da ma sauran jama’a. Ta na da ilimin-addini daidai gwargwado da na boko duk da iyakacinta daga sakandire ta tsaya ba ta ci gaba ba haka kuma bayan ta auri Bakura bai bar ta ta ci gaba ba.

Samira ta fito ne daga babban gida ma’ana gidan arziki

da mutunci. Mahaifin Samira mutumin Kano a unguwar yakasai yake. Ta na da kanne da yayye ba adadi kasancewar mahaifinta mata hudu gare shi. Dukkansu su na nan da ransu reras. ‘Amaryar gidan ma har yanzu ta na haihuwa.

Ta auri Bakura saboda tana sonsa Zahra ce babbar

‘Yarsu ta fari kasancewar sunan mahaifiyarsa ne yake kiranta da

• Yagana. Zahra tayi matukar yin kama da Babanta ko ba’a fada maka ba dan ka kalli Bakura ka kalli Zahra ka san irin su daya.Banbancin shi namiji ita kuma mace. Da wuya ka kira shi Babanta sai dai ka dauka Yayanta ne kasancewar auren wuri yayi da haihuwar quruciya. Zahra tafi mahaifinta haske kasancewar ta dauko hasken fatar mahaifiyarta amma ba dukka ta dauko farin ba ta hada da bagar fatar mahaifinta sai ta bada kala mai kyau wato hasken duhu (chocolate colour).

Wannan kalar ta Zahra ta sake fitar mata da kyawunta,

dogon hancinta siriri har baka irin na barebarin asali, bakinta dan garami har ya fi na mahaifinta kyau, haka fararen hagoransu da wushiryar sama da qasa duk iri daya. Ga wani lallausan gashi har qasan geyarta bakikiirin mai tsawo. Jikinta abin sha’ awa, doguwa ce siririya. Kirar kamar Bakura ba su da kiba.

Mazan kuwa Abubakar, Umar da Usman ga farin har

gajeran hancin sak irin na mahaifiyarsu sak, gaba dayan su sun yi kama da mahaifiyarsu, amma sun dauko tsayin mahaifinsu dogaye ne sosai. Allahu Akbar!! Allah mai halittar bayinSa duk yadda Ya SO:

Kwana biyu Bakura ya kasance cikin yawan tunani da

damuwa ga uwa uba rikirkicewar tunani. Ya na cikin damuwa; gigita da tsantsar son binciko wai shin menene alagar Sa’ida da Zuhuriyyarsa, idan akwai.

Bakura ya taso daga wajen aiki, sai ya ji a ransa ba zai

Kara iya daurawa ba bari kawai ya zarce gidan su Sajida ko Allah zai sa ya samu abinda ya ke nema, ma’ana labarin asalin su Sajida.

Bakura ya na tsayawa da motarsa a bakin gofar gidan su Sajida sai ya bude kofar ya. fito yayin da gardawan da ke zazzaune a kofar gidan su ka zuba masa idanuwa su na kallonsa su na gasgata ni’imar da Rabbul samawati ya yi masa. Ya yi shigar fararen kaya, farin takalmi da farar hula, motarsa kuma kirar BMW 7 SERIES mai launin ruwan zuma. Ya fito ya tsaya-yayin daya zare farin gilashin dake fuskarsa ya dubi jama’ar da ke zazzaune a gofar

• gidan daga dukkan alamu makarantar allo ce karatu su ke dauka.

Malam Yakubu shine mai makarantar wato mahaifin

Sajida. Ya na zaune akan kujerar katako rike da zabgigiyar dorina, yara su na gabansa suna daukar karatu, da zarar sun kuskure sai ka ji ya faula musu bulalar. Malam kenan!

Bakura ya garasa gaban Malam Yakubu ya yi sallama

sannan ya durqusa ya gaishe shi. Cikin fara’a Malam ya amsa gami da ce wa “yaro ban gane ka ba.”

Bakura yayi murmushi ya ce “watakila saboda ba

waccan motar ba ce shiyasa ba ka gane ni ba. Ni ne wanda na zo kwanakin baya da yamma game da maganar Sajida da Abdul Abdulmajid.” Sai Malam ya fahimta ya fada cikin sakin fuska “to, to, to na gane ka yaro, to mu je wajen motarka mu tsaya.”

Su ka garasa jikin motar su ka tsaya. Bakura ya sosa

gefen kunne yayi dan murmushi ya ce “Malam yaya yara, yaya jama’ a?

Malam ya ce “Alhamdulillahi, mun godewa Allah. Yaro ka taimaka mana fa matuga domin ni a iya sanina Sajida ba ta da waya. Ashe waya ya hada mata take labewa su na yin magana ba tare da mun sani ba. Har takai ta kawo Sajida za ta yi min dubara ta fita ta je su hadu a wani waje ban sani ba. Saboda yaron nan fa

Hmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE