KAI KAFI CHAN CHANTA CHAPTER 7 BY JAMILA UMAR TANKO

unguwar su na zuwa daukar karatu. Ni da limamin masallacin muke koyar da su, Yanzu ma haka su na can su na yi, na fito ne neman ilmi ko akwai abinda zan samu in koya, ka san ance ilimi kogi ne ya na da yawa.”

Malam ya ce “haka ne, ai gobe sai mu yi hadisi, fikihu

da tauhidi.”

Bakura ya ce to madalla Allah ya -kaimu goben

Malam.”• Bakura ya mike tsaye ya na shirin tafiya sai ya ji Malam

ya ce “Bakura ka jira ni in shiga gida in fito.”

Bakura ya amsa da “to malam.”

Ya bi malam da kallo har ya shige cikin gida Bakura ya

shiga zulumi, ya na tunani ya na tambayar kansa da kansa meyasa malam ya ce ya jira, kuma ya shiga gida? Wa zai kira, ko me zai dauko masa daga cikin gida? Allah Ya sa mahaifiyar Sajida zai kira su gaisa ko Allah zai sa ya gane ko Wacece. Ya ci gaba da sake-sake a ransa tabbas Saida da mahaifiyarta za ta yi kama tunda ba ta yi kama da mahaifinta ba ko kadan, amma qaninta Yahuza kallo daya za ka yi masa ka yiwa mahaifinsa ka ga kama.

Bakura ya na tsaye qikam kamar itacen bishiyar da bata da reshe balle ganye, idonsa kyam akan gofar shiga *zauren gidan, ya na jiran fitowar malam Yakubu.

Ba tare da Malam ya dade da shiga ba sai ga shi ya fito dauke da wata baqar leda a hannunsa ya qaraso inda Bakura ya ke tsaye.

Ya mika masa gami da cewa “Bakura ga wannan,

shadda ce tsadaddiya wani daga cikin jama’ata dan siyasa ne mu ke yi masa addu’oi shine ya kawo min su kala-kala da yadiddika har kala bakwai shine nace bari in dauko maka daya kaima ka dinka irin taku ce ta manyan ‘yan gayu. Ni kuwa ina fama da tuwo ;

da miyar kuka ina faman cakuduwa a cikin almajirai ina ni ina saka farin kaya.”

Bakura yayi mamaki matuka, ya bude baki ya na kallonsa sai ya hau jujjuya shaddar, tabbas babbar shadda ce ta gaske irin shaddojin da ya ke dinkawa ne. Sai ya dubi malam ya yi dariya ya ce “Malam ayi haka kuwa? Me zai hana kaima ka dinka ka caba adonka ga daurin aure, fatiyar suna, kwalliyar idi-ko juma’a sai ka saka kayanka. Shima wanda ya baka idan yana gani a jikinka zai ji dadi gobe ya karo maka wadanda su ka fi haka tsada da kyau.”

Malam ya yi dariya ya ce “kai haba, meyayi Saura da

har zamu zauna muna caba ado ai fatanmu yanzu sauran shekarun ko watanni ko kwanakin da suka rage mana ya zamamo zikiri ne, salla, azumi da; karatun kur’ ani mu cika da imani. Ka sân Allah Ya ce sittunaaù- saba una. Ga shi yanzu ina sittin da biyar. Je ka da ita Bakura ba’a mayar da hannun kyauta baya, kyauta ce nayi maka saboda jin dadin zumuncin daka qulla a tsakaninmu”

Sai Bakura yaji jikinsa ya mutu bakinsa ya kasa cewa

komai, kalmar da ta fito daga bakinsa itace

“Allah ya saka da alkhairi, nagode malam. Sai gobe Idan mai dukka ya kaimu da magaruba zan zo.”

Ya Juya ya shiga motarsa ya tafi, ya na tafe ya na

mamakin malam Yakubu. Lallai Malam Yakubu dattijon arziki ne wanda abun duniya bai dame shi ba. Yadda Malaman zamanin nan da yawa suka lalace saboda kwadayin abun duniya shi kuwa Malam mai bayarwa ne ba mai saka ran zai samu ba.

*******六六六

Washegari asabar da yamma Bakura da Samira matarsane su ke zaune a kan doguwar kujerar babban, falonsu su na kallon wani dadadden bidiyo casset mada can wato wakokin Dan anace wanda ya yiwa Shago.

Yara gaba daya su na makarantar islamaiyya. Domin

idan ka ga Bakura ya zauna ya na kallo to ka tabbatar wakokin shata, dan kwairo, Dan anace, Dan maraya, Haruna uji, Garba Super, Sani Aliya Dan dawo, Barmana coge, Uwaliya mai amada ne. Ma’ ana wakokin ‘yan dambe, ‘yan farauta, ‘yan tauri da dai sauran finafinan al’adummu na° Hausa wanda gargajiya ce tsagwaro babu kwaikwayon turawa a ciki. Da Samira ta san da haka sai ta bazama ta shiga nemowa maigidanta abinda za ta ja hanklinsa, ta Siyo masa su kala-kala. Na, bidiyo, na CD da na radio, ta zuba masa a mota, wasu a dakinsa, wasu a falonsa Don haka duk lokacin da Bakura ya ke gida ya na zama tare da iyalinsa su yi ta kallo cikin nishadi annashuwa. Wakokin su kan tunawa Bakura labarai na can-can shekarun baya sanda ya ke yaro karami.

Bakura ya dubi Samira duba irin na jin dadi Ya ce

“Gimbiya, da ace ni shugaban gasar Nageria ne da na rusa duk wani kyale-kyale da kwaikwayon al’adun turawa, ana ganin shine wayewa alhalin ba wayewa bace ci baya ne. Duk wani dan Nigeria mata, yara da manya dole atamfa za su dinga sakawa, kar kice atamfar za su yi dinkin da suke so ko matsatstsan siket da matsatstsiyar riga, a ‘a wadatacciyar riga da mayafin atamfa ma’ana falle biyu irin na da, da ake yi riga da zani da mayafi a samo dan kwali daban a daura. Maza kuma yara da manya sai sun saka riga da wando da babbar riga da hula, kowa a kasar nan shigar da zai yi kenan. Saina hana saka mini siket, shirt, jeans, short kneekers, 3 quater, suits da dai sauransu.” Samira ta kwashe da dariya ta ce “haba Sweety,babbar riga fa ka ce? Yanzu ko ma su aikin a bankuna da likitoci

“babbar riga zasu dinga sawa, ai sai ta hana su aikin.”

Ya yi dariya ya ce “to na yarda su cire idan Likitôci za suyi operation, ma su aikin Bakin su cire su ajiye a gefe su na gama kirga kudin sai su mayar da ita.

Ta gyara zama ta ce “yanzu tsakani da Allah yaya

za’ayi ka hada Inyamurai da Yarbawa da mayafin atamfa?”

Ya ce “ai har yanzu Matan Inyamurai su•na dinkin

zannuwa biyu sai dai ba sa yafawa Sai su daura daya akan daya

kin ga idan na saka dokar daukar dayan kawai za su yi su yafa a jikinsu.

Su dukka su, ka kwashe da dariya.

Samira ta ce ina laifin ka ce mata suyi shigar abaya

doguwar riga mai dankwali ko hijab. Maza kuma doguwar riga fara da hirami, irin na Saudia ina ganin ai sun dan fi rashin nauyi.”

Bakura ya girgiza kai ya ce “na yarda shigar larabawa

shiga ce mai kyau itace shigar musulunci, amma al’adar Hausa na ke so in farfado da ita saboda al’adar Hausa al’ada ce mai kyau

wacce ke tafiya da Addinin Musulunci.”

Samira ta rige haba ta ce wai, waga ga ka zama

shugaban kasar Nigeria ‘yan Nigeria sun hadu da doka.” Ya ce lallai kuwa zan takura musu da dokoki kuma kowa, sai ya bi. Dole ne ayi da’ a, dole ne ayi aiki,dole ne ayi tsafta, babu zalunci. Na qasa dole ne ya yiwa na samansa biyayya, shugaba dole ya biya na qasa hakkinsa da dai sauran matsaloli

dake buwayarmu ‘yan Nigeria.” Ya sake kishingida kansa akan hannun kujera ya dube ta

ya ce “Gimbiya ina cikin wani hali wanda yake rikirkitacce mai daure kai, mai tsoratarwa matuqa.”

Ta gyara zama ta ce “me ya faru? Wani abu aka ce maka ya na faruwa a cikin gidan nan, a kaina ko a kan yara ko kuma a cikin masu aiki ne?” ;

Bakura ya girgiza kai ya ce “ko daya, babu komai game da cikin gidan nan. A can wata unguwa ne da ake kira Kawo.”Samira ta maimaita “kawo? Na san unguwar Kawo meke faruwa?”

Yayin da ta dafe kirji zuciyarta na bugun uku-uku.

Ya dube ta yayi murmushi. Ya ce “kwantar da

hankalinki ba wata matsala ba ce uwar tsoro.”

Su dukka su ka kwashe da dariya. Tabbas kishiya ce ta

fara fado mata a ranta. Ya sosa qeya ya gyara zama. Ya ce “Na ga wata yarinya

budurwa matashiya wacce shekarunta ba su wuce goma sha shida zuwa sha bakwai ba.”

Tuni hawaye ya cika idanuwan Samira domin ta san

Karshen maganar.Ta fashe da kuka ta dube shi. Ta ce “Abban Zahra, meye hadinka da yarinyar har ka zo ka ke bani labarinta?”

Bakura ya girgiza kai saboda har ya ji ransa ya baci, ya

dubi agogo ya juya ya dubi teburin da ke gefansa sai ya suri mukullin motarsa ya dora. hularsa akai ya mige tsaye. Ya dubeta duba na takaici Ya ce “babbar matsalata da ke kenan, ba ki da matsala wajen ladabi da biyayyar aure, ba ki da matsala wajen tarairayar miji, ba ki da matsala wajen koyawa yara tarbiyya, ba ki da matsala wajen iya girki da tsaftace gida. Babbar matsalarki itace mummunan tunani da tabarbarewar fahimta akan kishiya, 

Hmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE